Showing 15001 words to 18000 words out of 107121 words
Chapter 6 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
siririn gyale orange wai ita a dole zata birge,tayi shiga me
kyau,don kaya manya su atamfa nauyi suke mata,bata saba ba sam,batan me yasa take so yau
tayi kyau ba.wuce su omar tayi a Palo ta koma kitchen hade da kiran suhaila,abinci suka Jere a
gaban omar,kallonta omar yayi tayi kyau amma wai ita bata sa kayan kirki ne?ga bako ai
kamata yayi ta suturta jikinta,wato kowa haka yake kalleta tab,ummi ce tayi magana umaru bari
inje makwafta zanyi ta'aziyya anjima kadan zan dawo ba dadewa zanyi ba ka jirani,ba matsala
ummi sai kin dawo,kallon iklas ummi tayi tace sai ki zauna wajensa na dawo uwar giggiwa
kullum aikinki kenan yawo da watsatsun kaya,zigidir kullum da kayanki ba babu.
Umaru kaci abincin dan Allah kaji,ko albarka kasa mana,kar ka bari na dawo na tarar baka ci
komai ba,bazan ji dadi ba.ok ummi cewar omar.
Fitar ummi keda wuya dakin yayi dif ba Wanda yayi magana ga suhaila tayi bacci,sadda kai
kasa iklas tayi bata son kallon omar wani faduwar gaba take ji,
Kallonta yayi fuskar sa daure,ke a tsawace yayi maganar wato bakyajin magana ko,tun baki
tafasa ba za ki kone kamarki har kin isa zuwa wani party kuma partyn na wasu tambadaddun
yare,tsohuwa na zaune daku kina bata mata rai,ki kiyayeni wlh,da na kowa ne bar ganin bamu
hada dangantaka ba duk lokacin Dana kamaki,ko na ji kin yi abu rubbish sai na hukuntaki.itafa
iklas mamaki ya gama kasheta irin karfin halin omar,ina ruwansa da rayuwarsu wai,sai kace
ubansu,ko wani sabawa dajuna basuyi ba amma yake wani fada haka,lallai ma,Nima asmah
naga shishigin omar anan.
Turo baki tayi to birthday din maman ola ne fa sir,kuma....shut up ba inda zaki .to ai dama na
hakura sir cewar iklas a sanyaye,karma ki hakura.shuru dakin ya kara dauka can tace sir?Ina
jinki,kaci abincin mana to,jagwalgwalonki zanci an fada miki ina cin girkin irinki,dama ummi ce
tayi sai na ci.shuru ta masa dan taji haushin kalamansa,ta rasa why take daga masa kafa,ita da
take masifaffiya bata kyalewa amma akan omar ta kasa daukan mataki.ba komai ko dan
taimakon da yayi mana zan dinga kyaleshi.bani ruwan nasha kawai s ok ma maganar omar ta
katsewa iklas tunani,da sauri ta mike ta fara tsiyaya ruwa a wani glass cup me kyau da
tsafta,cikin izza ya karba yasha hade da mikewa tsaye idan ummi ta dawo na wuce ni ki sanar
mata
Pls ka bari ta dawo mana ko ka tsaya na kira ta yanzu pls,sallamar ummi sukaji ta shigo
palon,yawwa ummi zai tafi wai cewar iklas kuma baici komai ba wlh,hangame baki ummi tayi
haba umaru ya zaka Mana haka,mu ka taimakamana mun yarda mun karba duk da bamu
sanka ba,ba dangin iya ba na baba amma mun yarda da kai,yanzu dan mun baka abinci shine
baza ka ci ba,kamar mun baka guba ko wata cuta.
In dai kana so mu shirya gaskia kaci ko kadan ne idan kuma kyankyami kakeyi bazan ma dole
ba.da sauri omar ya koma ya zauna haba ummi ba wani abu kiyi hakuri bari naci.baki ummi ta
washe haba ko da kaifa amma ai sai ka sa muji ba dadi ai,iklas zuba masa bari naje na karasa
gyara wasu kaya.omar ji yakeyi tsohuwar na birgeshi,kallonta yakeyi kamar mama.
