Showing 60001 words to 63000 words out of 107121 words

Chapter 21 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

6649

ko baya nan wucewa takeyi ta dinga uzurinta ba ruwanta,akwatin
kayan bikinta ta janyesu ta mayar dakinsa,
Iklas tsabar kadifiri har kawayenta hadaddu ta gayyato guda biyu wata yar gayu yar gidan
wani kusar Gomnati suna ce mata ANGEL,sai wata yar wanka kyakyawa itama yar wani babban
soja ce wato PRINCESS, unguwarsu taje ta fadawa kawarta arniya DAMI DAMZEL itama za aje
da ita dan tana aiki a company tana kashe wanka duk cikinsu babu wacce za ace bata hadu
ba.kuma iya dinner Iklas ta gayayyacesu suzo.
Ummi ma ta gayyaci mata tsofaffi irinta na tsohuwar unguwarsu mutum uku,Sa'ade,Hasiya
da Maman saleem Haj kyauta.

Komai dai share.
Saleem duniya ta samu har sun canja unguwa ya siya musu gida shida mamansa sun koma
cikin Abuja city,har yayi motar kansa,
Mamansa ta uzura masa ta gaji da zaman kadaici ya nemo matar aure,shi kuma Iklas ya
fada mata yana so,sai tace ya bari idan taje musu biki zata sanarwa Ummi,sai murna yakeyi.
Umma Rahina yaranta ta Tara,kan kar su nunawa yan bangaren su Omar komai,idan ana
bikinma su nuna komai daya, ana zaman lfy,kuma suja Iklas a jiki ayi komai dasu,yanda idan
sunyi wata kulla kullar jama'a ba Wanda zai yarda cewar su suka aikata,dan tace ana gama biki
zata fara harba makami me linzami na bama baman tsiyarta bangaren Mama,zasu sha wutar
bala'oinsu.

An tashi yaune za ayi event har biyu daya 3pm-6pm za a dawo a koma na 9pm-3am ko
wanne wajensa daban za ayi, Iklas ce ta wuce Omar a palonsa fiiii zata shige cikin
bedroom,jawota yayi baya ina zakije haka,kinfa takurawa room dina, na gaji da wankemin bra

da panties naki ke ba matata ba ko kunya bakyaji na gani,

To mene abin kunya a pant da bra amma a t.v settelite ai nagani rannan kana kallon
american film da bra da pant jikinta kana kalla me yasa nan banga kaji kunya ba,sai idonka ma
da naga ka kara warewa,
Ni ai na saba gani,ke nake nufi,baki ta murguda to Nima bana jin kunya agaban kowa zan iya
shanyawa,da masifa Omar yace hey mind ur tongue,kar ki jawo na huce fushina kanki.
Ita Iklas duk haushin Omar takeji yaki cewa yana sonta, ta gaji da jiran sa.

Me zakiyi cikin Room din to, wankan party,no ki bari sai na 9pm zamuje.batayi musu ba tace
to Allah kaimu.
Da hannu ya yafitota come come muga lallen da akiyi miki jiya,na mantama ban gani ba,a
nutse ta wara masa hannayenta,kalla yayi sosai har na kafa dama gata fara kar, lallen ya gama
tafiya da Omar, harda shafa hannun,gashin ma ba a magana, har mamaki yakeji yaushe Iklas
tasan wurin gyara a Abuja haka. Omar bai San aikin Mero Lallausa bane me gyaran jiki.
Zame hannuta Iklas tayi,tabe baki Omar yayi mutum ya biya kudi an hanashi ganin na
kudinsa.
Je ki dafa min indomie da kwai,ki hada min coffee. Tafiya tayi cika umarnin Omar,Hips dinta
yabi da mayen kallo.

8pm sai shirin dinner party akeyi, su Abdallah shi ke yawo dasu Suleim 8:30 sunyi shirunsu
kajifa yara, bangaren Amare mafa nan ake cakarewa.
Iklas zata shiga wanka Omar ya sa key a toilet din wai baza suje da wuri ba,haka ta koma na
Mama duk shirye shirye akeyi,ita kuma baza ta shiga toilet din da wasu yan biki suke shiga
ba,sauran rooms du Mama tasa musu key.
Dolenta ta jira Omar sai abinda yace.9pm sannan Omar yace tayi wanka,10pm sun gama
shiri tuni frnds din Iklas sunje can,sai waya suke mata,Sultan da amaryarsa Yasmin, Raj ma
yaje.

