Showing 36001 words to 39000 words out of 107121 words
Chapter 13 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
kenan na gode.
Kallonsa Iklas tayi da kyar ta iya Jan numfashi sabo da kyan da Omar ya mata,amma a fili
tabe baki tayi cike da masifa wai ke Ummi an fada miki ya Omar bafa ya son matarsa kuma fa
itama ta tsaneshi kudin sa take so,ita bata son aure tafi son aikin Gomnatinta,kuma yar
isk......Omar ne ya cire kafarsa daga hadadden takalminsa ya dora tafin kafar a kan Iklas ya
dungura kanta kasa ya danna sabo da Omar a tsaye yake jingine jikin bango yana danna waya.
Ba shiri Iklas tayi shuru tana nishi,Ummi kuwa ta gama gane Iklas kishin Omar takeyi amma
ita kanta Iklas bata gane hakan ba.
Iklas ta dauka abin na Omar wasa ne,suna hada Ido taga idonsa ya canja yayi jajir kamar
dai ciwonsa zai tashi don jikinsa har rawa yakeyi.da kyar Ummi tazo ta janye Omar tana ke in
banda shirmenki Iklas me ya kaiki tsara karya kan matar mutum fada Ummi tayi mata sosai,ita
kuwa Iklas mamaki abin na Sir Omar ya bata.
Maza ni yar banza me Jan fadan tsiya kije kiyi wanka ga magrib zatayi,da sauri Iklas ta
shige wanka,Omar kuwa sai daya dauki like 5mnt ya dawo normal daga jin yanda zuciyarsa ke
masa zafi.
Bayan sunyi sallar isha Iklas ta dan Dasa kwalliya tasha Riga da skert English wears tayi
matukar daukan kyau,shape sosai ya fito ta dan yi acuci da gashinta tare da yana mayafi
karami,kwas kwas tasha choge,tana fitowa Omar ya watsa mata wani kallon koma ki canja
shiga,ba shiri ta juya ta sa shadda dark purple duk cikin kayan da Oga Omar ya mata ne.
Ummi suka yiwa sallama suhaila na bada sautun chocolate, suna fita already mota sabuwa
dal tana waje kamar yanda suka saba,yau Omar ba fara'a fuska daure Iklas tsoronsa takeji kar
ya shaketa,a tsorace ta miko masa hannunta gashi ka rike kar a samu matsala cike da bacin rai
ya fisgi hannun sai da kashinta yayi kara.
Da sauri sukayi take away na abinda suke bukata suka shiga mota,suna hanyar fita daga
wurin Sultan da security suka shigo wurin Sultan bai gane motar ba saboda Omar bai fiye
yawan hawa mota kala kadan ba,kullum cikin sake motoci yake,
Omar ma bai ga shigowar su Sultan ba yana can ya Lula duniyar tunani,suna dawowa gida
a bakin kofar Omar ya tsayar da Iklas kallon kallo sukeyiwa juna,u hv to be very careful wlh kika
sake kika fadawa wani yanda ciwo na yake sai nayi maganinki ya fadi tare da tallafe mata keya
tas ya zuba mata rankwashi kwas.
Kanta ta dafe tare da turo baki tana dire dire da kafafu kallonta Omar yaa tsaya yi sai kuma
yaji ta birgeshi tare da bashi tausayi,nan take ya tsinci Kansa cikin farin ciki gaba daya
damuwarsa ta yaye,
Hannu ya mika da niyar rungume ta,ita kuwa Iklas ta zata dukanta zaiyi da gudu ta goce ta
zura gida da gudu wayyo Ummi ta fada palon, daria ma ta bawa Omar.
Yau ko girkin dare ba Wanda yaci abunda Omar ya siyo musu shi aka baje aka ci aka sha
akayi dam.
