Showing 48001 words to 51000 words out of 117648 words

Chapter 17 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

ce “Bari naje na ga Danger sam bai San yarinyar nan itama y’ar rigima bace sai yanzu.


A zaune a gefen gadon ya sameta fuskarta a had’e sosai da alama ma hawaye ta gama sharewa.
Yana murmushi ya k’arasa kusa da ita kafin ya zauna a gefenta yana zuba hannayensa cikin tattausan hannunta “Shikkenan hankalinki ya kwanta ba zan tafi ba sai da sassafe.”
Ji tayi abinda ya tsaya mata a k’irji ya fad’a mata ta d’ago tana haske fuskarsa da murmushi ya lakace mata hanci had’e da jan hancin “Rigima idan ban da son kai haka kawai ki yiwa mata fashin mijinta, yanzu yau ya kike so ta yi bayan mun saba kwana gado d’aya.” Wani kallo da ta watso masa ne ya saka shi sakin dariyar da bai shirya ba Ya dafe k’irjinta yana fad’in “Zuciyar ta kwanta kishi ko? Ashe ana so na?” Ta lumshe idanunta kawai tana ture hannayensa “Ana so ana kaiwa kasuwa ai tunda kika ce sai na kwana yau kuwa zaki fanshi Nanna duk wani abinda take min kema sai kin yi min shi. Wanka kafin na kwanta ta kuma shayar da ni tea da bakinta.” Da sauri ta waro ido wata matsananciyar kunya na kamata ta ce “Ni fa ba don haka na ce ka kwana ba tsoro nake ji.” Murmushi kawai ya saki yana janta tsaye tana tattale k’afa da kyar taje tafiya tsaf ya sunkuceta “Yarinya idan ma za ki mik’e ki mik’e yau mai till down ce.” Ta runtse idonta jin lab’b’ansa a saman nata.






______________________


Ammi hankali tashe take kallon malamin da suke zube a gabansa kafin ta ce “Malam ban gane ka yi iya yinka asiri ya k’i shiga jikinsa ba?” Fuskarsa a d’aure ya ce “Hakan da na gaya miki shine gaskiya kuma duk wanda ya ce zai sake miki asiri akan yaronnan ya ci shi k’arya yake yanzu jikinsa a tsare yake kuma kullum sai ya yi azkar bana haufi akan haka.don duk aljannin da na tura jikinsa a k’one yake dawo min.” Sakina da Kady suka runtse idanunsu cikin tashin hankali suka mik’e. ko sallama ba su yi masa ba suka fice.


Ko a mota maganar da suka dinga yi kenan, Sakina ta ciji yatsa ta ce “Ga shi gari ba kusa ba balle mu k’addamar masa ina ga Didin kawai za mu aika da ita lahira don ni dai itace matsalata.” Kady girgiza kai kawai ta tabbatar mata hakan shine maslaha. “Ki nemi guba mai k’arfi ko ta shak’awa ce a saka mata a turaren wuta ta shak’a ta margaya.” Suka tuntsire da dariya had’e da tafawa don suna hango alamun nasara a tare da hakan. Kady ta saki dafa ta kafin ta ce “K’awata kafin hakan ya faru sai kin san yarda kika yi kika had’a gagarimin tashin hankali tsakanin Asma’u da Umar don na lura itace matsalarmu.” Sakina ta girgiza kai tabbas ta yarda da Zancen k’awarta tabbas Asma’u ita ce matsalarta a wannan tafiyar. Ta shiga tunanin irin makircin da zata k’ulla mata. Murmushin mugunta ta saki tana dafa kafad’ar Kady “In dai wannan ce ki bar ni da ita a darennan Ba sai gobe ba zan yi maganinta. Ba dai yau girki na ba sai na zautashi na rikita masa kwanya na gigitasshi kafin na wuntsilo masa da maganar Shegiyar.” Dariya sosai suka saka har suna sake tafawa Kady ta ce “K’awata ai na san ki ta wannan fannin ba sauk’i kina ragargazar y’an mazan. Na rasa wace irin baiwa Allah ya baki da har yau ba ki fara salamcewa ba.” Sakina ta yi murmushi kawai kafin ta yi reverse da mota tana fad’in “Shima gogan kullum zancensa Kenan kullum kamar sabuwa nake dal a leda.”
Haka dai suka yi ta hirarsu da makircinsu kafin su isa gida.






