Showing 6001 words to 9000 words out of 107121 words
Chapter 3 - MA'AIKACIYAR GOMNATI BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
maimakon hakuri sai zagi,ledar hannunta ta apple ta ajiye gefe,gabansa ta
sha ta rike kugu hade da harara,malam kamin laifi da barna ka kasa bani hakuri sannan ka
zageni,da nayi niyyar yafe ma amma wlh tunda ka zageni ka kasa bani hakuri to ba kira ba
abinda zaici gawayi,sai ka biyani each and every egg da ya fashe,dan akanka bazan dauki
asaraba,
Daria yace ta kamashi ya danneta,bai taba haduwa da funny girl haka ba sai yau,yar
yarinya da Karin magana haka,ga masifa har wani jijjiga takeyi gaban katon namiji kamarsa.
Allah ya taimakesu ba wasu mutane wurin sai masu shirya fruits,tasowa sukayi daya daga
ciki yace haba gomnati basai kinyi fada ba za a biyaki,shine me wajen,a fusace tace dama
haushinsa nakeji ni time din daya shigo yamin kallon Tara saura kwata,dan haka wlh sai ya
biyani,tofa wannan yarinya da kuruciya sosai kanta ga tsiwa cewar Omar aransa. Wasu
ma'aikatanne suka zo wajen suna haba gomnati ikon allah bamu sanki da haka ba,wani ciki
yace the manager wannan oganmune fa,murmushi ta saki jin an kirata da sunan da tafi so wato
gomnati, Wanda ya tafi da imanin Omar, tace to na yafe masa sabo da Ku
Gefe ta matsa tana gyara bokitin kwanta hade da kunkuni kawai an cuci mutum,wannan
days fashe ni haushina ma daya asararsa da akayi,yanzu wannan ya ishemu mu soya muci da
su ummi har na 5days,ko mu soya doya da kwai ta kwana biyu,ai kuwa da munci dadinmu.duk
surutun nan da takeyi Omar na jinta,sai daria yakeyi a zuciyarsa,yarinyar so funny,ya dade
rabon da yayi nishadi irin na yau,kwai aka kawo mata guda 100 a Leda,kallon mutumin tayi
laaaa ai nace na yafe masa wlh,ai oga ne yace a baki gashi guda 100 ma aka baki kinci
riba...no na yafe ai,fafur iklas taki karban kwan nan,,sunyi sunyi taki karba,Omar ne ya karba
hade da daka mata tsawa karba ban son shirme,tsoro ne ya kamata,taf aka cika botikinta da
kwai,aka kara mata apples da yawa sannan aka mika mata kudinta,mamaki tayi sosai ta kalli
Omar a tsorace na gode oga Allah kara arziki,sosai yaji dadin adduar ta matarsa bata taba
masa ba,sai wata a titi,it's OK zaki iya tafiya, uhm....uhm.....dama oga dazu kaga fadan Dana
ma,nayi ta masifa rainane ya baci kanwata na aika taki zuwa,shine raina ya baci,amma
maganar gaskia bada kai nake ba,da kanwata nake.
Murmushi Omar yayi Wanda yasa iklas sandarewa ganin kyau da dimple na Omar,shi kuwa a
ransa yace yarinyar nan da wayo take.a fili hade rai yayi ya tabe mata baki ya shige mota driver
ya ja suka wuce.itakam taji haushin tabe mata baki da yayi,ya rainata.anyway sun sami kudin
abinci lallai yau tazo a SA'A.
Yau taga lailatulqadari sunan da ta lakabawa Omar kenan kayanta ta dauka da kyar ta nemi
taxi,kayan sun mata nauyi,ga murna an vata komai kyauta,shi yasa yau ta shiga taxi,ta matsu ta
koma gida ta bawa kaka ummi labari.
Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
5
By
Asmabaffa
Har kofar gida me taxi ya sauketa da kayanta,da sauri ta shiga da kayan ta fara kwalawa
ummi kira tsohuwa kaka ummi...ummi...tsohuwa wai kina ina haka,ke lfy kike rafka min kira
haka kamar kina bina bashi cewar kaka ummi,iklas ce ta rungume ummi tana ummi lailatul
kadari na gani yau,kinga yau komai kyauta aka bani kwai da apples ummi sai nayi 1wk banje
sari ba,duk na kyauta zan siyar,kinga kudin yanzu zamu tafi kasuwa dama abincin mu saura na
kwana daya,
Kaka ummi ce ta kalleta da murmushi tana mai cike da farin cikin kalaman iklas,to iklas wai
waye lailatul kadari naga ta kaina yar nan karfa kiyi mana sabo,ummi oga ne me gidan kajin ya
bani komai kyauta,nan ta kwashe labari ta fadawa ummi,ummi taji matukar farin ciki,dama basu
da abinci ba kudi,
To alhmdllh iklas kece wacce ta iya tsari da lissafi sai muyi shawara,ai ummi yau baza mu
islamiyya ba,dan kasuwa zamuje da suhaila,Biro da jotter ta dauko suka zauna a tabarma nan
iklas ta fara planning,dama iklas akwai iya planning din rayuwa,nan ta rubuta abubuwan da
suke bukata ta tsara komai,ta bawa ummi na cefane taja hannun suhaila suka wuce kasuwa.
Omar direct gidansu ya wuce wajen mama,cike yake da tunanin yarinyar da yaji ana kira da
gomnati ko manager sunan ne ya bashi daria,ya kara nanatawa a ransa bai San sanda ya saki
murmushi ba,nan take ya shiga tunanin yanda take masa tsiwa a gidan gona,a haka ya karasa
palon mama
Zaune ya sameta suleim na gefenta suna game ita da abdallah,sallama ya musu ya kwanta
Shana Shana cinyar mama yana shagwaba sai shafa masa gashi mama keyi tana wani
lallabashi,dining ta jashi ta zaunar dashi,da kanta take bashi a baki har ya koshi,
Mama sosai take tausayin dan nata sabo da yanda tasan halin matarsa bata da
hali.adduarta kullum Allah masa chanjin alkhairi.Omar yayi aure amma kullum a gidansu yake
rayuwarsa,kullum babu Wanda zaice ya taba aure,Rabin kayan sawarsa gaba daya yana room
dinsa a part dinsa bangaren mama.bashi da banbanci da gwauro.mama kuwa bata hanashi.
Direct room dinsa ya wuce,wanka yayi hade da sallah ya kwanta sai bacci.iklas kuwa Niki Niki
suka shigo gida dauke da kayan abinci dai dai kudinsu.ummi ta kawo musu farar shinkafa da
miya hade da salat harda kifi,dan iklas duk talaucinsu bata yarda aci fara da yaji ba sai in suna
sha'awa ko da dalili,dan gaskia tana da son cin dadi,ita ta yarda su rasa komai suci abinci me
kyau,tunda suna Sana'a kuma suna samu ba laifi shi yasa take musu cefane me kyau na
talaka.Rabin rayuwar gidan kaf a hannun iklas take
Wanka sukayi suka zauna hira kafin magrib ta karasa,bayan sunyi sallar isha iklas ta shiga
kitchen ta dafa musu indomie da dankalin turawa harda kifi,a baki ta bawa suhaila taci ta
koshi,sannan suka ebo littatafansu sukayi karatu,nafila sukayi sannan suka haye gadonsu suka
kwanta,kaka ummi kuwa dama a katifa take kwana,wai gadon ji takeyi tayi sama
dogogo.suhaila da iklas a katon gadonsu,
