Showing 21001 words to 24000 words out of 107121 words
Chapter 8 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
suhaila,baby ya gida,kinyi karatu kuwa?anty Sai anjima
zanyi, to Allah kaimu..me kikaci after break? Ba komai anty..so kike ulcer ya kamaki ko,juyawa
tayi ta shiga kitchen,cake ta ebo da fresh milk ta dawo palo,a gaban suhaila ta ajiye gashi nan
maza ki cinye,komawa kitchen tayi ta ebo wasu snacks ta kawowa omar harda juice yasan
tabbas iklas sai ta rubuta cikin jotter dinta omar yaci cake da lemo,
Shi Sam baya son zaki juice kawai ya sha,iklas tana kitchen tana girki Omar ya shiga kitchen
din,gwagwa take ta yi wajen yanka wata kaza amma ta kasa dan ta mata tauri,sai huci takeyi
tana yarfe hannu,kusa da ita ya matsa hannu yasa ya karbi wukar,tsorata tayi sosai,ido suka
hada tace kash wlh har naji tsoro,kazar ya fara yanka mata,tana gefe tana mamaki yanda ya iya
aikin mata,sharp sharp ya yanka mata,satar kallonsa takeyi tare da yaba kyau irin na omar,shi
wai to baya daria ne,mutum kullum shuru haka,omar kuwa yaji ajikinsa tana kallonsa,yana
gamawa ya wanke hanunsa da liquid soap,yana juyowa ya dungure mata kai sai da ta kusa
faduwa,kina kallona kamar baki sanni ba wth ur big eye,nuna min kayan abincinku cewar omar,
nuna masa tayi yaga suna da su amma sun kusa karewa,wayarsa ya kunna ya kira wani daga
cikin yaransa,kwatancen gidan ya masa ya umarceshi ya kawo kayan abinci gidan,3hrs tsakani
aka cika gidan da abinci.amma basu ga omar ba domin yana dakinsa bai son a San Inda yake
ma kwata kwata,su kuwa yaransa sun zata yana office ko gidansa,ummi kuwa rasa bakin
godiya sukayi a wajen omar,
Maman omar kullum addua da kuka take zabgawa,harda kannensa su abdallah,su Aisha
bangaren haj rahina sai murna sukeyi yayinda labari ya riskesu,Wanda hakan Sam baiwa
sadiya dadi ba,an cuceta bata dau fansa ba,ga asarar kudin da tayi,Haj.rahina kuwa sai dadi
takeji tana nishadi,baffa kuwa manager ya kira ya tabbatar omar ba a San inda yake ba shi ke
kula da komai.gaba daya baffa ya daina walwala da farin ciki,Sam haj rahina ta kasa gane
kansa,domin ko sakar mata fuska bayayi,tattarowa yayi suka dawo Nigeria,
Waje waje gari gari suke bincike,sultan ne a gaba kullum basa zama Neman omar
sukeyi,sadiya na hango ta Tara yan dabanta su wajen shida,tace isa a.c da usy a boy ya kuke
ganin za ayi,kudina zaku bani ko kuwa yaya za muyi?isa a.c ne ya saki daria yace ke hajiya
karki kawo yawa mana,ya kike mana shirme ne,a boy yace dalla malama saurara yasin sai na
sokeki da wuka,karki raina mana hankali mana,ji mana ke ai munci kudinmu,taimako daya za
muyi miki duk ranar da muka ganshi idonmu idonsa zamu cika miki burinki,idan kuma bamu
gani ba sai ki ware kawai ko ya kukace.a boy ya zuki sigari ya fesawa sadiya yace ware kawai
hajia kar ki bari na canja mind dina na murde miki wuya
Tsorata sadiya tayi jiki na rawa tace kuyi hakuri ko me kukayi dai dai ne,hakan ma is
OK,motarta ta figa a 100 ta bar wajen,a boy ne ya kalli yaransa suka kwashe da daria kana
yace men this girl inaaaa ey na bad girl,she stingy bad.wani ciki ashar ya kunduma yar kut...da
wani dry leg nata,ko shape babu komai flat.