Asma’u ta samu Sadiya a d’akinta. Ta mik’a mata wayar hannunta bayan ta danna recording d’in da ta d’auki su Sakina kaf hirarsu ta d’azu ta fito a cikin wayar. Tsananin mamaki da frigici ya kama Mahmah ta kalli Asma’u kafin ta ce “Yanzu Umman yara shaid’anancin Sakina har ya kai haka? Ita ta rufewa Didi baki fa na ji tace.” Asma’u ta girgiza kai “Sharrin Sakina ya zarce hakan, kada ki gayawa kowa lokaci kawai nake jira da zan bayyanawa duniya wacece Sakina? Ki kuma tursasa Hammad ya dawo a yi mai gaba d’aya. Yanzu dai kin tabbatar da cewa k’arya take Hamda ba jinin Hammad bace?” Sadiya ta girgiza kai cikin jinjina girman lamarin ta ce “Tabbas! Idan kuwa haka ne ya zama dole d’anki ya dawo nan kwana kusa ya dawo mata da shegiyar y’arta da ta nanik’a masa ta je can ta nemi Ubanta. Ranar zan ga Abbu da wani ido zai kalleni bayan ya gama tozarta ni a idon matar nan duk abinda na yi ban iya ba Sakina ce ta iya. Sau tari ya sha kira na da Sakina madadin Sadiya. Shimfid’ar aure kuwa tuni na sallama mata don ko na kai kaina raina ne yake b’aci. Abincina sai ya ga dama yake ci. Akwai ranar da fa cikin dare ya buk’aci na siyar masa da kwana na ya je ya tara da Sakina wallahi Asma’u ranar kukan jini ne kawai ban yi ba sabida bak’in ciki. Shekara da shekaru fa bak’in ciki da nake fuskanta kenan.” Hawaye ne kawai yake malala a idanunta alamar abin yana mata ciwo sosai. Asma’u jikinta ya yi sanyi da jin wannan babbar lamarin tabbas sun san d’an Uwansu baya adalci a tsakanin matansa amma sam bata san lamarin ya ta’azzara har haka ba. Ta jinjinawa hak’uri irin na Sadiya da tarin kawaicinta tsawon shekaru tana k’unshe da wannan bak’in cikin tana danneshi a ranta. Tabbas ta cancanci lambar yabo. Kasa ce mata komai ta yi illa kama hannunta da ta yi ta manna mata wayar da Kiran Hammad ya shigo alamar ya ji Kiran da suka yi masa bai d’aga ba ya biyota. Muryar Sadiyar a dashe ta ce “Hello Hammad kana ji na?” Da sauri Hammad ya amsa da “Eh Mahmah ina jin ki, ya na ji kamar kuka ki ke lafiya dai ko?” Ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “Ya Zama dole gareka ka bi umarnina in dai ni na durk’usa na haifeka ka tattaro ka taho Nigeria a satin nan. Kuma taho musu da shegiyar y’ar su idan kuma ka k’i ina tabbatar maka ba ni ba kai.” Ta kashe wayar bayan ta kalli Asma’u Tana murmushi ta ce “Ummansu idan ba haka na yi masa ba ba zai zo ba, yanzu kuwa na tabbata hakan da na yi masa zai saka shi ba shiri ya taho.” Asma’u ta girgiza kai ta ce hakan ya yi.




Shi kuwa Hammad kasak’e ya yi da wayar a hannunsa yana shafa kan Hamda da ta dage sai ya sata ta yi barci kafin ya fice bayan sun yi sallahr asuba. Tana jinsa tayi lamo a jikinsa sam rabuwa ce bata son yi da shi. Tana son jinta a jikinsa manne da juna musamman Idan yana shafata sai ta ji ta a wata duniyar da bata fatan abinda zai raba su. Ta sake juyi a jikinsa ta na d’an bud’e idonta a kansa ya sakar mata murmushi “Bari muje na yi mana booking flight zuwa nan da nextweek za mu tafi Nigeria Mahmah ta matsa.” Sosai ta ware idonta a kansa har hakan ya saka shi kaiwa idon sumbata murya a sark’afe ya ce “Ki daina min wannan kallon Idan Ba so ki ke ta karb’i hak’kina ba ga tsoro ga neman magana.” Ta turo bakinta tana juya masa baya. Murmushi ya sakar mata a wuya yana mik’ewa da sauri ya fice daga d’akin don idan ya biye ta tata sai yara su yi late a school.


