Showing 33001 words to 36000 words out of 107121 words

Chapter 12 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

6643

Daukan da Omar ya mata bai direta ko ina ba sai daya kaita har Palo sannan ya jefata a
kujera da karfi tare da shigewa room dinsa,
Sosai Iklas taji zafi yar kara ta saki ohhh tare da dafe hips dinta..ko juyowa baiyi ba bare ya
San me take ciki.
Lokacin da su Omar sukaje saloon daya daga cikin yaran Maman Omar tare da wani abokin
Omar tabbas suma sunga Omar sun fito daga saloon hannunsa rike da na wata kyakyawar
budurwa.

Lallai sunyi mamakin Omar ashe tafiyarsa yayi yana sheke ayarsa da mata,amma ake ta
nemansa ana cewa ya bata.
Abokin Omar wato Raj ya daukin alkawarin zuwa ya fadawa Maman Omar cewar sunga
Omar a saloon da mace.

Haj.Rahina ta dauki akwati da sauran abubuwan amfaninta kadan tare da Tara yaranta tayi
musu hudubar banza sannan ta bar gidan ta koma gidan babban yayansu da ke zaune a garin
Abuja shima.
Tasha fada wurin yayanta saboda yayanta Alhaji Magaji mutumin kirki ne sosai ya nunawa
Rahina kuskurenta amma Sam ko a jikinta sai ma kara kaimi da tayi wurin son daukan
fansa,kuma ta sa a ranta dole sai ta koma gidan Alhaji Mohd.

Tunda su Maman Omar suka dauki Alhj Mohd wato Baffa suka yi hospital dashi gado aka
basu bayan aune aune da bincike ya tabbatar yana dauke da ciwon hawan jini kuma ya masa
babban kamu,sosai ake kula dashi a hospital Mama ta tsaya tsayin daka wajen mijinta,ita ke
jinyar sa,su sadiya ma suna zuwa dubiya amma kullum idan sunje sai sunci mutuncin Mama
tare da habaici da zage zage.
Mama na mamakin wai ga mahaifinka a gadon asibiti rai a hannun Allah amma su sadiya
suna shirme Allah kyauta.

Sultan ma kullum yana kan hanyar dubiya,kuma shi ke kula da Baffa kasancewarsa likita
babba,abokan su Omar ma kungiya kungiya suke zuwa dubiya,kamar yau ma Raj yazo yana
dakin da aka kwantar da Baffa tare da wannan yaron me yiwa Maman Omar hidima duk wani
aike me nisa da wasu abubuwan wannan yaron wato Nura shi ke wa Mama kusan same age
suke da Omar.kuma Nura yana da dangantaka tsakaninsu da Raj.gasu frnds ne shi da Raj,shi
yasa suke yawan fita tare duk da cewa Raj me kudi ne,

Raj suna zaune kusa da Mama suna hira sama sama yayin da Sultan ke gyarawa Baffa
kwanciya,Raj ya kalli Mama hade da gyaran murya Mama akwai wata magana da nake son
fada miki,wato yau kwana uku kenan abin na damuna,gaba daya dakin Raj aka zubawa ido har
Baffa da ya samu sauki shima ba a barshi a baya ba, Naje kusa da saloon in da Nura mun karbi sako a hannun wani Mama wlh munga Omar ido
da ido ga Nura nan ki tambayeshi kiji,har kokonto mukayi sai da muka karasa har kusa dashi
amma kafin mu is a wajensa sun shiga mota sunyi mana nisa,kuma Mama abin mamaki Omar
da mace budurwa zankadediya muka ganshi rike da hannunta da wata yarinya zasuyi same
age da suleim dinki,

