Showing 63001 words to 66000 words out of 117648 words
Chapter 22 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
da Didi suka dage min da addu’a. Na d’an samu sauk’in zuciya, ina kuwa barin k’asar na ji Nigeriar ma ta fice min daga rai baki d’aya. Amma na rik’e a zuciyata zan dawo d’aukan fansa ta hanyar aurar yarinyar na san idan na yi haka ne kawai zaku fahimci akwai lauje cikin nad’i, tunda kowa zai buk’aci jin me yasa na auri k’anwata da muke uba d’aya. Shi yasa ko da wancan karan ta jingina laifin a kaina zatonta ni na fad’a muku ban fito na kare kaina ba, duk da Abbu bai bani damar haka ba, na k’udirce zan b’ullo mata ta hanyar da bata yi tsammani ba. Wannan dalilin ne yasa na auri Hamda, kuma ina tabbatar muku aurena da Hamda halastaccen aure ne.”
Yana kaiwa nan ya ja baki ya yi shiru, majority na mutanen da suke wajen sai da suka saki ajiyar zuciya jin cewa Hammad ba shi da alak’a da waccan kwamacalar da ake danganta shi da ita na kusantar matar ubansa. Didi a zahiri take “Alhamdulillah, na tabbata dama zuli’al Utmanu ba zata yi lalacewal haka ba insha Allahu, Takina yanzu ke muke jila ki fad’a mana uban cikin y’al ki. Kada ki mayal da mu shashashai ki ce wani da aule kika haifeta ba ta yarda aka tab’a aule akan aule don haka muna jin Ki ko ki magantu ko na saka Umalu ya take ki yanzunnan.”
Sakina ta mayar da kanta kan Umaru har a lokacin still kansa a k’asa yake shi kad’ai ya san masifar da take ruruwa a ransa, tunanin cin amanar da Sakina ta yi masa yake duk da tarin k’aunar da yake mata ashe sai da ta bawa wani kanta bisa kawai dalilin son haifar d’a namiji. Tabbas ji yake zuciyarsa kamar ta daina aiki.
Ta mayar da kallonta kan Gadanga da shima fuskarsa ta nuna tana d’auke da matsanancin tashin hankali, musamman ganin yarda jijiyoyin kansa suka tashi rud’u-rud’u. Yana ta murza kan nasa da alama ya yi zurfi cikin tunanin da yake.
Murya da Didi ta yi amfani da ita wajen ba Sakina Umarni ne yasa suka d’ago gaba d’aya a firgice. “Takina zan ci Ubanki idan baki magantu ba mu zaki mayal y’an itka?”
“Didi ban ga amfanin wannan tashin tashinar ba, tunda dai ta tabbatar muku Hamda ba y’ar Yaya bace kuma y’ar halak ce Ku rabu da ita mana, babu amfanin ta gaya muku wanene ubanta amma a tawa fa fahimtar.” Maganar da Gadangan ya yi ce yasa d’aukacin mutanen suka zuba idanunsu a kansa, zuciyar kowa tana tsananta bugu, kada dai Didi ta ji Labari don ita zuciyarta ma kamar ta wuntsila ta fito saboda tsananin bugu da take. A firgice take kuma a tsorace da maganar Gadangan kada dai Gadanga ne uban Hamda?
Innalillahi wa inna ilaihillajiuna! Ke Takina ki fito fili ki gaya mana abinda yake k’udundune kafin ki Sa zuciyata ta buga, Kai kuma Gadanga an k’i a k’yaleta d’in tunda magana ta fito yau sai an fad’eta.”
Sakina ta share gumi da tarin hawayen da suke tsatstsafo mata ta bud’e baki da kyar ta fara magana.
“Ga duk wanda ya san ni tun lokacin y’an matanci na ya san ni da burin haihuwa yara maza. Da wannan na taso a zuciyata ban sani ba ko don naga irin yarda Ummeey na take fuskantar tsangawama daga dangin abeey bane a duk sanda suka ziyarcemu ko mu muka kawo musu ziyara Nigeria. Sun dinga kushe mu kenan suna furta ba abinda Ummeey ta iya sai haihuwar yara mata. Har wani suna suka rad’a mana gayyar yuyuyu.
