Showing 18001 words to 21000 words out of 107121 words

Chapter 7 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

6627

zasu kifa,ina gefe nace Allah tsare na cikinta Dana kan hanya,kuka
iklas takeyi musamman da goshinta wani katon kululu ya fito,parking yayi kofar gidansu,da
Sauri iklas ta fita dan ta ga mutuwa with her own koro koro eye,tana fita omar ya sauke glass ji
mana....juyowa iklas tayi, u hv to be very careful banda sauki ina gargadinki ki tausayawa
lafiyarki kiyi abinda ya dace kunnena yaji da wanda idona zai gani,zan dawo next time hukunci
yana nan zaki karba dai dai da ke cewar omar tare da figar motarsa ya bar layin gaba daya cike
da jin tsananin haushin iklas,shi kadai ya rasa ma ina zaije ya huta,wani katafaren guest house
dinsa ya nufa dake gwagwalada,da ma'aikata da komai a gidan so very neat.

Iklas kam ta Dade a tsaye tana tunanin to ita wai me tayi masa,mene hadinta dashi da haka
kawai zai tsaneta,ya dauki karan tsana ya Dora mata..tsaki taja tana mulmula ciwonta ta wuce
gida tana kunkuni za a kasheta a banza.

Ummi ce ta tsare iklas da tambayar me ya sameta a goshi,fada mukayi a schl ummi Da
wata,shine ta buga min kai da chair nima na fasa nata da dutse.kin kyauta iklas Allah taimaka
cewar ummi,shashasha matsa ko na makeki wacce bata San ta girma ba,bari Allah ya kawo
min yaron albarka umaru na fada masa tunda naga kinfi jin fadan sa.
To wai ummi ni me nake mikine dazaki dinga hadani da wani azzalumi bare can,bamu hada
dangi dashi ba amma har kinfi sonsa akanmu...ummi ce ta maketa da gudu ta mike ta wuce
toilet,sallah tayi,wanka da cin abinci,mikewa tayi ta kwanta tana tunani kala kala wanda yafi
yawa akan omar.tana tunaninsa kuma sai taji ranta yayi fari,ji tayi gwara tayi tunanin oga fiye
Dana schl,ita kadai idan tayi tunanin schl sai tace no sai tayi na omar,sai ta saki murmushi tare
da cewa kai ni kwai banza,mene abun tunashi,me ma zanyi dashi,ina Sam mijina yafi wancan
ogan kyau ma,

Maman omar ce ta kira wayar sahar sai da tayi mata 5 missed calls bata daga ba,after

40min sahar ta kira back tasan Maman mijinta ce tana da number amma sai tace hello who is
on the line pls?,who am I speaking with? Shuru mama tayi tana jin sahar na turancinta ta gane
me take fada amma baza ta iya mayar mata da turanci ba domin abdallah yana koya mata
sosai shi yasa tana ji sai dai baza ta iya mayar da magana da turanci da tsayi ba.
Sahar Maman omar CE...ohh mama ya gida ya aiki,lfy alhmdllh,sahar dama naji tafiyar da
kikayi ne shine naga rashin dacewar hakan,bai....din din din mama taji an datse wayar,kira ta
karayi ringing daya taji wata ta dauka tana ta watso turanci tabbas tasan sahar ce ta bada
wayar dan a ci mata fuska.mama taji zafin abin sosai amma bata fadawa kowa ba,da kanta ta
shirya driver ya kaita har gidan su sahar ta sanarwa iyayenta duk abinda ke faruwa,Maman
sahar tabe baki tayi to ai sahar yarinya ce hajia,dole Ku dau hakuri,mu yarmu gaskia banga
wani abu da takeyi ba,ya kuke abu kamar muna kauye,zamani ya canja balle ma sahar yar
boko ce tana aiki babba dole sai tayi tafiye tafiye.