Tana bude flask wani kamshi ya daki hancinsa me dadi,fried rice lafiyayya tasha hadi da su
hanta etc,zuba masa tayi ta kara bude wani bowl me kyau na glass kaji ne soyayyu zuba masa
tayi a gefe ga hadadden salat,mika masa tayi ta zuba masa lemon kwakwa.
Yatsina fuska ya dauki spoon da kyar ya fara ci,wani arnen dadi yaji kamar kunnensa zai
fita,sai santi yakeyi a ransa a fili kuwa yatsina fuska kawai yakeyi,iklas na kallonsa kafafunta
sunyi sanyi tun a fuskarsa ta gane baiji dadin abincin ba,kamar zatayi kuka bata San ace
girkinta baiyi dadi ba.
Musamman a wajen Omar bata San me yasa take so ya yaba girkinta ba.idonta har ya Tara
kwalla kadan,omar yana kallonta ya gama ganota tsab,a ransa sai daria yakeyi,ganin kaka
ummi bata kusa yasa yake ta wannan yatsina fuska,tunda yaga yanayin iklas ya kara yatsine
fuska dan yanzu har yi yakeyi kamar zaiyi amai,abin mamaki yaci abincin yafi Rabin plate,lemon
ma yasha yaji dadi amma harda rike ciki wai a dole yaci guba.can yace kai ummi ta takura naci
jagwalgwalo,babu dadi haka akeyin girki,wannan ai sai ki kashe mutane.
Hawaye ne ya digo dis daga idon iklas da sauri ta goge kar sir omar ya gani Wanda ta Riga
ta makaro a idonsa tayi komai.kitchen ta shiga sai gata ta fito da wata Leda me kyau a
hannunta,mikawa Omar tayi ga wannan ka kaiwa mom dinka,
Tunaninsa ne ya tsaya cak wannan yarinyar akwai mamaki acikin alamarinta,wai tana 15yrs
har tasan ta bawa mamansa kyauta yaji dadi kuma ta kara birgeshi.karba yayi hade da cewa
tnx kira ummi,sai gani yayi iklas ta tsaya rubutu a jotter bai San me ta rubuta sai da ta gama ta
wuce kiran ummi,ita kuwa iklas ta Riga tayi lissafi wannan week din sunyi dambun naman kaza
gashi basu ci ba ta bayar kyauta,shi yasa ta canja lissafinta..sallama omar ya musu ummi ma ta
bashi sakonta ya ba mama,
Gidansa yaje ya duba lafiyar sahar sabo da amanar aure dake kansa,yar aikinta ya
tambaya ina sahar ?ranka Dade tayi tafiya yau tace a fada ma ta tafi kasar ghana akwai wani
aiki za suyi..ok kawai yace ya koma gidan mamansa,abinda Omar bai sani ba sahar ta kara
lalacewa sai matan manyan alhazawa take kulawa Wanda suke da naira,wata kawarta hajiya
talatu matar wani gomnace ita ta bawa sahar shawarar tunda kullum a hanya take ga mijinta ba
wani shiri sukeyi ba kuma sahar akwai tsananin sha'awa kawai tunda tana da kudi a hannu ga
maza nan samari yara sai ta zaba tunda yanzu matasa sun zama kwadayayyu kudi suke nema
ta ko wacce hanya komai kudi,to ta mori dukiyarta ta samu wasu suna biya mata bukatarta tana
biyan kudi.amma ta daina zubar da ajinta wurin omar mijinta tunda shi baya taba nemanta itama
ta daina kai kanta.wa'iyazu billah mai makon muyi kokari mu gyara halinmu sai mu kara
dilmiyewa mu jefa kanmu halaka wacce har ka mutu kana da na sani.Allah shiryamu gaba
daya.dan yanzu wannan ya zama ruwan dare wurin wasu matayen musamman masu naira
Mama na room dinta tana shafa magani a kafafunta da suke mata ciwo omar ya shigo da
sallama,da fara'a ta amsa masa babanmu ina ka shiga ne haka ban ganka ba,maganin ya
karba ya karasa shafa mata,ina gida mama ga office ba sauki,omar kenan na dauka ma ko
suruka ta biyu ka samo min,murmushi yayi mama aure tun yanzu zan kara aure,ina zan kai