Hajiya rahina tsabar yawan bokayen da tabawa aiki ba a San Wanda aikinsa ya ci omar
ba,kowa kawai ta yarda kawai.ciki kuwa har karyar su HAJ bilki kawayenta.
Dare ya tsala kishirwa ta fito daga room dinsu shan ruwa,tazo Palo ta jiyo nishi dakin omar
sosai abin tsoro,lallabawa tayi ta shiga dakin omar a hankali ta murda kofar ta shiga,
A kudundune ta Ganshi ya hada gumi yana ta karkarwa yana nishi,da gani mafarkin abin
tsoro yakeyi,sai ciccijewa yake yana tirje tirje,tausayinsa iklas taji sosai karasawa jikin gadon
tayi ta zauna gefen bed din hade da kura masa ido,A hankali tasa hannunta a kafadarsa kamar
jira yakeyi ya juyo a sa hannu biyu ya damke hannun hade da kankamesa a kirjinsa,shuru iklas
tayi tana matukar tausayawa oga,da gani matsala ce jikinsa babba,ba tare da ta zare hannunba
ta Kurawa hadaddiyar sumarsa ido,tasha gyara tana kyalli yalala da ita,kamar TV haka ta
kurawa surar Omar ido,ta shagala sosai sai da ta share lokaci me tsawo,farkaawar da Omar
yayi ita ta dai daitawa iklas nutsuwarta,
Zumbur ya mike zaune yana kallonta tare da mamakin rike hannunta da yayi a
kirjinsa,mamakin iklas shine yana rike hannunta taga ya daina karkarwar tsoron,sannu oga
sir,hannu takai zata taba wuyansa,make hannun Omar yayi ya watsa mata harara mind ur
business pls,ruwa kawai zaki kawo min nasha,ni ba irin su Emma bane as u can see musulmi
ne ni,so u better get ths in to ur skull, ki daina gigin taba min precious skin dina.
Baki iklas ta tabe a fili tace sannu muslimu daga taimako,kuma hannuna kai ka kamashi
zuwa jikinka anji hannun yarinya me laushi ba a sababa an wani kankameshi,wuf ta fece daga
dakin,dan dai kawai ta tausaya masa ne amma da wlh baza ta kaimasa ruwan ba,
Ruwa ta dauka faro da glass cup ta koma room din,sadaf sadaf ta ajiye can nesa dashi a
tsorace take kadan take jira ta zura da gudu,kafafunsa ya daga hade da dafa cinya alamar zai
mike,kararaf ta kwasa da gudu ai kuwa ta daki kofa da hancintaa garin gudu ji kake
fas,wayyoooo ta furta hade da rike hanci,kara kwasa tayi da gudu zata arce,caraf omar ya riko
hannunta ba tare da yayi magana ba ya cire hannun da ta rike hancin,
Jini kadan ya gani alamar ta fara habo kadan,gashi kan tsinin hancin yayi ja ya kwarzane
kadan,tissue ya dauko ya matsa jikinta sosai suna jin numfashin juna,tuni jikin Omar har ya
shocking yana rawa a cikin jininsa,
Ita kuwa iklas wani kasala kasala taji kamar ya danyi hugging dinta haka taji,daurewa
kowanne yayi cikinsu,hannu yasa ya dago fuskarta ya goge mata hancin tas,yana karewa pink
lips dinta kaallo,kamar ya dan.....lol
Kije toilet ki wanke cewar omar, mika mata tissue yayi har wacce ya goge mata hancin, jeki
nyt.cike da tunanin kyan dirin Omar ta fice,toilet ta shiga sannan ta koma dakinsu,
Kaka ummi ke kuwa iklas zawo kikeyi ne?kin Dade daga cewa zaki sha ruwa sannan kiyi
fitsari,ummi bigewa nayi da kofar toilet kinga habo ma nayi,sallallami kaaka tayi tana ta faman
yiwa iklas saannu,harda shafa mata magani a hancin wajen da ta kwarzane,
Ni kuwa nace su iklas badai iya karya ba.kwanciya sukayi kowannensu cike yake da tunani
kala kala,iklas an kalli ceiling anyi kuri da ido ana tuno kasancewarta tare da Omar dazu,duk
sonta da aikin gomnati sai taji da tayi tunanin salary ko ta gama schl ta fara aiki,ga mota tana