Ita kuwa Hamda gabanta ne yake fad’uwa tsoronta d’aya kada suje Nigeria a raba su. Don tana jin sanda Mahmah ta kirata da shegiya! Shi yasa k’irjinta ya yi nauyi ta fara jin tsoro a ranta. Sam bata tunanin zata iya sake rayuwa a duniya ba tare da Hammad mahad’in zuciya da gangar jikinta ba. Musamman a yanzu da suka zauna na kwana biyun ta tabbatar da shi a matsayin lafiyayyen namiji abin alfaharin kowacce mace. Dama can a mafarki shine burinta balle yanzu da ya shayar da ita zumar k’auna ya lula da ita duniyar dad’i a zahirance. Ba ta jin akwai mahaluk’in da zai raba su.




To fa! Idan Mahmah ta zafafa fa? Ya za ki yi Hamda?
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Asma’u danne dariyarta ta yi, don ita kanta maganar Didin dariya take bata sai dai ta san da zarar ta yi dariyar yau ba ubanta Utmanu ba har kakanta sai ya sha zagi. Didi ta sake gyara zamanta ta ce “Ki je ki kilasu yau zaki ga futkar almura. Wannan karan Asma’u gagara k’unshe dariyar ta yi sai da ta yi saurin fita daga falon sannan ta saki murmushi.




B’angaren Mahmah ta fara shiga ta sameta zaune bisa sallaya da alama sallah ta idar ta zuba tagumi hannu bibbiyu. Lamarin gidan gaba d’aya ya fara fice mata a kai musamman matsalar mai gidan da bai d’auke ta a bakin komai ba. Ga matsalar Hammad da ya gagara fayyace mata gaskiyar lamari.


Sam bata san da shigowar Asma’un ba da take tsaye ta jera mata sallam ta fi biyar. Har sai da
Ta gaji cikin tausayawa ta k’arasa wajenta had’e da dafa bayanta sannan ta yi firfgitgit ta farko daga dogon tunanin da ta tafi idanunta ta d’ago tana sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya bayan ta ga Asma’un durk’ushe a gabanta.


Asma’u ji ta yi kamar ta saka kuka ganin irin ramar da Sadiya ta yi a tsukun wannan lokacin “Tunanin me kike yi Sadiya?” Murmushin yak’i ta saki da son danne damuwarta ta girgiza kai “Bakomai” “A’a wallahi zance ne ma ki ce bakomai kin luluk’a can duniyar tunani sannan ki ce min bakomai.” Ta fad’a tana jan hannunta cikin son kwantar mata da hankali ta ce “In dai matsalar nan ce ta Hammad ki kwantar da hankalinki ya tsumma a randa, zan iya yi miki rantsuwar da babu kaffara Hammad ba shi da alak’a da Hamda balle har a ce shi ya yi cikinta, haba Allah ba zai jarrabemu da wannan masifar ba, ita dai ta san yarda ta samo cikin d’iyarta.” Sadiya ta girgiza kai had’e da share guntuwar k’wallar da ta zubo mata ta ce “Idan ke baki yarda shi ya yi cikin ba ai ragowar mutanen gidan sun yarda. Ji fa yarda ubansa mahaifi ya yi masa korar kare daga gidan nan ba tare da ya tsaya ya ji ta bakinsa ba. Shi kuma ya tsallake ya bar k’asar nan bai damu ya sanar da ni yarda abin yake ba.” Asma’u ta girgiza kai ta ce “Duk wannan ya faru ne sakamakon d’aukewar maganar Didi amma yanzu ai komai zai daidaita tunda bakin Didin ya bud’e itace ma ta ce na tattaro mata kanku dukka.” Da sauri ta kalleta kafin ta ce “Da gaske?” Tana murmushi ta ce “Ki je idonki ya gane miki.” Suka mik’e gaba d’aya ranta fari k’al tana tunanin dukka matsala ta zo k’arshe da izinin Allah tunda bakin Didin ya bud’e.


