Showing 3001 words to 6000 words out of 107121 words
Chapter 2 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
ita ko me aikin gomnati ta gani a titi to birgeta takeyi,ko ji tayi ma'aikata na labarin wajen aikinsu
to sai ta tsaya ta saurara.
In tana tuno aikin gomnati ita kadai zaka ga tana daria,idan kana so kaga dariarta ko jin
dadinta to ka mata adduar Allah sa ki zama ma'aikaciyar gomnati ko ta company,dan haka duk
layinsu in ta wuce ko abokanan tallanta zakaji ana gomnati gomnati wasu suce
ma'aikaciya,arnan ko gwarawa da marasa jin Hausa da suka Santa sai kaji suna kiranta the
manager.murmushi take musu sosai,
Indai kana so a nuna ma gidan su iklas to kace gidan su gomnati ko ma'aikaciya,ko gidansu
manager.
Ya halayen iklas sukene
Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
3
By
Asmabaffa
Readers kar Ku gaji da hakuri da typing error sometimes ba time na editing.tnx
IKLAS nutsatsiyar yarinya ce kamila,ga addini hankali da sanin ya kamata,ga kamun
kai,tsabta da son kwalliya,bata so ace taci baya sai gashi talauci yasa ta zama sai a
hankali,gata da kokari ita da suhaila,gaskia iyayensu sun iya tarbiya kuma Allah ya amsa
adduarsu ya basu yara nutsatsu,ga yarda da kaddara,Sam basu dau duniya da zafi ba.
Iklas bata da tsoro,tana da hakuri amma indai ka tsokaneta ko ka rainata to fa ba
mutunci,bata kyalewa,gata tana da surutu amma ba me yawa ba,itama akwai zucia,gata da
fara'a da mutunci da karrama dan Adam shi yasa kaf yankin da suke kowa ya Santa kuma ana
sonta maza da mata,komai nata a nutse,ita sam bata son raini,Suhaila ita bata fiye son surutu
da hayaniya ba. In dai kaje unguwar su iklas baka isa ka nunata da yatsa ba yanzu matasa yan
unguwar zasu hada ma jini da majina,shi yasa suke zaune gidansu lfy.
Ummi ma tana fitowa za kaga ana kwasar gaisuwa sabo da iklas ta siyo musu
mutunci.wannan ne asalin da tarihin iklas .
Ci gaban labari
Baffan su Omar ne ya kirashi a waya,Omar na daga wayar baffa ya fara fada haba Omar
kasan ina Russia na bar ma komai na business dina a hannunka ga iyalinka can na jiranka
amma ka tare a London kaki dawowa,bayan Kaine babba wa zai kula da harkata in ba kai
ba,kasan kannenka basu da hankalin da zan dorasu kan harkata,pls ka koma gida nan da
3days.cike da ladabi yace alright baffa insha'allah zan koma yanda kace,dadi baffa yaji that's
my son,yana son Omar sosai.
Omar kuwa nazari ya shiga yana tunanin yanda zai je ya hadu da mahaukaciyar matarsa
wacce take bata masa kullum wato sahar.amma ba yanda zaiyi dole yabi umarnin baffansa ya
koma Nigeria,
Yana cikin wannan tunani sahar ta mako masa kira,tsaki yayi hade da daga wayar dan
yasan kudi zata roka ko wani shirmen,ba ko gaisuwa kawai ya London tace sannan tace baby
wlh kudin da ka bani sun kare kuma gashi za muyi bikin wata yar wajen aikin mu,
A hankali yace yace OK zan miki transfer,yanzu ke sahar baza kiyi hankali ba,yanzu haka ake
kula da miji.ganinki kinyi dai dai,tunda na bar gida ko kirana bakiyi ba,kiji tsoron Allah sahar,kiyi
amfani da damarki kafin ta wuceki,kunkuni ta fara yanzu ya kake so na maka,kullum bani da
time fa busy nake,kasan aikin mu ba daga kafa,ke kullum Aiki aiki baki da wani abu sai aikin
gomnati.