Kwaalliyar su Iklas fa


INA TARE DAKU MUTANENA




Asmabaffa

ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI

ⓂⓂⓂ

125-130


By
Asmabaffa




Iklas ce tayi shiri idan ba mugun saninta kayi ba baza ka gane ta ba,wani tsadajjen
material tasa na nunawa a gari,Red ne da zanen Arsh color jiki, yayi mugun kyau,duk yafi na
amare kyau da tsada,dan Omar ba karamin kudi ya zuba ya siya ba,Riga da skert ne,tasha
kyau kamar Ku saceta dan tsayawa ma fadar yanda shape dinta ya fito bata baki ne, Omar
yasan size dinta mayene.takalmi me tsini arsh da wata shegiyar pose yar gaske same color da
shoe,Omar ya fito daga wanka sai da kyar ya tabbatar wannan Iklas ce,
Iklas fa har gwagwaro itama ta kai aka Nada mata na kece raini,gashin nan ta gyara jelar
na reto a tsakiyar baya murtukekiya,ta fito da ita ta tsakiyar goggoro,dama ga jiki yasha gyara
ko ina kyalli takeyi,turaruka kuwa sai da Omar ya koreta,zama tayi tana jiransa yana shiryawq
tana ta guntse dariarta wai ganin sandar girman Omar a short wando,yana kalonta ta gefen
ido,kin San Allah zanyi maganinki ki koma Palo ki jirani kan me zaki sani gaba ki dinga kallona
kina daria,baki ta rufe da tafin hannu nayi shuru to.

Harara ya watsa mata yana ta shirinsa tana satar kallon jiki da kira me kyau irin na Omar,
Allah ya bashi diri da kyau ga skin dinsa kalarta ta kwashewa Iklas Imani,
Wani rantsatsen yadi me taushi Omar ya sa,shara shara sosai arsh color kalar material din
Iklas komai Arsh yasa,dinkin zamani dai dai jikinsa wandonma,Omar uban yan wanka suma taci
wani gyara me kyau,tayi luf,turaruka ya fesa sosai,ya fito kwas rike da waya,Iklas ma wayarta
fankaceceiya a hannunta,mikewa tayi daram ta isa wajensa yaya Omar kalli fa kayanka shara
shara har singlet ana gani,wandonka ma dan an masa landing daga samane amma ai sai
adinga hango uhmmm.....uhmm....da ka canja shadda ma ,ke jikinki ko nawa ina ruwanki cewar
Omar.kowa ance miki irinki ne me kurawa mazan wasu ido,let's go idan zakije if not na tafi,
Ita Iklas kar a kallar mata kyallin fatar miji,gashi tasan dole Sahar tana can.

Hannunta ya rike suka fito duk gidan Shuru sai yan aiki da suke aikin gyara gida kafin a
dawo.
Wata sabuwar mota fil arsh color itama Omar ya bawa driver key a baya suka kame kamar
sune amarya da angon,kajifa yan fassion
Har wajen driver ya kaisu,tun daga waje zaka San wajen ya girmi me karamin karfi.
Sahar da frnds dinta an kwafe a kujera tana baza idon ganin Omar,dama su gulma ce ta
kawosu da niyar wulakanta Iklas gaban mutane,
Amare da Angwaye ana kujera an fara shagali suna kallon masu rawa da liki,su Kansu Omar

suke son gani saboda frnds dinsu su kalli haduwa,najja da sauran kannensu sai iyayi akeyi a fili
ana kada hips,kaji kannen Amarya fa.Iklas ce ta masa rada pls ka fita munzo fa idan ka fita ka
bude min kofa na fito a Gomnati ta.
Driver ne ya budewa Omar kofa.
Murmushi Omar yayi tare da fita cike da kasaita,omar kuwa zagayawa yayi ya budewa
Gomnati itama ta fito,tana fitowa zuruf ta sakalo hannunta Dana Omar ta kara shigewa jikinsa
kamar zata shige jikinsa gaba daya ba space da ko tsinke zai iya shiga.wani kar kar kawai
Omar ke ji a cikin jininsa kawai Iklas yake bukata, kara manneta yayi suka tafi domin shiga hole
din,

Duk Wanda yayi tozali dasu sai ya saki baki da ido dan kallon kyau irin nasu,ga iya wanka,ga
shiga me tsada da ka gani ba sai ance ba,gasu sun birge masoya da gani wannan real love
ne,dama Iklas tace bikine daga mota sai hole shi yasa taki daukan gyale,

Sultan da Raj suka fara gani cikin wurin,daria suka dinga yi sun San Iklas sarai, wuyan
Sahar da frnds dinta kamar zai tsinke dan kallon su Omar,suma su Najja sai nunawa frnds
Omar sukeyi ga yayansu babba,wajen da aka tanadar masa najja ta nuna masa suka
zauna,Mama da Ummi suna can baya sunga su Omar har murmushi sukayi,Iklas ba dama
cewar Ummi.

