Showing 105001 words to 108000 words out of 117648 words
Chapter 36 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
ya zo, amma ya zaiyi da Nanna ai da kunya ya nuna mata ba ya buk’atar zamanta a Abuja ya fi son zaman amaryarsa ya runtse ido yana tuno yarda Hamda take magana cikin tsagwaron b’acin rai.
Ita kuwa tana fita ba wanda ta bari ya ganta d’akinta kawai ta shige ta mayar da k’ofa ta rufe har da murza key kafin kuka ya k’wace mata, gaba d’aya haushin kanta take ji da har ta bari zuciyarta ta rinjayeta ta so mai mata duk da ta san tsagwaron kishinta, kukanta ta sha sosai kafin ta yanke shawarar zuwa gobe ta rok’i Abbu ya saka Hammad ya sahhale mata auren da gaske ta fasa ba zata iya zama da mai mata ba, zuciyarta tana sake tabbatar mata da wata rana tsananin kishinta zai iya kaita ga hallaka ko aikata aikin da na sani koma zuciyarta ta buga gaba d’aya.
Hammad ya dinga k’ok’arin kiranta a waya tana rejecting k’arshe ma sai ta yi blocking d’insa ta barsa da waya a hannu yana zuba idanunsa cikin hotonta da yake kan phon book d’inta, lallai ya san ta yi fushi don bata tab’a masa rejecting kira ba ko fushi take da shi sai dai ta d’aga wayar ta saka a kunne ta yi shiru maganar duniya da zai yi ba zata furta ko da kalmar ‘A’ ba. Ya saki ajiyar zuciya yana tunanin yarda zai iya zuwa ya tunkari Nanna ya ce mata ita ta hak’ura ta zauna a kano da kunya, ita kuma Hamda Son da yake mata shi zai hana ya iya yi mata jan ido ya ce ta zauna dole a kano, ya saki ajiyar zuciya kawai yana sake kiranta amma still ta k’i shiga.
__________
Kashegarin ranar ya kama sallah ce, kowa da farinciki ya tashi idan ka d’auke Hamda da Hammad da suka ta shi zuciyarsu a cusgune musamman Hamda da bata san sanda barci ya d’auketa ba saboda tsananin b’acin rai ruwan kunun gyad’a ne kawai a cikinta, Hammad a ranar dama ya ajiye wa zuciyarsa za’a kai lefe don shi da Mami Lauratu suka had’a kayan lefen akwatina 2set ita kuma Nanna kud’i zai bata ta siyi nata, sanda ya yiwa KK waya ya sanar da shi fad’a KK ya hau shi da shi yana fad’in “Wa yace Ka wahalar da kanka Hammad? Na Riga na bada a had’a mata lefe, amma tunda ka yi ba zan hanaka ba, ka je ka samu Abbunku sai ya gaya maka inda za’a kai lefen tunda y’arsa ce ni kaine nawa d’an, idan ya gaya maka ka gaya min Zan turo mutanen da za su kai lefen naka sai a had’a da na wajena da key na mota guda biyu ta ta d’aya ta Nanna d’aya, akwatinan da na musu nata set biyu na Nanna set d’aya, don itama dole a mata adalci.” Hammad yana farin ciki ya dinga masa godiya “Ha’k’ki na ne Hammad, ina jinka kamar ni na haifeka fiye da yarda nake jin Hamda da Kamla Allah ya yi muku albarka. Don haka kada na sake maka abu ka min godiya ka d’auke ni kamar Abbu tunda ni ba ni da wani d’a namiji kai nake gani na ji dad’i.” Hammad murmushi ya saki bayan ya sauke wayar a kunnensa ya sake gwada kiran Hamda still wayar a kashe take, saboda tana fushi da shi ko kwalliyar sallahrta bai gani ba, sallahr idi ma da zata can ya hangota sanye da nik’ab, bugun da zuciyarsa take masa ne kawai ya tabbatar masa itace don in dai tana waje sai ya ji wannan bugun k’irjin.