Haj rahina tana ta kulle kullen mugunta kawarta na hango suna zuba hirar mugunta a zaune
a palon umma,ita da babbar kawarta hajiya binta suna shirya tuggun da zasu kullawa Omar da
mama,rahina tace binta ko wajen bokaye zan je ne?daria binta tayi tace share bokaye watarana
aikin baya ci,kin San munafukar akwai addua,mufa mata ne ba irin tuggun da baza mu iya kulla
musu ba Wanda zai jefa su cikin wani hali,ke in ta kama har gidan nan sai sun bari,tsabar iya
tuggu da sharrinmu,haba rahina kin manta mu ne, tun muna yara kin San tsiyarmu.daria da
shewa sukayi hade da tafawa, su sadiya yaran rahina sunaji sai murna suma sukeyi suna
tafawa,dasu ake shirya komai.sai kara zugasu sukeyi,
Iyaye da dama na kuskure manya manya duk wani gulma,munafunci hassada sai a dingayi
gaban yara,ana daria kaga wasu har tafawa sukeyi da yaransu mata ana cin naman wasu,duk
iyaye masu haka su sani suna gurbata tarbiyyar yaransu,da haka zasu taso suma sunayi,kuma
uwa ko yaushe batawa yaranta fada,tana wasa da daria ko yaushe da yara baza su taba jin
maganarta ba,rainata zasuyi,ba a hana hira wasa da Jan yara a jiki ba amma a dinga sanin
kalar Wanda za ayi,kuma wasa ba ko yaushe ba,shi yasa za kaga yara na dakawa uwarsu
tsawa,ta sasu abu sukiyi, suma fada mata direct baza suyi ba,sai kaga idan ubane an masa da
wuri a na rawar jiki,da yace a bari an bari,ba raini,amma mu iyaye mata mu ke zubar da
kimarmu gaban yaranmu,matsala iri iri,Allah sa mu gyara.
Omar na hango yana tafiyarsa ta takama sanye da wani blue jean pencil da red din Riga me
dogon hannu,wandon irin an dan farfasashi daga gwiwa zuwa cinya,amma ba me yaga ba dan
ba a ganin jikinsa,driver ne da sauri ya bude masa wata sabuwar arniyar farar mota,yana yin
ribas motar sahar ta cinno kai gidan,tsadajjen gogon hannunsa ya kalla yaga almost
5pm,kawayenta ya hango biyu a cikin motar.horn ta masa hade da daga masa hannu,haushi ne
ya kamashi, wurin 2days baya ganin sahar sai yau,ko yaushe tace duty dare ne da ita,kwana
takeyi a hospital,yanzu kuma da rana yawo da kawaye da shirme a gari aikinta kenan.sai shewa
sukeyi da frnds,wurin babban abokinsa sultan ya wuce,sultan doctor ne babba shekarunsu daya
tare sukayi schl a london,har secondary,sultan babansa ya rasu daga shi sai mamansa,sun gaji
dukiya ta gaske shi da mamansa,sultan baiyi aure ba amma an kai kudin aurensa gidan wata
yar beauty dinsa yasmin,a asibitinsa ya sameshi zaune a office,hannu ya mika suka tafa sultan
yace shegen kaya ya kk,ka dawo amma sau daya ka nemeni,omar yace bari Frnd kasan office
ba Hutu,baffa ya hadani da aiki,oh na zata amarya sahar ce ta boye min kai,kana can kana Jan
kaya,tsaki omar yaja kaifa dan iskane sultan,kasan komai tsakanina da ita kana min tsiya,Allah
kyauta cewar sultan,kaga malam gobe around 1pm zaka rakani wani company na baffa zan
duba aikin da akeyi,kasan da nisa fa sai an bar garin abuja.
Allah kaimu cewar sultan.wai Frnd har yau baka samu wacce kake so bane,tsaki omar yaja
karka dameni malam.daria sultan yayi yana ci gaba da tsokanarsa.