matan dayar ma da za a yagemin ita so nakeyi,daria mama tayi omar sai hakuri dan kawai ba
auren so aka maka bane kuma matar taka ba ayi dace ba shi yasa ka fadi haka,
Mama kinji yanzu na dawo gida wai ta bawa yan aiki sako a fada min ta wuce Ghana,duk
yawon da takeyi kasar nan bai isheta ba mama.mama ma ranta ya baci da jin abinda sahar
tayi,ka bari zanwa baffanku magana a waya sai aje gidansu a sanar da iyayenta tunda ta Gagari
kowa,ni ma zan kirata a waya,mama ki kyaleta pls kar tazo tana miki rashin kunya kin San
bazan kyale ba.ya isa omar dole a fada mata gaskia.to mama ba matsala.ledar da iklas ta bashi
ya mikawa mama,ledar kaka ummi ma ya mika mata gashi mama sunce a baki kuma suna
gaisheki,murmushi tayi na gode Allah saka,amma banana wannan su waye suka bani bazan
bude ba sai ka fada min,ohh mama wannan red din na kaka ummi ne wannan kuma na jikarta
iklas,
Murmushi mama tayi tana jin dadi tana fatan abinda tayi tunani ya zama gaske,a fili tace ban
ganesu ba ai...uhm..uhm yana Sosa kai yace aikine ya hadamu gidan gona.kyaleshi mama tayi,
tace angode kaga mutanen kirki bari mu gani mene ciki.
Ledar iklas ta fara budewa wata katuwar farar roba ce mai murfi shake take tam da dambun
naman kaza iklas yinsa tayi musamman sabo da suhaila na sonsa ganin omar yasa ta canja
idea ta juye masa duka me uban yawa ta bawa mamansa.mama taji dadi sosai,ta bude ledar
ummi kayan kamshi ne da sauran abubuwan miya busassu.mama sai murna takeyi omar har
mamakin murnar mama yayii,babana ya kamata ka kawo min su na gansu ko ka kaini
gidansu,ba yanzu ba mama to allah kaimu koma yaushene.kasan bana cin maiko sabo da ulcer
ta,kadan zan iba ni da su abdullah.dauki wannan kaje dakinka dashi..da kyar ya karbi na robar
wai a dole bayacin girkin yara,amma ya dauke ya wuce room dashi yana bata rai da muzurai.
Sadiya na hango sai masifa take zazzagawa tana dura ashar a compound din gidan,duk
wani ma'aikata sunyi luf suna jinta,suleim na hango da uniform jikinta tsugune a gaban sadiya
tana faman bata hakuri,anty sadiya kiyi hakuri ban San takadar tana da amfani ba shi yasa
Dana gani na yaga na zuba a dustbin,
Wani lafiyayyan mari sadiya ta kwadawa suleim Allah sarki yar yarinya sai ga shatin
hannun sadiya radede a fuskarta,kuka ta tsala hade da dafe kumatunta,gashinta sadiya ta ja da
karfi dan uwarki baki San darajar takarda ba,gadon tsiya ba laifinki bane uwarku ba ilmi ne da
ita ba jahila ce shi yasa Baku San darajar takarda ba,tsabar masifar da sadiya keyi ko kula da
motar omar wacce ta shigo har ya parker bata sani ba,hankada suleim tayi ta tintsira ta bige
kanta da bakinta,wani gigitaccen kuka ta fasa,omar Wanda yana kallon abinda ke faruwa ransa
ya baci,idonsa yayi jajir,zuciya ta tashi,karasowa yayi wajen ya ware hannu ya dinga zubawa
sadiya mari,tun tana tsaye sai da takai kasa,belt din wandonsa ya zare ya fara zabgarta gashi
ya riketa ram sai daya zaneta tas jikinta duk ya fashe,a hakan ma dan mama ta fito ta rikeshi
ne,duk yan gidan suna wurin suna kallo,kafin kace me su Aisha naja sun kama zage zage
suma,sannan suka kira baffa da ummansu dake Russia suka fadi karya da gaskia.