Sultan kuwa an zo wajen nan ya karbe zancen da cewa haba Ashe nima ba gizo idona ya
min ba don nima rannan tabbas naga Omar a garden kingdom sun fito shi da wata
charkwadediyar budurwa yarinya karama,Mama kamar yarinyar da ta kawo miki sakon envelop
da tace Omar ya bata,kuma kamar wata me tallan kwai a titi da Omar ke taimakawa, Daga Mama har Baffa Kansu ya kulle,to ko dama maganar Haj.Rahina gaskia ce da tace
Omar na gari sheke ayarsa yakeyi bin mata yakeyi,yaushe Omar ya zama haka,maybe zaman
London ne ya lalatashi ko kuma rashin samun kulawa daga wajen matarsa ne.
Gaba daya su Mama da Baffa sahar suka daurawa laifi sai kuma Omar da ya biyewa son
zuciya tare da zubar musu da tarbiyar gida da mutunci.

Baffa ransa ya kara baci da jin wannan magana,yasan Raj da Sultan baza suyiwa Omar

sharri ba,gaskia suka fada,lallai Omar ya bashi kunya zai kuma hadu da hukuncinsa duk ranar
da suka hadu.Mama kuwa harda kukan bakin ciki Omar ya watsa musu kasa a ido,amma ya za
tayi dole addua ce mafita,
Sosai su Sultan suka Shiga kwantarwa da su Baffa hankali tare da yi musu alkawarin nemo
Omar,dan sunce zasu sa ido sosai a kansa.zasu Dana masa tarkon da dole sai ya fada tare da
damke wannan tsinaniyar karuwar tasa wato Iklas.

Kwana biyu tsakani Baffan Omar har yau jiki yaki sauki sabida damuwa jinin yaki sauka
wahala yake sha wanda sai da su Sultan sukayi Dana sanin fada musu cewar sunga Omar.
Mama abin ya hade mata ga rashin lafiyar miji ga rashin Omar dinta tare da jin mugun
labarin yana neman mata.

Su Iklas anyi musu hutu daga Ta boko har islamiyya,sabo da haka Iklas ta rikewa business
dinta wuta yanzu ma tace sana'ar saida danyen kifi zata fara,kudin da ta samo gidan Maman
Omar su ta tattara kaf ta siyo katuwar freezer sabuwa dal ta ajiye a kitchen,saura kawai ta fara
saro kifi,duk tsare tsaren Iklas Omar bai sani ba, Dukkansu suna zaune a tsakar gida da yamma lis,Iklas na kwance a kan katuwar tabar ma
da wata Rigarta doguwa ta atamfa tayi kyau,Suhaila na kan cinyar Ummi kwance tana karanta
Arba'una hadith, Omar yana kan carpet gefe tare da laptop sai nunawa Ummi wakar shata me
ganga yakeyi,Ummi har gyada kai take tana Allahu akabar oh kaji mazan jiya,Allah sarki jiya ba
yau ba,Umaru danno min ta Ali makaho da Dan kwairo naji..daria yakewa Ummi ganin abu ba
wani Dandano amma Ummi dadinsa takeji ko dan azamaninsu ne akayi wakar,

Iklas littafinta ta dakko tana ta buga lissafin sana'ar kifi da zata fara domin gobe take sa ran
sarowa,juyowa tayi dan Allah Ummi a canja mana wakar zamani amma wannan mu bama
fahimtar me suke cewa,kaka Ummi dalla mata harara tayi aike ba hankali gareki ba amma ai
sune sukayi wakoki masu ma'ana,tabe baki Iklas tayi pls ya Omar kai mana wakar Timaya ko ta
Devido,
Ai kece Timayan see ur mouth anki a kunna miki manya na maga kina shiga ciki cewar
Omar,murmushi Iklas tayi cike da shagwaba ta ajiye littafin dake hannunta kajika ya Omar da
nawa ka girmeni,ai ko zaka girmen kadan ne,hmm na San da auren wuri nayi da tuni na haifi
kamarki,ummi ma tace fada mata Umaru in banda rashin kuya dudu shekararki nawa saboda
kinyi tsayin kafa,dadin abun dai a gaban Umaru kika fara Al'ada,ba wani iyayi da zakiyi masa
,kukan shagwaba Iklas ta fara haba Ummi wai mene haka dan Allah,kunya Iklas taji sosai,Omar
kuwa masu rayuwar London ko a kwalar rigarsa,saima kafe Iklas da yayi da kallo,idonta ta
dauke daga kallonsa a ranta tana kai Sir din nan dan duniya ne harda kallo na.
Su dama Maza munafukaine abinda suke so kenan dama taji frnds dinta suna fada a schl.

