Showing 12001 words to 15000 words out of 107121 words
Chapter 5 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
magribaba,ban yarda
ba duniya ta lalace.mutane ba tsoron allah ne dasu,suje su lalata minke,a jawo mana
masifa,dan yanzu da kike ganinki karama sai samu matsala.ba musu tace to ummi nifa tunda
na dan Tara na abinci zanyi hutun 1wk bazanje tallaba.
Ina ruwana da in na ce ki huta ai kin yarda kikeyi Yanzu gashi ai kin bi shawarata.kwantawa
tayi jikin ummi tsohuwa zaki ci girki me dadi na zamani har na 1wk.daria ummi tayi oh ni jikar
luba ta kaiwa iklas rankwashi.
Omar kuwa birgeshi sukeyi,baren ma acting iklas tana abu kamar namiji magidanci,ga iya
planning rayuwa,kai Wanda ya aureta yaji dadi,ga yanda take kula da kanwarta.ummi ce ta
katse masa tunani da umaru kayi shuru,ba komai ummi ni zan tafi sai wataran,to har zaka tafi
mun gode Allah saka da alkhairi,mun gode kwarai da kulawarka,hannun suhaila ya rike zo ki
rakani beautyn anty.dadi suhaila taji dan gayu yace mata beautyn anty.
Har mota sukaje da suhaila kudi ya dauko bundle guda na dubu dubu yace gashi beauty ki
bawa ummi kice suyi cefane,ya kara dauko wasu manyan kwalayen sweets masu dadi da tsada
da biscuits yan gaske da wasu snacks cikin katuwar Leda gashi wannan duka nakine,har kasa
tace tnx uncle tana ta murna,wata ledar ya kara daukowa katuwa wannan suhaila baza ta iya
dagawa ba,yace jeki ki kai wa ummi kisha sweets dinki,sannan ki cewar antynki tayi sauri ina
kiranta,kafin ya rufe baki ta fada gidan da gudu,ummi murna da dadi ya rufeta,kakarsu ta yanke
saka,tsalle sukeyi da murna kaka harda rawa da juyi,Riga damammiya pink bodyhug ce jikin
iklas da wani jean skert shima da kadan ya haura gwiwa,
Kallonta yayi ya tabe baki,mika mata kayan yayi gashi nan kuyi manage kafin na
dawo,godiya ta shiga jerowa,juyowa yayi cikin hade rai da kakkausar muryar dake firgitata karki
sake na ganki kan titi kina talla wlh,sannan ki daina yawo tsirara ga kaya nan,daure fuska tayi
har zatayi magana sai kuma taji tsoro gani tayi yayi mata kwarjini.
Amma aranta tace kuji min iyayi da shishigi,ina ruwansa da tallana,uba nane shi,shi zai dauki
nauyinmu in banje talla ba,wai ina yawo tsirara kut..yayi sa'a shi ya fada min haka ina ganin
mutuncinsa da wanine wlh sai ya San wace gomnati.
Kafin ta gama wannan zancen zucin nata tuni omar ya Dade da figar motarsa ya bar layin,
bayan motar ta hango kadan.gida ta wuce itama,
Nan fa murna sabuwa gidan su iklas, ready made dogayen riguna ne masu tsada da kyau
dai dai iklass kamar an aunata kala biyar,Riga da skert kala uku readymade suma,takalma kala
uku flat,da yan gyale,brst basu isa sa bra ba panties kawai ya siyo kala 10,vest da tight wando
guda uku,rigar bacci na yaran gida kala uku,bai San iklas Nada kanwa ba shi yasa bai siyo da
ita ba,sai ya bata sweets da snacks din,atampofi kala biyar masu tsada du iklas tace kaka ummi
ta dinka nata ne.
