Showing 102001 words to 105000 words out of 117648 words

Chapter 35 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

zama duk sharrin da ta nufo ki da shi yana jirgewa a kanta, idan ba’a yi sa’a ba anan bigiren sai ki ji ana yamad’id’i da ke ana kin asirce miji wance bata da katab’us a gidanta sun manta ubangiji ne yace idan bawa na ya zama mai kusanta ta a koda yaushe sai na zama jinsa da yake ji da shi, na zamo ganinsa da yake gani da shi na zamo hannunsa da yake damk’a da shi na zamo k’afarsa da yake taku da ita, kin ga kuwa ta ya duk ubangiji yana kula da wannan b’abgarori na ki zai bari wani abu ta sameki na daga sharri. Har ila yau sun manta Ubangiji da kansa yace duk wanda ya dogara ga Allah hak’ika ya isar masa, shine isashshe akan duk al’amari yake kuma da iko akan k’addaruwar komai, ‘Waman yatawakkal alal Lah fa huwa hasubuh Innallaha baligu amrih k’ad Ja’alallahu li kulli shai’in k’adra’ don haka don girman zatin Allah Salma ku yarda makaman yak’inku ita kanta yarinyar idan ta ga kin ja girmanki sai ta fi daraja ki sab’anin ki tayar da hankalinki raini ya shiga tsakaninku, shi kansa mijin daraja da k’imarki zata k’aru a wajensa.(anan na ke jan hankulan y’an uwa na mata da cewa a duk lokacin da muka yi sallah mu dinga rok’on ubangiji ya sauk’ak’a maka kishin da yake zuk’atanmu, ya bamu abokan zama na gari ya bawa mazajenmu ikon aikata adalci a tsakaninmu) Dida bata gushe ba tana cigaba da jan hankalin Nanna da Salma ta hanyar nasiha da misalai iri-iri har sai da zuk’atansu suka yi la’asar nadama mai tsanani ta shiga tsakaninsu, daga lokacin Nanna ta janye duk wani mugun nufi a zuciyarta ta shiga addu’ar samun sauk’in zuciya ‘Allahumma la sahla illa ma ja’altuhu sahlan wa anta taj’alal hazna iza shi’ita sahlan. Tunaninnika suka shiga zuciyarta tabbas shaid’an yaso wasa da zuciyarta sai dai tana godiya ga ubangiji da ya bata jajirtacciyar Uwa mai k’ok’arin d’orata bisa turbar gaskiya, ta runtse idonta tana jin wasu hawaye masu sanyi suna kwaranyo mata da tun faruwar lamarin sai yanzu zuciyarta ta samu salama daga takaicin da take ciki, banda sharrin zuciya idan ba’a auren ta ya wad’annan tarin matan da suka baza gari za su auru idan ta tuna itama tana da y’ay’a mata tana da k’anne wanda ta yi imanin da wani mai mata zai zo ya so su ba zata hana ba, ashe kuwa ba ta bi fad’ar manzon Allah (s.a.w) ba da yace ka sowa kanka abinda ka sowa d’an uwanka, sosai ta fad’a jikin Dida hawayen na sake kwaranyowa take furta Astagfirullah ya Allah, ina rok’on afuwarka da gafararka, ubangiji ba ni da ja akan duk wata k’addararka Allah ka bamu zaman lafiya ka kawar duk wata fitina da zata wanzu a tsakaninmu.” Salman ma d’an hawaye take tana jin takaicin yarda ta zama uwar banza take zuga y’ar yayarta. Dida ta saki Hamdala a zuciyarta da Allah ya farkar da su daga barcin asarar da ya d’abesu ta shafa kan Nanna ta ce “Ki godewa Allah da ubangiji ya baki miji irin Hammad masu wuyar samu a wannan zamanin ki kuma jajirce wajen biyayya da kyautata masa ki kuma sawa zuciyarki don Allah kike wannan biyayyar ba don ki fi waccan kishiyar ta ki a wajensa ba, ki sha mamakin yarda ubangiji zai d’aga martabarki da k’imarki a wajensa ba boka ba malam, Allah yasa mu dace. Zan kuma cigaba da miki addu’a akan samun sauk’in kishi.” Nanna murya a dashe tace “Nagode Dida madallah da samun uwa ta gari ya Allah.” Dida ta lumshe ido kafin ta janye Nannan a jikinta ta ce “Ina son na ga canji daga yau, don haka ki tashi ki tarkata komatsanki ki wuce d’akin mijinki a can duk wata martaba taki take.” Nanna tana murmushi ta d’aga kai, had’e da mik’ewa ta fara tattara shirginta don haka kawai da ta fice daga gidan Hammad d’in tana jin haushinsa.