Nanfa hajiya rahina ta haukacewa baffan su omar,wlh bazan yarda ko a dauki mataki ko na
dauka da kaina,an Dade ana zalinta ni da yarana Sam bazan yarda wlh,akan haka sai dai in ka
sakeni amma billahillazi bazan yarda ya kashe min yara ba.tsawa baffa ya daka mata ki saurara
min shashashar banza,duka kannensa ne yana da damar hukuntasu,nasan dole omar yana da
dalilinsa me karfi,yaran naki bansan halinsu bane an fada miki, marasa tarbiya omar ne wakili
na yana da daman yanke komai a gidana.kuma wlh tun kafin na koma ki fada musu dukkansu
su fito da miji,na gaji da zubar min da mutunci da sukeyi a unguwa..... Wai wai ai rahina
kururuwa ta sa da gunjin kuka,baffa kuwa gidan ya bari.
Asmahbaffa na godiya gareku masoya readers,masu commenting idan nayi posting kunfi
kowa birgeni, domin kuna bani kwarin gwiwar typing, na tabbatar kuna jin dadinsa.
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
10-15
By
Asmabaffa.
Pls readers a dinga kula ana amfani da sakon da muke isarwa me kyau,marar kyau ayi
watsi dasu, bukatata kenan,kuskuren da mukayi Allah yafe mana kuma readers ayi mana
afwa.Allah tsarkake mana zucuyoyinmu,a dinga rula sakonni nake isarwa ko wanne page lol na
gode muku yan readers dina ina ji daku.kunyi male male araina.
Tunda baffa ya fita taki daina kuka sosai take sheka kuka an Zane first daughter dinta me irin
halinta sadiya,sai da ta koshi da kuka daga bisani ta jawo wayarta,ta kira haj bilki babbar
kawarta tas ta kwashe zance ta fada mata,lallai yaron nan kwai tsinane tambadadde cewar haj
bilki,rahina tace shi yasa na fada miki kije min wurin babban malaminki na kasar Mali ayita ta
kare,na gaji da tsinannun mutanen nan,akan wannan zan iya dawowa Nigeria muje tare bilki ki
rakani,duk wanda na sani nawa malaman ba kudin da ban kasheba abu shuru,nasan naki
manyan shegu ne,daga bangaren haj.bilki baki ta tabe daga bisani taji dadi a ranta tana adduar
insha'allah bazaiyi aiki ba,yar iska wai ke mijinki me kudi har yanga kike mana kin fimu kudi,ga
yaranki masu aikin gomnati,ai sai na miki sanadiyar barin gidan alhaji mohd wlh,hauka nake na
yarda ki samu daula ke kadai,Baki San yanda nake miki bakin cikin auren alhaji mohd ba,dan
yafi mijina kudi...
Haj rahinace ta katsewa bilki mugun tunanin dake ranta tana ta hello....hello....inajinki
network ne wlh rahina,kina jina ki kwantar da hankalinki ni danake babbar kawarki ai dole zanje
kasar Mali ko dan ke,ki bar komai hannuna,ammafa sai kin turo isassun kudi,babu matsala
wannan cewar rahina,kuma dole sai mun haada da tuggunmu na mata.kin san yanzu sunfi tsafi
aiki wajen maza,wasu maganganu haj bilki ta tsarawa haj rahina wanda koni banji me suke
cewa ba readers.
Suna katse wayar haj rahina tace shegiya haj bilki tasan takan duniya....banza marar wayo
yar matsiyata kina taimakamin na samu abinda nake buri ko kawa nafi karfin nayi dake,jahilar
banza yaushe ma inba dole ba zan tsaya ko kusa dani ki raba,iyakarki primary schl.nan umma
rahina ta kwashe da daria,a karshe tace har a bada bilki sai dai ki zama baiwata ba kawa ba.haj
bilki kuwa tsaki taja tace shashasha naci banza,kudinki zan cinye na Gina kaina,ta zata
shawarar Dana bata zata bulle,hhhhh lallai alhaji mohd zai saki dattijuwar banza zaki gane
wace bilki.
