Showing 57001 words to 60000 words out of 107121 words

Chapter 20 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

6648

a gadon a hankali murya dashe ya furta
calm down bazan take dokar Allah ba,ba abinda zan miki.

Hawaye Iklas takeyi itafa za ayi mata ciki bata fara aikin Gomnati ba,Omar ganin tana kuka

ya fara lallashinta yana shafa gadon bayanta tare da mannata a kirjinsa,a nutse yace mene kika
kuka?

Narkewa ta karayi tana shesheka haka kawai... zaka.... min... ciki ban....fara....aikin... Gomnati
ba,subhanallah Iklas kefa ba matata bace taya zan miki ciki,hannunki ma da na ke rikewa ba a
son raina bane kema kin sani,
Da Sahar kika ce ma zanwa ciki sai na yarda tunda ita matatace,kishi da bacin rai mai yawa
Iklas ta tsinci kanta ciki kwace jikinta tayi cike da masifa fuuuu ta sauka kasa kan shimfidarta
tana kunkuni sai kaje wajen Sahar din ai.

Maganar duniya Omar yayiwa Iklas amma taki amsawa,wayarsa ya dauka ya tura mata text,
lallai zaki rasa aikin Gomnati yarinya,da Saudi ta masa reply cike da
masifa tace na rasa mana aikin Gomnatin me,basai nayi business ba,
Wa zai baki jari to?
me sona Wanda nake so
waye shi? Bazan fada ba nima,ni kadai basan kayana
,tsaki Omar yaja.

Sannan ya gyara kwanciyarsa ya ajiye wayar ko me ya tuna oho kiran Iklas yayi a waya duk
da cewar dakinsu daya suna tare tunda taki magana a fili.
Da sauri ta dauki wayar kamar ba room daya suke ba,
Hlo? Mene kuma cewar Iklas,kiyi magana that's what want dit ya kaashe wayar,tare da leko
da Kansa ta kasan bed din,kamar an mintsineta tace ya Omar a saitin fuskarsa,na'am ya akayi
kaje dani Office dinka na dinga tayaka aiki sai ka koya min,bazanje dake ba kefa kikace baza
kiyi aikin ba,wasa nake ma Allah ko dan danani kayi na hau kujerarka me jujjuyawar nan,
Ko signing sai namaka pls,komawa yayi ya kwanta yace sleep joo kin dameni,da kyar Omar
ya samu yin bacci sabo da sha'awar Iklas, Iklas kuwa kusan kwana tayi tana tuna kiss din da
sukayi da Omar,da yanda ya mirzata.

Sultan da Raj tare da sauran wasu frnds. Din Omar ne suka zo da yamma,sai hira sukesha
na bikin sultan da za ayi nan da 1wk,
Karar Iklas suka jiyo daga compound wurin garden,Omar ya Riga kowa fita waje,su najja da
Aisha ya gani sunwa Iklas taron dangi suna dukanta,daga nan suka dauketa suka jefa cikin
swimming pool dake wajen ji kake tamjam.

Cikinsu babu Wanda yasan Omar ya zo wajen,Iklas da yake jaruma ce tuni ta fito da kanta
daga ruwan,hannun najja ya cafke Dana Aisha ya had a wuri daya,igiya ya samu ya hadesu a
jikin bishiya ya dauresu tam ya zare belt ya fara laftarsu ba ji ba gani sai da ya farfasa musu
jiki,dakyar su Sultan suka rike Omar,Iklas kuwa gwalo take musu tana kwalawa da karfi wlh sai
ya Omar,kara musu,yawwa a kara musu,idan taga sun Sosa wajen sai ta fara Ce musu asosa
mata asosa,
Su Sultan har daria Iklas ta basu,Umma Rahina ce tazo kamar zata cire bakinta sabo da

masifa zagin Omar da frnds dinsa take ta uwa ta uba, tare da shako wuyan Iklas Omar ne ya
fincike Iklas daga hannun Umma gaba daya suka bar wajen,
Kwance yaranta tayi ta jasu suna ta kuka ba ji ba gani.

Wajen Baffa ta wuce ta tarar bayanan,waya ta maka masa yana dagawa ta dinga zazzaga
bala'i,ki bari na dawo sai nasan abinda zanyi ya kashe wayar,gaba daya Rahina ta hana
gidansa zaman lfy.

Baffa yana dawowa ya kira Omar ya sanar masa komai Baffah nan ya watsar da zance bai
kara saurarar Haj Rahina ba.haushi kamar su mutu Mama kuwa kallonsu kawai takeyi

Omar ya warke sosai ko munanan mafarkanma ya daina yau bikin Sultan Saura 2days
gashi Baban Yasmin budurwar Sultan ya hana party da sauran shagali,walima da daurin aure
kawai sai kai Amarya, Omar ba zama
Iklas duk ta shiga damuwa bata ganin Omar ,gashi 2days ita kadai take kwana a room din,duk
sai taji kewarsa,shima Omar dan kawai Sultan ne ya zame masa dole.da bazai iya zama ba tare
da Iklas na kusa dashi ba.

