Showing 27001 words to 30000 words out of 100763 words

Chapter 10 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2866

rigimar na sako da sako, amma ita Hajiya bata taSa kawowa al'amarin zai lalace har girman yaranta ba, a zahirin gaskiya tsanar da Amaan yakewa Majid tayi yawa da har sai da kowa yayi magana. Wani irin tsana ce irin na matukar na samu dama sai naga bayanka. Amma a bangaren Majid babu wannan tsanar kawai shi mutum ne da yasan ciwon kanshi da darajar kanshi,. Sannan bai kullaci Amaan har haka ba. Kamar yadda shi ya kullace shi, reni ne baya so kuma ya fahimci Amaan yana da reni da son abin duniya.

Kiyayyar tasu ta faro ne daga lokacin da Alhaji Mamman Ba'are, ya bar wasiyya akan cirewa kuri'arshi ya gadarwa Majid, sannan ko a halin jinya yadda Alhaji Mamman Ba'are yake ta rokon a nimo mishi Majid ya roke shi gafara kada ya mutu da hakkinshi ya kara tunzura dayawan mutanen dake jikinshi, bawan Allah nan har ya mutu da rokon a kira mishi Majid, don Allah ya yafe mishi.

Duk da akwai hakkin iyaye akan Yaransu, haka akwai hakkin Yara akan iyayensu, wannan al'amarin ya tab'a zuciyar kowa na jikin Mamman Ba'are musamman Hajiya Nana wacce idan taji yana cewa Majid ba zaka zo ba, Majid kana ina ne? Majid zan mutu ban ga fuskarka ba. Majid nasan na cuce ka, Majid kazo. Shi yasa bayan kome da ya warewa Majid, akwai wasu takardun da ya bawa abokinshi. Wanda babu wanda ya sani daga Hajiya sai Abokinshi Alhaji Abubakar Abzin, shima shahararren dan kasuwa ne da yake garin marad'i, kuma wani ikon Allah Alhaji Abubakar Abzin bai tab'a takowa zuwa Niamey ba, idan abubuwa suka shiga gaban Hajiya wurinshi take zuwa. Yanzu ma tunaninta kafin hutun Majid ya ?are zata kai shi garin marad'i, su gana.
Wannan shine shirinta.
Sai da Majid ya jira Amaan ya shiga dakin, sannan shima ya shiga ya mikawa Hajiya kudin tare da mata magana da idanu, ta bawa Nabeeha. "Barka Hammayo." Inji Salaha matar Amaan, "Barka!" Ya fada a hankali, idan baka saka kunne ba, ba zaka ji me yace ba. Shigowar yara uku suna ihu, yasa shi juyawa. Sai wani guda daya da yake bakin kofar shiga falon Hajiya. "Appa kaga Shuraim ya dake mu ko?" Yaran suka nufi wurin Amaan, mikewa Amaan yayi tare da nufar Shuraim Win. Shima Aryan har zai mike Majid ya kalle shi, a fusace ya koma ya zauna yana kwafa. "Kai wato munafurcin da ka gada daga wurin wancan dan iskan Yaron shine zaka fara." Ya rike kunnen Yaron. Amadadin yaron ya fasa ihu, sai ga Amaan yana fasa ihu, babu wanda ya san me ya faru, sai yaron ne kawai ya san me ya faru. Daukarshi Majid yayi suka fita. "Daada taka mishi kafa kayi ko?" Ya rad'a mishi a kunne. "A'a" "Daada Allah yana kona me karya inji Ummina." Dakinshi ya shiga da shi, ya Ciro katon kwalin chocolate, ya mika mishi sannan ya kara dauko dayar ya ce mishi. "muje!" Haka ya riko hannunshi har falon Hajiya suka koma, zama yayi ya kira sauran Yaran, Yaran Amaan dake duk mata ne, tasowa suka yi duk da harara su da Amaan yake, haka suka tawo wurin Majid ya ajiye su a gefensu. Sannna ya mikawa yar karamar yar Aryan hannu da sauri ta taso. Ya ajiye ta" Kai Ayyan ka sammata a naka, Anum da Widad zan basu anan."