To ni kaga karka dameni dan ka samu na kiraka,da bukatarki ta taso ba,ae hakkinkane ai
taja tsaki hade da kashe wayar.omar sarkin zucia har zucia ta kawoshi wuya,take idonsa ya
canja,sai bacin rai da huci yakeyi.
Mama ya kira a waya suka sha hira ta hadashi da kannensa suleim da abdullah sun sha
labari.yau ne ranar da omar zai dira a Nigeria,karfe 4:30pm mama,suleim da abdullah suka
dauko handsome daga airport,sai murna sukeyi cike da kasaita ya bisu suka wuce gidansu na
alfarma.tunda yaran hajia rahina wato umma sukaji labarin saukar Omar suka fara gulmace
gulmace,hassada da bakin ciki,ko wacce part dinta daban amma su umma wato rahina sun
dami rayuwarsu sabo da mugun halinsu.
Sadiya ce ta parker motarta kuuuuuuuu ta fito dawowarta daga wajen aiki kenan,direct part
dinsu ta wuce,duka yan matan kannen nata da umma suna zaune suna gulma da zage
zage,sadiya ma zama tayi dabar kasancewar ita ce ba,umma kice tsinanne ya dawo
kasar,Aisha tace na tsani yaya omar wlh waishi dole me kyau,me kudi,umma tace duk Ku
saurara shi din banza wlh sai nayi maganinsu gaba daya har uwar tasu,
Zainab tace wlh umma karki daga musu kafa,naja tace har mu zai nunawa kudi aikin banza
wai wannan sahar din matarsa har ta isa ta ganni tamin kallon banza,yanda take ji ita me kudi
ce muma haka,domin aikin gomnati ne muma shi mukeyi,
Sadiya tace hmmm umma zatayi maganin ogan nasu ai,haka suka kai har dare suna zage
zage,a karshe suka yanke zasu je masa sannu da zuwa don sugano kwakwaf,
Ita kuwa baiwar Allah mama tasa danta gaba yaci ya koshi dan tasan matarsa ba matar kirki
bace,addua take Allah masa canjin alkhairi,amma ita kam wulakancin sahar ya isheta,nasiha ta
masa sosai tare da Jan kunne wajen dagewa da addini,sannan ta turashi kan dole yaje ya gaida
hajiya rahina umma,
Badan yaso ba bayan sallar isha ya isa part din,da zuwansa ya gansu a Palo rida rida a kwance
ko wacce na latsa waya,umma na gefe,suna ganinsa dukkansu gabansu sai daya fadi dan
mugun tsoronsa sukeyi,ga kwar jini da yake musu, Sam baya musu ko murmushi,dama duk
zaginsu a bayan ido sukeyi,risunawa yayi ya gaida umma,da kyar ta amsa tana masa kallon
harara,su kuwa yan matan kowacce yaya sannu da zuwa ka dawo lfy,lfy kawai yace ya
ficewarsa cike da kasaita
Yana fita suka dasa gulmarsu kunga maye yanda ya kara kyau ga iya daukan wanka,ko
wanne kaya yasa kyau suke masa.wurin mama ya wuce ya roketa kan ta barshi ya kwana gobe
sai ya tafi gidansa,kyaleshi tayi dan tasan matarsa ba kula take dashi ba,
Suleim tana manne a jikinsa sai bacci takeyi,washe gari da safe uban yan daukan wanka
omar sakkowa yayi daga sama yana zuba kamshi,sanye yake da wani yadi fari Sol ya matukar
masa kyau,hattana takalminsa fari ne,ba hula a kansa sai gashi kwance luf.sallama yawa mum
bayan ya cika tumbinsa ya basu tsaraba,wucewa yayi gidansa dake zone 11princess suit,gidan
ya tsaru,
Driver ne ke tukashi har gidansa,tun daga compound yake jiyo hayaniya sama sama,a nutse
ya shiga palon da sallama,frnds din sahar ya hango arna da musulmai maza da mata suna jin
kida hade da hira,ga kayan ciye ciye nan,