Baban sahar kuwa gyaran murya yayi am hajiya za a mata fada kar Ku damu,yarinya kuma
sai hakuri domin dole tayi aiki,kuma ita yar dangi ce dole sai da ziyarar yan uwa,aikinta kuma
gaskia baza tayi wasa dashi ba dan yanzu rayuwa planning akeyi,amma tunda kunce tayi laifi
kar Ku damu za a mata fada.haka mama ta dawo tana jimamin halayen iyayen sahar da sahar
din kanta.ko omar bata fada masa ba.

Sadiya tayi shige shige ta samo yan daban ta inda ta basu kwangilaar a sassara mata
omar,in ta yiyuwa su hallakashi nan da 3wks,kudinta kaf da ta Tara na albashi shekara da
shekaru ta basu.

Ita kuwa hajiya rahina ta ajiye shawarar da haj. Bilki ta bata sai nan da wani lokaci zata fara
hada makircinsu,yanzu wata kawarta hajia magajiya ta hada da wani shahararren malamin
bokanta ta sanar masa so takeyi kawai omar ya bar gidan ubansa da kafarsa.yayinda haj bilki ta
samu kudin da rahina ta tura mata na bokan kasar Mali ta bude makeken wajen saloon dinta
dama ta gama ginawa rashin kudin siyen kayan ciki ya jawo ta kasa budewa,

1wk da faruwar hakan Omar ya fara jin baya son Sam yaje gidansu,haka gidansa ma bai son
zama ciki dole yake zama,mama kanta taga omar ya rage zuwa wajenta,sai ta dauka ko sahar
ta gyara halinta ne sun shirya,har tana murna,omar sabo da mama yake daurewa watarana ya
shiga gidan,dan in ya dauki hanyar gidan ji yake kamar za a zare masa rai,ga wani mugun
bakin ciki da faduwar gaba,haka the same da gidansa,steal guest house nasa ma hakan
take,ya canja gidaje da dama nasu amma hakan yakeji,hotel ya koma da zama yafi jin
sauki,office kuwa bashi da ikon zuwa.duk wani harkar kula da dukiyar baffa sai wani manager
su me amana ya dora akan komai ba wasa

Kuma salisu manager ya kafa ya tsare kan komai,shi yasa baffa yake ganin komai
normal,sadiya yaranta sun bazama Neman Omar.amma Sam sun kasa gane inda yake kwata
kwata,yayinda Omar ya hada kayansa ya tare a hotel,hakanma kullum tsoratashi akeyi,ga
muggan mafarkai,a firgice yake kullum,ya rame,kullum kwakwalwarsa a tunani take ina zai je

yaji dadi,ya samu peace of mind,

Omar gashi ya kasa fadawa kowa halin dayake ciki,yayi niyyar sanarwa sultan da mama sai
yaji bakinsa yayi nauyi,ita kanta mama taga omar kwata kwata baya hayyacinsa,ko sun
tambaya sai yace office ne,kuma sai su Dade basu Ganshi da idonsu ba,abin ya dami mama da
sultan,mama ta sanarwa baffa yace suyi masa addua kawai ko da wani abun a ransa da yake
damunsa wanda bamu sani ba,

Yaran sadiya sai Neman omar suke su aikashi garin da ba a dawowa,amma abu ya
fassakara,sadiya sai masifa takeyi an kasa cika mata burinta,yayin da omar ya kara boye kansa
a hotel yana karbar masifu a jikinsa,

Dan yanzu Sam ya bacewa ganin su mama,ya kashe wayoyinsa,an rasa inda ya
shige,yanzu ko bacci baya iyayi da kyar yakeyin sallah ma,amma addua ta gagareshi,ko Quran
ya dauka tofa faduwa yake ya sume,idan addua zaiyi sai bakin yaki motsawa,kawai gaba daya
ya yanke shawarar barin hotel din ko garin abuja duka,
Wani tunani yazo masa ransa take ya tattara trolley dinsa ya shiga taxi har kofar gidan su
iklas,cike da izza ya tura gate din yana shiga gidan yaji mugun nutsuwa ta shigeshi,hankalinsa
ya dawo jikinsa,ga wani ni'ima hade da nishadi a cikin zuciarsa,tofa readers,wani hanin ga Allah
baiwa,haj rahina tsafinta yaci Ashe gata Allah yayiwa omar,domin yaran sadiya sun kara nemo
wasu manyan yan daba duk Inda suka San wurin kashe naira na yan Hutu,na masu kudi sunje
sunje amma Sam ba Omar ba labarinsa,shi yasa komai kaga ya sameka na kaddara Allah
yafika sanin dalili,sonka yake.