Murna wurin kaka ummi ba a magana ita kuwa suhaila ta sweets kawai takeyi,omar Kuwa
wurin sultan ya tafi gaisar da mom din sultan,sannan suka je wajen wasu frnds nasu,sultan yayi
yayi omar ya rakashi wurin Yasmin budurwarsa amma omar Sam yaki zuwa,sultan ne yaja tsaki
wlh zan rama omar,Yasmin din da zan aurace baza kaje wajenta ba?shuru omar baice uffan
ba,sau daya fa ka ganta Frnd shima a hospital office dina kuka hadu.malam karka dameni kafi
kowa sanin waye omar bana zuwa rakon zance,so pls excuse me cewar omar,nasan halinka
mana maramutunci,miskilanci,da rashin damuwa da matsalar wani sai in matsalar ta me tallan
egg ce.headphone omar yasa a kunnensa yana jin wakar Chris brown.
Kallonsa sultan yayi dan iska tashi ka tafi gidanku ka bar min daki ba abinda ka iya bakin hali
ba annuri a fuska,gaka da mata amma baka da maraba da gwauro,gwauron banza
kawai.murmushi omar yayi ya mike tare da shigewa toilet din sultan wanka ya fesa,wani closet
din sultan ya duba da yake ajiye sababbin singlet dasu boxers,3quater dan bangaren new da
ba a taba sawa ba daban suke,sultan ma kwai kyau tsabta da daukan wanka,sultan shi ba fari
bane chocolate ne,ya danfi omar kiba da kadan,shi yasa size dinsu kusan daya,
Farar singlet omar yasa da 3quater ya fesa turaruka,sultan na shan kallonsa,kayan jikinsa
daya cire ya eba ya zuba a mota,ya dawo room din sultan karar ruwa yaji yasan sultan na
toilet,wajen mom din sultan ya wuce yaci abinci suna ta hira a kayataccen kantamemen palonta
kamar aljanar dunia,30mnt yawa mom sai da safe ya wuce room din sultan,sultan ya hango jikin
mirror ya hade cikin wata arniyar gezna sai turaruka yake fesawa,
Tabe baki omar yayi daga bisani yace malam kayi sauri ina jiranka,da wata uwar masifa
sultan ya juyo ubanwa zaije dakai gidan surukai haka,kamar inyamuri,ga suma duba fa
shigarka,tsaki omar yaja ya sake bude layin sababbin jallabiya,wata milk color me mugun tsada
ya dauko,siririya me shape dai dai jikinsa ta manyan guys,Turare ya kara fesawa sannan suka
fito,mom suka gani a Palo suka mata sallama cike da fara'a hade da jindadi gami da birgewar
abotarsu ta musu adduar dawowa lfy,7:30pm suka cinna hancin motarsu cikin gidan su
Yasmin,gate man ya wangale musu makeken gate din su yasmin,har katafaren palon baki aka
musu iso,kafin wani lokaci an cika gabansu da kayan motsa baki,
Karaar takalmi sukaji das das,sannan kamshinta ya iso,cikin nutsuwa ta shigo da
sallama,sultan ne ya amsa,ba laifi Yasmin kyakyawace fara ba kal ba amma tafi sultan
haske,sun gaisa da omar ya dan jira for 15mnt ya fice ya koma mota,karfe 9pm sultan ya kira
omar har umma da abbun su Yasmin suka gaisar.omar ranar gidan su sultan ya kwana.
Asmabaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
9
By
Asmabaffa
Wannan page din dominku nayi shi readers masu yabo da jinjina.