Ran omar ne yayi mugun baci suna masa magana amma ko kallon su baiyi ba ya wuce room
dinsa,ita kuwa sahar baki ta tabe hade da Jan tsaki,
Saida wata kawarta zuby tace sahar kije wajen mijinki kinga kamar ransa ya baci,tsaki sahar
ta ja to sai me yanzu akansa zaku tafi haba mana frnds,next time zamu dawo yanzu kije wajen
mijinki cewar wani saleem abokin aikinsu,bata so ba suka tafi ,yar aikinta ta bugawa tsawa kan
tazo ta gyara wajen,direct dakin Omar ta nufa tana cika tana batsewa,sanye sahar take da
T-shirt baka da skert din atamfa sun kamata kam,kanta ko dan kwali babu,
Tana shiga ta ganshi kwance kan gado yana latsa waya,baki ta turo ta kare masa kallo
gaskia mijinta me kyau ne,ga iya wanka,a nan take sha'awar Omar ta motsa mata ba abinda
takeso sama da ya biyaa mata bukatarta,gashi tasan fushi yake yi yanzu bare ya mata abinda
take so,
A gefen gadon ta zauna sannu da zuwa baby ya hanya?tunda yaji haka yasan tabbas
sahar wani abun take so ya mata,dan bata aikin banza sai da dalili,ko kallonta baiyi
ba,sha'awace ta kuma lullubeta tace baby kayi hakuri nasan na ma laifi,kallonta Omar yayi
tabbas yasan da dalili,sahar baza ta taba bashi hakuri ba tare da kudirin wani abu ba,a hankali
yace ya wuce,in mutum yayi da kyau shima ya sani in ya bata ma ya sani,kisani ke baki isa ki
sani bacin rai ba,Wanda ka damu dashi shi ne in ya bata ma rai kake damua,sahar taji haushin
kalamansa amma sabo da tana neman wani abu tayi shuru ta kara cewa am sorry hade da
hayewa kan bed din,yana kallonta ya gano me take nema,sha'awa ya hango zalla a
idonta,kwancia tayi a kirjinsa,dan sahar ita bata da kunya ko kadan.
Shafashi ta fara tana wani shagwaba,babyna I missed u alot,tabe baki yayi yana kallonta ta
fara cire masa Riga,baya son ya wulakantata,kuma yasan hakkinta a kansa musamman da ya
tafi London ya Dade bai dawo ba,sabo da wannan dalilin ya biye mata yayi manage ya
biyamata bukatarta,sahar tana jinta zam zam dan Omar gwarzon maza ne ya tsaya ya biya
mata bukatarta sosai taji dadi har jinjina iya sex na Omar takeyi,guy ya hadu ta fannin romance
da sex,ni kuwa nace danma ba zabinsa bace ke,bashi da feeling akanki.
Sahar tana jin zam zam ta mike tayi ficewarta,shi kuwa Omar baiji wani dadinta da yawa ba
dan sahar ko dan gyaran da mata keyi na shan tsumi bata yi Sam,ita fa indai ba aikin gomnati
ba to bata ganewa komai.washe gari Omar ya shirya tsab cikin suit baka yayi kyau yana baza
kamshi ya sakko cike da takama da kasaita,dakin sahar ya shiga tunda ya tashi bai ganta a bed
dinsa ba,room dinta ma wayam bata nan,Palo ya zo ba kowa sai hindatu me aikinta,ina sahar
take cewar Omar,har kasa hindatu ta duka ta gaisheshi da sakin fuska ya amsa,yanlabai ta tafi
wajen aiki tun 6am wai tana da tiyata,
Tsaki yaja ya fice gaba daya daga gidan ko dining bai kalla ba,yana mamakin yanda sahar ta
rainashi ace matarka ta fita ko fada ma baza tayi ba,tsaki yaja hade da ci gaba da karanta
jaridarsa yayinda ya kame a bayan wata luntsumemiyar motarsa Wanda takai milyan 40,driver
ke gaba yana tukashi,shi Omar Sam bai damu da driving ba yafi so a tukashi kaji manya fa
readers.
