Showing 114001 words to 117000 words out of 117648 words
Chapter 39 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
taso mata, ba zata iya cigaba da fushi da shi ba ko da tana son aikata hakan zuciyarta ta k’i bata dama shi d’in dai shine mahad’in zuciyarta da gangar jikinta gaba d’aya, tun bata san so ba take hasasho shi a matsayin mijinta, tun kafin ya furta mata kalmar so gangar jikinta da nasa suna gauraya a cikin barci suke gudanar da wata iriyar gugitacciyar soyayya. Bata san sanda ta d’ora hannunta a zagayen lab’bansa ba ta shiga kewaye leb’en dasu. Lamarin da ya dinga d’imauta shi da ma a kusa yake sai ga shi tana sake hura masa wutar abin ya dinga jin duk wata garkuwar jikinsa tana motsawa, gaba d’aya ya wargazota jikinsa ya bata wata iriyar kyakykyawar runguma gaba d’aya ya manta ma a gadon asibiti yake sai da ta ankarar da shi, ta hanyar nuna masa cannular da take hannunta. Bakinsa kawai ya cije yana mayar da wani irin numfashi yanayin da yake jin jikinsa ji yake tamkar bai tab’a kusantar wata mace ba. Ya dad’e idanunsa a lumshe kafin ya bud’e idanun da suka jirkice cikin wahalalliyar murya a kunnenta ya rad’a mata kalmar da ya saka ta runtse ido ba shiri saboda girma da kunyar kalmar kafin ya kamo hannunta yana wasa da shi murya a k’asa ya ce “Am serious Hamda wallahi idan ba a yi wasa ba son ki zai hallaka ni, yanzu fa bana ji bana gani, wata irin baiwa ce da ke da wani irin taste mai gigitarwa don Allah kada ki yi amfani da wannan damar ki dinga wahalar da ni.” Idanu ta zuba masa kafin a hankali ta janye jikinta idanunsa akan k’irjinta ta ce “Ni da ba ka so baka damu dani ba ka d’auke matar so ka wuce da ita sannan da ita zaka tare a Abuja ni ka bar ni a kano mai yasa baka had’amu ba?” Ya dad’e yana kallon bakin da ta turo tana masa shagwab’a kafin ya kaiwa bakin cafka ya shiga tsotsarsa tamkar ya samu alawar yara yana yi yana mata wasu irin sabgogi a sassan jikinta “Ba zan iya adalci tsakaninku ba Hamda, shi yasa ba zan had’aku ba, saboda in dai idona zai gan ki ba Zan iya yiwa Nanna adalci ba, ki barta ta zauna a can bana son kowa ya rab’eni a loakcin da nake tare da ke shi yasa, duk Thursday da magriba ina kano kuma ba zan wuce ba sai monday early in the morning ai kin ga kamar ma kwanakin ki sun fi yawa saboda you are the best among the best.” Tsit ta yi tana samun sukuni a zuciyarta jin bai shirya wulak’anta ta ba, ya dinga aika mata wasu irin sak’onni da itama ta shiga mayar masa da martani ta manta da batun ciwo sai dai bata barshi ya zarce zuwa can ba ta dakatar da shi daga zafafan romance. Knocking d’in da ake ne ya saka shi dawowa cikin saitinsa da kyar ya mik’e yana gyara mata rigarta ya bud’e k’ofar ya san dai koma waye dole ya san a halin da suke amma bai dameshi ba, yana bud’e k’ofar yaga Doctor Najeeb ne abokinsa murmushi ya d’an saki yana sosa k’eya. Doctor Najeeb ma murmushin ya yi ya ce “Haba H. D’an Borno a asibitin ma ba zaka barta ta huta ba, bayan gadon Didin ma.” Hisham ya kai masa bugu kafin ya ce “Malam ka sallameta ko na samu a kai min matata wannan jan ran ya yi yawa mata da ciki ace sai an mana wani biki zata tare.” Doctor ya girgiza kai “shi yasa jiya na ga ka kasa cewa hakan a gaban Didi, ai na san tana nan tana jiranku.” Hamda dai lumshe ido ta yi cike da kunyar Doctorn. Bai d’au lokaci ba ya yi