Showing 54001 words to 57000 words out of 117648 words

Chapter 19 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

ya mik’e a daren ya je ya ci mutuncin Asma’u. Cikin takaici ya sake janta jikinsa sosai ya fara aikin lallashi ita kuma ta samu abinda take so ta shiga jera ajiyar zuciya a hankali tana sake masa mita da yi masa famfo akan y’an uwansa tuni ya hau kai ya zauna ya k’addara tilas ya yi maganin Asma’u da safe. Murya a k’asa ya rad’a mata a kunne ki yi hak’uri dearling da safe zata tattara ta tafi gidan mijinta ai Didin ta samu sauk’i. Babu mai tab’a min ke wallahi na k’yaleshi yau na sake amicewa da har abafa kece mahad’in zuciyata.” Dad’i ya shigeta da farinciki ganin yarda ta juya shi ba boka ba malam sai zallar iya sarrafa shimfid’a ta shiga wasa da gemunsa tana jaddada fad’in “Thanks Kalbeey zaman Asma’u ai masifa ne a gidannan.” Burinta ya cika Asma’u na tafiya zata zuba guba a abincin Didi kuma a na gidan Sadiya zata zuba mai aikinta zata siye da mak’udan kud’i ta bata ta zuba gubar. Ta saki murmushin tarin farin cikin samun nasara a lokacin da ta sare.
Dama sau tari shi yasa bata fiye yarda da malamai da bokaye ba da kanta take sarrafa mijinta son ranta.






_________


Da sasafe suna gama shiryawa da Abbun ta had’a masa lafiyayen breakfast cikin tarairaya ta dinga bashi abincin a baki tana yi tana sake ingiza shi game da Asma’u da Lauratu k’annensa. Shi kuma hakan yana sake tasiri a ransa ya tabbatar shine basa so tunda ba sa son Saknarsa mai ba shi farin ciki a ko da yaushe. “Tashi muje dearling a yi komai a gabanki.” Ta mik’e cike da farinciki ta manna masa sumbata a gefen kumatu ya saki murmushi ya ja hancinta a cikin kunne ya rad’a mata “Shi yasa a ko ina nake alfahari da samun mace kamar ki.” Ta lumshe idanunta suka fita tana sakin shashshek’ar dariya ta tabbata yau lamarinsa da Asma’u ba mai kyau bane.




A falo suka samu su Didin da Asma’u suna karya wa. Abbu cikiciki ya yi sallama ita kuwa Sakna da alamar shak’iyanci a muryarta ta yi sallamar tana jifan Asma’u da kallon mugunta. A gefen Didi ta durk’usa murya cike da ladabi ganin Abbun ta shiga gayar Da Didi shi kuma Abbun yana lura da kallon banzan da Asma’u da Didin suke jifan Saknarsa da shi. Ya tabbatar da abinda Saknan ta ce don haka ransa ya yi k’ololuwar b’aci ya kalli Asma’u a fisge ya ce “Ashe abinda ake gaya min gaskiya ne, nema kike ki haddasan wutar masifa a gidana. Idan banda haka me baiwar Allahn nan ta yi miki tunda ta shigo kike wurga mata harara.” Asma’u da Didi suka saki baki suna masa kallon mamaki ganin yarda yake masifa da kumfar baki son ransa. “To ni ba zai yiwu ba gaskiya Didi ta tattara ta koma gidan mijinta ai suna da masauki anan garin. Tunda dai Allah ya baki lafiya kuma zan samo miki abokiyar zama ko a cikin dangi ne amma dai Asma’u ta bar gidannan.” Didi ta gyara zamanta ranta a b’ace tana girgiza kai da gaske lamarin nasa ya fara fitgitata ta shak’a sosai kafin ta gama jin tijararsa “Ba Takka, to tannu Utmanu don dai a wannan jallin ka wuce d’a te dai miji ko uba. To bud’e kunnenka da kyau ka ji babu inda Atma’u zata je har te tun tati tafiya, te dai idan har ni zaka had’a ka kora tatata kawai da mace ta riga ta gama da ti. Ina jiye maka lanal da na tani Ummaru ko hakkin Tadiya kawai ya iteka ya hanaka kwanciyar kabali.” Didi ta dinga masifa sosai ya dad’e ma bai ga b’acin rai kwatankwacin wannan a fuskarta ba. Ta wurgawa Sakina harara a zafafe ta ce “Munafuka lana dubu da ta b’alawo ce lana d’aya ta mai kaya.” Sakna ta fice jikinta a sanyaye idanunta suna Kawo ruwan hawaye na rashin samun nasara. Asma’u kuwa tana zaune mamakin d’an uwanta ya hanata magana ji take kamar ta fito da recording d’in nan amma tana tunanin akwai sauran lokaci.