Direct wajen Abbu ya wuce ya isar masa da sak’on KK farin ciki ya cika zuciyar Abbu da wannan daraja da k’ima tawa da KK ya masa ya ji duk duniya ya daina jin haushin wancan lefin da KK ya masa cikin fara’a ya ce “Kira min shi.” Yana d’agawa Abbu suka gaisa ya ce “Na ji sak’onka nagode k’warai a kawo nan gidan zuwa magriba insha Allah.”
KK cike da jin nauyin Abbu ya ce “Ba godiya tsakaninmu Ai Hamda y’arka ce, ba ni da hurumi a kanta yarda ka yi wahala da ita kad’ai ya isa a jinjina maka, alfarma d’aya zaka min ka bar min yaro na Hammad a daina shiga huruminsa ya zama ni ne Babansa please!” Abbu yana murmushi ya ce “Na bar maka dama naka ne Allah ya taya mu rik’onsu.” KK ya ce “Ameen ya Allah, yau za su zo insha Allah.” Daidai lokacin Ammi ta shigo idanunta zube cikin na Abbu ta ce “Su waye za su zo? Na ga sai zabga fara’a kake?” Yana murmushin ya ce “Masu kawo lefen Hamda, sai ku fara shiri ko da yake ba huruminki bane bari na je na gayawa Didi.” Jikin Ammi ne ya yi sanyi jin abinda Abbun yace wai ba huruminta bane, kawo lefen y’arta shine ya zama ba huruminta bane, har wata k’wallace ta fara son zubo mata ganin da gaske Didi ta mata fashin y’a tana ji tana gani. Hammad da ya lura da ita murmushi kawai ya saki ya mik’e yana ficewa daga d’akin ko da wannan kad’ai aka barta ya tabbata ya isheta takaicin da zai saka mata hawan jini.
-
__________
Abbu na gayawa Didi ta rangad’a gud’a fad’i take “Lokaci ya zo abu na mu maganin a kwab’emu, ai sai a zo a fara shiri a musu orderr kayan ciye-ciye a kuma tanadar musu kud’in tukuici don na san kaya ne za’a kawo ba na wasa ba.” Abbu murmushi kawai ya saki yana kallon Umma Asma ya ce “A yi abinda ya dace, sai ki turo min Zan tura miki ta account d’in ki.” Tana murmushi ta ce “To” Hamda da take d’aki tana jiyo Abbu ta yi saurin fitowa idanunta fal k’walla ta zube a gaban Abbun, gaban Hammad ya fad’i ganin yarda duk ta bi ta birkice da sauri ya hau girgiza mata kai, ita kuwa dafe cinyar Abbun ta yi murya na rawa ta ce “Abbu ina da magana.” Gaba d’aya Abbu ya tattara nutsuwarsa kanta yana shafa kan nata ya ce “Maza Hamda gaya min me ya faru?” Kuka ta saka tana jin nauyin furucin da zata furta amma ya zama dole don bata san jefa kanta a hallaka “Abbu na fasa aurensa don Allah ka saka ya rabu da ni…”
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Gaba d’aya falon Didin ya Samu bak’uncin shiru, dukkansu a razane suke Kallon ta cikin mamakin furucinta da ya zo musu tamkar dirar aradu, Ammi ma zancen ya dirar mata a nata kunnen daidai lokacin da ta sawo kai zata shigo falon Didin, tuni ta ja jikinta baya ta koma ta jingina da bango tana mayar da numfashi takaici da haushin wautar maganar Hamdan ya sata runtse idonta. Ban da wauta wace irin magana ce Hamda take yi bata ji kunyar Abbu ba, bata ji ta Didi ba balle ta uwa uba Hammad da yake zaune a wajen. Ta ja tsaki kafin ta juya ta fice daga sashen Didin tana ayyana yarda zata samu damar ci mata mutunci yau. Sa’ada kanta ta ga ragon azancin Hamda sosai ta ga wautarta musamman ganin yarda Hammad d’in idanunsa suka kad’a suka yi jajur alamar ransa a matuk’ar b’ace yake. Didi kuwa k’ank’ance ido ta yi tana k’arewa Hamda kallo tana son ta gano shin a cikin hankalinta take. Abbu ya ja ajiyar zuciya kafin ya ce “Me yasa ki ke son ya sake