__________________


Tun daga nesa ya tsura musu ido, duk da hijabi ne a jikinta bai hana bayyanuwar tudun k’irjinta da faffad’an k’ugunta ba mai d’auke da tsukakkiyar mara. Takaici mara misali ya kamashi ganin ita a cikin Hijabin ma sai surarta ta bayyana, kishinta sosai ya tokare masa numfashi yana jin anya kuwa zai iya barin Hamda ta dinga fita ba bisa k’wakkwaran dalili ba, ya tabbata duk namijin da ya yi katarin ganin surarta sai ya ji wani abin ya tsarga masa zuciyarsa. Ya lumshe ido yana ganin yarda take taku kamar bata so. Ba tayi niyyar tambayarsa zuwa gidan lallen ba, amma Ammi ta tilasta ta sai ta tambayeshi gudun fad’awa fushin ubangiji. Yana zaune suka k’araso idanunsa na kan tattausar k’afarta mai kama da ta jarirai da ta yi kyau a cikin bak’in flat shoe d’in da yake saye da k’afar harta k’afarta ta kishin wani ya gane masa ita yake.
Fushi yake da ita don haka ya tattare fuskarsa ya k’unshe duk wata walwala da take cikinta, yana wurginta da kallo kafin ya mayar da idanunsa cikin na Sa’ada yana sakar mata murmushi a wasance ya ce “Amaryata sai ina?” Wani irin kallo Hamda ta jefeshi da shi da ya kusan saka shi dariya, Sa’ada kuwa murmushi ta saki ta ce “Y. Hammad tsokana ko?” Ya girgiza kai “Ba wani tsokana ai ba haramun zan aikata ba, na lura k’awarki ba zata iya d’auke hidimata ba, kin ga gwara na had’a da ke tunda ita lazy ce. Ina zuwa?” Ya fad’a idanunsa cikin na Hamda da take had’iye wani irin yawu mai matuk’ar d’aci wanda ta tabbata na zallar kishi ne ji take kamar ta kai masa duka. Sa’ada na murmushi ta ce “Gidan lalle za muje to Ammi ta takura sai munzo mun tambayeka.” Ya girgiza kai “Ke dai ki je ki yi lallenki, amma ita na yafe in dai ni zata yiwa.” Ya fad’a yana k’issima yarda lallen zai zauna rad’am ya yi mata kyau a tausashahiyar k’afarta shikkenan maza sun samu na kallo ina ba zai iya ba, duk sanda ta tare a gidansa ya tabbatar ba wanda zai ganta ta dinga masa lallen ba yanzu ba da kare da doki za su iya ganinta.” Idanu ta zube a kansa kamar ta yi kuka kafin ta ce “Ban gane ba zan yi lallen sallah ba?” Ya tsai da idonsa a kanta yana d’aga mata gira cikin wani irin kallo da ya tabbatar da zai gigita zuciyar y’an matan ya ce “Eeh haka nace, ba za kiyi lalle ba, don ban ga amfanin lallen ba, duk wata matar aure tana yin lalle ne don ta ja hankalin mijinta ke idan kin ja hankalin nawa mai za ki ba ni?” Kan kace me Sa’ada ta bi bayan Munira da sauri da taga ta yi gate, ita ma ta saka k’afa zata bi su ya mata wani irin ja da yasa ta tsayawa ba shiri idanunsa cikin nata tsawon lokaci yana yawo da su a jikinta kafin ya ce “Na haramta miki fita daga yau, lalle kuma na yafe shi kin ji na gaya miki.” Wata irin janyewa ta yiwa jikinta da ya saka su gogar k’irjin juna duk da k’ok’arin sa na kaucewa hakan da sauri ya runtse idanunsa yana turata gefe ya ce “Malama kada ki b’ata min azimi.” Ta watsa masa kallo kafin ta d’aga k’afa zata tafi ta ji yace “Kunun gyad’a da k’osai nake so na shan ruwa.” Wannan karan cak ta tsaya murya a cunkushe cike da tsiwa ta ce “Ka saka Sa’ada ta maka.” Yana murmushi ya ce “Kin san kuwa ina cewa zata min, wallahi kada ki saka na auri yarinyar nan da gaske.” Tana harararsa ta ce “Allah ya bada sa’a.” Ta shige sashen Didi hawaye na zubo mata ba na hanata lallen da yayi bane na zallar takaicin cewa zai auri Sa’ada ne, sharrin shaid’an sai ta ji zuciyarta na ingiza ta da tabbatar mata ba mamaki ma yana son Sa’adan saboda ya ga ta sallama masa jikinta ta dantse leb’enta tana jin takaicinsa har tsakiyar k’ok’on zuciyarta, ta tabbata da itace Nanna aka mata kishiya kai tsaye zuciyarta zata buga.
Umma Asma cike da mamaki take kallonta, “Ke kuma ina Lallen?” Murya a cunkushe ta ce “Ya hana.” Umma ta waro ido “Ya hana? Ban gane ya hana ba? Shi da za’a wa kwalliya shine mai hanawa, ai shikkenan ya yiwa kansa.” Didi kuwa tab’e baki ta yi tace “Jarabbaben kishinsa shi zai sa ya hanata.” Ita dai Hamda d’akinta ta shige dama barci ne a idonta lalle kuwa duk ranar da yaga dama ya barta ta yi.