Sallama yayi gidan su iklas,kaka ummi ya iske ita kadai tana kulla citta a Leda,iklas tasha
baccin rana ta mike ta fito kenan tana mika hade da yin hamma,vest ce jikinta pink da skert
dogo me roba.wuf ta koma daki da sauri,ummi kuwa baki ta washe tana tarbar oga umaru,a
tabarmar da ummi take nan ya zauna gefenta.



Ku kara shiri readers yanzu za a fara.



Asmabaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

15-20



By
Asmahbaffa



Ina godiya masoyana masu karatu,ban San wanne irin farin ciki ma zan nuna ba yanda
kuke kara min karfin gwiwa.tsakanina da Ku sai addua.


Tunda omar ya zauna gefen kaka ummi suka gaisa bai kara magana ba,Sam ya rasa me
zai ce mata,ummi kuwa ta fuskanci umaru matsalace dashi babba,tun daga yanayinsa ta gane
gashi ya dan rame ya kara haske,gashi harda trolley dinsa kamar dan gudun hijira,

Kallonsa ummi tayi a nutse kana tace umaru iceko dai lfy?naga kamar kana da damua,omar
kamar zaiyi kuka amma bazai iya fadan matsalar sa ba,uhm...uhm...ummi kawai ina cikin
Matsala akan lafiyar jikina,nan ne kadai Dana shigo naji nutsuwa,ban San me ya sameni
ba,kawai ki tayani da addua ummi,
Kallon omar ummi tayi tabbas iyaka gaskiarsa yayi maganar,ta tabbatar akwai Matsala tattare
da omar,gashi kowa yasan babansa a kasar nan kuma da alama suma basu San matsalar dan
Nasu ba,


To umaru me kake so ayi?ina
kaje haka?ummi ko ina ya gagareni zama,nan gidan kadai naji na samu nutsuwa,jinjina lamarin
ummi tayi amma har yau bata gano matsalar omar ba,dan kar ta takura masa da tambaya ta
kyaleshi sai nan gaba idan ya kara samun nutsuwa,

Umaru zaka zauna damu kafin komai ya daidai tane?cewar ummi cike da murna ya daga
mata kai,murmushi ummi tayi ko ba komai gidansu zai kara armashi samun namiji tsayayye
cikinsu,duk hirar nan da sukayi iklas tana labe jikin labile ta zuro kanta waje,sai da taji komai,a
ranta tace to shi me ya sameshi,sai kuma ta tuno yanzu room din da take kwanciya shi za a
bawa wannan ogan,

Ta gama planning dinta an rusa mata,yanzu wajen ummi da suhaila zata koma da kwana,daki
daya zasu ruguntsuma,abin haushi cewar iklas a ranta.

Omar tunaninsa ya canja state ko ya koma wata kasar amma sabo da baffa ya ce dole ya kula

da harkokinsa ba inda zaije,ummi ce ta kwalawa iklas kira,wuf ta yo waje gani ummi jeki kwashe
kayanki a dakinki umaru zai zauna zuwa wani lokaci,kallonsa tayi shima kuwa ya dago da
kansa sukayi 4eye,Wani sanyi iklas taji a ruhinta,idonta ta janye ta gaisar dashi,yau ya dan
sakar mata ba laifi,kayanta ta kwashe tas,ta kara gyara room din sai kamshin ni'ima,daga bisani
ta kai masa karamar akwatinsa ciki,alwala yayi yau a nutse yayi sallar azahar da la'asar duk a
gidan,

Suhaila kuwa murna take ta tayi dan gayu zai kwana gidansu,zasu dinga shan sweet,shi yasa
ta makale kusa da omar.

