Showing 18001 words to 21000 words out of 100763 words

Chapter 7 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2848

kawo mata ziyara daga kano suka tafi tare da Addah, ashe tafiyarta Kano Saudiya ta tafi.

Wato mu yan gidanmu Allah ya zuba mana baiwar kyau, sai ma dai nice da nake da duhun fatar Mamana. Haka yasa yan gidanmu suke yawan min ba'a. Bayan tafiyar Addah Baban Zulaihah yaso Waukarta, amma Kakanmu Alhajijo yace ba zai dauketa ba, sai ta kai shekaru bakwai a duniya.
Haka muka taso da Zulaihah duk da ta girme.ni, haka Mamana ta haWa mu ta ri?e. Tunda Addah tabar Nijeriya ta isa Saudiya, take tukaranci da rashin jin magna, har dai ta samu yadda take so.

A nan kuwa ba zance me ya faru ba, domin a lokacin ban wuce shekaru Biyar ba, aka nime Mamana aka rasa, sama da kasa ta b'ace, wannan al'amarin ya daki babana da Alhajijo a lokacin ya kwanta jinyar da tazama ajalin sa,, haka muka zama marayun dole ni da Zulaihah. A lokacin Baffa'm ya saka ni makaranta, kuma cikin ikon Allah sai Ubangiji ya min baiwa na daukar karatu, domin ina da shekarun goma a duniya na gama primary school. Na shiga secondry school, a gurin a saka sunana a registered din yan jss one aka saka a na yan jss two, haka Baffa ya cika musu kudi domin shi mutum ne mai son yaga kayi abinda yake so.
Ina da yayu maza biyu, Babangida da Habibu, sai Munaisah take bin Habibu. Sai ni nake bin Munaisah, sai Kuluwa take bina, sannan Dizah burin Baffa'm akan mu yayi yawa amma haka Nenne ta kashe mishi burin akan Yaranshi,ni ce kawai yake da iko dani, shi yasa ina shiga jss3 a shekaru goma sha daya na kara ri?e wuta, koda muka shiga Ss1 bana wasa, ina shiga ss2 na nime Baffa'm ya biya min waec da neco, sanin ina kokari yasa shi biya min ikon Allah sai gashi da muka yi jarabawar naci, duk da bani da shekaru amma ina da dan tsawon kafa. Sannan ni siririya ce sosai. Kamar mamata haka nake.

A shekarar da na gama secondary Hajiya Addah ta dawo, ganin mu yasa ta fara shiri akanmu, sannan a gefe guda kuwa burinta ya kusan cika, don haka ta kwana biyu ta sayi shanu ta bawa baffanmu, ta koma ashe a Lagos take da aka kore hausawa masu tuwo-tuwo shi ne ta dawo fatakwal. Ganin mu kawai yasa tana komawa tayi gaggarumin shiri, tana zuwa ta dauko Ummi da Munaisah,suka zo watansu biyar suka dawo. Ni da Zulaihah da zasu koma aka tawo damu,a lokacin Baffa'm ya bani takarduna,nayi kokarin niman cigaba domin ta gaya mishi zan koma makaranta. Da muka zo kuwa kudin da ya bani taso kwacewa ni kuwa na ce ta mai dani gida baki Waya shekaruna sha huWu, ina da wayewa ta ilimi,domin saura izu goma na sauke Kur'ani mai girma.

Wannan dalilin yasa addah nima min, diploma a bangaren ilimin lissafi, kuma dama Allah ya min baiwar iya lissafi. Har yan canji suna kirana na taya su aikin lissafi idan ban tafi makaranta ba, a hankali Addah tayi ta fito da asalin kalarta akan lallai mu bi maza, ni kuwa naki na sha duka da wahala, ga azabtarwa yunwa kada ku manta wannan shafa ce domin a gidan Ubana ma na horu da rashin abinci, Zulaihah ce aka samu kanta, domin ba zata iya jurewa ba, haka na samu number din baffa na gaya mishi, shi ne yasani na hada shi da wani iyamurin gefen gidan Addah yana turo min kuWin makaranta da na abinci. Yayarshi ce babu yadda ya iya da ita idan yayi magana zata ce ya mata rashin kunya,haka yasa ya zuba mata ido. Kullum zai kira yaji ina nan ko na tafi, baya kira a wayata sai wayar addah.