discharging d’in ta ya mik’awa Hammad Hannu “Allah raba lafiya abokina.” Hammad ya saki murmushi kawai yana komawa bakin gadon da kansa ya zira mata hijabinta har k’asa kafin ya ce “Taho mu tafi ko na Goya ki?” Ta girgiza kai kafin ta ce “Ka shirya goyo dai nan da three days ka san sabon amarci zan fara.” Ya sunkuya yana lek’a fuskarta kafin ya ce “In ye amaryar ba, in dai za’a jiyar da ni waccan harkar mai dad’in gaske ai kuwa zan yi goyo har da zani k’albeey ta.” Ta saki murmushi had’e da mak’ale kafad’a “Ni wallahi sai na haihu laulayi fa nake.” Hammad ya ware idonsa kafin ya ce “Ashe kuwa zan yi kwanan asibiti don komai zai iya faruwa matuk’ar za ki min rowar abina bayan ga ni ga ki a gado d’aya tabbas a sume za’a kawo ni asibiti.” Ta turo baki kafin ta ce “Na barwa Maman Khairi kai wallahi sai na haihu.” Ya girgiza kai “Allah ya kaimu jibin idan na aikata miki wani abin da kan ki zaki kawo kan ki, Hajiyata.”
Jikar Nashe.✍🏽✍🏽
08033748387
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: A cikin harabar ‘Dan Borno family house ya yi parking, tana k’ok’arin fita ya yi saurin rik’e hannunta ba tare da jin kunyar su Sa’ada da suke baya ba, ganin hakan yasa suma da
Sauri Suka fice daga motar. Idanunsa ya shigar cikin nata sosai kafin ya ce “Remain 3 days dai a daina min rowar jikina.” Da sauri ta janye hannun nata tana danna lock d’in motar ta fice, ya bi bayanta da kallo yana sakin ajiyar zuciya Allah ne kad’ai ya san wahalar da yarinyar nan take ba shi. Kafin ya fito ya bi bayanta sai da ya ciji lab’b’ansa yana sakin murmushi.
A falo ta samu Didi a zaune kusa da KK da yake ta barcinsa cikin kwanciyar hankali, da alama ya da’de bai samu barcin irin haka ba, za ta yi magana Didin ta yi saurin saka yatsa a lab’b’anta alamar ta yi shiru, Hamda ta saki ajiyar zuciya tana bin bayan y’an uwanta su Sa’ada da suka shige cikin d’aki. Sai dai kafin ta kai ‘daki ta jiyo atishawar KK da sauri ta jiyo shima Hammad daidai lokacin suka shigo da Kamla da Abulkhairi. Gabansa ne ya fa’di ganin KK ‘din kamar mara lafiya ya shiga cikin sanyin jiki kafin Didi ta ja tsaki ta ce “Kun tashe shi hankalinku ya kwanta, haba ni ban tab’a ganin jaraba irin wannan ba, kai mai ma ya shigo da kai nan?” Kk ya mik’e yana murmushi hannayensa rik’e da kansa da ya ji yana ‘Dan sara masa ka’dan ya ce “Ki barsu Didi, ai na ma ‘Dan samu sauk’i dama ciwon kaine ya matsa min.” Ya zuba idanunsa akan Hamda da ya ganta kamar mara lafiya ya ce da Hammad “Me ya faru da iyalinnaka na ganta so weak haka?” Tsagal Didi ta yi kafin ta ce “Me zai sameta banda ta sake kwasowa kanta ciki don tsiya irin ta Hamda sai da na ce kada ta sake ta saurari yaron nan sai an danganata da ‘dakin miji amma ta yi burus da ni ta nuna ban isa ba, ai ga shi nan ya kai ki ya baro za’a yi taron biki da ciki, dama idan za ki yi Amanki don Allah Hamda ki taimakeni kada ki yi shi kusa da ni.” Kunyar duniya ta gama kama Hamda bata san sanda ta mik’e tana hawaye ba ta shige ‘daki KK dariya ya yi kawai yana bin cup ‘din kunun da Didi take mik’a masa “Maza ka sha kunun tsamiya ne zaka samu afuwa in sha Allah.” Gefe guda Kuma peppe soup ne na naman rago ta masa mai yaji mai yawa ganin kamar mura yake. Sosai ya ji da’din kunun ya yi murna da shigowarsa cikin rayuwar su Didi ga shi yanzu ita yake gani matsayin mahaifiyarsa.