Mu bakwai ne cis mata a gaban Ummeey kafin Allah ya bata haihuwar autanta namiji jal a cikinmu. Amma duk haka Ummeey bata fasa fuskantar bak’ak’en magana daga gurin kakata ta wajen uba ba. Kullum guri da habaici take mata. Raina yana sosuwa sosai kasancewar nice babba a cikin mu yasa na d’amfarawa zuciyata son haihuwar yara maza ko don na wankewa mahaifiya bak’in cikin da yake zuciyarta.
Ko san da Abbu ya fara nuna yana sona har gaya masa nake na ce ni idan mu kayi aure maza nake son haihuwa zato na shi zai dage ya bani d’a namijin. Tun a lokacin shina ya nuna min muradinsa na yara maza ne. Don har sunansu yake fad’a min zan saka Hammad zan saka Humaid Hamidan Hameed da Hamood kullum zancensa kenan nima kuma na ji sunayen sun zauna rad’au a bakina. Don har a bangon d’akina nake rubuta su kuma har mafarkinsu nake su biyar gwanin sha’awa.
Sai dai abin Allah da aka yi auren na samu ciki sai labari ya sha banban. Na ci buri sosai don Abbun da kansa yake kirana Maman Hammad. Ina amsawa da farin ciki. Abin al’ajabi itama Sadiya a tsukun lokacin ta samu ciki. Na dinga addu’a da yi mata fatan mugunta akan Allah yasa ta haifi mace ba tabbata yaro na sai ya fi shan gata wajen babansa.
Cikin hukuncin Allah da na tashi haihuwa sai ban haifo Hammad ba na haifo Najwa. Ranar ku san kwana na yi ina kuka gaba d’aya laifin na tattara shi kan Umar, shi ya dinga lallashina yana kwantar min da hankali tare da tabbatar min insha Allah zan haifo masa yara maza har sai na gaji.
Hankalina ya kwanta musamman ganin y’ar kyakykyawa kuma Abbu yana sonta yana ji da ita shiga da fita bakinsa Najwa, komai ya samu kuma ya siyowa Najwa.
Bayan wata biyar Sadiya ta haihu ita sai Allah ya bata d’a namiji tun da na ji rangad’a gud’ar Didi tana fad’in mai gida ya sauka na rasa duk wata nutsuwa ta na tabbatar Sadiya namiji ta haifa. Tunda ni san da na haihun Didi kishiya ta sauka ta ce. Wani abu ya tokare min a k’irji na kasa fita ko tsakargida balle na je na ga yaron. Duk da ita Sadiya san da na haihu ita tayiwa Najwa wanka ta gyara wajen.
Tun azahar aka yi haihuwar amma har la’asar na kasa lek’awa na ga babyn bak’in ciki yana nuk’urk’usar zuciyata. Duk da ina jin karakainar mutane masu shiga da fita mak’ota da y’an uwan Sadiya. Har sai da Didi ta gaji ta lek’o ta ga ko lafiya ina kwance a gadona na ji motsinta a falo hakan ya sa na runtse idona kamar mai barci. Didi ta d’aga labulai tana k’are min kallo kafin ta ce “Ke Sakina, na ce baki ji y’ar uwarki ta haihu bane kusan awa biyu amma baki lek’oba.” Na mik’e zaune ina murtsika idon k’arya kamar mai barcin gaske na ce “Ban ji ba Didi barci ne ya kwashe ni.” Kallo na take yi sama da k’asa da alama bata yarda dani ba sai kuma na ga ta kyab’e baki ta ce “To Sadiya dai ta haifawa Ummaru Magaji ba kiga yaro ba sak Ummaru san da na haifeshi yana k’arami.” Zuciyata ta sake cunkushe jin cewa bayan kasancewarsa namiji kuma kama yake sak da Ummaru, ji yanzu yanzu har Didi ta rad’a masa magajin Umar tun yanzu har an fara yar min da habaici. Didi ta gaji da kallona tana mamaki na sai naga ta saki labulan tana Allah ya kyauta. Da kyar na had’iye wani irin yawu mai kama da mad’aci a zahiri na ce Akwai matsala idan aka ce Ummeey na gado na tabbata Didi ba zata kyaleni da gorin haihuwa yara mata ba. Da kyar na mik’e ina share guntun hawayen da yake idona na fito na nufi sassan Didi tunda a can Sadiyar ta haihu.