ja,suna zaga kasashe ita da su suhailanta sai taji yanzu kamar tafi jin dadin tunanin oga
omar,kawai fuskarsa in ta tuno dadi take ji,a'a juyi ta karayi taja tsaki,yanda omar ke daure
fuska ta tuno sai taji sanyi,a ranta tace oh zuciyata yanzu fushin nasa ma birgeki yakeyi tab,da
kyar bacci ya sace iklas,bangaren omar kuwa mugun mafarkin da yayi yake tunani,ga tunanin
family dinsa musamman mama ko a wanne halin take oho,rayuwar da yake ciki yanzu ya tuno
da iklas me kwai sai yaji dan sanyi a ransa,ya yanke shawarar yanda zai sa iklas ta masa wani
acting yanda zaiji lafiyar mama da baffansa,hade da kwantar da hankalinsu,yasan iklas tsab
zata iya,ko ya wannan abu zai kasance readers oho,za dai muji nan gaba.da wannan shima
yayi bacci,
Da safe su iklas sunyi shirin schl,omar kuwa fitowa yayi so yake yaga ya hancin iklas
yayi,uniform ya gani sun mata kyau,bai taba ganin wacce uniform yawa kyau haka ba irin
iklas,kallo ya kare mata suka gaisar dashi,ummi ma ya gaisheta,iklas ya kalla ya kara fakar idon
ummi ya dagawa iklas gira daya,hade da nuna hancinsa yana murmushi me kayatarwa,tasan
tsokanarta yakeyi ba wani dubiya,baki ta turo,ta juya masa baya tana yaba muguntar
omar,ummi ta juya tana gyarawa suhaila jaka ya dan ja hijab din iklas kadan,waigowa tayi itama
ta dage masa gira daya,alama yake mata da hannu kamar kurame,kaka ummi ta tarfa su,sosai
sun bata daria,umaru shirmen iklas kake kulawa ko,so kake ka koyi shiriritarta naga
alama,ummi kalli hancin ta fa,hmmm umaru baka da dama ai jiya a bayi ta bige da kofa,ta dade
tana habo,da kyar ta samu tayi bacci,daria omar yayi sosai jin karyar da iklas ta tafka,kallonta
yayi suna hada ido ta kifta masa wai ya rufa mata asiri,kafada ya rike alamar yaki din,kaka
ummi na kallonsu tace ohhh yau kuma umaru kurame kuka zama haka,wlh ka daina saurarar
iklas,ummi wannan jikar taki bata ji ne cewar omar.
wani yaronsa daban Omar ya kara kira ya gwada masa gidan su iklas,dalleliyar wata motar
omar ya dakko ya kai su iklas schl,sai kallon su iklas akeyi a schl.
Shima dai Wanda ya kai su iklas schl bai San daga ina omar ya kirashi ba,gashi ko wanne
da new sim yake kiransu,kuma yan amanarsa yake sawa aikin Wanda yasan duk runtsi baza su
bashi matsala ba,kowanne sai ya gargadeshi kar ya fadi ya kirashi a waya.
Iklas kam yau daga schl company ta wuce ta saro kaya,yaron omar ne ya kaisu ko ina ya
dawo dasu gidansu sannan ya tafi
Kafin su iklas su dawo omar ya fadawa ummi zai aiki iklas gidansu ta gano masa lafiyar
iyayensa,umaru kai da kanwarka sai ka nemi izinina,dadi yaji sosai su iklas na dawowa ya sata
ta shirya cikin doguwar Riga da mayafinta,wajensa taje yana zaune tsakar gida a kan kujera
sanye da Riga armless fara,da black jean gashin kansa ya kara yawa,
Ummi tana Palo suhaila na gefenta suna kallo da cin abinci,envelop ya mika mata nan ya
Shiga tsara mata yanda zata yi acting a gidan nasu, hhhhhh iklas ta kama daria yanda taga
Omar ya gwada maganar mata, kallonta ya tsaya yi,yanda daria ke matukar yi mata kyau,
tsayawa tayi da dariar ganin omar ya kafeta da ido,daga bisani tace action ta fara gwada masa
yanda ya koya mata har kara masa idea tayi,sosai sunji dadin moment din,iklas uwar shirme ji
tayi inama suyi ta yin wannan film haka me dadi.