"A baco na Yaya!" Injin yarinyar. "Bushrah!" Babanta ya daka mata tsawa. D'ago kai Majid yayi ya watsa mishi harara. "Tow shi kenan tunda baki son na Yaya Anum a san mata?" Gyada kai tayi, ya bude musu kwalin ya ciro chocolate din ta ce mishi. "Dada a bacon na Anunu." Ta maida hannunta baya. Hajiya kuwa me zata yi ban da dariya ta ce mishi. " Ai yadda ka bawa sa'anta kwali itama haka zaka dauko mata kwali domin bata yarda a raba kansu da yan uwanta."
"Uwata taso muje." Ya dauki su Anum ya zaunar dasu a saman kujerar ya dauki Bushrah har dakinshi ya dauko mata nata, tun da ya bata, ta fara bashi labarin da Allah ya gani bai fahimci Yaren ba, har suka isa falon, bashi labarin take.
"Ja'ira mara kunya, dole ki bashi labari anya takwara haka zamu yi dake."
"Jiya babu luwana dake, ban baki cokulet dina ba " ta zauna ta yaga kwalin. Ya zube dukka. "Dada ashe min!" Wato ya kwashe mata, "abawa jiya." Ai kuwa Hajiya ta wafta ta ce. "Sai dai kada abawa gobe, amma jiya kan zan sha."
Haka aka yi ta hira har wani lokaci kafin lokacin magariba tayi duk suka tashi zuwa Masallaci..
*Sansanin gudun hijira*

#thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*010*
*Sansanin Yan gudun hijira*
Adamawan Kamaru.

Abu na farko da muka fara fuskanta a camp din, shine rashin matsuguni da kuma kayan amfani, wai a haka dai an kawo mu nan saboda akwai inda zamu zauna, sai dai tunda aka yasar damu a asibitin wanda ba laifi an gwada mana kulawa da duk wani abun da ya dace, sai dai kuma babu wanda ya kuma zuwa da zancen ga yadda zamu yi, kwanan mu goma duk da haka mun samu lafiya daidai gwargwado. Idan ka cire Nenne da Yakumbo lantana da kullum jininsu yake hawa. Ita kan Yakumbo idan ta zauna sai ajiyar zuciya tana kiran sunan Sa'idu. "Ayya ayya akan idanuna suka kashe min shi. Ko tausayin rai basu ji ba, suka kashe min Abubakar yaron da bai gama koshi da nono ba." Sai ta fashe da kuka, ita kan Nenne bata hummm bata hmmm, hasalima tsayuwa mai kyau bata iyawa, domin a bakin Munaisah nake ji wai an mata Winki ciki da waje, sakamakon yadda suka mata kaca-kaca. Ashe wani lokacin kuka ma rahama ce, har yau ina son nayi kuka amma ko da wasa ban zubda hawaye ba, sai dai idan na tuna mutuwar Baffa'm sai naji har zuciyata tana wani irin bugawa, can kuma naji kirjina yana min ciwo, dole sai na kwanta. Lokacin da likita yazo na gaya mishi, kura min idanu yayi kafin ya ce min.
"Kina son ki mutu ne da kuruciyarki? Me yasa kike tuna abin da ya faru?" Sunkuyar da kai nayi, ina wasa da yatsun hannuna. "Zan bada test a miki, kada ki sake na ga wani abu domin zan na miki allura kullum."
Murmushi nayi nace mishi. "Ni." "Ke ke! Meye?" "Ina son nayi kuka ne?" Kura min idanu yayi kafin ya ce min. "shi kuka yana zuwa ne idan lokacin bukatar shi yazo, lokaci na zuwa zaki yi kuka kin ji." Gyada mishi kai nayi, ina faWin. "Nagode!" "Ba kome yar fillo!" Daga haka na fito daga office din, na fita daga cikin asibitin can harabar asibitin na nufa na tsaya ina shakar kamshin ?asa, domin ina son na samu nutsuwa. Idan nace ina jin dadin rayuwa nayi karya, ko dariyar da nake a dole nake yin shi ba wai yana kaiwa zuciyata ba ne. "Nan kika fito?" Juyawa nayi na kalli Addah ko daga ina take oho. "Hmm!" Nace mata, gyara tsayuwa tayi domin itama har yanzu bata gama jin dadin jikinta ba. "Zahra babu wani abu ne, kin ga saboda Lantana da Matar Babanki anki sallamar mu, balle har mu samu damar barin asibitin nan."