Wurin 3wks kenan su Sultan suna aikin neman Omar amma shuru Allah baisa sun hadu da
Omar ba,
Ummi kawo mu siyo miki naman miyar cewar Omar,to Umaru kuje da Iklas akwai dan nisa
tsakaninmu da wajen da muke siyarwa,yawwa Ummi kinga ma dan wasa kafarmu cewar Iklas
tare da zaro hijab dinta iya cinya me hannu,Omar kuwa jallabiya ce fara jikinsa,
Suna fita ya rike hannun Iklas kamar kullum suna tafiya amma Iklas ce kadai ke bashi labarin
babanta da babarta da suka rasu,
Sai kallonsu akeyi kamar sabon aure kowanne naji da nasa radadin kyan.
Sunsha tafiya a kafa har baabban titi suka tsallaka sun siyo, sun bar wurin me naman kenan
wasu suka parker da motoci wajen guda biyar,kartai ne manya manya wajen su biyar suka fito
daga cikin mota daya, basuyi wata wata ba suka fisge hannun Omar daga na Iklas tare da
make iklas gefe can har sai da ta fadi kasa,da gudu Omar yayi kanta da niyar dagata,wasu
manyan kartin ne suka sake fitowa su hudu,sukayi sama da Omar tare da cusashi a mota,
A gigice Iklas ta kama ihu da fadin barayi Ku taimakamin jama'a sun sace minji,kajifa Iklas
wai miji, help me pls my husband oooo shuru babu Wanda ya jita wurin ba mutane gata abj ne,
Motocin sun Fara tafiya Iklas na kuka ta zo tsallaka titi mota ta banketa a kan idon Omar
domin yana bayan mota sun daureshi tam tam da igiya saboda sunga ya fara fisge fisge kamar
me aljanu,Wanda su basu gane ba ciwon omar ne ya tashi sosai ba Iklas kusa.
Omar na kallon mota ta bige Gomnati ya rushe da kuka a motar kamar yaro,ga zafin ciwo
gashi mota ta bige masa iklas Gomnatinsa.
Tuni kartan nan sun sanarwa Baffa da Sultan cewar sun kamo Omar,murna sosai sukayi
baren ma Mama.
Omar har yau hawaye yakeyi ga zafin ciwo,duk wani masoyin Omar suna nan sun hallara
damkam a compound din gidan,ana son tarbarsa bakin kowa a washe.
Iklas kuwa tuni jama'a sun taru a kanta,labari ya watsu mota ta bige gomnati, kaji fa popular.
Wani dan saurayine me dan saukin kyau ya fito daga motar da ta kade Gomnati,baiyi wata wata
ba ya sureta sai asibiti.
Asmahbaffa
[29/03, 02:07] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
65-70
By
Asmahbaffa
Wangale gate din su Omar akayi tare da jera Shiga wakeken rangadeden gidan da motocin
gaba daya wannan kartan sukayi,Omar Wanda ya gama galabaita gashi an kawoshi har gidan
da bazai iya rayuwa ciki ba,ji yake kamar za a zare masa numfashi yayin da motar da yake ciki
ta shiga cikin gidan iyayensa,kafin ka bude ido Omar ya fara shuru shure da make make,gashi
an daure shi kamar wani huhun goro,mutanen da suka taru za a tarbi Omar jiran fitowarsa
kawai sukeyi suna washe Baku,Abdallah da suleim sai zumudi sukeyi,yayin da kungiyar
haj.Rahina suka tsaya suna zage zage da masifa,aikin banza akan wannan fasikin suka wani
taru aikin banza cewar Aisha,
Bude motar akayi wasu mutum biyu suka fito da Omar dake cikin mawuyacin hali,Mama
salati ta kwada tana hawaye ganin halin da danta yake ciki,da karfi Omar ya fisge kansa tare da
girgije kartin nan daga jikinsa sai gasu kasa zube,huci kawai yake yana gurnani,kara ya fasa
tare da zubewa kasa a yana ta birgima daga nan ya suma gaba daya numfashinsa ya
dauke,mutanen dake wajen ko wanne salati da lahaula yakeyi,Mama kuwa kan Omar ta fada
tana kuka haka ma su suleim,da kyar Baffah ya janyesu,su sultan ma har hawaye suka digar
tare tausayin Omar,duk wani masoyin Omar sai da ya tausaya masa,su haj.Rahina kadai ke
murna tare da shigewa part dinsu suka saki sautin kida.