Da safe tare sukayi break sultan,omar da mom sultan,sannan omar ya wuce office.bayan
kwana biyu da zuwan omar gidan su iklas,wasu ma'aikata suka zo da kayan gini a motoci cewar
oga omar ya turosu za suyi musu kitchen a canja toilet da sauran wasu abubuwa,abin har kaka
ummi ya daure mata kai amma me zasuyi,nan da nan cikin 3days anyi toilet ta zamani tasha
tiles,kitchen ma haka,rooms dinsu ma daga baya ya bada umarnin a sake sababbabi,kai
readers gidan dungurugum aka sake ginawa komai sabo na zamani,2room da Palo
tsakiya,toilet kitchen duk a tsakar gida yanda suke kawai Palo aka kara musu,ansa kofofi da
windows na zamani,gidan tiles da tiles dan dagwas dashi gwanin birgewa,sai murna ake
tayasu,su kuwa sai suce dan uwansu ne ya Gina musu,Palo sun maida kayansu na da, sai ya
tashi haduwa,daya room din kuwa gani sukayi ankawo bed mirror sip new yan gaske aka
shirya,duk rooms din an sa musu labile na zamani,next day suka kara ganin mota guda ta
kayan abinci a tsorace suka yarda suka shirya kayan a kitchen komai akwai,dama suna da
fridge me kyau da girma da tsada,
Har gas da kayan kitchen kamar amarya an kawo an shirya musu,shifa omar kawai kudi
yake bayarwa da umarni,next day aka kara kawo wasu kayan a Ledoji wai inji oga,dayar kaji,kifi
da naman rago,a fridge suka zuba,harda lemuka masu tsada a takaice readers komai yaji a
gidan na jin dadi,
Next day kuwa wasu kayan aka sauke,ai iklas kuka tasa kaka ummi ma haka su dai karfa
ace watarana su biya,dadi ya zama wahala,duk Wanda ke musu har anfi 1wk basu ga keyarsa
a gidansu ba,sun shiga uku karfa ko ba nasu bane,ko aljanune ma,
Kayan suka bude bayan sun gama kukan,uniform suka gani na wata schl dake kusa dasu
schl din me tsadace,iklas dai dai ita,itama suhaila kamar an gwadata,mamaki sukeyi wai to a
ina yasan size dinsu,uniform din har kala 4-4 ya musu,ga books din kowa a schl bag kala
3-3,takalman schl ma kala 3-3,a cikin jakar iklas yasa takadda me dauke da rubutunsa,
Da sauri ta dauko ta fara karantawa kamar haka.
ki duba cikin wata Leda akwai envelop in kunje schl din da ita zaku tafi, ki bawa p.c din,7:30
za kuga me kaiku yazo,banda talla a titi,ki gaisar da ummi.
Omar
Ai tsalle suka fara da ihu suka cika gidan,wlh ummi shine yayi mana komai,lailatul Qadari
Allah maka albarka,ai duk sallah sai na ma addua cewar iklas,kaka ummi babaLola science sec
schl fa ya biya mana kinga receipt har na gama an biya min,suhaila iya js3 ya biya mata,..
Daya ledar suka jawo gaba daya kayan suhaila English wears masu kyan gaske kala
10,takalma masu kyau harda kayan baccinta kala biyu,pant itama dasu vest kala 10.kuma nan
ma kamar an gwadata.
Tsalle kawai takeyi tana murna,saura wata ledar atampopi kala biyar dinkakku diff
stile,shaddoji kala 4 yan gaske suma sunsha aiki,lace kala 3 sunsha dinkin zamani,da material
kala 6,suma gaba daya an dinkasu dai dai jikin iklas,lace2,shadda2 mayafai manya masu tsada
kala Biyar, ba a dinka ba takadda manne jikinsu anyi rubutu kamar haka.
Na ummi ne ki bata ta dinka,ga kudin dinki nan cikin lace,mayafaima nata natane.karamar
ledar karshe suka bude,hijabaine masu hannu kala biyar size din iklas dagwas,kala uku na
suhaila,kala uku manya na ummi,mayafai suka Ciro yan madaidaita masu kyau da tsada kala 6
na iklas,sai uniform din islamiyyarsu da ya gani jikin suhaila ya canja musu new kala 2-2.