Abinci iklas iklas ta kawo masa ita tayi girkin kasancewar yau ba islamiyya,tuwon danyar
shinkafa miyar egusi,da dan namansu na talaka,rabon da omar ya ci abinci a nutse haka har ya
manta,iklas wani table da chair dinta ta jawo ta zauna kai ita fa bata yarda ba ma'aikaciyar
gomnati ce,shi yasa in tana kai tana lissafinta wani dadi take ji,kanta kara girma yake sai ta
dinga hangota kamar a office,

Tunda omar ya fara cin abinci yake satar kallon shirmen iklas,sai yanga takeyi tana ta faman
rubutu,sai da ta gama karatun schl ta jawo jotter lissafinta ta fara,har yi take tana kwankwasa
tsinin Biro a dole babbar ma'aikaciyace,

Ummi na gefe suna kallonta,har gumi ta hada sabo da lissafi,readers duk lissafin nan da
iklas keyi bai wuce kan karuwar omar da suka samu a gidan ba,dole komai yanzu na ci dashi za
ayi lissafi,shi yasa take ta tarawa da ebewa,ummi ce tayi murmushi su kuruci dangin hauka,in
kin gama sai ki tashi ki hadawa umaru ruwan wanka.
Ba tare da ta dago kanta ba tace ok,sai da ta dauki lokaci me tsawo sannan ta gama ta kalli
agogon dake sakale a hannunta sannan ta mike ta maida littafin palo cikin drower ta dawo,sai
da omar yayi wanka sannan ya shiga dakin da aka saukeshi,gaba daya jinsa yake a takure,zafi
ya dameshi,ala dole zai danyi kwanaki a gidan nan kafin ya tafiyarsa,ina Sam bazai iya rayuwa
haka ba,komai a takure,dan karami kamar yana prison haka yake jinsa,dan ma akwai wuta
available, Daren ranaar gaba daya ya kwashi bacci cikin nutsuwa,har makara yayi,sai 9am ya
farka,su iklas yau ma Sunday ba schl,tuni har sun gama gyara gidan kawai ummi ce bata
karasa musu breakfast ba,fitowa waje yayi dan toilet ma sai iya ta tsakar gida dole,brush ne a
hannunsa da wani tsadajjen toothpaste, omar kwai kunyar a kallar masa jiki shi yasa da 3quater
da singlet farare ya fito,harda towel dinsa,kallon yan gidan yayi yaga duk sunyi wanka kowa
radau dashi,iklas ya kalla wacce ta wani hakimce a farar kujera tana latsa kuturwar
wayarta,ummi ta kitchen tace umaru ka makara ni na hana a tasheka saboda naga akwai gajia
jikinka,guntin murmushi yayi ya wuce toilet,kalar sabulun omarma daban suke,yana Shiga
wanka iklas ta shige room dinsa zuruf ta gyareshi fes fes,aka dame masa bed,roomfreshner da
turaren wutar data sa masa yafi na ko ina yawa.

Palo suka hallara da kayan break ana jiran oga dan kwalisa ya fito,sallah yayi da addua ya
shirya cikin wata jallabiyya dark brown yayi kyau,,duk gidan ya dau kamshinsa,yana fitowa ya

gaisar da ummi,ta amsa tana tsokanarsa da bakunta,suhaila kuwa tsam ta mike zata je wajensa
iklas ta riketa ram,zauna malama zaki je ki kama hawan masa jiki,jikinkine? Ya fada fuska
tamke,ummi tace kyale iklas da iyayinta,sharesu tayi ta gaishesa ya amsa tare da jawo suhaila
kusa dashi,
Kunun gyada ne da chips girkin yayiwa omar dadi,kallon ummi yayi yace amma daga ji
tsohon hanu ne yayi girkin nan ko? Daria ummi tayi sosai tasan sarai iklas yake tsokana,

Iklas kuwa haushi taji ta katse maganar da tsohuwa yau zanje wuse market,a dawo lfy saura
ki kwaso wannan yan iskan gwanjunan dangalallu da kike kwasowa,