Duk Iklas ta kasa sakewa yanda taga yan mata na kallon Omar,kamar tayi kuka,shi kam
Omar ta kansa yakeyi ganin Saleem a wajen su Angel kawayen Iklas,
Yayan amare aka kira kan ana so ya chashe a fili dama Iklas ta matsu su shiga fili rawar
Igbo zatayi yau tace, ai kuwa kafin Omar ya juyo sai gani yayi Iklas har ta danyi doro kamar
zatayi ruku'u tana ta kada hips,tafi da ihu fili ya dauka kafin kace me an rufeta da liki maza da
mata,su Kansu su Sadiya ta birgesu rawar, Maman waleeda ma sai liki takeyi sai da ta karar da yan kudin cefanen da Baban waleeda
ya bayar na 1mnths,kinga ta kanki da me zasuyi girki,Jamila sule,Haj jamila duk sai balle bakin
jaka sukeyi,Zulaihat da su Juwairiya duk an Hallara a fili,sai Diyar katibi me gyara fili ce tazo ta
koresu kasa tukunna.
Omar sannan ya fara likiwa Iklas yan dubu dubu,itama mikewa tayi ta gama rawar ta fara
barin kudi musamman Omar ya bata dama,masu DJ sun washe da Naira, Omar ne ya janye
Iklas suka koma mazauninsu sai radar masifa yake mata kan tayi rawa,
Angwaye da Amare na fitowa suma sai da su Iklas suka yi ruwan kudi.su Aisha ransu ya
fara baci fa anzo gidansu ana satar musu dukiyar Uba ana bawa wata banza,
Sahar takaici ya kamata ganin inda Iklas ke barin kudi Omar ne kuma yake bata,a gabansu
ma ta karbi wasu,ita kuwa sahar taga ko time din da take matarsa baya bata haka.

Da kyar ya bar Iklas taje wajensu frnds dinta da saleem suka gaisa sai kiranta yake a waya
ta dawo wajensu,komawa tayi ta barsu suma suna kallon ,tana zama Sahar ta karaso
wajen,hararar Iklas Sahar tayi,Iklas ma ta rama harda karin Jan tsaki,

Sahar dauke idonta tayi ta kalli Omar how far kwana 2,ko da yake nasan wasu sun manne
maka yayan matsiyata,sun hanaku sakewa a gid....saukar ruwan lemo me sanyi Sahar taji a
fuska da kirjinta,wacce ba kowa bace tayi sai Iklas,Omar kuwa yaga sanda Iklas zata aikata
kyaleta yayi ta rama. Kawayen Sahar ne suka zo da niyar dukan Iklas Sahar ce ta hanasu Ku bari a gama party
tukun,komawa wajensu sukayi suna jiran a gama party su karya Iklas,
Iklas kuwa hankalinta kwance tasan gata ga Omar.

Frnds din Iklas ma sun zo sun gaisa da Omar,dinner party yayi dadi gaskia,haka har aka
fara tafiya gida,su Mama ma sun tafi,Saleem da frnds din Omar Dana Iklas duk sun tafi,Iklas ta
rakasu ta dawo wajen Omar wani Frnd dinsa ya tareshi yana ta jansa da surutu kuma wannan
duk plan din Sahar ne,
Radawa Iklas yayi je ki jirani a motar mu,tana fitowa ta ci karo da su Sahar sunyi da'ira,ta
tsure ganin ba Omar gashi mutane sun tafi,ta tsorata sosai, amma bata nuna ba,sai ma
murguda musu baki da takeyi tana ja baya,
Sahar kukan kura tayi ta damko hannun Iklas daya, tana danna mata ashar iri iri,

Kawaye na zuga Sahar,da dabara Iklas ta dago kafarta ta Ciro takalmi daya me tsini ai kuwa
ta kwalawa Sahar a kanta wajen ya fashe sai jini,arcewa Iklas tayi tare da banke wata kawar
Sahar dake kan hanya,da gudu ta fada motarsu tacewa driver sa lock.haka driver jiki na mazari
ya danna lock, Sahar sabo da bacin rai ji tayi kamar ta kashe kanta ta huta,jikin Motar tazo da niyar shako
Iklas amma ina a kulle gam,Iklas lekowa tayi tana ta yiwa Sahar gwalo iri iri, ta murguda
baki,tayi fari da ido,ta kebe baki,ta tale mata baki,ga gwalo.iya kuluwa Sahar ta kai
karshe,juyawa tayi suka shiga motarsu da frnds dinta suka wuce da niyar irin hukuncin da zasu
yankewa Iklas idan Sahar ta koma gidan Omar.