Yaro kam tunda ga nesa na tabbatar Didi ba tayi k’arya ba don Umar ne sak. Abbu yana zaune d’auke da shi a cinya walwalarsa ta kasa b’oyuwa ya mik’o min shi “Shigo Sakna ki ga Hammad ya zo mai kama da ni.” Wani k’ululu na ji ya tokare min a k’irji jin sunan da aka sakawa yaron. Sunan da na san shine mafi soyuwa a zuciyar Umar amma shine ya sakawa d’an Sadiya bayan ni yake kira Maman Hammad wato ba zai jira ni na haifi Hammad d’in ba. Hannu na na rawa idanuna cikin na Umar nake jifansa da kallon tuhuma kafin jikina a sanyaye ba karb’i yaron. Tun a lokacin tsanarsa ta d’arsar min a rai…
J
I
K
A
R
N
A
S
H
E✍🏽✍🏽✍🏽
❤️❤️❤️❤️❤️🙏 [1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Na sake bin idanunsa da kallo kamarsa da mahaifinsa har ta b’aci. Ganin idanun Didi kafe a kaina yasa cikin cunkushewar murya na ce “Sadiya Allah ya raya.” Ba komai a fuskarta ta amsa “Ameen” Didi kuwa jifana take da kallo mai cike da ma’anoni iri-iri. Na fita gwiwoyina a sage har jiri na fara ji kafin na dangana ga d’akina.
A ranar Umar bai shigo sashena ba Sai daf da magriba, yana can ya tare wajen Didi sun saka Yaron a gaba, Haka ma su Gadanga da Asma’u duk suna can tare da shi. Wanda ni a tawa haihuwar ba’a Yi min wannan karar ba, wannan ne yasa na sake yardar anfi son haihuwar d’a namiji fiye da mace.
Sai lokacin kwanciyar barci sannan Umar ya shigo d’akina yana washe baki kamar gonar auduga. Ya ja jelar gashina Kafin ya ce “Maman Najwa ya aka yi?” Wani abu ya tokareni a k’irji tabbacin yau na tashi daga Maman Hammad da yake Kirana da shi, ya mayarwa da wata sunan. Zuciyata ta dinga zafi na ji duk soyayyar da nake masa tana rikid’ewa tana komawa k’iyayya. Muninsa na dinga gani tamkar bak’in kumurci. Ya zauna a gefena ganin kamar bana cikin nutsuwar zuciya “Wai me ya faru ne ina ta magana shiru?” Hawaye kawai na ji ya b’alle min daga idanuna ina kallonsa. Hankalinsa ya tashi ya dinga tambayata ba’a sin hawayena. Sai da na gaji da tambayar da yake min sannan nace mai yasa zaka sakawa Babyn can Hammad alhali ka san ni ce Zan haifi su Hammad. Wannan karan mamakina k’arara ya Bayyana a fuskarsa ya ja hannuna cikin tausasawa ya ce “Menene abin damuwa ina ce shima Hammad d’in d’an ki ne?” Girgiza kai na hau yi cike da tabbatarwa na ce “D’anta dai, ita kafi so ita ka yiwa cikin d’a namiji ni kuwa da baka damu da ni ba sai ka yi min cikin y’a mace.” Wannan Karan dariya na bashi sosai sai da ya dara “Yanzu ke fisabilillah a karatun da kika yi ne kika karanto cewa matar so ita ce take haihuwar maza?” Kuka na saka masa sosai. Ya gaji da jin kukan nawa ya ce “ Kin ga tashi mu yi magana don na lura akwai yarinta cikin lamarinki. Ita haihuwa da ki ke gani Allah ne yake tsara kayansa Ba mutum ba. Ba ni da ikon da Zan Sa ki haifi d’a namiji wannan ikon Allah ne, ki cigaba da addu’a idan da rabon Zaki haifi namiji sai ki ga kin haifeshi.” Duk da zuciyata ta yi sanyi da jin furucinsa hakan bai hanani cewa “To yanzu wa kafi so tsakanin Najwa da Hammad?” Ya dad’e yana kallon k’wayar idona kafin ya saki murmushi ya ce “Duka ina son su, babu wanda Zan iya zab’a na bar wani a cikinsu. Son su nake har cikin jinina tunda dukkansu jinina ne.” Na gyara zama fuskata a had’e don Ba haka nake so na ji yace ba, tunda na san a tsakanin ni da Sadiya ko makaho ya shafa ya san ni yafi so, to don me ba zai fi son nawa yaran ba? Sai dai ban yi masa magana ba na ja bakina na guntse amma daga yanayin kallon da yake min na san ya gane ban yi na’am da amsar sa ba. Ina kallo ya d’au Najwa suka fita falo cin abinci. Na bi bayansa da harara ina ji tamkar na guntile igiyar Aurensa na huta.