________________


Yana zaune a falonsa Nannan ta kira wayarsa, mamaki ya kamashi ya mayar da kallonsa kan wayar a zuciyarsa ya ce “Mhmn ta daina fushin kenan?” Yana d’agawa ya ji tana gaisheshi da waccan kammalalliyar muryar ta Nannan da da ya sani mai cike da nutsuwa da kwantar da hankalin mai sauraro ya ji ta ce “Habibi kazo ka d’auke ni.” Wata irin sanyayyar ajiyar zuciya ya saki, ya tabbatar Nannan yau ta huce daga fushin da take murya a tausahshe da son nuna d’akinsa ya ce “Okey Madam on my way In sha Allah.” Ta saki shashshek’ar murmushi kafin ta ce “Take care, bye-bye.” Ya zare wayar a kunnensa yana sake ware idonsa akan screen d’in yana son tabbatar da gaske Nannan ce ko kuma wata daban?
Wanka kawai ya yi ya zura jallabiya ya fice zuwa d’auko tan.


Koda ya shiga gidan Didi gaba d’aya ta saka su a gaba da yi musu nasiha, ta kuma ja kunnensa da ya aikata adalci matuk’ar baya son tashi da shanyayyen b’arin jiki ranar alk’iyama Hammad kada ka wulak’anta uwargidanka akan amarya, saboda uwargida itace tushen gidan idan ka darajata ka daraja gidanka idan kuma ka wulak’anta tabbata ka wulak’anta gidanka, idan ka ga ana zaman lafiya a gida mai gidan ne ya so, idan ka ga ana tashin hankali a gida mafi rinjayen laifin Yana wajen mai gidan don haka sai ka jajricewa zuciyarka wajen tabbatar da adalci da son ranka ko ba so a tsakanin matanka, Allah ya had’e maka kansu ya baku zaman lafiya mai d’orewa. Ka ji ka k’i ji ka gani ka k’i ka gani sai ka ga kun zauna lafiya.” Daraja k’ima da mutuncin surukartasa ya sake bunk’asa a zuciyarta ya tabbata samun irinta a rayuwa yanzu matuk’ar dace ne. Sosai ya mata godiya suka mik’e shi da Nannan zuk’atansu fes ba kamar sanda Nannan ta taho gida ba zuciyarta na zafi da k’una.( anan na ke son jan hankalin iyaye mata don Allah mu zama masu k’arfafa zuk’atan iyayen mu a zaman rayuwar aure ba masu ruguza musu tarbiyya ba da zubar da mutuncin kansu a idanun surukansu k’ima da darjarsu ta zagwanye madalla da samu iyaye na gari.)