Anje daurin aure sun dawo angama walima da komai yan mata da samari cike taf a side din
Sultan wasu da matansu suka zo ga wasu dangin su Sultan yan mata birjik,sai shishigi sukewa
Omar Wanda a wajen Omar ko kallo basu isheshi ba tunanin Iklas yakeyi.
Iklas tana zaune tayi tagumi da waya a hannunta,tunaninta daya kar Omar yaga wata
budurwar ya kyasa,ko abinci ta kasa ci su Ummi sunyi sunyi har sun kyaleta.

Kara wayarta tayi alamar kira ya shigo, Sweet Omar ya bayyana akan screen dinta,da sauri
ta daga kafin tayi magana yace ki shirya kisa driver kice ya kawoki gidan su Sultan kiyi sauri
fa...OK tace tare da fadawa toilet wanka tayi tasan gidan biki ne dan haka ta zauna ta tsantsara
kwalliya wata doguwar rigar lace tasa light blue da baki rigar daga sama ta dame kasa kuma
tayi tirgija kamar amarya bata daura dankwali ba siririn gyale baki da jaka da takalmi bakake
tasa takalmin me dan tudu tayi kyau sosai abinka ga farar fata.
Mama da Ummi tayiwa sallama ta fita kanta tayi acuci maza tayi kyau,kowa ya ganta sai ya
kyasa,driver har gidan su Sultan ya kaita ya juya,cike da cat walking dinta ta taka har ciki,kowa
sai kallonta akeyi wasu ma kamshinta ne ya jawo hankalinsu Omar yana saman bene yana
kallonta,nan take yaji kishi dama bai ce tazo ba daurewa yayi ya danne zuciyarsa,
Raj ne ya mata iso har wajen Maman Sultan ta mata Allah sanya alkhairi,sannan ya kawota
Palon da Omar yake,maza ta gani damkam wasu da matansu,ido aka zuba mata kunya ta
kamata,kafin tayi magana Omar ya dallawa Raj harara an kawo Iklas wajen maza za a kalleta,
daria Raj yayi yace a to mu mene namu ciki.
Tsaki Omar yayi ya riko hannun Iklas suka shige wani bed room.sai daria mazan keyi sunawa
Omar tsiya,kowa da abinda yake cewa.

Asmabaffa

ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

120-125


By
Asmabaffa




Dakin Ummi ta shiga da sauri,Hajiya lafiya kuwa gani nazo.
Da mamaki Mama ta bambaya wa yace ina kiranki? Iklas ce ta shigo ta sanar dani babban
al'amarine,daria Mama tayi oh yayan zamani nan ta labartawa Ummi yanda kan maganar take,
Wannan ko shashar yarinya cewar Ummi, Mama tace naga yaran nan son junansu sukeyi
sosai Babana ma yace a aura masa ita,idan yazo wajenki kice ya nemi soyayya wajen
Iklas,idan muka ga ko mai ya dai daita sai a bashi matarsa.na sanarwa Baffansu ma komai
shima ya yarda da shawarata, An godefa Allah saka ya tabbatar mana da Alkhairi cewar Ummi,Mama tace ameen ameen.
Haka kuwa akayi Omar takanas ya samu Ummi ya sanar mata yana son Iklas ta bashi ita,ce
masa tayi ya nemi soyayya wajen Iklas in tana sonsa ta bashi ita sai biki.godiya Omar yayi,yana
ta tunanin ya zai yi ya fadawa Iklas yana sonta
Kar taki karbarsa yaji kunya amma bari dai zuwa nan gaba zaiyi shahada ya furta.

Bikin su sadiya saura 3days Mama ma takanas take sa driver yana kai Iklas wajen me
gyaran jiki daga nan har ranar da za a bawa Omar ita,tana zuwa schl idan ta dawo driver ke
kaita,tayi kyau ta kara mirjewa da cikowa,skin dinta sai kyalli takeyi,
Omar mamaki yakeyi yanda Iklas ke ta canjawa,in ya tambaya ina ake kaita sai suce
Islamiyya take zuwa.