Hadadden gidansu yace a kaishi direct wajen mama ya nufa,a Palo ya sameta tana turaren
wuta rungumeta yayi hade da gaisar da ita,mama kintashi lfy?lfy babanmu ya gida,great
mama,to alhmdllh.mama breakfast fa?juyowa tayi da alamar tambaya gidanka ba a baka ba,wlh
mama kin San dai komai,yan aiki keyi ni kuma kin San bana son kazanta,kuma yau mama
inaso naje na duba gidan gonarki da kike kiwon kaji,kinga an Dade ba a duba ma'aikatanba da
sauran abubuwa,murmushi tayi yawwa babana Allah maka albarka,da har na yanke shawarar
zuwa da kaina,haba mama da raina da lafiyata na barki ki wahala.to Allah maka albarka.su
abdallah suna schl ae ai ka sani.OK.
Haj amina tana da shahararren gidan kiwon kaji dake wajen garin abuja,baffan su Omar ne
ya gina mata ya bata kyauta ganin haj rahina na aikin gomnati shi yasa ya bata wannan kyauta.
Haj rahina umma ta tafka bala'i akan wannan kyautar ta baffa,haka ta hakura.
abinci yaci ya koshi yawa mama sallama ya wuce office,karfe 2pm ya bar office ya wuce
gidan kajin mama.
Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
4
By
Asmabaffa
1:30pm iklas ta shigo gida ta dawo daga tallanta,domin schl din da ta koma 8to12 ce ta irin
manyan mutane ce Wanda basuyi karatu da wuri ba,irinta ta koma sabo da tallan da take zuwa
domin da shi suka dogara,dan haka 12 tana dawowa zata tafi talla kan titin kwalta,1-1:30pm ta
dawo,tana cin abinci zata shirya ta tafi saro apple da egg,tana dawowa sannan suhaila ta dawo
sai su shirya su tafi islamiyya,Saturday Sunday kuwa da safe take zuwa talla zuwa 3 to 4pm ta
dawo,haka take rayuwa kullum ba Hutu,gashi watarana har girkin gida ummi take sata dan bata
so iklas tayi aure bata iya girki da sauran ayyuka ba,dan haka take sata dole,shi yasa ta iya
komai dama gata jaruma,
Wanka tayi ta shirya cikin wata yar rigarta doguwa itama wata Igbo ce ta bata ita,light blue ce
me ratsin ja ja da digo digon baki,daga sama ta dan matseta kasa ta bude amma itama da
kadan ta wuce gwiwarta,basu da kayan kirki,dan ma waiyayenamure na taimakawa su basu
kayan da suka musu kadan,wasu kuma har sabo suke basu,ita ma suhaila tana samun na
yaransu,wasu kuma iklas na kokarin sai musu gwanjo,shi yasa kusan kayansu gaba daya
English wears ne,tsangalallu ne badan suna sa dankwali ba sai ka dauka arnane suma saboda
rashin wadata.to daya suke samun na ci ma.
Bakin gyale siriri ta yana kanta,batayi kwalliya ba powder ta shafa kawai sai Vaseline da ta
shafa a lips dinta,tayi kyau dama me kyau ko ba kwalliya me kyau ne,wani takalmin roba me
igiya baki ta saka,shima wani ne da yake siyarwa ya bata kyautarsa yaga tana da hankali,ga
babu ta zauna musu.tayi kyau sosai a nutse ta dauki botikin saro kwai da ledar siyo apple ta
yiwa ummi sallama ta wuce,a kofar gida suka hadu da suhaila ta dawo daga schl,anty har kin
shirya?yeah iklas ki jirani muje tare mana,no je kici abinci ki huta ki shirya zuwa islamiyya kafin
na dawo OK.OK anty sai kin dawo,Allah tsare shafa kanta tayi ameen suhaila,tana matukar
kaunar kanwarta.