Baki ta turo ta Mike ta wuce room dinsu,omar kuwa har fadi yake anya kuwa iklas ba aljanu
gareta ba lol,ya matsu ta tafi kasuwa ya sace book din nan da yake gani tana lissafi,so yake
yaga wai me take rubutawane kullum,

Yaso ya hanata fita amma wannan kudirin nasa yasa ya rabu da ita,fitowa tayi sanye da
atamfar da omar ya dinka mata red da yellow Riga da skert,tayi kyau sosai das da ita,ansha
jambaki maroon,bata daura dankwali ba,gyale siriri ta yafa a iya kanta,gata jajir da ita ta haske
ko ina tal,duk suna zaune Palo ta fito,idon kaka ummi omar ya faka ya dallawa iklas harara,ya
mata nuni da ido kan ta koma ta canja gyale babba,ko tasa hijab,kafada ta make cike da
shagwaba ta buga kafa alamar taki din,ido ya zaro ya daure fuska yayi kamar zai mike ya
kamota da gudu ta fada daki,ta dauka kamata zaiyi,tasan muguntar omar dan bata manta
wahalar da Tasha ba cikin motarsa,

Hijab tasa yellow me hannu yakai tsayin Rabin cinyarta,ummi ce ta kalleta da mamaki tace
yar albarka ko kefa,Ashe kin fara hankali,a lallai shi yasa akace komai da lokacinsa,Allah miki
albarka yar nan,sai kin dawo kinji jikalle,tana fita ta leko kanta taci sa'a su ummi surutu suke da
suhaila,a hankali ta dan girgiza labile yanda omar zai gani,kallon wurin yayi ai kuwa suna hada
ido ta murguda masa baki,shi daria ma ta bashi,a take ya saki murmushi ya nuna kansa irin
ni?ido ta karkada far far ta daga kai alamar eh din,kai ya jinjina alamar zaki dawo ne.ummi ce ta
juyo wuf iklas ta sake labile ta bar gidan,shi kam ogan naku wani matsewa yayi.ya dauki remote
ya kunna TV,

Kaka ummi ce tace to ni umaru na shiga zan dan matse,bacci nakeji,to ummi a fito lfy.iklas
kuwa kayan ta kwashe ta maida kitchen,tana fita Omar ya sadada a dauke jotter iklas ya shige
dakinsa,

Kwancia yayi a bed ya fara dubawa,murmushi ya farayi ganin harda date take sawa,kuma
kome ta rubuta sai ta zanashi,Daddawar miya ya fara gani tace ta Dari biyu for 1mnth,sannan
yaga ta zana daddawa,su tattasai,da sauran kayan abinci

Yanaa ci gaba yaga irin bashin da take bi su ma gasu nan,ga wani bangaren business dinsu
ne,abinda ya bashi daria kwandala in ta shiga ko ta fita sai ta rubuta,wani bangaren ma

planning rayuwarsu da budged tayi na 1-2yrs,bai gama shan mamaki ba sai dayaga ko bako in
akayi sai ta rubuta tayi lissafi nawa aka kashe a kansa,rufe littafin Omar yayi yana daria ganin
an rubuta har dambum naman da ta bashi kwananki,komai na rayuwar gidan na lissafe a cikin
littafin,gajia yayi da karantawa dan kato ne littafin,ga lissafi da rubutu kaca kaca mayar mata
abinta yayi inda ya dauka,a Palo yaga suhaila na kallon cattoon, kwancia yayi a 3seater yana
tunanin rayuwarsa,da mamansa halin da take ciki,

Yana wannan tunani tare da adduar Neman agajin Allah suka tsikayo sallamar iklas ta
dawo,tana shigowa ta durkusa tasan tayi laifi,sannu da hutawa oga sir


Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

20-25


By
Asmabaffa




Tana kifta ido fiki fiki da gani bata da gaskia,sum sum ta wuce,sannu da zuwa anty cewar
suhaila, tsayawa tayi ta dawo wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login