Yau har nafila sukayi suka dinga godewa Allah tare da yiwa Omar addua da iyayensa,next
day kayan kwalliya iri iri Dana gyaran gashi da turaruka aka kawo musu,3days tsakani ya turo
da wasu latest takalman roba na mata da jakankuna cikin Ghana must go babba,da address din
company gashi nan suyi business,su dinga siyarwa a cikin gida babu zuwa talla,ai kuwa haka
akayi,iklas an kulla alaka da company nasu omar,banda jaka da takalmi har wasu abubuwan
take sarowa suna saidawa a cikin gida ake zuwa ana siya,sai schl tana kaiwa.sosai suke samun
kudi,ga schl me kyau,sutura me kyau,ci da sha zam zam,ga tsabta da kwalliya suna
bugawa,gasu wayayyu sai suka kara kyau haske da kiba.
Tun zuwan omar na farko bai kara zuwa gidan su iklas ba,komai da yayi musu aike yayi
dasu,su kuwa sun matsu su ganshi ko godiya suyi masa,amma shuru,gashi basu da number sa
bare su nemeshi dan iklas ta siyawa ummi wata karamar tecno sabuwa,ita kuma ta siyi wata
Samsung me kyau touchscreen,haka kawai iklas ta ji ta shiga damuwa na rashin ganin omar,
Kullum sai ta tunashi,shi kuwa omar a ganinsa har ga Allah ya taimaka musu badan wani
abuba,me zaije gidansu yayi,me zaice dasu yayi aikin ladansa suzo suyi zarginsa ko da wata
manufa yayi.shi yasa tace Sam bazai kuma lekasu ba,tunda komai yayi dai dai shike nan.amma
me zuciyarsa kawai sai yaji yana son yaga lafiyarsu musamman iklas,yana so ya ganewa
idonsa ya suka koma,
Baffan su omar yayo waya cewar bazai dawo ba sai nan da 2mnths,dan haka ya umarci
daya daga cikin matansa ta bishi Russia, ai rahina wuta ta bude dole itace ta tafi Russia wurin
baffa Wanda Sam baiso itace zata zo ba amma ya zaiyi.
A can ta dage tana ta kulla makirci,hade da kiran tsofaffin bokayenta tana danna musu kudi
suna sheka aikinsu,sun bata tabbacin maman omar ba abinda zai iya cinta na tsafi dole tana
nan daram,kuma baffa bazai daina sonta ba,dan haka tace to danfa a koreshi ya bar gidan,nan
ma sukace shi zai iya tafiya amma bazai nisa da gidan ubansa ba,kuma dole zai dawo,cewa
tayi koma yane ayi mata ya bar gidan.
Sahar kuwa tunda ta dawo yanzu tafi da fita gantali,dan yanzu tafiyar kwananki takeyi.tun
omar na fada da damua ya gaji ya kyaleta.kowa harkarsa yakeyi.
Yau watan omar 1 da zuwa gidan su iklas,ya gaji da daurewa,yau dole ne yaje ya ga
lafiyansu.saturday ba islamiyya ya sani,sanye yake cikin pencil wandon jean arsh color da farar
Riga me rubutu da baki jiki,ga suma taci kudi,kai ka rantse bature ne 4:30pm ya parker wata
jibgegiyar sabuwar motarsa a kofar gidan,da kyar ma ya gane gidan,dan ma ma'aikatan sun
nuna masa a waya ne,knocking yayi suhaila ce ta bude sanye take da vest da wandonta iya
Rabin cinya,gashinta yasha gyara,tun daga kallon suhaila yasan sunci gaba wlh.