ki?” Wannan karan hawayene yake kwaranya akan fuskarta kafin ta mayar da kallonta kan Hammad da ta ga ya sunkuyar da kansa wani Abu mai kama da tausayinta yana son tsirga mata, sai ta maze tana tuno Yarda ta hangoshi da matarsa suna cikin farin ciki da walwala kishi ne yake damunta sosai ta runtse idonta kafin ta ce “Abbu bana son mai mata, ina da tsananin kishi ina tsoron fad’awa halakar ubangiji.” Tsit falon ya sake d’aukan bak’uncin shiru Abbu ya shiga tunanin mafita don ya hango tabbas Hamda tafi Sakna kishi, haka ya yi fama da Sakna kafin ta saba duk da har yanzun ma ba gama sabawar ta yi ba, ya dafa kanta kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce “Shikkenan za’a san abinda za’a yi. Ta shi ki je ciki.” Ta mik’e jikinta a sanyaye ta shige d’aki, Hammad kuwa ya bita da kallo cikin tsananin takaicin ta da mamakin yarda har ta ke neman ya saketa, Hamdan Sa dai da suke matuk’ar son Juna sai ya ga kamar an jirkita mata tunaninta. Ya runtse idanunsa yana jin yarda bugun zuciyarsa ya canja lokaci guda, zuciyar ta cunkushe waje d’aya sai wani irin zafi k’irjinsa yake masa, maganar da Abbun ya yi masa ita ta dawo da shi cikin hankalinsa “Me ka yi mata da har take neman saki a wajenka?” “Me kuwa Zai yi mata shak’iyanci ne irin na y’ayan zamani da kuma ganin yana nuna mata soyayya, mama kuwa in dai ina raye Ai ba mai raba Aurennan. Ehe sai da zuciyarta ta buga ta mutu.” Abbu shiru ya yi jin abinda Didin ta ce ya mik’e kawai ba tare da ya sake cewa komai ba, sai da ya kai k’ofa ya kalli Hammad d’in ya ce “Ka sameni a sitroom d’ina.” Hammad da duk hankalinsa ya jagule ya mik’e ya bi bayan Abbu. Yana jin kamar zuciyarsa ta fito don tsananin b’acin ran Hamda.
A falo zaune shi da Abbu ya kalleshi “Matarka kishi ne yake damunta, kai kuma baka san ta yarda zaka tafiyar da lamuran mata masu tsananin kishi ba, ita mace mai kishi a duk sanda kake tare da ita bata son ta ji kana ambaton ko da sunan y’ar uwarta ce, menene musabbabin dalilin da ya sa take neman saki?” Idanunsa sun kad’a sosai ya d’ago ya dubi Abbu “Akan mun yi magana da ita ta fi son zaman Abuja, ita kuma Nanna ta ce min itama tafi son zaman Abujan shine na ce tunda itace k’arama ta hak’ura ta zauna anan, abinda ya jawo ta ji haushi kenan.” Abbu ya saki murmushi kafin ya ce “Dole zata ji haushi, ka san me yasa? Saboda ka mata baki biyu, me ya sa ka bata zab’i kafin ka bawa Nannan da take gaba da ita zab’i? Kuskuren da maza ku ke yi kenan a yayin neman aure idan baka jajirce ba zaka zama lusarin namiji yanzu dai ka ga gaba d’aya abin ya b’aci, shawarar da zan baka tunda gidajen masu girma ne kowacce ka bata part d’aya wata sama wata k’asa idan yaso idan kuka zo sallah Ku zauna a gidanku na Kano Abuja ma kuna tare.” Hammad ya yi shiru, duk da yana tunanin hukuncin Abbun shine daidai amma shi sam bai masa ba, baya son had’a su waje d’aya don ba abinda hakan zai haifar illa tashin hankali ya san Hamda da d’an banzan kishi. Ya ja ajiyar numfashi kafin ya ce “Please Abbu ka dai rarrasar min ita, amma wallahi had’a su akwai matsala don Hamda tana da kishi.” “Raba su ma akwai matsala don matuk’ar kana can da Nanna anan ma Hamda rigimar zata ta yi maka.” Abbu ya fad’a cike da son tabbatar masa. Hammad ya sake sakin ajiyar zuciya kafin ya ce “Hakan shine masalaha