______________


Yana zubesu a makarantar ya jiyo, ji yake kamar ya koma wajen Hamda amma ya San bai Isa ba. Dole ya koma wajen uwar gida sarautar mata ya goge mata abinda ya tsaya mata a zuciya.


Tas ya sameta ta yi wanka ta tsuke cikin kananan kaya. Gidan sai zabga k’amshi yake. Ga chicken peppe soup ta yi masa da chips da egg. Tana zaune zuciyarta sam babu dad’i saboda yarda take jin tamkar zargin mijin nata yana nema ya d’arsu a ranta. Ta sake bin jikin ta da kallo ta ganta tsaf a hasashenta.Tana son saka wando da riga sai dai k’ira da dirin jikinta ba na wando da riga bane. Kallonta yake sosai ganin duk don shi Tayi wannan kwalliyar sai dai da zai bata shawara da yace ta dinga shigar hausawa sun fi yi mata kyau akan wad’annan matsatstsun kayan da take sawa. Ganin kallon da yake wurga mata ne ya sata murmushi a tsammaninta ta gama gigita tunaninsa ne. Don haka ta mik’e tana kashe masa ido d’aya duk da tana jin haushinsa amma tana kewarsa sosai ta fad’a jikinsa had’e da sakar masa kyakykywar runguma cikin wani irin zak’uwa take furta masa “Me yasa kake neman canja mana farin Cikin da
Muka rayu da shi ne, kasan jiya kuwa a yanda na kwana jina ni kad’ai a gadonmu sai turarenka da ya bi ya addabeni please me yasa ka kwana a wajen aiki?” Kokarin zame jikinsa yake amma tak’i ba shi damar hakan sai sake narke masa take don dole ya biye mata a ransa yana ayyana ta matsanta masa.


Sai da ta samu nutsuwa sosai sannan ta bi shi da kallo suna kwance a gadon ta ce masa “K’amshin turaren da na ji a jikinka ya barranta da naka,Kayan da ka dawo da su ba da su Ka fita ba. Menene dalili?”
Ta fad’a tana jifansa da kallon da tuhuma..”
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Cikin takaicin lamarin ta juya da sauri ta rurrufe ko ina na gidan sannan ta kashe kayan wuta. Tana tsaki ta ja trolley d’inta ta fice daga gidan.