Sahar dake wajen itama domin sai da aka shigo da Omar sannan tazo wajen tana ganin
abinda yakeyi tabe baki tayi ta kalli Baffa ta yatsina baki a kyaishi psychiatric hospital,
Harara Baffa ya watsa mata ya wuce wajen Omar,ita kuwa sahar glass dinta baki ta kafta a
fuska ta shige dalleliyar motarta ta koma inda ta fito.
Kwance daurin da akayiwa Omar Sultan yayi,sannan suka taru aka dauki Omar aka kaishi
room dinsa Wanda yasha gyara,wasu Allurori Sultan ya masa,gaba daya kowa ya tafi gida
Sultan da Raj ne kawai zaune suna jiran tashin Omar suga taya zai farka.
Mama da Baffah harma da su Abdallah suna palon Omar sunyi jugum jugum suna jiran
tsammani,Umma Rahina tana ta yiwa frnds dinta waya cike da Murna tana basu labari,haj Binta
tana jin labarin haushi taji taga lallai in tayi sake nan gaba Burin Rahina zai cika,don haka tace
Sam wlh bazai yiwu Rahina ta fini kudi ba dole na wargatsa shirinta,sai na karya wannan tsafin
da ta yiwa Omar. su sadiya kuwa rawa kawai suke takawa.
Hospital Iklas kwance tana bacci saurayin da ya bigeta yana kusa da ita yana jiran tsammani
tare da karewa surarta kallo,
Saleem yana jin labari a rude ya fada wajen Ummi,da sauri ta tari saleem yawwa saleem
maza ka bimin bayan Iklas daga aikensu amma har dare ya kusa yi,Ummi bafa lfy Iklas wai tana
asibiti mota ta bigesu,innalillahi wainnailairrajiun,Ummi sai kuka Suhaila ma hakan dannan in
sun mutu Ku fadamin,Ummi ba kuka za kiyi ba zo mu tafi kawai asibitin mu San a wanne hali
take,guruf guruf Ummi ta sa takalmi ko mayafima suhaila ce ta mika mata hijab a waje,saleem
rike da hannun suhaila suka shiga taxi suna bulayi har Allah yasa wani ya musu kwatancen
asibitin da aka kai Gomnati.
Fadawa dakin sukayi sai ganin Gomnati sukayi kwance saurayin na gefe,Ummi da Suhaila
sai hawaye suke sharewa,Ummi na oh mun shigesu tsautsayi yasa na aikeku da nasan haka
zata faru da ban fara ba sai ta kara fashewa da kuka,saurayi kuwa sai hakuri yake
basu,haushinsa ummi taji ta juyo da masifa kwalabar ubanka dan jakar uba zaka dakeni ka
hanani kuka ne?
A ransa sai dariar zagin kaka yakeyi,a fili sai hakuri yake bayarwa,kai da Allah ka rufe min baki
cewar Ummi.likita ne ya shigo tare da cewar Goggo a daina hayaniya pls ta kusa farkawa,bata
da wata matsala Allah ya gajarta wahala.
Likita ina daya saurayinfa?wanne fa?dama su biyu aka bige?da Sauri saurayin yace no kaka
wannan kadai na bige banga namiji ba,kan kakane ya kulle to Ina Umarunsu,dole su jira
farfadowar Gomnati suji ina Omar ya tafi.sosai Ummi ta damu rashin sanin inda Umarunta ya
Shiga.
Baccin 6hrs Omar yayi sannan ya farka,ciwon dai yana nan sai dai Omar jikinsa Sam ba
karfi dakyar yake daga yatsansa sabida Allurar da Sultan ya masa.