Ban sare da lamarin ba, Sai da na sake samun ciki, wannan karan ma Sadiya cikina yana wata uku ta samu nata cikin. Kullum addu’ata har a cikin Sallah Allah ya bani y’an uku maza ziryan. A wannan k’adamin har wata rama na yi ta fargabar abinda Zan haifa na kuma k’i zuwa scanning don kada suce min mace Zan haifa.
A zuciyata na sakankance mace Zan haifa don haka sawai nake jina. Cikin hukincin ubangiji da haihuwar ta zo still mace na haifa wacce aka sakawa suna Nasma. Gaba d’aya duk wanda ya sanni ya san ban yi farin cikin haihuwar ba sai dai na dake na dinga yak’e. Sadiya duk sanda ta d’au yarinyar sai na ji tace Masha Allah ina ma ni na haifi wannan zuk’ekiyar yarinyar. Harara nake zabga mata a zuciyata na ce kinibabbiya don na tabbatar farin ciki take da hakan. Ana gobe suna su Ummeey suka zo daga can k’asar mu Jordan. Kasancewar duk haihuwar da bake ba su tab’a zuwa ba wannan karan da ta ji sunanta aka saka Abeey ya ce Su taho.
Murnar ganinsu da na yi ita ta mantar da ni bak’in cikin haihuwar Nasma. Na shiga cikin dangina da k’annena sai farinciki nake. Amma ina lura da yanayin kallon da Ummeey na take wa gidan ita da k’annenta. Bata dai yi magana ba ganin Didi na wajen ta ja baki ta tsuke. Sai dai yanayinta kawai zaka kalla ka tabbatar bata yi farin ciki da inda ta sameni ba.
Sai da kowa ya watse kafin su yi shirin tafiya masaukinsu na kalleta cikin yaren garin mu “Ummeey me yasa ba za ku kwana a gidana ba.” Ta girgiza kai had’e da tab’e baki tana waige-waige ta ce “Nan ne wajen da kike kira gida? Allah ya kyauta miki ke dai da kika mak’ale sai d’an nigeria za ki aura. Ji gidan da kike ciki kamar kango.” Gaba d’aya annurin fuskata ya d’auke. Ba tun yau ba na san Ummina bata farin ciki da Aurena da Umar, sai dai yau ne na tabbatar lamarin k’iyayyar aurena da shi ta girmama a zuciyarta. Kifa kaina na yi a cinyarta ina sakin kuka ta shiga shafa min kaina murya k’asa-k’asa ta ce “Kin san duk cikin yarana ke ce mafi soyuwa a wajena, amma ba zan b’oye miki ba, ba na son aurenki da Umar wallahi, gashi kinzo sai haihuwar yara mata ki ke. Alamar k’wayak’wayanki da nasa na samar da yara mata ne kawai kamar yarda nawa da na ubanki ya zama.” Ta fad’a tana cizar leb’e “Allah dai ya kyauta tunda ke ki ka ji,ki ka kuma gani. Don haka ba ruwana.” Duk maganganunta basu dameni ba, kamar yarda ta ce wai ba zamu haifi yara maza ba ni da Umar. Hankalina kam ya tashi na runtse ido ina jin yarda take sake kambama lamarin.