_____________________
Sosai babban hall ‘din dinnerr ya cika kana ganin wajen zaka san Naira ta ci k’aniyarta. Hamda da yayyanta ba k’aramin kyau suka yi ba, cikin tsadadden lace ‘dinsu sea blue, Dinner ce ta mata zalla ba maza ko masu ‘daukan hoto mata ne zalla kamar yarda KK da Abbu suka zartar ba sa son caku’de’deniya tsakanin maza da mata sun kiyaye dokokin ubangiji k’warai da gaske.
Yana mota yana jiranta kamar yarda ya yi alk’awarin a yau zai zarce da ita gidansa ba sai gobe ba kamar yarda aka tsara. Ya gaji da wa’dannan bidi’oin ba kuma zai tsaya sai wani gayyar y’an kai amarya sun kai masa matarsa ba, da kansa zai kaita har gidanta, sai dai su shafa su ji ba amarya. K’amshi kawai yake zabgawa daidai lokacin da Ya ganta sun taho tare da Sa’ada kana ganinta ka san a galabaice take don da kyar ma take tafiya sosai take buk’atar hutu. Hannu yasa ya bu’de mata gaban motar kafin ya kalli Sa’ada murya ba wasa ya ce “Please Sa’ada we need privacy ki koma motar su Munira.” Sa’ada ta waro ido tana kallonsa ya ‘d’aga mata gira cike da son tabbatar mata. Murmushi kawai ta saki ta juya shi Kuma ya shige motarsa.
Kyan da ta yi ne yake sake jan idanunsa yake kallonta yana sakin ajiyar zuciya yana k’iyasta da mai zai kwatanta yarda yake sonta a zuciyarsa. Da sauri ya ja motar ganin tana shirin kuka yana fara tafiya wani barci mai nauyi ya ‘dauketa ya saki murmushi a hankali ya furta “Ki farka ki ganki a gadonki na gidan ki na aure haba wannan gantalewar ta yi yawa.” Ya fa’da Yana shafa kumatunta masu sulb’i da wadataccen taushi. Hannun ta ta sa ta rik’e masa hannu ba tare da ta sani ba saboda barcin da yake idonta.
Bai tsaya ko ina ba sai a harabar katafaren gidansa da KK ya mallaka masa gari guda mai tsari da zubi irin na k’asar waje. Wani abu kawai ya danna a hannunsa mai kama da mabud’in mota kyakykyawan gate ‘din ya bu’de shi kuma ya danna hancin motar ciki, yana bin harabar wajen da kallo da k’amshin damuna da na bishiyoyin wajen suka gama hancinsa ya zuk’i k’amshi yana sakin murmushi ha’de da jaddada godiyarsa ga Allah mamallakin kowa da komai, mai ikon canja komai a duk lokacin da ya so kuma ya ga dama.