Abbu, idan yaso zan dinga tahowa every thursday da yamma na hak’ura da aikin friday d’in sai na koma monday da safe kaga na raba musu kwanakin kenan.” Abbu ya jinjina kai kafin ya ce “Hakan ma dabara ce amma fa sai uwar gayyar ta yarda tukun na ka san yarda zaka shawo kanta ta amince.” Ya d’an saki ajiyar zuciya kafin ya ce “In sha Allah, zan bi da ita ta yarda zata amince.” Ya mik’e a zuciyarsa yana tunanin ya zama dole ya fitowa Hamda a namiji kafin raini ya shiga tsakaninsu. Abbu ya bi shi da kallo cikin murmushi yana tunanin tabbas Hammad shima ya d’aura k’afa a irin tasa wahalar da alamar Hamda ma Sakna ta d’auko mai gigita kwanyar d’a namiji lokaci guda.
______
Ammi kallon Sa’ada kawai take tana mamakin kaifin basira irin na Sa’adan “Wallahi Didi na nema ta lalata Hamda Ammi, idan ba kiyiwa tufkar hanci ba, duk wani rashin mutunci da takewa mijin ta da d’aurin k’afar Didi, ita take sata raina mijinta wallahi, shi kuma soyayyarta ta rufe masa ido baya gane rashin daidanta sai nan gaba idan yana son ya juyata ta ce bata san zancenba.” Ammi ta ja ajiyar numfashi kafin ta ce “Maza Sa’ada je ki ki kira min ita, duk abinda ta yi ina ji akan kunnena ta yi shi, kada kice ni nake nemanta.” Sa’ada ta d’aga kai ta fice da sauri. Tana shiga taga Hamdan kanta akan cinyar Didi tana taje mata gashi tana ji Didin tana sake zugata “Kin ji na gaya miki wallahi ki kafe ke Habuja ki ke so haka kawai ga garin shugaban k’asa bak’in ciki zai min don kada na je wani azimin na tare a gidanki, banda ma haka ke da gidan ubanki ba ubanki bane ya bada gidan ai sai inda ki ka zab’a za’a ce miki wai ki zauna a kano gari duk hayaniya ita ga y’ar mai ya kaita Habuja, mata sai uwar k’ibar tsiya da kyar fa take juya mazaunanta.” Sa’ada tana hararar Hamdan ganin yarda take tuntsira dariya ta ce “Hamda d’an zo ki ga wani abu.” Hamdan ta mik’e tana zura hula ta bi bayan Sa’ada, ba su dire ko ina ba sai falon Ammin. Tun daga kallo d’aya da tayiwa Ammin ta tabbatar yau lamarin Ammin ba wasa, nan kuwa Ammin ta shiga surfeta da masifa “Don ubanki da kika kalli idon ubansa kika nemi saki baki ji kunya ba, ke shashashar ina ce idan banda Lusaranci uban me ya yi miki da za ki nemi saki, kin san hukuncin macen da ta nemi saki wajen mijinta kuwa? Balle ki kalli idon mahaifinsa ki ce wai d’ansa ya sake ki.” “Ni yaushe na kalli idon Babansa na ce ya sake ni, ai Babansa bai zo gidannan ba, Abbu ne kuma Baba na ne shi da kansa ya fad’a kuma ni Ammi kin san me ya min na ce ya sake ni?” “Uwarki ya miki, kin ji na ce Uwarki ya miki, ba baki na miki ba idan kika bari Hammad ya sake ki ba za ki samu wanda zai maye miki gurbinsa ba, don yana da duk qualities d’in duk wani mijin da ake kira na k’warai na sake jin kalmar saki a bakinki wallahi sai ranki ya b’aci, shashashar banza ko da yake ban ga laifin ki ba rainon Kaka ce haka za ki je ki yi ta shirme a gidan miji.” Sunkuyar da kanta ta yi kawai tana sauraran fad’an Ammin da daga baya ya juye ya koma nasiha zuciyarta ta yi sanyi musamman da Ammin ta saka tattausan hannunta tana share mata hawayen da suke kan fuskarta. Ta sake saka ta a hanya sosai da yarda zata yi ta mallaki zuciyar mijinta “Kishiyarki tana da wayo Hamda dole sai kin dage dantse idan ba haka ba ki ji a salansa Allah ya muku albarka gaba d’aya.”