Hawaye Omar ya fara ga ciwo na cinsa ga tunanin mota ta kade masa Gomnati, Sultan ne
ya lura da farkawar Omar,da Sauri shi da Raj suka nufi wajensa,Mama,Baffa dasu Abdallah duk
sun banko cikin room din,Omar kuwa ido jajir,ga karkarwar jiki tare da danne saitin zuciyarsa da
hannu daya, Sultan ya kai hannu da niyyar taba Omar amma duk halin da Omar ke ciki saida ya make
hannun sultan wai kar ya tabashi,Mama ce ta matsa kusa dashi ta riko hannunsa tare da dora
kan Omar a cinyarta tana hawayen tausayi,Omar na jinsa a jikin Mama yaji ciwon ya karu,kuka
ya fara tare da rungume Mama yana ajiyar zuciya,Baffa ma hannu yasa ya dago Omar
jinginashi a jikinsa,
A hankali Mama tace Babana fada min me ya sameka haka?wacce cuta ce ta sameka haka
ka kasa fada mana?wai ni wanne ciwo wannan Banana?
Baffa ma haka ya dinga lallaba Omar yana tambayarsa meke faruwa,amma Omar yaki
magana,kwanciya ma yayi kan bed yana numfarfashi.
A hankali Omar yayi magana da kyar muryarsa ke
fita,Ba..bazan..iy...iya...zama....nan..Gi...dan...dan..ba,Ku fitar.....da...in....Don't...Allah.
In..kuna... So...na...za...una...Ku can...ja... Min gida...pls
Zuciyarsa ya kara dannewa yana idan....Ku...ka...barni... Nan... Mutu....wa... Zanyi sai hawaye
ya ziraro daga idonsa.suma du mutanen dakin sai da suka goge ido.
Yaci gaba da I....na..da matsala...a....lafiyata...Ku...fahim.....ce....ni.
Da sauri mutanen dakin suka hada baki da karfi wallahi mun fahimta mun fahimceka Omar.
Murmushin karfin hali yayi Ku...canja...min...wa...ni gidan....ko.....Ku..nemo...min...Gomnati,
To fa mene kuma Gomnati?cewar Mama
Iklas...na...ke ...nu....fi.a...dubo...min...lafiyarta...mo...ta...ta...kad..e..ta....ku
memo...mi...n...ita...itace.....maganina.....da karfi ya kara volume cike da zafin ciwo She IS MY
MEDICINE MAMA yana fadin haka ya kara sumewa,Sultan wasu alluran ya kara makawa Omar
daga suma yaci gaba da bacci,sannan ga drip ya sa masa.kowannensu ya hallara a Palo suna
tattauna maganganun Omar ya za a bullowa lamarin,Sultan yace Baffa da farko dole mu koma
Neman Iklas a garin nan ina ganin itace Ummi wacce yake rike hannunta,wacce ta kawo sakon
envelop gidan nan,kwarai kuwa Sultan cewar Mama.sannan dole fa a canjawa Omar gida a
kaishi wani guess house din cikin gidajensa,kafin a nemo wannan yarinyar,sannan ya dace ayi
masa maganinsa Hausa cewar Raj.Baffa ma yace dama hakan na fara tunani kawai.haka suka
kwana a palon,baccinsu kadan ne.
Da dare misalin 11 Iklas ta farka da Kuka wiwi kamar ranta zai fita sai shure shure takeyi an
sace ya Omar,Ummi wlh wasu ne suka sace oga Omar,yanzu mu yaya zamuyi mun Shiga uku
wayyo sir......wayyo Omar dinmu na mutu Ummi...na mutu Ummi....naga ta kaina...mene
amfanina a duniya ni kuma Ummi...tawa ta kare...saleem ne ya riketa yana lallashinta da kyar
aka samu tayi shuru,taki cin abinci ma wanka kawai tayi ta fara sallah bayan ta wacce ake binta
ta koma yin nafeela ba ji ba gani har sai da ta kai 4am sannan Allah ya kawo nurse suka tsira
mata Allurar bacci aka shimfideta tare da sa mata drip.