Shiru nayi ina nazarin wace irin zuciya ce da Addah haka. "Naji Zulaihah tana cewa akwai wani abu a wurinki." Sai lokacin na samu zarafin mata magana. "Zuzu ba zata gaya miki akwai wani abu a hannuna ba, sai dai idan Munaisah ta gaya miki." Na fadi haka ina kallonta, sai kuma ta fara kame-kame. "Yauwa ashe." "Addah don Allah bana son damuwa, ki je kice ta baki kudin ki kyale ni."
"Hmmm! Ai kin san dai zuzunki ba zata tab'a bani wani abu ba." Ta fada tana hararata, na ga karfin hali a wurin Adda. Haka ta taso ni a gaba, har dakin da aka kwantar damu, na nufi wurin Zuzu nace mata. "Bani jakar nan" a hankali ta d'ago kai ta kalle ni, bari na gaya muku wani abu dukar da aka mana ya haifarwa Zuzu rashin ji da kunnenta daya. Bata ji sosai sai ka mata magana da karfi, ni kuma bana son na sabar mata da yawan magana da karfi. "Me zaki yi da shi?" Ta tambaye ni, tana kallon Addah da ta haWe rai ita kada ma ta sakata a cikin lissafin ita ta turo ni. Itama kuwa Zuzun tawa haWe rai tayi ta ce da ?arfi. "Ban san inda yake ba." Tunda ta fadi haka nasan wallahi ba zata bada ba, kuma duk abin da za ayi sai dai ayi amma ba zata tab'a bada jakar ba. "Ai kin ga irinta, waye ya gaya miki ana mu'amala da irin Zulaihah da tana da jin ta ma ya aka kare balle ta rasa jin." Juyawa nayi na kalli Munaisah tana matsa kafar Nenne, Ummi tana kwance gefen Yakumbo. Ni daya ce bani da uwa anan, ita me uwar ma bata samu tausayi da jin kai ba. "Addah lalurar Zuzu ba siya tayi ba, sannan likitocin kwakwala da kunne sun ce zata dawo da jin ta kamar baya, matukar tana amsar magani, me yasa kike mata gorin ji? Idan tausayi da jin kai bai shiga tsakaninku ba, Addah kada tsangwama da hantara ya shiga tsakaninku domin wata rana ita ce zata tsaya miki."
Daga haka na koma wurin Munaisah na ce mata. "Ya jikin Nenne?" Idanunta da suka yi bullu-bullu sakamakon kukan da take yi ta ce min. "Jikin Nenne kara zafi yake, gashi yau bakiWaya bata ko magana." Wani irin tausayi ne ya cika min zuciya, na ce mata. " Bari na je na ga Dr Moses!" Haka na fita, a hanya na hadu da Nurse rabeka, "yar fillo ina zaki?" "Yawwa Aunty Nurse zo ki duba min Mamanmu." Ba musu ta bi bayana har dakin mu, tana shiga ta fara dubata da sauransu. Kallona tayi ta ce min. "Yar fillo bari na kira Dr Moses!" Haka kuwa ta fita can sai ga su tare da wasu likitoci biyu, haka suka dubata sannan suka saka Nurse Rabeka da Nurse Ali suka dauketa a keken marasa lafiya aka fita da ita, haka muka bi bayansu. Har wani wuri can da aka rubuta ICU da manyan harufa. A wurin muka tsaya aka shiga da ita, tunda muka tsaya a wurin Munaisah ta fashe da kuka, kuka take tana faWin."me yasa? Me yasa sai mu? An kashe mana iyayenmu, anci zarafin mu da iyayenmu, an kona mana dukiyarmu da muhallinmu me yasa gwamnati ta zama makauniya?" Rungumeta nayi, ina buga bayanta. "Zahrah Nenne kawai ta rage min sai ke, Zahrah idan wani abu ya samu Nenne ba zan tab'a yafewa Gwamnatin Nigeria ba, ko ina ka shiga kome mugun aikin da aka yi, zaka ji ance Fulani me yasa aka tsane mu? Kowa yasan bafulani daga kiwo sai sayar da madara yake, amma a yau duk wani aikin ta'addanci zaki ji