Tun daga nesa Nanna take jifanta da wani irin kallo gabanta yana dukan tara-tara ganin yarda Hamdan ta fito ta yi wani azababben kyau fatar jikinta ta murje sosai asalin natural skin d’inta ta sake bayyana zallan kyanta game da laushi da santsin fata. Ta amince Hamdan number one ce a wajen kyan fata, don ko farin mutum ba zai gaya mata d’aukar ido ba. Sanin cewa tare yake da matarsa ya sa ta had’e fuskarta tamau tamkar bata tab’a dariya ba. Da kansa ya fita ya bud’e mata boot d’in motar ta cilla trolley d’inta a ciki. Idanu take so su had’a kawai amma ya fuske ya d’auke kansa don ya san muddin zai had’a ido da ita to komaima zai iya canjawa. Takaici ya sake kumeta wato sabida yana tare da matarsa yana tsoron b’acin ranta shi yasa ko kallon arziki ba zata samu daga gareshi ba? Ta ji kamar ta zunduma ihu ganin har ya shiga motar ya tayar bai damu da ya ce mata ta shiga ba. A zuciyarta ta ayyana tabbas auren mijin wata masifa ne. Ji yarda ya banzagatar da lamarinta da su kad’ai ne ta tabbata yarda yau ba sa azimin nan saboda tafiya sai ya kusanceta kafin su taho amma saboda munafunci jibi yarda ya yi shakulatun b’angaro da ita. Jikinta a sanyaye duk da fuskarta bata nuna karaya ba ta bud’e bayan motar ta shiga. Tana gyara Glass d’in da yake fuskarta. Idanunta cikin na Nanna da ta lura tana yi mata kallon mamaki. Ba k’aramin dauriya ta yi ba ta angije abinda yake ranta murya a cunkushe ta ce “Ina kwana Maman Kamla?” Nanna ta saki hucin b’acin rai kamar ba zata amsa ba sai kuma itama ta mayar mata a cunkushen “k’alau.” Daga haka ta ja baki ta tsuke itama Hamdan gefen window ta mayar da kanta tana kallon kyau da tsarin garin Birmingham d’in. Shi kuwa ta cikin black glasses d’in da yake idanunsa yake k’arewa Hamda kallo shi kansa yana mamakin yarda jikinta ya sake murjewa ya yi kyau. Shi kad’ai yake murmushin ganin yarda take cika tana batsewa shi kansa ya yi mamakin yarda har ya iya basar da ita haka? Tabbas nan gaba akwai darun rigimar da zata sassauke masa idan suka kad’aita. K’okari yake kawai su had’a ido sai dai ta basar da lamarinsa, ko kallon inda yake bata sake yi ba ta ba banza ajiyarsa.


Har suka isa Airport d’in ba mai magana a cikjnsu kowa da tunanin da yake a zuciyarsa. Nanna kam kasa daurewa ta yi kafin su fita daga motar su je airport d’in ta ce “Ke kuma ina mijinki ya barki kika taho ko rakiya babu?” Da kyar Hamda ta had’iye abinda ya tsaya mata a wuya ta fice daga motar kawai ba tare da ta bawa Nanna amsa ba. Gaba d’aya ma haushin Hammad take ji idan banda munafunci me yasa har a lokacin ya kasa sanar da matar tasa ya aureta? Kada fa ya cuceta ya kaita y baro. Tunanin da ya sark’eta kenan ta shiga taune lips d’inta ba tare da ta shirya ba.


Ganin bata san yarda zata nufa ba, yasa dole ta ja tunga ta tsaya tana kallo sanda suka taho sai ta ga tamkar da gayya ma Nanna take sake shigewa jikinsa tana nannarkewa tsaki ta ja a fili har tana zabga musu harara ta cikin glass d’in da yake idonta. Har suka zo ta gefenta suka wuce Hammad ya sauke idanunta a kansa yana sakar mata murmushi kad’an. Ta kau da kanta ita kuma tana jifansa da harara.








_______________




Gaba d’aya Mahmah (Sadiya) cikin farin ciki take na dawowar Hammad ya warware bak’in k’ullin da waccan makirar matar ta k’ulla.


Lokacin ma tana aikin shirya musu abinci a kitchen.Umma Asma’u ta shigo fuskarta fal fara’a don yanzu sam bata da buri irin na tozartar Sakina. Musamman ganin yarda take k’ok’arin lalle sai ta had’a ta fad’a da d’an uwanta. Abinda ta yi mata ranar ba k’aramin tsaya mata ya yi a rai ba daga ita har Didi da kyar suka runtsa a daren ranar Didi juyi kad’an sai ta ce “Iyye Ba takka lamalin Umaru ya girgimama. To ba dani da a yi wannan itkantin ba babu matal da zata zo ta laba min kanku. A to Takina dai te dai ta ci kanta.”