Tafiya tayi da dan nisa ta isa gidan kaji domin siyo kwai da apple,mutane da motoci birjik
sunzo sarin kwai da apple suma,gaskia kowa ya kalli gidan gonar yasan an kashe dukiya,part
part ne wurin kaji da kwai daban,part din fruits daban,kifi daban,ga sauran tsuntsaye da
abubuwa kala kala.
Da araha suke bada sarin shi yasa ake cika gidan gonar,shi yasa iklas ke saro nata can dan
ba karamin riba take ci ba,ratsa ciki tayi ta shige,ma'aikatan ciki sai fara'a suke mata suna
gaisawa,dan sun saba da ita,gashi sun karanci nutsatsiya ce me mutunci da kamin kai,suna
tausaya mata mace kamar ta tana sa'a irin wannan,da gani suna cikin talauci,shi yasa suke
Mata arha fiye da kowa.
Tana tsaye tana jiran a sallami Wanda suka rigata, wata arniyar mota ta shigo cikin
wurin,kowa bin motar yake da kallo,babu Wanda ya taba ganin kalar motar,har jira ake aga
waye me motar,
Ita kanta iklas duk tsaiwarta a titi bata taba ganin mota irin wannan ba,su kuwa ma'aikatan
gidan sun San bazai wuce Omar ko mama ba.sun San irin wannan babbar harka sai iyayen
gidansu Wanda suke jin dadin aiki karkashinsu,shi kuwa Omar tun shigowarsu kansa na kasa
yana duba jarida,driver ne ya fito da sauri ya bude masa kofa,subhanallah shine abinda iklas ta
furta a ranta ganin takalmi da kafafuwan Wanda ke fitowa,
Basu gama sumewa ba sai da Omar ya fito gaba dayansa daga mota,wani daddadan
kamshi ne ya mamayesu gaba daya,iklas tana kallonsa gabanta ya fadi ji kake daram
dam,sunga zallar baiwar kyau da kwarjini da cikar zati,iklas tace tab yau ga Wanda ya takeni a
kyau,ido ta lumshe hade da bude kafafen hanci tana shakar ni'imantaccen kamshin Omar, shi
kuwa Omar iklas ya fara hangowa da tsangalalliyar rigarta,kasancewar fara ce kar sai ta haske
gidan. Gonar gaba daya,kallo daya ya watsa mata shima gabansa yayi mugun bugawa,bai taba
ganin dan Adam me kyanta ba,duk kyansa sai yaga ga wata yarinya ta fishi,shi bai taba jin
faduwar gaba ba sai akan wannan tatsitsiyar yarinya,
Fuska ya yatsina kamar yaga kashi yayi mata kallon kaskanci ya wuce ta gabanta,da
mutanen wajen maza ya gaisa ya mika musu hannu,sannan suka dan kebe da babban me kula
da wajen suna magana.
Iklas kuwa ta cika fam sabo da irin kallon banzan da ya mata,bata son raini,dan suna
talakawa shine zai yatsina mata fuska,hmm duniyace a ranta take wannan magana,ana haka
har akazo wajenta aka cika mata botikinta ta mika kudi,lokacin Omar ya gama da wajen kwai ya
wuce wajen fruits,da kyar take daga bokitin ta karasa wajen fruits itama ta mika kudi aka cika
mata katuwar ledarta da apple,ta juya zata wuce sukayi karo da da botikin kwanta tayi karo da
mutum gwaraf,amma batafi saman cikinsa ba,botikin kwai ya tuntsire wajen guda ashirin sun
fashe,shi kuwa take yaji wani mugun shock a jikinsa zirrrrrrrrrrr wanda bai taba ji ba,sakamakon
haduwar jikinsu,daurewa yayi ya dawo hankalinsa,tsaki yaja ya furta psycho kawai,haushi ta
karaji ya mata abu