sunan bafulani ni ne, me yasa Zahrah me muka yi? Zahrah bamu da yanci anan mu da bakin haure daya ne, babu tausayi, babu tausassawa, babu." Rufe mata baki nayi. "Kowane bawa da yadda rayuwa take zuwa mishi, idan muka kalli yadda tazo mana, sai mu amshe ta da hannu bibbiyu, kada mu zama masu son rai, shi Ubangiji bai tab'a jarabtar bawa akan baya sonshi ba, yana jarabtarshi ne gwargwadon karfin imaninshi. Ki cigaba da addu'a Allah ya bata lafiya.". Wato ko Munaisah yar gata ce, tunda ga Mahaifiyarta a raye, ni fa? Gani a kasar su mahaifiyata, amma ban san ta inda zan fara nemanta ba. Haka na hadiyi tawa damuwar, domin ba lokacin bayyana tawa bace, haka na cigaba da zama da ita, domin Addah bata biyo mu ba, Zulaihah kuwa bata iya tafiya saboda kafarta da aka mata dauri. Ta samu tsagewar kashi, muna zaune a wurin har suka fito, mikewa nayi na nufe su. "Ya jikin Mamanmu?" "Da sauki!" Dr Moses ya faWa, yana kallon yadda muke raba idanu. "zamu iya ganinta?" Girgiza min kai yayi yana faWin. "tana ?ar?ashin kulawar computer ne." Sabon kuka Munaisah ta fashe da shi, tana rike kirjinta. "Wayyo Allah na, Wayyo Allah Nennena. Don Allah ku barni na ganta." Girgiza kai yayi yana faWin. "zaku kanta amma ba yanzu ba, sai ko zuwa gobe."
Rufe bakina nayi, cikin rudani ina kallonshi. Ita kuwa Munaisah kuka take me tab'a rai, baki Waya na rasa ina zan saka kaina. "Yar fillo kada ki damu fa, zata ji sauki kawai an dora ta akan kulawar computer ne, ki cewa Fulani ta daina kuka haka. Nenne zata ji sauki." Gyada kai nayi, ina kallon Munaisah, haka suka tafi suka bar mu a wurin.
Dakyar naja ta muka koma dakinmu, sallah muka yi. Abincin da ake rabawa na asibitin aka kawo mana, ban iya cin ko loma daya ba, haka Munaisah itama bata iya ci ba. Muna idar da sallar Isha, na mike xan fita Munaisah ma ta biyo ni haka Zulaihah ma ta ce mana. "Ku jira ni." Ummi da take jikin Yakumbo ta ce mana. "Zahrah akwai maganar da Yakumbo tace zata gaya miki don Allah." Kallonsu Zuzu nayi nace musu. "Kuje ina zuwa." Zuwa nayi na zauna a gefen Yakumbo. "Gani Yakumbo!"
"Zahra'u!" "Na'am!" Ga Ummi nan na baki amanarta. Ta shiga lallubar hannuna, kallon Ummi nayi da ta dauke kai, tana share hawayen da yake zuba mata. "Sis yaushe yakumbo ta daina gani." Murmushin karfin hali tayi ta ce min. "Zahra'u, don Allah ki taimaka min ki maida Ummi Yola wurin Dan Malam, ina tsoron kada na mutu rayuwar Ummi ta lalace." Wato sai na rasa ya zan kwatanta halin da nake ciki, shin zan fadi ne na mutu ko kuma zan fita ne nace a bude zuciyata a ciro min shi a rage damuwar mutane da yake cike a bar min tawa. Ajiyar zuciya na sauke sannan na rike hannunta. "In sha Allah, zan cika alkawarin da na daukar miki." Itama rike hannuna tayi da kyau ta ce min "Ki yafewa Nenne, don Allah ki yafe mana, don Allah ki yafe mana ko zamu samu rahamar Allah." A wannan lokacin ina son nayi kuka ko zan rage nauyin da yake zuciyata, amma ina zuciyata sai kara zafi take tana kara taurarewa, ina ga ba mamaki an sauya min zuciyata daga tsoka zuwa dutse. A hankali na zubawa Yakumbo idanu. "Duk abinda ya wuce ya wuce abar shi har a wurin Ubangiji ya wuce."