Asma’u ta dafa kafad’ar Sadiyan ta ce “Hope dai ko Abbu baki sanar da shi dawowar ta su ba, don haka waccan makirar matar zata iya wargaza shirinmu. Ko ba haka bama na fi son yarda ta sakankance d’in nan ta gansu bagatatan lamarin zai fi jirkita tunaninta.” Sadiya ta saki murmushi kawai had’e da gigiza kai a fili ta ce “Allah yasa shi uban gayyar Abbun ya yarda, don jiya ban da na kai zuciya nesa tabbas da na bar gidannan. Daga fa ba masa nasiha akan duk abinda ta kawo masa dangane da maganar mutane ya fara tsananta bincike tukun kafin zartar da hukunci.” Shikkenan ya dinga sakar min bak’ak’en maganganu har da min gorin da ma ai tunda ni zab’in Didi ce dole ta fi so na, shi yasa kuma kuka fi so na aka saka masa mata a gaba to shi haka yake son matarsa duk da munin halinta da muke gani shi baya gani ciki da banta kawai kyanta yake gani. Bai tab’a sakar min bak’aken maganganu ba kamar jiyan nan.” Ta fad’a tana runtse idanunta har tana shirin yankar kanta da wuk’ar da take hannunta da sauri Asma’u ta rik’e hannunta “Me ye haka kike yi Sadiya, sai kin jiwa kan ki ciwo a banza a wofi? Ina hak’urin da kika had’iya na shekara da shekaru sai yanzu da komai yazo gangara zaki zubar da ladanki. Ki jure kwana kad’an ya rage ko nace awoyi kad’an.” Sadiya ta share k’wallar da ta sake kwaranyo mata tana sakin murmushin dole. Ita kanta ta san hak’kkinta kad’ai ba zai bar Sakina ta zauna lafiya ba don ta d’au tsawon shekaru tana cuta ta zahiri da ta bad’ini. Asma’u ta cigaba da kwantar mata da hankali har sai da ta tabbatar ta samu nutsuwa tukun na ta fita daga sasan nata.








______________




Zama kawai ta yi a gefe a airport d’in tana bin jama’ar da suke wucewa da idanuwa. A zahiri idan ka ganta sai ka zata da ma ta saba da zuwa airport sam ba alamar rashin wayewa a tare da ita.


Fuskarta sam ba annuri kuma inda ta nema ta zauna suna da tazara sosai a tsakaninsu. Amma duk da haka tana hango yarda suke hira cike da murmushi a fuskokinsu alamar suna cikin nishad’i. Ta ciji leb’anta ya fi sau nawa da zai cire tabbas da ya gaji leb’en ya cire. Ta ayyana ya zama dole ta nad’awa Ya Hammad sarautar mayaudaran duk duniya. Sab’anin hasashenta da tunaninta gangar jikinsa ce kawai a tare da Nanna zuciyarsa gaba d’aya tana d’amfare da ita. Duk abinda take yana kallonta ta cikin glasses d’insa. Yana kuma son ya jita a jikinsa ba Nanna da ta shige rabin jikinsa ba.


Hamda ta sake sakin tsaki ganin yarda Nanna ta kwanta ta sanya kanta a cinyarsa wai sanyi take ji jijjiga kai kawai ta yi kafin ta juya musu baya ta daina ganinsu gaba d’aya sai dai jikinta da zuciyarta wani irin b’arin b’acin rai suke yi. A wannan halin ta ke har ta ji an fara kiran su alamar tafiyarsu ta zo. Tana ji ta yi burus da shi. Ta ayyana ko Nigeriar suka je ba zata kulashi ba kai sai ya ma sakeni ni ba Zan iya zama da mijin wata ba.” Ta fad’a a fili ba tare da ta san yana tsaye a kanta ba hannayensa zube a cikin aljihun jibgegiyar rigar sanyin da take jikinsa. Murmushi kawai ya ke jifansa da shi. Jikinta ne ya bata yana gurin don ta ji kaifin idanunsa da suke yawo a jikinta hakan yasa ta k’i ta d’ago ta kalleshi. Ta dai tabbatar Nanna ba ta wajen shi yasa ya zo ya tsaya yana jifanta da kallo da wannan muggan idanun nasa. “Yarinya zaki ta shi ko sai na sunkuceki?” Ya fad’a cikin wata irin husky voice da ya yi whispering a kunnenta. Ta d’auke idanunta tana k’ok’arin kawar da b’acin ran fuskarsa “Ina matar son?” Ta fad’a ba tare da ta kalleshi ba. Murmushi ya saki kafin ya murza hannunsa cikin dokin wuyanta “Ta je toilet.” “Mhnm kawai ta ce tana k’ok’arin janye jikinta “Ai gwara ka koma kafin tazo ta kama ka.” Dariya ce taso sub’uce masa sai dai ya maze ta gefen ido ta ga ya ciro wata k’waya ya cilla a cikin lemon da yake hannunsa da mamaki take kallonsa har shima ya d’ago ya sakar mata murmushi “Ina son kasancewa da ke Nuri ta, don haka zan saka ta barci maganin barci Zan bata da zai d’auketa some hours da zarar mun shiga jirgi sai hankalinki ya kwanta ko? Zan zo ki jini manne a jikinki kamar yarda ki ke so.” Baki sake take kallonsa kafin ta ciji gefen d’an mitsilin leb’enta ta furta “Allah ya kyauta.” Bai amsa mata ba ya yi sauri jan trolley d’in sa mik’e mu je an fara boarding.” “Kada ka bata maganin nan. In dai nice ka je ka ji da matarka matsalarkuce muna zuwa Nigeria za ka sakeni nima na auri mijina ba mijin wata ba.” Ya juyo da niyyar murzar leb’enta ya hango Nanna sai kawai ya waske yana jijjiga kai alamar za mu had’u da ke.”