Tsayar da motar bai saka ta farka daga nauyayyan barcin da ya yi awon gaba da ita ba, ya bi jikinta da kallo yana sakin murmushi musamman ganin bak’in hadarin da ya lullb’e sararin samaniya. Da kansa ya ‘dauketa cak, kasancewar a gajiye take ya sa ‘daukan ya mata da’di ba tare da ta farka ba ta sake narke wa a faffa’dan k’irjinsa tana zuk’ar k’amshin turarensa da take jin sa tamkar a mafarki. Bai tsaya a ko ina ba sai da ya mata masauki a kan faffa’dar kujerar three seater da take parlourn. Sai sannan ta ware idonta a kansa, da sauri kuma ta mik’e tana dube-duben inda ya kawota. Tsararren falon da ya ‘dau black tiles ta dinga bi da kallo kafin ta sauke ganinsa a kanta ciki kasalalliyar murya ta ce “Ina ne nan?” Murmushi yake saki yana bin ta da nasa idanun kafin ya ce “Gidanki na kawo ki mana.” A firgice ta mik’e tsaye ta ce “Gida na kuma? Me yasa ina y’an kai amaryar?” Ya zare babbar rigar da ta bi ta addabeshi kasancewarsa ba mai son manyan kaya ba ya ce “Sun tafi tun kina barci.” Bata yarda da maganarsa ba don kuwa ba yau aka yi za’a kawota gidan ta ba don haka murya a raunane ta ce “Please Y. Hammad ka mayar da ni gida kafin ka sake jawo min maganar Didi dama ban tsallake wannan da ka jawo min ba kullum sai ta min gori a cikin mutane balle kuma ta ji da kaina na kawo kaina gidan miji ai wallahi ta samu na yi.” Bata ankara ba ta ji ya janyota jikinsa cikin wani irin lamari ya dinga gigita tunaninta har ya samu bakin nata ya yi tsit. Ta shiga amsar duk wasu sak’onni da yake aika mata ba tare da ta shirya hakan ba, tsawon lokaci yana aika mata da wasu irin zafafan romance kafin ya sake ta yana mayar da ajiyar numfashi. Cak ya mik’ar da ita “Mu je mu yi Sallah K’albeey wannan daren bana son saurarar kowacce k’aramar magana ina son in nuna miki irin tanadin da na miki, ki daina min maganar wannan magananniyar tsohuwar ta da’de ba ta yi surutunba b’acin ranta ba abinda zai ja miki kamar yarda nawa b’acin ran zai kai ki wuta.” Da kansa ya kaita toilet ya ha’da mata ruwan ‘dimi mai zafi so yake ta wargaje duk wata gajiyar biki da ta kwaso kafin ya sake saka mata wata sabuwar gajiyar. Ta ji da’din ruwan sosai don tunda ta shige bathtub ‘din ta samu wata irin gamsashshiyar nutsuwa tana bin toilet ‘din da ya ji kayan alafarma da kallo komai black and white, ta shiga wanke dukka sassan jikinta kafin ta fito.
Tuni ya fito mata da wata Nighty gown ta alfarma da Ammi ta sa aka saka mata a wardrop wani irin k’amshi kayan suke fitarwa da ya ja hankalinsa har bai san sanda ya cafko rigar ba yana shinshina k’amshin turaren da yake sake birkita masa nutsuwarsa da kyar ya samu shima ya tafi na sa ‘dakin don yin nasa wankan. Bayan ya shiga kitchen ya saka kaza a micro oven don ta ‘dima ma.
Sai da ta sake turare gashinta da ha’din mutanen jordan gashin ya dinga ba da wani irin k’amshi kafin ta janyo rigar ta saka, ita kanta ganin yanayin rigar a jikinta sai da ta ji wata irin kunya ta rufeta ga shi sai da Ammi ta mata garga’di akan dole ta saka rigar. Jin motsinsa ya sa da sauri ta zumbula dogon hijabinta na sallah kafin ta zauna ta takure a gefen gadon kamar wata sabuwar amarya.
Tray ‘din hannunsa ya ajiye mai ‘dauke da Laban Almara’i na k’asar Saudia gefe guda kuma dabino ne na ajwa a cike a wani ‘Dan bowl sai kazarsa da ya na’deta a wani tray daban. Bai bi ta kanta ba don ya tabbata idan ya zare hijab ‘dinnan ba zai iya tsayawa ya gudanar da Sallah a nutse ba, k’arshenta ma sallahr ta shiriri ce. Ya shimfid’a sallaya ya juyo yana kama hannunta murya can k’asa ya ce “Tashi Mu yi Sallah.” Jikinta ba k’wari ta mik’e ta tsaya a gefensa suka kabbara Sallah.
************
Tun ana saka ran dawowar Hamda har hankula suka fara tashi ganin har lokacin ba labarinsu. Didi sai Addu’a take ja dafatan Allah yasa lafiya suke.