Washe gari da wuri Iklas ta saro kifinta Carton daya na gwajin kasuwa,Omar yana bacci bai
San Iklas ta fitaba,sai fitowa yayi yaga Iklas na shirya kifi a fridge Omar ya shiga kitchen din
dauko furarsa dagashi sai jallabiya fara me hula dai dai jikinsa gashi sabo da baya fita baya
shiga rana ya kara haske sosai skin dinsa har wani sheki takeyi, Kamshinsa ne ya bigi hancin Iklas a take jikinta ya mutu murus,kasala ta sakko mata,ta

gefenta ya raba zai wuce jikinsa ne ya gogi nata baisan sanda a hankali yace ushshsh shshi
sabo da wani irin yanayi daya tsinci kansa ciki.furar ya ebo a glass cup tare da zuka,ke me kike
yi haka,duk wannan kifin da wa zaki cinye?kallonsa Iklas tayi tare da murmushi tace au baka da
labari ai kifi zan fara siyarwa danye,da kudin da Baffa ya bani na kafa jarin,kaga sana'a goma
maganin me gasa,kaga kala kala nakeyi kenan,
Jinjina son kudi irin Na Iklas yayi a ransa,idanuwansa kyawawa masu matukar haske ya
zubawa Iklas Wanda yasa Iklas dimaucewa hade da jin kunya,sunkuyar da kai tayi ta tsinkayo
muryar Omar ba a nan gidan za ayi wannan sana'arba,baki isa ki cika mana gida da karni
ba,duk sana'ar da kikeyi bata isheki ba sai kinyi kalar wannan,haba mene aibun wannan sai da
kifin,ummi ma fa da kyar ta yarda wai bata so nayi,nidai ina son siyarwa sai nayi,

Tamke fuska yayi to baki isa ba,ba a gidan nan ba na fada miki idan kuma kinga ina wasa
dake kiyi na gani,da shagwaba tace pls Sir nasan in ka fada Ummi bayanka zata bi,ke kika sani
ni kam na gama magana ko ki je ki mayarwa Wanda kika siyo wajensu ko a cinye a gida,ko ki
bayar kyauta,tab lallai inyi asara ba riba,sai dai ka biyani kudin Dana kashe in kuna so na daina, Zare ido Omar yayi ina wasa dake,tsorata tayi ta fara bin bango tana rabewa hade da tafiya
kadan Kadan ta fice da gudu daga kitchen din tana ae na fada a biyani kudin Dana kashe tare
da kulewa dakinsu.

Daria Omar yayi sosai ya fita shima,washe gari da safe Omar ya fito da brush da toothpaste
zai shiga toilet sai ga Iklas ma ta fito tana kallon Omar ta wuce da sauri ta rigashi shigewa toilet
din.Ummi sakin baki tayi yau naga yar banzar yarinya,ke dan bantan ubanki fito Umaru ya
shiga,kyaleta Ummi zanyi maganinta,daki Ummi ta koma tana cewa kunfi kusa.
Iklas kuwa har ta fara brush Omar ya jawo rigarta kiiiiiii ya jefota waje,kafin ya rufe toilet di
Iklas ta kara bankawa ciki,murmushi Omar yayi oh..yanzu na gane me kikeso Ashe wanka kike
so na miki,damkota yayi kamar zai fara cire mata kaya tuni Iklas ta fara kuka tana Neman
agaji,da gudu ta fito daga toilet din,Omar ya rufe kofar tare da Jan tsaki karamar yar iska da kin
tsaya kin gani.
Iklas kuwa a ranta tace kut lallai Sir cikakken dan iskane.yau Iklas shiri tayi tsab domin zuwa
gidan su Omar so take ta dubo masa lafiyar su Mama,fito tayi Palo tare da yiwa su Ummi
sallama,da sauri Omar yace muje tare unguwar na kaiki,batayi musu ba ya kira a take aka kawo
wata new Car din.
Tofa kunji masu karatu.





Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR

GOMNATI
ⓂⓂⓂ

60-65

By
Asmahbaffa


MASOYANA READERS NA GAISHEKU,MASU COMMENT AKAN WANNAN NOVEL
ALLAH MUKU ALBARKA GABA DAYA INA GANIN SAKON KOWA.



Fafur Omar yaki yarda saima room dinsa daya shige ya bar Iklas waje tana tunanin
yanda zata bude kofar,hakura kawai tayi ta kyale Saleem a waje yana jira.tunda Saleem yaji
Iklas shuru shuru yasan bazai wuce wannan shedanin yayan nasu bane ya hanata fitowa
Tunda Omar suka bar su Baffa da salati cikinsu ba Wanda ya kara koda tari,Suna a haka
Sultan da Raj suka shigo,tambaya suka fara yi Lafiya sunga Mama ta rafka tagumi,da kyar
Baffa ya fadawa su Raj halin da ake ciki,suma sosai suka sha mamaki,
Sultan ne ya fara Baffa da kun sani Baku kori Omar ba,da kun barsu sunyi bayani,Omar
nasan baya abu ba reason,me yasa ba a fada min a waya ba nazo wajen,Mama kema kin
manta halayen Omar masu kyau,na tabbata zai wahala idan Omar zai iya aikata abinda muke
zargi,
Raj ma haka ya fada Baffa da Mama sai sukaji dama sun tariyo baya sun tsaya sun saurari
Omar,sun yanke hukunci cikin bacin rai,ta leko ta koma ga Omar amma sun koreshi,Baffa ne ya
dubi su Raj..Sultan yanzu mafita daya kusa ido a garin nan,da sauran abokan Ku da security
duk inda aka ga Omar a kawo minshi har gida,in yaki binsu a kawoshi ta karfi ko da igiya Ku
dauroshi a kawo min shi,
Aje a sanarwa mutane,nan take suka fara waya tare da hada connection,shima Baffa
haka,kwana 2 tsakani aka sallami Baffa,yana hutawa ya koma gidan su sahar wannan karan
sunci sa'a an lallaba iyayen sahar da sahar sun dawo da ita gidan Omar,sahar kuwa dama kudi
take so ta karba wajen Omar masu yawa tattalin arzikinta yayi kasa shi yasa ta yarda ta
dawo..yayinda da taci gaba da sheke duniyar ta.

Tana nan tana jiran ganin an dawo da Omar gida,bayan dawowar Sahar Baffa da yan
uwansa suka je bikon haj.rahina,sai murna su sadiya sukeyi,gogar kuwa dama ta samu rana ta
bude mata sai shanya,dama abinda take nema kenan Baffan su Omar ya lallaba ya dawo da ita.
Sultan dasu Raj da sauran mutanensu sun fara aikinsu ba ji ba gani,kullum basa zama
Neman Omar sukeyi ba dare ba rana,