Kudin da take samu a wurin su Ummi da Munaisah da Zulaihah,da shi take turawa gida ana saya mata dabbobi, gashi bata gajiya da kai karana na mata kaza nayi kaza. Ya kira ya min nasiha, domin ban tab'a boye mishi abinda take son nayi ba, shima kuma yace naji tsoron Allah yana gani na idan ni bana ganinshi.
Haka muka cigaba da rayuwa, gashi har na zama cikakkiyar budurwa, domin ban wuce shekaru goma sha shida ba, haka yasa maza rawar jiki a kaina, amma naki Ba su fuska, sai ranar da ?addara ta haWa ni da mutumin nan da ya soka min wuka,koda yake shegen iyayi na ya kai ni. A daren da abin zai faru wannan sojan yazo wurin Tuwon mu ya matsawa Addah ta barshi ya dauke ni, amma taki domin ya tab'a daukar Ummi bayan ya kwana da ita ya mata dukar kawo wuka ya korota. Sai da ya zuba mata kudi, sannan ta barni muka tafi, daga na bishi na amso kudi ya tafi da ni.

Koda ya kawo ni, da farko bai nuna damuwa akan yana son wani abu ba, sai da na je na kwanta ina nazarin yadda zan fita ya shigo min tsirara, ai kuwa garin na kwaci kaina na bude mishi wani abu can, ai kuwa ya fadi can, da haka na gudu, daga nan na hadu da Aminin duhu.

....... Biyar na yamma muka isa taraba, daga nan kuma muka dauki shatar mota har har zuwa Takum kai ba zan fadi yadda farinciki yake wanze akan fuskar mu ba, amma tabbas mun yi kewar garin mu, ai kuwa bamu isa ba, sai dare shima ba cikin gari ya shigo damu ba.
"Driver ai da ka kaimu sai mu kara maka kuWi."
"Gaskiya Hajiya ba zan iya barin takum ba, ina ma zaku?"
"Jenuwa" shiru yayi kafin ya ce mana.."zaku ?ara min dubu ashirin?"
"Eh zamu kara maka!"inji Zulaihah domin ta kagu ta isa gidan. Gyara tsayuwa yayi ya ce mana."tow muje!" Haka ya cigaba da tukin har muka isa garin mu, dake shigar dare muka yi, har kofar gida ya kai mu ya sauke mu, sannan ya juya abinshi....
#thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*007*
Tunda muka sauke kayanmu naji bakiWaya wani irin sanyi ya lullube ni, sanyin dadi domin babu inda ya fi mahaifarka, haka na karewa garin kallo cikin wani irin tsananin so da kauna. Buga kofar rugar mu muka yi muryoyin mu na tashin sallama, Baffan Ummi ya fara fitowa yana faWin. "Ikon Allah Hajiya Addah kece a garin mu a daren nan?"
"Eh Modibo gani nan jenuwa babu shiri. Bari mu shiga mu huta."
"A'a bari a taso Lantana ta dama muku fura." "Barshi Modibo bari mu huta haka." "Tow madalla, ku huta lafiya." Ya juya zuwa bangarensu, mu kuwa ni da Zuzu tsohon dakin Mamana muka shige domin dama babu kome sai tsohon gadonta da tarkacen da ake zubawa a dakin, haka muka kwana a gajiye, dake Allah ya taimaka duk mun yi kasaru a Yola sallah Magariba ma sai da muka yi a hanya. Wani abu da ya dame ni, shine na kasa barci haka nayi ta juyi har asuba ta gabato, daga nan na tashi nayi sallar Isha da na asuba, sai lokacin barci me nauyi ya Wauke ni.