A daren ranar masu kawo lefen suka kawo, gida ya kacame da ganin lefen Hamda, akwatina set hud’u kowanne dank’am da kaya na alfarma, da mukullin motarta, ita kuma Nanna nata set biyu itama da nata key d’in motar galleliya irin ta Hamda sak, Hamda kanta da ta ga kayan sai da ta jinjinawa Hammad tunda bata san wasu kayan Daddynta bane ya yisu ya shige d’aki zuciyarta cike da farin cikin ganin kayan wai ita Hamda ita ta rikid’e ta koma y’ar gata haka, Hamda dai da take a wulak’ance banda a wajen Didinta itace yau Ta zama abar so a wajen kowa ta kuma zama sanyin idon mahaifiyarta, duka dai dalilin Hammad, sai ta ji tana son ta ji muryarsa duk wancan fushin ya kau, ta shiga kiran wayarsa sai dai bugun duniya bai d’aga ba, sai ga Hamda tana hawaye tana sake kiransa sak’o ya turo mata “Na aiko da takardar ne?” Ras gabanta ya fad’i ta shiga duba sak’on tana zaro ido ga zuciyarta ta kasa fassara mata sak’on daidai da sauri hannunta na rawa ta rubuta masa “Takardar me?” Wannan karan bai jima ba ya amsa mata da “Saki mana, ba shi ki ke so ba?” Hamda ta runtse idonta tana jin nauyin k’irjinta yana k’aruwa kada Fa Hammad ya ce zai ji haushin abinda ta masa ya saketa, da ina zata saka kanta bata jin zata iya rayuwa ba Hammad, daman duk kurari ne irin na y’ay’a mata, sak’onsa da ya shigo ne ya sake tarwatsa mata zuciya don tsananin bugun da take gumi gaba d’aya ya jik’eta ta shiga k’ara ware ido tana nazarin anya da gaske yake abinda ya rubuta…..
Jikar Nashe ce!
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Idan kin amince za ki zauna a kano shine muradina idan kuma ba haka ba, ki zab’i abinda ya yi miki saboda na lura don kin ga Daddynki ne ya bani gidajen ki ke neman yi min iko a kansu…” wannan ne sak’on da ya turo mata tsananin mamakin sak’on ya sa ta shiga ware ido tana nazarinsa ne Hammad yake nufi itace zata masa gorin gida shikkenan zata amince ta zauna a duk inda yake so, ta runtse idonta zuciyarta na wani irin zafi da gaske dama haka auren mai mata yake? Sai yarda matarsa ta juya shi. Sam bata san hawaye na sauka daga kwarmin idonta ba har sai da ta ji d’imunsu akan lab’b’anta jiki a sanyaye ta saka hannunta ta share hawayen haka kawai ta ji tana jin haushin aurenta da Hammad d’in tun yanzu har matsaloli sun fara samun mafaka. Shigowar Sa’ada ce ta sata tattaro nutsuwar dole ta saka a fuskarta don bata son kowa ya san sirrinta da mijinta. Sa’adan ma maze wa ta yi bata nemi ta ji ba musamman dama ita can haka take rayuwarta bata damu da sanin abinda ba - saka ta a ciki ba. “Kai Hamda lefenki ya yi Kurt ko y’ar