Kayan gyara kala kala Mama da Ummi ke ba Iklas tana amfani dasu,da yake Iklas tasan kan
gari shanyewa takeyi,har nata take hadawa kanta da fruits.
Mama tayiwa Ummi da Iklas dinkunan ankon gidan kaf,har wasu ta dinkawa Ummi,Omar
kuwa duk dinkin da yayi iri daya Dana Iklas,wasu kuma color ne iri daya,idan ya dinka mata
material golden color to shima yadinsa ko shaddar ko suit etc irin same color da nata,
Akwati guda ya kawo dakin Ummi kayan bikin su Sadiya na Iklas,takalma jaka da gyale duk
ya hada,har jelweries ma.Ummi ma ya dinka mata wasu kalar masu tsada kala Uku.

Iklas sai murna zata nuna wa su Sadiya ba a ja da ita,dan haka ta dage sai shirye shirye
takeyi,tace duk sai ta kere su a daukan wanka kuma dole ne ma tana motar Omar zata kame a
gaba taga me kallonsa.
Bangaren su Sadiya kuwa suna ta shirya karya,sai sunyi bikin da yafi na yar shugaban
kasa,Umma ta sakar musu kudin salary dinta da Wanda tayiwa Baffa cuwa cuwa,suma yaran
nata haka,sai tatse angwaye sukeyi,
Sai da suka shirya event sunfi 8,ko wanne a tsantsararren waje me tsada.anko kuwa
yawansu ya baci,Baffa ya musu kayan daki na bugawa a jarida,duk abinda ya kamata an
gamashi na biki,omar gudunmuwar 5million ya bawa amare suyi amfani dashi,tabe baki sukayi
suka dinga zage zage an kwashi kudin Ubansu an musu kyauta dashi dan ace shi me kudi
ne,yana sace musu gadon ubansu baza su yafe ba.

Omar yaji komai amma ya toshe kunnensa ya sharesu,dan kawai a zauna lfy, saboda suyi
was kawayensu karya su nuna yayansu me kyau ne hadadde na nunawa sa'a zasu nunawa
frnds dinsu yayansu dan gayu me kyau ne,wannan dalilin yasa suka kawowa su Mama nasu
pass card dinsu,kuma Haj Rahina tana tsoro kar fa bata yashi dukiyar Baffa ba ya saketa akan
tambadadde Omar.amma da badan wannan dalilin ba bikinma sai dai su Mama suji anayi.
Amare ba Hutu shi yasa Iklas ta samu sakewa,ba duka ba zagi bare bakar magana,amma
da badan haka ba ita kanta tasan da tuni taci wani dukan.
Omar yana zuwa office sosai shi yasa bai cika samun time ba,Iklas kuwa sai schl da kuma
gyaran jiki,haka kullum HAJ MERO LALLAUSA me gyaran jiki ta gama tangarar da Iklas wajen
koya mata dabarun zaman aure da kula da miji ba kunya.
Iklas har tambayoyi takeyi wai duk dan ta kwacewa Sahar miji.burinta taga Omar bai son
kowa,baya kula kowa sai Ita babbar fadar Gomnati take son kafawa a zuciyar Omar.
Omar kuwa son Iklas da kaunarta sun hana masa sakat,kullum cikin kallon pics dinta
yake,idan kaga Omar yasa headphone yana jin kida to za kaga yana latsa waya Wanda ba
komai yake ba face kallon pics din Iklas yana tuna shirmenta da abin dariarta da sexy body
shape dinta,yana jin shauki da nishadi.shi kadai zaka ga yana murmushi kamar Wanda yazo
daga zazzau zaria. Lol.

Iklas Gomnati kuwa yanzu akan ta dauki jotter tana rubuta plan gwara tasa kida me dadi
tana tunanin gata ga ya Omar suna ta zuba love,watarana in tanajin kidan har hangosu takeyi a
wata arniyar mota sun fito ga kida na tashi ana ta kallonsu,ko ta gansu a shegen restaurant sun
gama cin abinci yana ta kissing dinta a gaban mutane,saboda tsabar sonta da yakeyi baya iya
boyewa a gaban uban kowa.ko ta hangota taci kwalliya ta gama hadewa Omar na ta kallonta da
mugun so da sha'awa amma tana masa yanga.
Watarana kuma in tana jin kidan sai ta gansu a gidansu na aure, suna girki,ko tana shiryashi
ta masa wanka etc.

Kai watarana kuma da cikin Omar take hangota yana lallabata,shi yasa take kasa tsinana
komai sai tunanin Omar,yanzu gani take ma ganin Omar kawai ma yafiye mata Aikin
Gomnatinta kai schl dinma gaba daya gani takeyi an cuceta an hanata ganin Omar akan

lokaci,gwara ma ta dunga rakashi Office yana kusa da ita.