Ko a mota kallonta kawai yake yana sakin murmushi ganin yarda ta kwantar da hankalinta murya a sauk’ak’e ya ce “Dida uwace ta nunawa sa’a ki godewa Allah da yasa kika fito a tsatsonta.” Ta saki murmushi kawai kafin ta ji ya ce “Yanzu da wata uwar ce daga fuskarta Zan ga b’acin ran na yiwa y’arta kishiya wata ma daga nan zata d’ora y’ar a hanyar bin malamai shikkenan sai komai ya kacame k’arshe a kai ga saki Allah ya Yi mana tsari.” Ta lumshe ido kawai Kafin ya sake Cewa “yanzu gimbiyar a ina take son Zama Abuja ko kano?” Tana murmushi ta zube idanunta a cikin nasa Kafin ta ce “Abuja mana, na fi son na ganni ga katara ta ga taka. Tunda a can zaka fi zama.” Wani irin taratsatsi ne ya shiga zuciyarsa har ya kusan sakin sitiyarin kafin ya jiyo ya ce “Abuja kuma Madam?
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Cikin son k’ara tabbatar masa ta d’aga kai tana lumshe ido, daga cikin k’wayar idanun nata ya tabbatar babu maganar wasa a cikin furucin nata, jan ajiyar numfashi ya yi yana tuno irin dangerr da Hamda zata masa tunda ta ce tafi son Abuja, a wannan gab’ar ba shi da ta cewa tunda dole ya bawa uwargidansa zab’i haka shari’a ta amince. A kasalance ya dinga jan motar har suka isa gida ya rasa hukunci d’aya da zai zartar.


Tana tsaye a harabar gidan ta hango sun fito daga mota, fuskokinsu d’auke da walwala ranta ne ita kuwa ya sake b’aci musamman yarda ta hango yana cikin matuk’ar farin ciki ita kuwa ya k’unsa mata bak’in ciki ta hanyar hana ta zuwa lalle duk da ga shi nan ta hango lalle rad’am a hannu da k’afar matarsa ja da bak’i, yanzu haka ma lallen ya kaita a kayi mata ita kuma ya mayar da ita sha ka tafi. Ido biyu suka yi da Nanna, sai ta ga ta sakar mata murmushi duk zuciyarta na tsananin takaici haka ta hak’ura ta sakar wa Hamda murmushin amma Hamda ta zuba mata ido cike da b’acin rai kafin murya a cunkushe ta ce “Ina wuni Maman Khairi.” Bata jira amsarta ba ta shige sashen Didi, idanuwan Hammad zube a kanta yana hango tsagwaron jin haushin da take nasa. Ya saki murmushi kawai yana sosa k’eya musamman da ya hango Nannan ta kama shi dumu-dumu da kallon Hamdan, basarwa kawai ta yi itama don ta d’au alk’awarin ba zata sake bayyana b’acin ranta ba zata yi ta rok’on ubangiji ya yaye mata kishin da yake cunkushe a zuciyarta. “Amaryarmu na ga ta sake kyau, sai wani haske ta ke.” Ta fad’a tana jin k’unar furucin da yake fitowa daga bakinta, sai dai har k’asan ranta tana mamakin yarda Hamdan ta sake kyau cika da gogewa tamkar mai shigar yaron ciki. Hammad bai amsa mata ba illa shigewa da ya yi b’angaren su shima a zuciyarsa yana ganin kyan da Hamdan ta sake.