Sa’ada ce ta fito daga ‘d’aki jin cigiyar ta yi yawa yasa ta kallesh ta ce “K’alau fa su ke Y. Hammad da kansa ya je ya d’auketa amma ban san ina suka je ba.” Didi ta ‘dago tana mata wani irin kallo kafin ranta a b’ace ta ce “Kan Uba! Wannan ‘da akwai jarababbe bayan ya ‘dirka mata cikin ma har yanzu bai mayar da maitarsa ba sai ya sake ‘dauketa….”
Jikar Nashe ce ✍🏽✍🏽
08033748387
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: ******************************
***** ALHAMDULILLAH*****
********MURFI**********
Komai ya yi farko yana da k’arshe banda ikon Allah. Ina godiya k’warai da had’in kan da kika bani Ubangiji ya saka muku da aljanna, masoya mabiya YA ABIN YAKE?
Na sadaukar da littafin nan kacokam da mabiya na group ‘din Jikar Nashe Real Fans. Sai Allah ya had’amu In Sha Allah a cikin sabon littafina bayan sallah idan muna da yawan rai. Saboda watannin da za su shiga watanni ne masu alfarma da bai kamata bawa ya shagalta da abubuwan duniya ba, mu dage y’an uwa wajen ribatar watannin na masu alfarma. Bissalam. Jikar Nashe ke muku fatan alheri.🙏😊😊😊
Ba wanda ya bi ta kan Didi illa ‘daukacin mutanen wajen mamakin Hammad ya kusa sumar da su a tsaye. Nanna jikinta ne ya yi la’asar ta fara rok’on Allah a ranta akan Allah yasa dai Hammad ya zamo mai adalci a tsakaninsu, saboda ayyukansa muraran suke nuna tsagwaron son da yake wa Hamda. Mahmah Sadiya ma a tsoracen take itama fatan ta ‘daya kada soyayyar Hamda ta rufewa Hammad ido ya kasa kwatanta adalci kamar yarda mahaifinsa ya zama, duk da dai yanzu komai ya daidaita yana k’ok’arin gaske wajen kamanta adalcin sab’anin lokutan baya da suka shu’de, ga shi tana ganin nutsuwa da tarin ladabi a wajen Hamdan ta nan kam bata da matsala da surikan nata shi yasa itama ta ‘daukesu ‘daya take jin su kamar y’ay’an cikinta. Ammi kuwa farin ciki ne ya lullub’eta ba don komai ba sai don ko anan aka tsaya Hammad ya nunawa duniya tsananin son da yakewa Hamda tana fatan kuma hakan ta ‘dore har abada.
*******
Lokacin da can a gidan ake cecekuce su b’angaren Hammad da Hamda ma ba su san me duniya take ciki ba a wannan lokacin wata iriyar soyayya suke yi cike da tsananin son juna da ‘doki game da zakwa’di kai kace first night ‘dinsu. Hammad a gigice yake sosai jin yarda Hamdan ta sake canja masa bai san sanda ya dinga furta mata wasu irin kalamai na daraja wa da suke barazanar tarwatsa zuciyarta, saboda yarda ta dinga jin kanta yana girma ta tabbata a wannan daren da kyar za’a samu wata mace mai sa’a irin tata. TA MUSU ZARRA. Sai mu ce Hamda Allah ya bada zaman lafiya.
_______________
Watanni sun shud’e kamar yarda kwanaki suka dinga tafiya suna zama satittika haka sati suka dinga zama watanni har zuwa sanda Allah ya kawo Haihuwar Hamda. Gaba ‘daya familyn ‘dan Borno sun yi murna da haihuwar da aka yi musu. KK jinsa yake a wata irin duniya saboda tsananin farin ciki. Yarinya kyakykyawar gaske mai kama da Uwa da Ubanta duka saboda yarda kamannin nata suka yi caku’de’diniya sai Kyan nata ya zama mai ban k’aye.
Didi ce a tare da ita a asibitin sai Mahmah da itama ta kasa tsare duk da Didi na ta mata shagub’e amma Mahmah ta yi funfurus kamar bata gane da ita take ba. Wata irin soyayya takewa Hamda musamman yarda ta kwantar da kanta take yi wa Nanna biyayya Duk wannan kishin ya ragu sai dai ‘dan abinda ba za’a rasa ba. Yanzun ma da Nanna da yaran Nannan duka suna asibitin da su ake