Cikin wani irin yanayi mara daWi, nake barcin nan, make min cinya aka yi na bude idanuna. "Ya?" "Kawu na kiranmu." "Karfe nawa yanzu?" "Tara da rabi." Tashi nayi ta mika min kofi da dafafen madara."sha ki hada da magani sai mu tafi." Yatsina fuska nayi domin bana son shan madara, haka Allah yayi ni bana son madara idan ba dole ba, haka kuwa na sha, ina tsaki sannan na mike muka fito zuwa dakin Baffa'm, bayan na sha kayan sanyi. Koda muka isa yana bakin kofarshi yana zuba ma Yaran Baffa Modibo shayinsa. D'ago kai yayi ya kalle ni sannan ya saki murmushi, yana faWin . "Innawuro sai yanzu kika farka?" "Eh Baffa." "Zulaihah kema shigo." Haka muka shiga dakinshi, zama muka yi ga dadi da dumi. "Kun iso lafiya?" "Alhamdulillahi, mun same muku lafiya?" "Masha Allah, Alhamdulillahi. Ya jikin naki?" Sai a lokacin fuskarshi ta sauya kaWan. Zuba min Idanu yayi kafin ya gyara zama ya kira sunana. "Fadimah Zahrah!" Gabana ne ya fadi, na kalle shi kafin nayi kasa da kaina. "Na'am!" "Idan aure kike so, me yasa baki gaya min ba?" Girgiza kai nayi, a hankali ya shiga min nasiha, Baffa'm yana da matukar hakuri da sanyin hali, haka yasa ba zaka tab'a jin shi yana faWa da wani ba. Sai da ya gama ya zuba mana idanu yana son jin me zamu ce. "Kawu shad'ari!" Kallon Zulaihah yayi zata magana na rike hannunta. "Meye kike son hana ni magana?" "Ya wuce, a barshi ya wuce har gaban Ubangiji ya wuce." "Kawu laifi ne don ta kare kanta daga dattin zina? Yar uwarka azzaluma ce, bata da imani."
"Kuyi hakuri nasan Allah yana tare da ku, kuma me yasa baku gaya min zaku zo ba? Garin jenuwa babu lafiya, ai da ban barku kunzo ba. Muma zaman dar-dar muke."
"Lafiya kawu?"
"Lafiyar kenan, sai dai wasu daga cikin yan uwa Makiyaya kuma abin da na fahimta ba?in haure aka samu suka shiga gonar mutanen suka musu barna sannan suka kashe musu mutane kusan goma. HaWe da yiwa matansu fyade, tun ranar juma'a suke son daukar fansa, hukumar tsaro suka shiga cikin lamarin, yanzu haka babu dad'i garin baki daya, shi yasa nake son idan da hali gobe ku bar garin nan."
"Baffa'm na dawo kenan fa." Kura min idanu yayi na wasu dakikai kafin ya ce min. "Kiyi hakuri ki koma can, idan kin samu miji maza ki kirani ki gaya min."
"Baffa'm Sabiru fa?" Kaina a sunkuye."Allah bai nufa shi ne abokin rayuwarki ba, yayi aure suna jalingo da Matarshi da yake yana aiki a can." Wani irin sanyi ya shige ni daga waje har cikin jikina, na hadiye wani irin yawu me daci. "Baffa." Kura min idanu yayi sannan ya ce min. " Allah yana sane dake, ga wannan takardun, ki tabbatar kin nime Mahaifiyarki, domin duk inda take tana cike da kewarki."