______
Sai da aka sha ruwa sannan ya shiga b’angaren Didin duk yawancin suna zaune a falo har yaran Umma Asman, ya sannu waje daga gefe yana hararar Hamda k’asa-k’asa ganin yarda take zaune ko mayafi babu hular kanta ma ta zame sai zuba zance take da su Sa’ad d’in Umma Asma. Sam bata ankare da dalilin hararar tasa ba, itama tunzira baki take tana watsa masa nata idanun, Hammad ya ciji leb’ensa na k’asa kafin ya mik’e ya shiga kitchen d’in Didi, Didi ta bi bayansa tana k’wala masa kira “Ba fa na son rashin arziki Hammad, kada ka kwashe min naman miya na ga dai yanzu rowar tsiya ce da kai, yaushe rabon da ka kawo min naman.” Mahmah da Umma Asma suka tuntsire da dariya ganin kallon da Hammad d’in ya watsa mata kafin ya ce “To kura, ni tea zan zubo. Ke Hamda zo ki zubo min black tea.” Kunyar Mahmah ce ta sata mik’ewa, Mahmahn na kallonta k’asa-k’asa ta na godiya ga Allah da ya bawa yaronta lafiyayyiyar yarinya tabbasa ta so ta tafka wa Hammad asara. Hammad ya bi bayanta dama ba wani tea da yake so so yake ya bud’e mata ido ya ja mata warning ta daina masa wasa da halittun jikinta kowane banza yana gani bata san zuciyarsa zata iya bugawa a duk lokacin da ya fuskanci wani namijin yana sha’awarta. Suna shiga kitchen d’in ya jata jikinsa ya mata wata irin runguma kamar zai tsaya jikinsa ya mayar da ita, wata irin kewarta ce take katantanwa da rayuwarsa, gaba d’aya yake lalubeta yama manta a inda suke burinsa ya kai ga can ta yi saurin tureshi ganin hankalinsa yana shirin gushewa ita kanta muryarta a cakud’e ta ce “A kitchen fa mu ke.” Lumshe idanunsa ya yi yana jan hannunsa ya d’ora saman k’irjinta murya a dashe kamar mai rad’a ya fara magana a kunnenta “Hamda ya kike so na yi? Ke kika jawo komai ma, gudu na kike kamar ba ni da ha’k’ki a kanki sannan ina shigowa kika haske ne da wad’annan abubuwan kin zube su kowane banza yana gani, wallahi koma cikin gida kike na sake ganinki ba hijab gaban maza sai kin gane baki da wayo, kina ji na.” Ya fad’a yana wata irin lasa a wuyanta, gaba d’aya ji ta yi tana shirin shid’ewa da sauri ta ja jikinta ta zame ta zauna a k’asa ba tare da son ranta ba ta fara fad’in “Please Yaya Hammad, ka fita kada wani ya zo ya ganmu.” Bin ta ya sake ya sai gani kawai ta yi ya d’auke ta cak ya d’ora akan working space d’in kitchen d’in yana kai mata sumbata a baki, sosai ya sumbaceta kafin ya saketa yana mayar da wani irin numfashi ya ce “Duk wanda ma ya gani shi ya jiyo wa yace su hana ni mata ta? Gaskiya ana d’aukan hak’kina da ma ban d’and’ana bane da sauk’i to ni na san mai na jiyo.” Hamda da sauri ta Durga daga wajen tana shirin fita ta ji ya ce “Nanna ta zab’i Abuja, don haka ki gayawa su Didi a kano za’a miki jere don na san may be kafin ku wuce Saudiya za su buk’aci zaman gida, sannan jibi insha Allah za mu wuce Birmingham da Nanna.” Wani irin Burki ta ja kafin ta juyo ta zube idanunta cikin nasa, k’una take ji sosai a ranta “Ita zai raina wa hankali kawai ya fito ya gaya mata ya fi buk’atar matarsa a kusa da shi fiye da ita, meye na mata k’umbiya-k’umbiya idanunta na zubar da hawaye take k’ok’arin furta masa ko Kamla d’aya amma ta kasa, yana k’ok’arin janta jikinsa ta fincike cikin ajiyar numfashi ta ce “Jikina kawai kake buk’ata, soyayyarka da kulawarka gaba d’aya ka bawa matarka, to wallahi matuk’ar haka ne ba zan tare a gidanka ba, kuma na fasa aurenka ko ma me zai faru ya faru.” Daga haka ta ja wani abu muk’ut da ya tokare mata wuya ta juya da sauri ta fice daga kitchen d’in, Hammad ya ja ajiyar zuciya don ya hango abinda ta fad’a d’in da gaske take har k’asan zuciyarta, gabansa ne ya fad’i yana hasashen ranar da za’a ce ya rabu da Hamda wani banza can ya aureta ya tabbata a ranar ajalinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login