Washe gari kamar kullum 1pm tana titin kwalta sai bin motoci takeyi a round tana daga
apple da kwanta a ledoji ,ga yayyafi anayi ruwa ya jiketa da dangalalliyar rigarta wacce taje
gidan kaji da ita,duk ruwan sama ya jikata kayan sun kara dameta a jikinta,sai boobs dinta kana
kana duk sunyi caro caro,hips ya fido,gashinta ya kara kwantowa a goshinta sai digar ruwa
sukeyi,
Omar da sultan suna bayan mota a lafke driver na jansu,suka kawo dai dai danjar da iklas
take,suna tsayawa ta karaso wurin motar tasu ga iska ta taso haka take daga musu,ido hudu
sukayi da Omar wata uwar zabura yayi hade da nunata da yatsa yace you? Bata jin me yace
saboda glass din motar a zuge yake,amma ta karanta lips dinsa ta gane me yace,murmushi tayi
me kayatarwa ta daga masa hannu,itama tace oga da karfi,yaji abinda tace ai bai San sanda ya
saki murmushi ba,yawa driver umarnin zuge glass kasa,kallonta yayi yanda iska ke
daukanta,gashi ta falle mata gyalen da ke kanta gashi yaraf har kusan duwawunta,iska na
kadashi sai ta kara kyau,driver yawa umarnin karbar apple da egg din hannunta,dubu biyar
yawa driver umarnin mika mata,yana bata ta karba ta duba,hangame baki tayi ta dauki dubu
daya,dama shine kudin apple dinta da egg da suka karba,ta mikawa driver sauran,da sauri
omar ya kalleta yace karba nakine na baki,daria tayi ta glass ta girgiza kai tace tnx oga amma
bazan karba ba.lips dinta ya karanta ya gane me take nufi,hannu ta daga masa ta juya cikin
nutsuwa ta dauko dan gyalenta ta wuce,omar kasa dauke idonsa yayi daga kanta,sultan kuwa
tuni yayi suman zaune yana kallo da mamakin abokinsa tare da jinjina kyau irin na iklas.
Danja taba da hannu amma omar sai waiwaye da kallon iklas yake,yanda take kai kawo a
tsakiyar titi,yarinya irin wannan amma tana wannan sa'ar.take yaji ransa ya baci tausayinta ya
mamaye zuciarsa, yar waye wannan aka barta tana garari a titi,tana da kuruciya haka,musulma.
Asmabaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
6
By
Asmabaffa
Tsaki omar yaja,a ransa yana gaskia an cuci yarinyar nan.sultan Wanda mamaki ya
kasheshi shi yayi karfin halin taba kafadar omar frnd ,juyowa omar yayi lfy malam karfa ka
takuramin,murmushi sultan yayi yace iyye Ashe kayi sabon kamu frnd wannan zukekiyar fa
gaskia tana da kyau,amma ka bani mamaki omar duk matan turai da yawon da kayi a duniya
ban taba ganin ka kalli mace da idon rahma ba,amma gashi akan yar yarinya me talla a titi gaba
daya ka haukace ka fita a hankalinka,harara omar ya balla masa,kaga halinka ko sultan,me
zanyi da wannan yarinyar,tsaya malam nifa ka gama kasheni da mamaki omar kai da baka
shiga shirgin wani bare har ka taimaka masa ba tare da ya nema wajenka ba,hasali ko mu
maza sai mu Dade bamu ga murmushinka ba sai gashi karamar yarinya tatsitsiya kakewa
murmushi haka har hakora su fito,ka bata kyautar kudi bata nema ba,tana kin karba kana
tursasa ta kan ta karba,,harda siyan abun titi kai da baka cin abun kan hanya.
Sultan wai pls mene haka what is ur problem kasan me ya hadani da ita,za kazo kana wani
talk na shirme,yarinya karama zanso,me zanyi da wannan me talla a titi,tallan ma mafi
muni,tausayinta naji shi yasa.
Sultan ne ya kwashe da daria mai da wukar amma wlh wannan yarinyar ka fara sonta ko kaki
ko kaso.da karfi omar yace God for bit,over my death body.daria sultan yayi ya leka fuskar omar
inye anyi budurwa me kyau,gaskia ka iya zabe,dama omar ka iya murmushi haka me kyau,nima
naci albarkacin new catch dinka na gani yau,tsaki omar yaja sai kayi ai.