Kunji fa readers ko wacce cin amanar ko wacce takeyi,kuma wannan cin amanar ya zama
ruwan dare tsakanin kawaye musamman mata,kowacce bata son yar uwarta taci gaba
hassada,ga mugun nufi wannan ya zama ruwan dare a rayuwarmu ta yanzu,taya zamu ga dai
dai wannan ya jefi wannan ,wannan ya jefi wannan.Allah ka tsarkake mana zuciyoyoyinmu.
Bangaren su oga omar kuwa abin nasa yaci tura,da kyar mama ta janyeshi suka dauki
suleim,family doctor mama ta kira yawa suleim dressing,abdallah harda kuka an jiwa kanwarsa
ciwo,omar kuwa jikinsa sai rawa yake ran maza ya bacifa readers,dama can ya gaji da halin
kannen nasa,sharesu kawai yakeyi amma komai da sukewa mama da kannensa ya sani
kyalewa yakeyi dan a zauna lfy,amma tunda haka suka zaba zaiyi maganinsu idan basu nutsu
ba.sadiya kuwa sai ihu takeyi jiki ya kumbura,sun hadu a kanta su Aisha suna ta Gasa mata jiki
yayinda suke ta zage zagensu iri iri,sadiya kuwa jinsu kawai takeyi dan Allah ne kadai yasan irin
matakin da zata dauka kan su omar da uwarsa,dan tayi alkawari ko zata mutu,ko zata karar da
salary dinta sai ta kulla musu bala'i,yanzu ta fara ta daina jiran ummansu yanzu itama ta zauna
da kafafunta daram sai taga karshen omar da wanda ya rabeshi gaba daya...ruwan zafin da
Aisha ta danna mata a gefen wuya shi ya dai daita tunaninta ta saki kara da ihu hade da cewa
Aisha zanci uwarki kasheni zakiyi.tana ta ciccijewa sabo da azaba..ni kuwa nace heeee..na fece
daga wurin,
Omar bakin ciki ya cunkushe masa zucia,haushin gidan yakeji gaba daya,mikewa yayi ya
bar gidan gaba daya,har ya dauki hanyar office din sultan ya fasa ya canja hanya,dan yasan
idan yaje wurin sultan bacin rai zai kara masa,da gudu na bishi readers na tafi
gulma....lol.mayenta layin su iklas na ganshi gheto area yana Jan motar a slow yau 6days
rabonsa da gidan,a tsakiyar layin gefen titi ya hangota tana magana da wasu maza igbo su
biyu,sanye take cikin uniform 1:30 da alama daga schl take,
Wani bakin ciki ne ya kara mamaye cuciyar oga omar,ya kwaso bakin ciki yaci karo da
wani,haka kawai ya tsinci kansa cike da bacin rai ganin iklas da wasu kucakan maza Igbo,tana
ta surutunta hankali kwance.omar na karasowa wajen ya danna wani horn da karfi wanda ya
janyo hankalin kowa dake wurin suka zubawa shegiyar azababbiyar motarsa na mujiya,cikinsu
harda iklas me dafaffen kwai,glass ya sauke sukayi 4 eye da iklas,alama ya mata tazo sallama
tayiwa mazan Igbo bye Emma a gwarance suka ce gomnati gomnati murmushi iklas tayi tare da
mikawa Emma hannu suka tafa hade da cewa NO BE SMALL THINGS WOOO,Dayan Dennis
yace,ur first salary is my share,nanfa gomnati tace,never mind A NO DEY CARRY LAST MY
BRO,daria sukayi dukansu sannan ta daga hannu tana WE GO RUNNERM,U ASEY DEY
NOOOOW.ta nufi motar omar kafin ta karasa wani bahaushe saleem yace gomnati sai kinci da
biro hannu ta daga masa tare da bude gaban motar ta shiga,ta glass ta leko da kanta tace
saleem salary na farko da kasonka ciki,fisgar motar omar yayi ji kake gwaf kan iklas ya bigi
gaban motar,birki yaci kyaaaaa....ta koma da baya jagwaf...kafin ta nutsu ya kara fincikar motar
ta kuma gwaraf da kanta a jikin glass,kuka ta kece dashi yanda zafi ya hadata ta ko ina.cisgar
motar omar ya karayi kamar