Kudi ya mika mata na taxi tare da address ta tafi kuwa.yau zata ga gidan su oga da family
nasa,ya za aga haduwar su cewar iklas.
Sahar kam sai Allah ita cewa tayi Omar makaryacine yana can London munafiki za a ce ya
bata kato dashi,to saceshi za ayi dan haka iyayenta suka ce ta dawo gida tayi zamanta tayi
aikinta.haka kuwa akayi ta kwashe komai nata tas ta bar gidan cike da nishadi ta samu yanci.
Tun daga waje iklas take kallon haduwar gida kamar baza a mutu ba,gate ta buga,masu gadi
wajen biyar suka leko ganin tsaleliya iklas suka ce wannan da gani kawar yan gidan nan
ce,suma mamakin kyan iklas sukeyi kamar larabiya,gashi da ganin rigarta ta masu kudi
ce,dama a rigunan da Omar ya batane tasa daya,
Da sauri sukace ta shiga suna ciki,tana shiga nan ta rantse a ranta da zata yi bacci ta farka ta
ganta a wannan gidan to cewar zatayi ta mutu tana aljanna.
Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
25-30
By
Asmabaffa
Page din nan naki ne DIYAR KATIBI.
Tunani iklas tayi domin omar ya gwada mata yanda gidan nasu yake ba tare da tasha wahala
ba ta gane part din maman omar,shiga tayi dakin part din tare da danna door bell din da omar
ya fada mata,abdallah ne ya bude kofar,iklas dauke da hand bag a hannu an wani shanye
hannu irin na wayayyun mata,kallon abdallah tayi da ganinsa kasan kanin oga omar ne,
Kallonsa iklas tayi pls mama nake nema,OK shigo tana ciki cewar abdallah sai bin iklas
yakeyi da kallo yanda yaga baby me kyau haka,shiga ciki tayi salati take maimaitawa a ranta
yanda taga tsaruwan palon,a kujera ta zauna abdallah kuma ya hau sama domin kiran
mama,suleim ce ta fito cikin shirin islamiyya,sannu da zuwa ina yini cewar suleim,lfy zo mana
mu gaisa cewar iklas,zama tayi kusa da iklas,can iklas ta kunna video recording a wayarta tana
daukan suleim,wani katon pic din omar ta gani a palon,suleim waccen yayankine?ae anty
amma ya bace,an nemeshi ba a Ganshi ba,mama kullum sai ta yi kuka tana ta addua,dady ma
addua yace mana mu dinga yi,kinga su anty sadiya kuwa nurma sukeyi sosai,har kida suka
kunna a gidan nan,suleim kwai surutu.
Yanzu in suka ganmu da mama suyi ta mana daria,kuma anty sahar matar yaya omar ta
gudu gidansu wai ba za ta zauna gidansa ba,gaban iklas ne ya yanke ya fadi jin an ambaci
matar yaya omar,dama yana da mata? Take taji wani bakin ciki a ranta,gabaa daya jikinta yayi
sanyi,cikin kankanin lokaci suleim ta bawa iklas labarin gidansu,duk da batasan su waye anty
sadiya ba,suna haka mama ta fito ita da abdallah,yi tayi kamar tana latsa waya nan kuwa video
take musu,tsugunawa tayi cike da ladabi ta gaisar da mama,mama kuwa me aiki tasa ta
kawowa iklas kayan motsa baki,
Ganin kalar girkin hadadde yasa iklas sauka kasa ta baje kamar gidan ubanta ta kama cin
abincin cikin dabara takewa kanta video record tana cika baki da abinci,
Mama da abdallah har suleim daria sukeyi ita kuwa iklas tana sani tayi haka dan su saba da
ita,sai da taci ta koshi sannan ta kalli mama tace mama wlh har na dawo hayyacina bakuga
wahalar Dana sha ba kafin na gano gidan nan,kwashe kayan mama tasa akayi,yan mata meke
tafe dake ne? inji mama,sultan ne yayi sallama ya shigo palon,iklas taso ta ganeshi amma ta
rasa Inda ta sanshi,shima bangaren sultan hakan take sai kare mata kallo yakeyi ya kasa
ganeta,domin tun iklas na tallan kwai ya taba ganinta,yanzu kuwa ta kara haske,kiba,kyau da
girma.