Haka dai aka yi suna, Umar ya yi bajinta k’warai da gaske har sai da na dinga mamakin yarda yake b’arnatar da kud’i, kuma na tabbatar don ya yiwa dangina bajinta ne ya kuma nuna musu Ba a wahala nake ba. Sati guda suka yi cur kafin su tafi, duk da dama a hotel suke kwana. K’anwar mahaifiyata da muke kira Hala ta dinga fanfani akan lamarin Aurena sai dai ban ji ba.
Bayan haihuwar Nasma da watanni Sadiya ta sake sankato d’a namiji. Haka mu ka yi ta yi ni na haifi mace Sadiya kuma ta haifi maza duk kuma haihuwar da zata yi sai na saka kaina a d’aki na yi kuka sosai. Hankalina bai fara tashi ba sai da naga Gaba d’aya hankalin Umar ya fara tattara ya koma kan yaransa maza wani irin so da k’auna ta musamman yake nuna musu. A hasashena tabbas ya fi son mazan fiye da su Najma da suke mata, duk da dai ni duniya ta shaida ya fi so na amma fa bai damu da lamarin yara na ba. Sau tari zai saka yaran a gaba su fice ni kuma ya bar min nawa y’ay’an. Kuka nake sosai a d’aki na yi masa k’orafi ya fi a k’irga amma sai ya ce Hidimar mace sai mace y’ar uwarta. Dukkanmu yaran mu uku.
Gashi mun koma sabon gida. Lamarin nasa ya sake girmama bayan Hammad ya k’ara girma ba ya iya b’oye k’aunar Hammad a zuciyarsa. Ga shi ba ni da wata aminiya a Nigeria, ban san kowa ba kafin Allah ya had’ani da Kady. Wanda Zan iya cewa ita ce sanadin komai ita ta gurb’ata min tunani ta bani shawarar da har abada ba zan daina nadama ba.
Ranar da muka had’u da ita ba zan manta Ba a asibiti ne lokacin ina da tsohon cikin Munirat. Na fito daga wajen likita d’auke da takardar scanning. Kasancewar wannan karan da kaina na zo a yi min scanning d’in. Sakamakon yarda cikin ya yi girma sosai fiye da cikkuna na na baya. Hakan yasa mutane suka fara kyautata min zaton namiji zan haifa ko y’an biyu. Son tabbatar da lamarin yasa na je a haska min. Sai dai sakamako ya bayyana k’uru-k’uru macece rusheshiya a cikina. Tun daga wajen Likitan na fara kuka har san da na fito mu kayi kicib’us da Kady. Wanda ya zama sanadin had’uwar kenan. Cikin firgici ta rik’oni tana fad’in “Subhanallahi yi a hankali mana, ke kuwa baiwar Allah ya da tsohon ciki ki ke shiga irin wannan damuwar?” Ban bata amsa ba har muka isa wani waje da ba hayaniya sosai muka zauna. A wajen kuka na ya tsananta na shiga bajewa Kady sirrin zuciyata ba tare da la’akari da cewa wannan ce had’uwarmu ta farko ba. Madadin na ga ta tausaya min sai na ga ta saki murmushi ta yi tsaki ta ce “Ke ki godewa Allah ma kina haihuwar matsalarki mai sauk’ice. Ni nan da ki ke gani na ban tab’a haifewa mijina k’wansa ba, sai dai na haife k’waya-k’wayan y’an uwansa.” Na ware idona ina kallonta ta girgiza min kai “K’warai kuwa, Mijina ba ya haihuwa amma shi kansa bai sani ba kuma ba mazauni bane, a duk sanda ya yi tafiya anan nake shek’e ayata da k’annensa guda biyu d’aya cikinsu d’aya ma’ana uwa d’aya ce ta haifesu d’aya kuma ubansu d’aya. Kuma y’ay’an suka d’ebo dangi ta yarda ba yarda za’a yi ace ba nasa bane, ba ma wannan ba ko mutuwa ya yi za su iya cin gadonsa tunda gadon nasa na iyayensu ne, wannan yasa hankalina