Gaba daya Sahar tace sai ma ta kashe Iklas du.
Queen mermu ma kungiyarsu duk sun tafi dama kallon bikin yan gayu suka zo, 2:30am
Omar ne ya fito tare da bude mota ya shiga,shigarsa ke da Wuya ya ga Iklas sai gyangyadi
takeyi,
Mikar da ita baki isa kinmin bacci ba a mota wa yace kizo sai da na hanaki zuwa amma kika
ce ke sai kinzo Ashe burinki kiyi rawa ki kadawa maza jiki,kinci sa'a daya muna wajen mutane
da na nuna miki yanda ake ball da mutum.

Cike da jin bacci ta kwanta a cinyarsa pls ka barni nayi bacci,kyaketa yayi tare da Dora
hannunsa kan cikinta,dayan hannun kuma yana cire mata goggoro kanta,wai taji dadin bacci,
Munafuka Iklas idonta ras baccin karya takeyi wai dan kawai taga yanda Ya Omar zai
lallabata,sai dariya takeyi a boye,

Kara juyi tayi tace wash na gaji kafafuna,takalmi ya zare mata ya Shiga dannan mata
kafafun.

Iklas aranta tace inye ni din ba,naji dadina tun ban shiga ciki ba kenan,kai Allah ya Omar so
na yakeyi, duk a ranta take zancen ta

Kukan shagwaba ta fara uhm..uhm...uhum..bakinsa ya kara saitin kunnenta yana matsa
mata kafafu a hankali yace ya akayi wai?yunwa nakeji ni,tuni Omar ya bawa driver umarni ya
kaisu wani tsantsararen eatery suyi take away.
Anzo wajen Iklas ta hana Omar tashi Sam wai ni....ka aiki driver ya shiga ya siyo,haka driver
ya je ya kawo gashashiyar kazar hausa,da h-bugger sai chips da kayan sha na sanyi.
Sunzo gida tace Sam baza ta iya takawa ba,abin na Iklas da iskanci cewar Omar kayan ya
kwasa yayi gaba abinsa,dole ta fito takalminta a hannu ta shiga part dinsu,kowa yayi baccin
gajiya gidan shuru,
Wajen Ummi taje ta ganta tana sallar dare,sallamewa Ummi tayi Iklas ki dawo ki kwanta nan
nafa gaji da halinki,kinbi kin nacewa mutum ki ja ajinki namiji ya biyoki amma ke kamar ba mace
ba.

Turo baki Iklas tayi in kun San hakane me yasa aka bashi ni,kuka aura masa ni,in hakane
Ku kyaleni yazo ya nemi auren da kansa mana sannan Ku bashi ni.

Amma kun masa aure kun hana bawan Allah matarsa,Ku fada masa ma ni matarsa Ce kun
kasa, kun hana mu fada,ni wlh in na gaji fada zanyi,kune kuke ganin abinda nakeyi a rashin
class mu zamanin mu irinmu ake nema,
Baki Ummi ta saki tana kallon Iklas,carbi ta Zara ta zabga mata a baya yar banza wacce bata
da kunya ko daya wajen ubanki kikayi gado bazanga laifinki ba,haka shima yake akan matar sa
bashi da kunya.tafi ki bani waje kije kiyi ta kwana dakinsa.
Idan ya miki ciki ke kika jiyo,daria Iklas tayi wlh ni kuwa na haifo Dana kece zaki min wankan
jego amma sai ya Omar ya yarda,kuma Allah ki gasa masa cibi ta gasu.

Banda mugunta ki sa yaronmu kuka ki shaka masa sabulu wajen wanka,Ummi ji tayi Iklas
ta bata kunya ma,ba shiri taci gaba da sallarta.
Wanka Iklas tayi tana fitowa taga Omar ya kawo Mata take away,Ummi tana ta Sallarta taga
Omar ya wuce wajen Iklas sai rada sukewa juna bata San me suke cewa ba.

Iklas ta koyawa Omar rashin kunya cewar Ummi, yaro nutsatse ya susuce kan mace ni na
gaji ana gama bikin nan a bawa yaro matarsa su karata can,zan sanarwa mahaifiyarsa.
Abincin da suka siyo ya mika mata yace karba,ki tabbatar kinci da da yawa,zan kiraki
anjima na tabbatar kinci,

Ummi ya juya ya kalla Ummi sallah kike yi dan Allah ga amana nan kisa taci da yawa tayi
bacci ta huta gobe daurin aure da safe baza ta samu damar yi ba,
Sallamewa Ummi tayi ba shiri tace kaci gidanku Umaru,dan iyayenka kaima ka zama
fitsararre ko,Ku kiyayeni,murmushi yayi ya kalli Ummi zanzo Ummi idan na samu time zamuyi
wata magana.Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login