Iklas ta gaji ta yanke shawarar sanarwa da Ummi abinda ke faruwa da Ya Omar,tausayinsa

takeji sosai gwara ta fada ko Allah zai sa a nemo masa magani,Omar kuwa kullum addua
yakeyi sosai akan matsalolinsa,
Yau Ummi ce ta dauko naman ganda ta jikashi a cikin ruwa a wani bowl,Omar ta mikawa da
soson karfe da wuka Umaru gyara wannan yau ganda nake son ci,ragadada zan bararraka
mana,Omar kuwa bin naman gandar yayi da kallo Ummi wannan tsohon abin tun na last year ai
ki bari a siyo mana fresh mana,yaushe za aci guba a ciki,kaga idan baza ku gyaramun ba to na
dauke abina ban son iyayin banza,ke uwar yan lissafin duniya matso kema ki tayashi Ku gyara
da sauri,yanzu in aka gyara wannan yaji hadi kamshi ne zai cika unguwar nan,murmushi Omar
ya saki Wanda ya janyo hankalin Iklas ta kafe Omar da ido tana kallon kyan da murmushi ke
masa,
Ummi nifa ban iya gyara abin nan ba cewar Omar tare da toshe hanci,sannu gayu mutanen
Allah Iklas matso ki koya masa kuyi maza.

Hand globe Omar ya nemo yasa a hannunsa wai kar hannunsa ya dauki warin naman,Iklas
kuwa tuni ta fara gyaran a garin yi ta fallatsowa Omar ruwan a fuskarsa ruwan ya sauka a
kumatun Omar,sorry cewar Iklas tare da ci gaba da dirzar gandarta,kyankyami ya kamashi
Omar ya fara wanke fuskarsa da ruwa bayan ya gama ya dawo yana wlh kika kara bata min jiki
sai na miki wanka da ruwan wanke naman gandar nan,

Baki Iklas ta tabe ya Omar dama shan ice cream ka kaimu shi nake sha'awa muje pls da
dare,harara ya watsa mata kin isa ma na kaiki daga nan ki kaini wajen su Baffa ko?haba dai ni
na isa da wanne idon zan kalli Mama cewar Iklas to shike nan zan kaiki ke da Suhaila amma
yau sai dare zamu fita,dadi Iklas taji sai washe baki take,kara fallatsawa Omar ruwan naman
tayi a farar T-shirt din dake jikinsa,
Haushi yaji kin kara bata ni da warin abin nan saboda kin rainani fuskarsa a daure ya dan
ebo ya shafawa Iklas a fuska sai daria take tana rokonsa ya bari,yatsunsa ne suka sauka kan
lips dinta wani taushi yaji tare da shagala wurin shafasu yana yawo da yatsansa kan lips
dinta,goce fuskarta tayi gaskia ya Omar baka kyauta min ba ,jiba face dina ta fada cike da
shagwaba kamar zatayi kuka,

Sannu yan mata ni da kika min har sau biyu fa,Ummi ce ta fito daga daki tare da kallon
bowl din taga ba abinda suka gyara kawai jagwalgwalo sukeyi musamman Omar ma,dauke
bowl dinta tayi tace kuje Ku karaci shashancinku,haba Ummi ki kawo mu karasa miki cewar
Omar,a'a kuje na yafe.
Cike da shagwaba Omar yace Ummi kalla rigata yanda jikarki tamini da ita gaskia ta tashi ta
wankemin abata,yanda Omar yayi shagwabar abin daria kamar yaron da aka yaye jiya,Sosai ya
bawa Ummi daria a ranta tana lallai Omar masu kudin gaskene naira da gata ya gama ratsa
jininsu.
Iklas kuwa bata San sanda ta kyalkyale da daria ba dan shagwabar Omar abun daria gashi
tayi mugun yi masa kyau,Omar kuwa ya manta Ummi ba Mama bace ga Iklas kusa zata
rainashi dan shi a zahirin gaskia bai San yayi bama don kallon Ummi yake kamar Mama.

Daure fuska Omar yayi tare da shigewa room dinsa,kayan jikinsa ya cire ya fito ya fada toilet
tare da sake feso sabon wanka kaji fa dan gayu readers,
Wasu kayan ya canja jean fari da wata tsadajjiyar T-shirt baka me rubutu fari an rubuta I do
what I want da many an baki,
Kallonsa Ummi tayi Umaru sarkin wanka ga iya shiga oh matarka tana shan kallo.murmushi
kadan yayi Ummi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login