Baki ta washe ta daka tsalle ta daneshi,oyoyo uncle,muna ta nemanka baka zo ba,to ai gani
beauty yana murmushi kadan,sama ya shilla suhaila ya sabata a kafada suka shige gidan da
sallama,kaka ummi ce ta fito tana amsa sallama..turus taja birki da mamaki tabbas wannan
umaru ne da suke nema ido rufe domin suyi masa godiya,ummi baki har kunne ohhh dan nan
yanzu sai yau kazo,muna ta jiran ganinka shuru,abubuwan arziki sai barkowa sukeyi ta
hannunka,nanfa kaka tahau zuba godiya harda kukanta,daga nan ta fara yi masa hira,shi omar
a bai son labari da yawa amma haka yake amsawa a dole,
Kuma yana jin dadin labarin da take masa domin masu amfanine sosai a wurin dan
Adam,dan ita ummi bata surutun shirme a nutse take,suhaila kuwa tana cinyarsa ta lafe,
Iklas sanye take da wando 3qutr tight fari kal da riga dark blue,siririn gyale ta daura a kanta
fari,tana kitchen ta gama shirya musu abinci ta gyara kitchen,sai surutun ummi take jiyowa dan
ita bata ma San anyi wasu bako ba,wanka take so tayiwa suhaila itama tayi domin ita ke yiwa
suhaila wanka saboda da wai suhaila jika jika takeyi kawai.fada sukeyi da suhaila sosai kan
wanka,dan suhaila tace ta iya wankanta ita.
Da sauri ta fada palon da sallamarta....ummi wai surutun me kikeyi hakane?ina suhaila tazo
na mata wank......bata karasa ba takai kallonta kan 2seater ai cik ta tsaya ganin Wanda ko a
mafarki bata zata ba,ganinsa tayi ya kara kyau da kwarjini,ai da Saudi ta durkusa sannu da
zuwa sir,ina yini,ya hanya? Da kyar ya amsa da lfy yana shan kamshi,ga fuskarsa ba rahama
tamke,
Ganin yanda ya amsa mata bata samu karbuwa ba a wulakance,kamar bai Santa ba yasa ta
mike tare da fadin taso suhaila na miki wankan,kafada suhaila ta make a jikin omar...ni anty na
iya wankana fa zanyi da kaina,no ban yarda ba jika jikar da kikeyi,kinga baby dont waste my
time ki taso na miki,ina da wurin zuwa.
Omar a ransa mamakin iklas yakeyi yanda takeyi acting kamar babbar mace bayan ita kanta
iklas din bata wuce a mata wankan ba.
Ganin suhaila bata da niyar tashi yasa ta karasa wurin omar ta jawo hannun suhaila nan
suka fara kokawa,suhaila ta tura hannun iklas da karfi ta hade hannun da kirjin omar sai kiciniya
sukeyi iklas na kokarin zaro hannunta wani azabar bala'in shock ne ya shigi omar,bai San
sanda yace shishsh a hankali,tana janyo hannun ta fara masa sannu da bada hakuri duk ta
dauka bigeshi tayi yaji zafi,...tsawa ya buga mata get lost stupid kin takurawa yarinya,
Kaka ummi zabura tayi Allah maka albarka Umar yarinyar nan bata da kunya wlh wani halin
banza ta dakko na son girma,gashi bata jin maganata na rasa inda zanyi da iklas wlh ka ganta
duk wannan haukan da takeyi sauri takeyi zata je party na makwafta.dan ta taba taimakamana
shine wai dole sai taje partynta na murnar zagayowar haihuwa,
Giya fa suke sha a wurin umaru rawa maza da mata a cure ana badala nayi nayi akan Kar
taje amma takiji,bata jin maganata sai abinda ta tsarawa rayuwarta kaka ummi ta fashe da kuka
wiwi.
Asmahbaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
10
By
Asmahbaffa
Wannan shafin nakine MAMAN WALEEDA ina godiya sweet sis.
Kiyi shurunki ummi yanzu zan kula da ita duk wani iskanci da take ji dashi zan gyara
ta,cuno baki iklas tayi ta bar palon,wanka ta samu tayi ta palon ta wuce sanye da hijab,kwalliya
ta tsantsara ta sa daya daga cikin rigunan da ta siyo rannan a kasuwa wata yar gaunt me
dogon hannu ta haura gwiwa da kadan,daga sama ta matse kasa ta bude,orange and black
color tayi kyau ba laifi harda yafa