Ita sashen Didin ta tafi da sauri. Ita kuma Asma’u ta nufi sashen Ammi Sakina. Ta dad’e tana knocking kafin Munira ta zo ta bud’e cikin fara’a da girmamawa ta shiga gaisheta Asma’u ta dafa kanta itama tana jin Munira a ranta kuma tana son ta musamman don yanayin halayenta da ya farrak’a da na y’an uwanta “Munira ya makaranta?” Munira tana murmushi tace “Hutu ake” Asma’u ta danna kai cikin falon tana fad’in “Suma sun so zuwa yanayin karatun na sune ya yi zafi na ce su bari sai an yi hutu.” Tana nufin yaranta.


A hakimce ta tarar da Sakina da Kady a zaune a tsakiyar carpet d’in da yake falon. Sun baje tarkacen kayan ciye-ciye iri-iri da suka gama ci. Gefe d’aya kuma kayan kitchen ne na amare suke ta dubawa. Sallamarta ya sa suka yi saurin d’aga kai. Sakna ta yi kicin-kicin da fuska don haushin zuwan Asma’un take ji musamman da suka saka Didi a gaba da magungunan karya asiri. Ba ta damu da yanayin kallon banzan da take mata ba, ta samu kujera ta zauna fuskarta d’auke da murmushi na zallar mugunta ta ce “Barkanku da safiya matar Yaya, sak’o daga Didi tana son ganin kowa a fadarta har mai gidanki.” Da sauri ta d’aga kai tana kallonta tana shirin rud’ewa ta ce “Didi kuma?” Asma’u ta d’aga kai cikin ginshira da k’asaita ta ce “Yes Didi dai ta mu ta gargajiya Allah ya bud’i bakinta yau.” Daga haka ta mik’e “Mintuna ashirin ta bawa kowa ya hallara a gabanta.” Wannan karan k’iris ya rage Ammi bata saki gudawa a wando ba. Gaba d’aya ta gama rud’ewa har bata san sanda Asma’u ta fice daga d’akin ba. Kady ta ja tsaki kafin ta ce “Tashin hankali matsala sabuwa! Amma in dai haka ne malamin nan ya yaudaremu da ya ce bakin almura ba zai tab’a bud’uwa ba.” Sakina ta mik’e ranta a jagule ta ce “Ta ya bakinta ba zai bud’u ba alhalin shegiyar matar nan ta zo k’asar nan mijinta fa shehin malami ne.”
Asma’u da take leb’e a bakin k’ofa ta yi saurin sakin murmushi sannan ta sake komawa falon idanunta cikin na Sakina da ta sake firgita da ganinta ta ce “Am sorry wayata na manta.” Ta zura hannu ta d’au wayar da ta danna recording a kujera ta fice tana sakar musu murmushi zuciyarta fal farincikin samun nasarar nad’e maganganunsu ko wannan ya isheta kafa k’wakkwarar shaida.


Sakina bata kawo cewa recording ta yi ba amma murmushin da ta gani a fuskar Asma’u ya tabbatar mata duk ta ji abinda suke cewa ta rik’e kanta had’e da fad’in “Kai wannan mata akwai almura.” Ta shige sashen Abbu don ta taso shi.




Gaba d’aya an hallara a falon Didin har da su Gadanga da Lauratu kuma Didin bata nunawa kowa ta fara magana ba.