Na fada ina kokarin barin dakin, "Kina nufin kin yafe mana?" "Har a gaban Ubangiji bana fatar haka ya tsayar damu a kan wannan abin, na yafe maku." "Ki bari na gaya miki abin da muka aikata mana!" Juyawa nayi na koma wurinta, na saka hannu na rufe mata bakinta. "Nace na yafe, kuma ko kin gaya min ba zai sauya kome ba, sai ma lalata kome da zai yi. Ina fatan nima Ubangiji ya yafe min laifin da nayi mishi ya rufa min asiri, ba ya tona min ba. Yakumbo abar maganar Allah ya baku lafiya."
Rike hannuna tayi tana faWin. "Lallai Allah ya albarkaci rayuwar Aminatu a duk inda take, ta haifi daya tamkar da dubu. Zahra'u Alfarma daya zaki min, ina son na mutu a wurin dan Malam." Kallonsu nayi kafin nace mata. "Yakumbo in sha Allah za a maidake wurinshi." Daga haka na fita, ICU na nufa, a hanya na tsaya tare da jingina da bango,na rasa me ke min dadi, sai da nayi nazari kafin na wuce wurin su Zuzu. "Sai yanzu?" "Eh!" Na fada ina me zama a gefen Munaisah. "Zuzu Yakumbo tana son komawa gida, ko muma mu koma ne?" Gyada kai tayi kafin ta ce min. "idan mun koma wurin waye zamu zauna?"
"Wurin Ya Dan Malam mana!" Na fada mata, ina kallon reaction Winta. "Hmm! Shima nima yake, ba laifi idan kin saka su Yakumbo a motar, amma har ga Allah na yafe Nigeria, domin nasan sun kashe min har mahaifina." Ta fada tana kallon kofar icu Win. Kaina a kasa ban kuma magana ba, har dare ya fara yi na riko hannun Munaisah. "Sister taso muje." "A haka xan bar Nenne a nan? Idan wani abu ya same ta fa." Girgiza kai nayi sannan na riko hannunta, "Muje babu abinda zai faru, in sha Allah." Daga haka muka juya zuwa dakin mu, dukkansu sun kwanta nice kawai nake zaune, ga Addah da bata zama haka kawai ta tsiro da yawo, ina zaune a wurin har wani lokaci na tashi na shiga ban daki nayi alola na fito na shimfida dan kwallin kaina na fara sallah.
Sallar nafilla nayi ta jerawa, ina rokon Allah ya yafewa iyayenmu da suka rigamu zuwa gareshi, ya musu rahama. Ni kuma Allah ya bayyana min mahaifiyata. Su Nenne kuma Allah ya basu lafiya. Haka na cigaba da sallah har wurin karfe biyu, a lokacin Addah ta shigo. Gadonta ta nufa ta kwanta. "Addah ke daya ce me lafiya a tsakaninsu Yakumbo, amma Addah kin ki bamu lokacinki sai ki tafi yawo ba zaki dawo ba, sai dare ya raba."
"Tow Zahrah sai ki rufe ni da duka, dake an ce miki yawon banza nake tafiya ba."
Ban kara ce mata uffan ba, ina jin Zuzu tana kwafa, idan na fahimta idanunta biyu. Kawai ba zata yi magana ba ne, haka na kwana, kusan kamar nurse domin ina jikin Munaisah ina kula da Yakumbo. Wannan al'amarin ba karamin tab'a rayuwata da lafiyata yake ba, da gari ya waye bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login