Bata sake magana ba har suka shiga jirgin tana kuma kallon sanda ya turawa Nanna lemon a bakinta lokacin suna layin boarding ta tab’e bakinta in dai nice ka bata a banza don na daina yarda ka mori jikina har sai ka sanar da kowa ka aureni”




Allah ya taimaketa ma ba wajen zaman su d’aya ba ita a can gefen window take su kuma suna d’ayan side d’in. Haushi kamar me ya kama Hammad ganin yarda wani bature ya zauna a kusa da ita. K’okarinsa kawai barci mai nauyi ya d’auke Nanna ya je ya tashi baturen daga kusa da matarsa. Allah ya taimkeshi ma sai ya ga baturen ya mik’e ya canja wajen zama. Hammad ya sauke ajiyar zuciya kawai yana takaicin yarda maganin yak’i d’aukar Nanna balle barcin ya kwasheta.


Sai bayan kusan mintuna talatin sannan barci mai nauyi ya yi awon gaba da Nanna. Lokacin kuwa Hamda wani irin amai da tashin zuciya ne kawai yake turnik’ota, ga wani sanyi mai kama da zazzab’i da take jinsa har cikin jikinta. A takure take sosai ga shi ba mataimaki ta ji kamar ta saka hannu a kai ta yi ta kurma ihu. Yawunta gaba d’aya ya tsinke ya zama wani marar dad’i ita sai ta ji ma kamar k’arni yawun yake mata. Tun tana daurewa har ta mik’e a gigice ta yi hanyar toilet d’in jirgin. Hammad da ya ganta shima da sauri ya bi bayanta bayan ya zame Nanna da ta narke a jikinsa. Kafin ya isa har ta fara kelaya aman kamar zata kelayar da duk abinda yake cikinta. Ta galabaita sosai. Hammad bai tsaya sanya ba ya sanyata a jikinsa ya rungume hankalinsa a tashe jin yarda jikinnata yake b’ari ga zafi ya d’auka. Ganin k’afarta tana rawa ya ciccib’eta kawai yama manta da wata Nanna can baya inda ba kowa ya nufa da ita. Direct a cinyarsa ya yi mata masauki ya rungumeta sosai, kamar zai mayar da ita ciki. Abinka da turawa ba wanda ma ya kalli abinda suke. Jikinta kawai yake murzawa da tattausan hannunta ta cikin rigarta. Gaba d’aya jikinta ya gama saki hakan da yake mata sai ta ji tana samun sau’kin wasu abubuwan duk da dai tarin haushinsa take ji. Yanzun ma k’ak’arin zamewa take a jikinsa amma ya k’i bata damar hakan ya manna k’irjinta a nasa yana jin yanayin yarda zuciyarta take bugawa Ta hanyar d’aguwa da saukuwar k’irjin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login