Ana gobe za a fara shagalin bikinsu Aisha,Gomnati tana dawowa daga schl ko abinci kin ci
tayi kamar bikin kanin ubanta ta dauki hanyar fita ita da driver karo sukayi da Omar ya dawo
dauke da ledar oasis a hannunsa,
Labewa tayi a bayan labile,jawota yayi gabansa baki da gaskia tunda naga haka kikewa su
Mama in kinyi laifi,na ganki da hijab ina zakije,tsadajjen agogon hannunsa ya kalla yanzu kika
dawo daga schl fa,
Har zaki kara fita,kuma time din Islamiyyar taki baiyi ba ai,da Sauri tace na dauki Hutu sai an
gama biki zan koma.

Kallonta Omar yayi lalai zakici duka,a gida ma sun zaneki inaga kinje musu biki,kiyi zamanki
yafiye miki, naga ma ko abinci baki ci ba, na koshi ni lallen biki zanje ayi min da gyaran gashi,
hmm duk wannan zumudin da wa zakije?da saleem mana aikin da Mama ta bashi har yayi kudi
ya siyi mota fa. Lallai to ki fada masa kar ya sake yaje bikin kannena bama nemansa.look at u wai kannenka
bayan tsine ma sukeyi,rannan ma akanka suka murdemin yatsu,
To amma zakije bikinsu?ae ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar,ya zanyi na hadu da
jininsu ai danginane nima.ban gane ba cewar Omar, saurayi nayi dan uwan ummansu fa.
Kaga sun zama dangina,jikin Omar yayi sanyi gani yayi kamar da gaskene zancen Iklas,in
kuwa hakane to lallai watan mutuwarsa ya kama.

Ita kam Iklas a kan Omar tayi magana tunda su Sadiya wai sun zama dangin mijinta, kuma
so takeyi kishin Omar yayi tsanani har yace mata shi yake sonta don har yau tana tuna
maganar Inusa me wanki yace Omar sonta yake.
Damuwa dankare a zuciyar Omar a fili kuwa snacks da yazo dasu ya dauki daya ya budewa
Iklas a tsaye bakin kofa ya dinga bata a baki tana ci aranta tana wlh maganar Inusa me wanki
gaskia ce,in ba me Sonka ba wa zai kula da kaci ko baka ci ba,a gaskia zanji dadina a gidan
Omar. Sai lumshe ido takeyi tana lamushe snack,
Shi kuwa Omar yanda take lumshe idon ne ke birgeshi sai kalle mata fuska yakeyi da pink
lips dinta,

A haka ya dinga bata har ta koshi ya bata lemo da ruwa a hannunta tare da zaro kudi ya
mika mata kiyi me kyau kuma idan naga batayi kyau ba sai sun goge miki ita.
Daria Gomnati tayi ta wuce tana masa bye bye,wajen Mama Omar ya koma shi asan yanda
za ayi dashi a aura masa Iklas,Mama tace sai ta yarda kaje wajen Iklas.haushi yaji ya ficewarsa
zasu karasa rabawa frnds IV na biki shi da Sultan,

Baffa ma yana gari ya gama kawai ranar Sunday yake jira tazo a daura aure,tuni an masa
waya kan ya koma Russia ana nemansa a office aiki yayi yawa.

Baban Sahar har gida ya samu baffa kan Omar ya maida Sahar dakinta tayi nadama zata

koma,Baffa yasan karya ne ba wani hali da zata canja Indai Sahar ce,amma idan an gama biki
zai shawarci Omar yaji,idan yanaa so ta koma sai a kai masa Iklas itama gidan su zauna gaba
daya.

Iklas bata dawo gida ba sai wurin 11 na dare suka dawo da driver, tasha gyaran gashi da
lalle.
Ummi tace ke kuwa yar nan kamar kin tafi lallen Shiga Aljanna wannan dadewa,Ummi bafa
ni kadai bace wajen,kingani tayi kyau?masha Allah ta Umaru tayi kyau,nasan sai ya bada tukuci
daria Iklas ta kyalkyale da ita na jin dadi ta shige wanka.

Saida ta fito daga wanka ta duba wayarta missed calls din Omar ta gani da yawa,ga text
birjik yayo mata kan ta dawo gida dare yayi.
Reply tayi so sorry na sata a silent banji kiranka ba,na dawo tuni.Omar yana bacci sai da safe
ya gani,Iklas har makarantar boko ta dauki Hutu sai an gama biki.

Gida yayi gida,bangaren su Umma a cika sosai da yan uwa da abokan arziki masu
kwana,kawayen amare makil sashensu daban,bangaren su Mama ta gayyato yan uwanta suma
na nesa sunzo da yawa zasu kwana,har a gama biki,Iklas hayaniya ta dameta ta gaji dan haka
gani su Ummi na hada hadar biki basu San me takeyi ba kusan gaba daya a part din Omar
takeyin komai ko yana nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login