Washe gari da safe aka sallami su Iklas,gaba daya Gomnati ta birkice,bata uhm bare uhm
uhm,ta daina ma magana wai duk cikin Bacin ran sace Omar take,damuwa ta shiga sosai su
Ummi sai lallashi sukeyi tare da kwantar mata da hankali,Ummi tace kin San fa Baban Umaru
me kudine yana can babansa ya sa a dauko masa dansa,ke banza ce wa zai iya sace Umaru,ai
ba a satar manyan mutane yara ake sacewa idan aka dafa su ance sunfi manya dadi..Iklas
kuwa dadi taji wai ba a sace Omar ba,daria ta saki kuma fa hakane Ummi ko a radio cigiyar
yara kadai akeyi,can mintuna kadan suna Shiga gida Iklas ta fara kuka tayi missing din Omar
sai gidan yayi wani iri,
Tunowa tayi da cutar Omar yanzu tasan ma yana can ta tashi kukanta ta kara sautinsa
sannan ta ruga da gudu jikin Ummi ta jata Palo suka zauna sannan Iklas ta kwashe labarin
cutar Omar ta fadawa Ummi
Ummi ma harda kuka Allah sarki Umaru,Iklas wayon banza ne dake me yasa baki fada min
da wuri ba,wannan aikin sihiri da jinnu ne da tuni munyi kokarinmu an karya abin.nan Iklas ta
Kara bawa Ummi labarin gidan su Omar kaf,harda dukan da aka mata su sadiya,da sahar matar
Omar.sosai Ummi taji haushin Iklas da bata sanar mata ba. Ke rabu dani shashashar banza gashi nan ai kin jawo matsala da kin fada tun wuri da tuni
haka bata faru ba,Ummi shi yace kar na fadawa kowa,yaushe dama ababen dake jikinsa zasu
bari ya fada kar a masa addua.
Ummi gobe muje gidan su ya Omar mu gani,ban yarda ba Iklas ki bari tukun muga abinda
Allah zaiyi...kawai muyi masa addua,jiki sanyaye tana kwalla tace to Ummi sai kuma kuka ya
kwace mata ta rufe ido da tafin hannunta biyo tana tunowa da rayuwar da sukayi tare da Omar.
Yanda ya taimakesu,yake hanata kula kowa,kula dasu,yanda suke fada da kuma wasa da
dariya.
Kara tunowa tayi sanda ya shafa mata ruwan naman ganda a fuska sai kuma ta fara daria
ga kuma kuka da hawaye duk ita kadai.
Ummi kuwa tausayi Iklas take bata,Suhaila ma damuwa ta shiga babu me siyo mata kayan
sawa da sweet.da Sauri Iklas ta shige dakin Omar tana shakar kamshinsa tare da kwancia a
bed din tana tunanin lokacin da taga Omar a mota tana talla a kwalta,yanda take kwala masa
Kira ta glass din window tana Oga tare da daga hannu,murmushin da Omar ya sakar mata a
lokacin shi ta tuna.
Mikewa tayi ta cire kayan jikinta tare da daukan singlet din omar fara tasa, sannan tasa
wandonsa short fari tayi kyau dama gata fara,ga gashi har tsakiyar baya.lekowa dakin Ummi
tayi taga shigar Iklas daria Ummi tayi ta koma kitchen.Iklas kuwa mayyar Omar a dakinsa ta
kwana tana jin kamshi tasha bacci kuwa ji tayi kamar ta rungume Omar shi yasa tayi bacci
sosai.
Omar washe gari haka ya farka da ciwonsa yana a nemo min Magani ta,Iklas Mama kuma
a fitar dani daga gidan nan,bakwa tausayina Baffa?ba shiri Su Sultan suka sashi Mota tare da
kaishi wani rantsatsen gida ga yan aiki da security ko ina.Alhmdllh kuma Omar ya dan ji sauki
sauki,har yayi wanka da kyar tare da cin abinci abincin ma saida Raj yace in bai ci ba baza