Driver na jinsu shima ya yarda da zancen sultan,minti kadan za kaga sultan nawa omar daria
sai dayaga omar yakai wuya wajen bacin rai ya ja bakinsa ya tsuke,dan yasan halin omar kwai
zucia da zafin rai,sultan ne yace idi driver miko mana apple da kwan nan muci girkin
amarya,omar ko kallonsu baiyi ba,ana miko kwan da apple omar ya fisge a hannun sultan,baka
isa kaci abun nan ba sultan,
Daria sultan yayi au na manta hannun amarya ya taba abun kana kishi kar mu rigaka ci.shi
dai omar shuru ya musu,har sukaje suka gama abinda zasuyi omar na fushi da sultan,a
hanyarsu ta dawowa omar sai zare ido yakeyi ko zai hango iklas bai ganta ba.
Sultan ne ya kalleshi ya kara kwashewa da daria am sorry Frnd ban San dariar zata fito
ba,amaryar ta tafi gida ka daina waige waige,tsaki omar yaja ya dauki apple daya cikin Wanda
ya siya wurin iklas glass ya sauke ya zura hannunsa ta window ya wanke apple dinsa fes da
ruwa ya kama cin apple dinsa ji kake baras,har wani lumshe ido yakeyi,sai daya ci guda biyu,ta
karfi sultan ma yaci biyu,aka bawa driver ragowar biyun,
Can suna tafiya a mota omar ya kwance ledar kwai yaci daya ya mikawa driver duka.sultan
harga Allah abin na omar ya shiga bashi tsoro kamar tsafi,omar da baya cin abun hanun
yara,gashi bayacin abunda rana ta dakeshi a kan titi,yau gashi hankali kwance har dafaffen
kwai na titi yaci hankali kwance lallai wannan yarinya ta masa babban kamu.
Har gida suka kai sultan suna tsayawa omar yace dalla malam fitar min daga mota,zaka
nemeni next time sannan zan rama kuma kasan ramuwata me zafi ce cewar sultan.gidansa ya
wuce yau bazai biya ta wurin mama ba,yana shiga ya tadda sahar kwance a doguwar kujera
tana chat,sallama ya mata ta amsa kuwa tace sannu ta ci gaba da chat dinta,shima ko kallo
bata isheshi ba ya wuce room dinsa,wanka yayi sannan ya dauko take away da ya zo dashi ya
dauko yaci a kyankyame sannan yayi sallar la'asar,karatun Quran yayi da sauran abubuwan
lada har magriba tayi ya wuce masallaci,inda ya bar sahar haka ya dawo ya sameta ba
sallah,har ya gaji da fadan.
Dakin haj rahina sadiya ce da naja ke hirar samari suna bawa umma labarin yanda suke cin
kudinsu,Aisha tace ai ni full tank nake ja,zuka nake da yawa,jane dani,sai na cika tanki na.tana
tsakiyarsu suna ta hirarsu,daga nan suka mike sukayi mangaren maman omar,su uku ne suka
je kamar abin kirki, yan matan ne yau cewar mama,tsaki sadiya ta ja ta mata kallon baki
isa,suma sauran haka sukayi,can naja tace an wani faffake gida matsafa kawai.wlh sai mun
kawo karshen makirci cewar sadiya,abdallah ne ya mike ya cakumo naja suka fara kokawa
tukuri,suna ganin ya fara naushin naja,suka hadar masa abinka da namiji yana karami amma da
kyar suka sha a hannunsa.part din suka bari Aisha tace sai kayi dana sani yaro.
Mama kuwa danta ta janye tayi shigewar daki dan inda sabo ta saba,Sam bata damua.haka
tasa suleim da abdallah gaba ta kira driver dinta ya tafi dasu shopping har mama,suna fita omar
na zuwa gidan,yaga part din kulle dama shima yana da spare key din part din mama,room dinsa
ya shige a ciki yayi sallar isha,coffee ya hada ya sha yabi lafiyar gado ya kwanta abinsa.
Tunanin iklas ya addabi zuciyarsa,to shi mene hadinsa da ita har zan na tunata cewar omar a
ransa,lallai ya kamata yasan tarihin yarinyar nan,gashi ya rasa dalilin da yasa ya damu ya sake
ganin kyakyawar fuskarta, sunanta ya fada a fili GOMNATI.Da kyar ya samu bacci ya daukeshi.
Mama batasan a gidan ya kwana ba gani tayi ya sauko daga part