Zama yayi suka gaisa da mama,iklas ma ta gaisar dashi,shi dai sultan wannan bai taba
ganin me kyau irinta ba sai me tallan kwai da apple ta Frnd dinsa omar,kai har muryarma suna
kama,amma wannan da gani yar masu kudi ce,waccen talakace haka Allah ke ikonsa wani ba
dangi yayi kama da wani duk a ransa sultan ke wannan tunani.
Iklas ce taga sultan na kallonta,shima sai da ta masa video record,mama iklas ta kalla tace
mama dama wannan na hoton tayi nuni da yatsanta jikin pic din omar dake jikin bango
ne,harrrrr su mama sukayi aka zubawa iklas ido a ji bayaninta,naje company dinsu Neman aiki
da dan dadewa,shine aka turani office dinsa naje interview,shine yace bazan samu aiki a
company dinsu ba,amma nayi hakuri kuma yana Neman alfarmata na kawo wa mamansa sako,
Shi zaiyi tafiya ne,har naki karba amma ya dage,mama baki gani ba har kuka yayi kan sai
nazo gida wajenki na baki sakon,Baku gani ba abin tausayi har kuka ya min cewar bashi da
kowa da sukafi mama da baffa,sune farin cikinsa iklas ta karashe tana matsar kwalla,mama
tace Allahu akbar da su suleim tuni hawaye na ambaliya a fuskarsu jin labarin omar,tabbas iklas
ta tausaya musu amma ta dau alkawarin gano wannan lamarin dake faruwa da omar da family
sa ko zata tallafa.
Sultan ke bawa su mama baki bayan sun nutsu iklas ta zaro envelop daga jakarta ta mikawa
mama,wannan yace na kawo miki,Allah bai bani iko ba sai yau,
Mama batasan karantawa don bata so ta karantowa kanta bacin rai,sabo da wannan ta
mikawa sultan takarda,sultan nutsuwa yayi yana karantawa can su mama suka ga yana daria
da fara'a wannan ya nuna sakon dadi ne bana bacin rai ba.
Kwace takar dar mama tayi taga guntun rubutu ne ma,fara karantawa tayi kamar haka:
SALAM......MAMA NAYI MATUKAR KEWARKI BURINA KI DAGE MIN DA ADDUA INA DA
MATSALA A LFYR JIKINA,KI BAWA BAFFA YA KARANTA DA KANNENA SULEIM DA
ABDALLAH,NAYI KEWARKU,SULTAN MA ABASHI HAKURI,INA NAN A NIGERIA MAMA
CIKIN KOSHIN LFY,BANYI NISA DAKU BA,ZAN DAWO SOON,KUNSAN BAZAN TABA YIN
ABU BA KWAKWARAN DALILI BA,A SANARWA BAFFA NASAN SHIMA ZAI FAHIMTA.
Dadi mama taji dukkansu sai murna da jin dadi sukeyi,iklas kuwa sai video take musu,mama
ce ta rungumeta yata yar albarka mun gode kwarai,kowa godiya yakewa iklas,mama tace
yaushe ya baki sakon?ya kai week nawa?sati dayafa kenan cewar iklas,,take kowa ya kara cika
da murna,suka tabbatar da Omar yana kusa kuma lfy yake,hankalinsu ya kwanta,
Dakin baffa mama ta nufa yana ciki ta shiga ta labarta masa komai tare da mika masa
takardar,yana gamawa ya dago fuska cike da annuri,dama na fada miki ki kwantar da hankalinki
yana nan ni nasan son namijin gaske ne, sai mu dage masa