Ta sake gyara zamanta kafa d’aya kan d’aya kafin ta b’antari goro ta sake sawa a bakinta tana taunawa tana jifansu da wani murd’ad’d’en kallo da kowa ya kasa gane ma’anar sa. “Bayan Tawon lokacin da bakina ya tamu a date Yau Allah ya bute min ti Alhamdulillah” kaf ahalin wajen da suka ji muryar Didin ba wanda bai d’ago kai ya zuba mata ido ba. Cikin tsananin farin ciki idan ka d’auke Ammi da take dariyar yak’e gabanta yana dukan tara-tara, duk da k’ok’arin tattaro nutsuwa ta sawa kanta al’amarin ya gagara sai share gumin da yake tsatstsafo mata take “Ta kanka zan fara Umaru, tabbat da utmanu yana raye tai ya yi Allah wadaran halinka. Ina aka tab’a tali’a haka fitabilillahi ba a
Ji ta bakin Hammad ba ka zartar da hukunci. Ko da yake ni ba dan te komai ba amma Hammad dai do ya warware k’ullin kowa ya fahimci yarda abin yake. Ku tati ku bani wuri dama abinda dan fad’a kenan kuma don uwal mutum ya take danne min baki.” Ta fad’a wurgawa Sakina harara. Lauratu kam sai da ta dara son ranta kafin ta kalli Didin ta ce “Ikon Allah Didi maganarki ta koma ta yara.” “Ta uwal yala ta koma ba ta yala ba kin ga laulatu ki kiyayeni. Ja’ila kawai ki tattara tilginki ki tafi an gode da diyala.” Lauratu ta k’unshe bakinta sannan ta shige d’aki.






_______
Tunda ta koma sashenta ta ja hannun Kady suka danna uwar d’aki sannan ta rufe k’ofa har da murza key. Ba kad’an ba lamarin ya gigita ta. Ta dubi Kady ta ce “Aminiya na shiga uku wannan almurar matar so take ta jefani a masifa, yanzu maganr dawowar Hammad take wai ya zo ya warware musu yarda abin yake.” Ita kanta Kady zufa ce take keto mata gaba d’aya kanta ya k’ulle ta rasa mafita in dai haka ne kuwa tabbas suna cikin gararin masifa ta dad’e cikin nazari kafin ta d’ago ta ce “Kurciya za’a yi masa ya ji sam ba ya son dawowa Nigeriar ma har almurar tsohuwar nan ta mula tukunna.” Sakina ta saki ajiyar zuciya tabbas wannan shawarar ita ce hanya mai b’ullewa madalla da samun k’awar arziki kamar ki Kady.”








______________


Wata iriyar duniya suka wulla daga ita har shi har bata san sanda alamuran suka jirkita zuwa yarda ba tayi tsammani ba, har sai da ta ji ya amshi mutuntakarta ta d’iya mace sannan ta ankare bayan ta ji wani zafi da rad’ad’i da ya ratsa mata har k’ololuwar kanta. Didi kawai take kira tana sake kai masa bahagon cizo.
Murmushi kawai take sake bayan ta gama tuna duk abinda ya wakana tana kalli bayansa yana shigewa toilet don yin nasa wankan da kansa ya taimaka mata ta yi wankan saboda d’an banzan raki da take masa sai yau ya tabbatar shagwab’ab’b’iya ya aura kalar matar da yake so. Ta mik’e zaune da kyar tana bin d’an b’ingilin towel d’in da yake jikinta da kallo kunya ta kamata ta yi saurin suturce jikinta da undies sannan ta saka doguwar riga har k’asa. Duk abinda take tana yinsa da sauri ne bata san ya fito ya sameta ga zafi da rad’d’in da take ji yana sake hauhawa yana neman haifar mata zazzab’i kan kace meye wannan kuwa hak’oranta sun fara barazanar datsewa cikin sauri ta shige cikin bargon tana kakkarwa still ba ta daina jin sanyin ba.




Ya dad’e a toilet d’in cikin nishad’i yake lumshe idonsa tabbas da kansa yau ya yarda da wani mawak’i yake cewa mata suna suka tara. Ashe ba k’aramin gata ya yiwa kansa ba da ya auri Hamda ni’ima daga indallahi.
Bai k’i a lokacin ma ya sake kusantarta ba sai dai ya lura Hamdan akwai d’an banzan raki bata daga cikin layin mata masu juriya a wannan fagen. Da kyar ya fito daga kwamin wankan sanye da rigar wanka yana goge sumar kansa da towel fuskarsa fal murmushin da ya kasa barin fuskarsa.


Da wak’arsa ya fito idanunsa suka sauka a kan ta da ta k’udundune kanta tana rawar d’ari da sauri ya k’arasa bakin gadon ya d’an bud’e dubet

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login