"Baffa'm me yasa ka bani?" Na tambaye shi lokacin wani irin sanyi da zazzaSin sun rufe ni. "Akwai rayuwa akwai mutuwa idan na kasance araye zan tayaki nimanta, idan muka bana raye zaki tsayawa kanki, Zulaihah ku rike amanar juna,kada ku sake wani abu ya raba tsakaninku, ita duniyar ba kome sai rud'i da karya, ba kome zaka bashi damar fushi ba, na horeku da zumunci, kuma duk abinda Addah zata muku, kada ku sake ku yi fushi Allah yana tare da masu hakuri." Nasihar Baffa'm yake mana, sai da ya gama sannan ya shiga tsokanarmu. "Kun tuna kuna yara kuke damben wace ce zata sha furar Alhajijo." Ya dauki wani allon karfe, ya shiga rubutu yana kallona. "wannan zamanin dole ka nimawa kanka mafita, idan ba haka ba, sharrin zamani sai ya hada da zuri'arka." "Haka ne Kawu " murmushi yayi sannan ya cigaba da rubutun,yana jan mu da hira har ya gama ya wanke a kwanon shan, ya dauko wani saiwa ya jefa yana faWin. "ku dai rike gaskiya da Amana, ban da cuta da cinAmana, zalunci bai da tsawo domin idan alkadarin ya karye sai an tozarta."
"Haka ne!" Suka ci gaba da hirarsu da Zalaihah ina jin su, har ya gama.ya bawa kowacce ta sha. "Idan kun fita ku bawa Ummi da Munaisah, su sha." "In sha Allah!" Muka fada, "Baffa'm rubutun me ka bamu?" Murmushi yayi ya ce min. "Tsarin jiki ne?" Gyada kai nayi, har zan fita ya ce min. "Innawuro!" Juyawa nayi, "zo nan!" Komawa nayi na zauna, bude wani ?unshin takarda yayi ya mika min. "Ina ta ajiyewa kafin aurenki, ki saka a wannan abin me kama da lalita, wata rana zai miki amfani kada yunwa ko talauci ya sa ki.aikata Zina don Allah ki rufa min asiri kinji. Duk inda zaki kada ki zauna babu sana'a wannan gwal ce na Mahaifiyarki."gyad'a Kai nayi, a hankali na mike ina mishi godiya, har zan fita ya mika min wasu leda. "Shi wannan abubuwan masu mahimmanci ne, na yaran Harirah ne nasan..." Burr muka ga shigowar Nenne, fisge ledar tayi, "wato ga yar so, ni kuma nawa yaran da baka so su mutu da bakinciki da yunwa bani. Ai keda ganin uwarki sai a lahira."
"Harirah kenan. Allah ya bamu sa'a." Daga haka na fita na barsu, tana saukewa Baffa'm tijara. Ni kan cikin gidan na nufa duk da wani irin zazzaSin da nake ji, bai hanani zuwa sassan Baffa Modibo na gaishe su ba,har dama-dama Yakumbo bata da matsala, sai Amaryarta ce ma Bama shiri. Yakumbo wacce sunanta Sarai tana da yara hudu, Shu'aibu shine babba yana yola a can yake karatu shine yaron da ya fita Zakka a bangaren Baffa Modibo. Sai Jamilu yana nan domin yayi aure yana garin takum, sai Sa'idu kafin Ummi.
Amaryar Baffa Modibo kuwa, tana da Yara kusan shida duk maza ne, sannan irin haihuwar nan na kunika. Yaran kamar kwarkwata.
Aminu shine babba, sai Zakaria, Amadu, Adamu, Abdullahi, Abubakar dan karaminsu, wucewa dakin mu nayi na kwanta, ina ganin Zuzu tana dafa mana abinci,domin doya ce take dafawa zata mana miyar kwai. Zulaihah akwai kokari domin duk inda zata, tafi da gidanka take yi, har indomie tazo mana da shi, ga kifin gwangwani irin me Mai din nan. Tana gama dafa doyar take bani labarin yadda tayi da ruwan rubutu,ta ce min. "ke nabasu suka ki sha, ai kuwa na sha rabi na bar miki rabi."
Ni dai bance mata kala ba, na cigaba da kwanciyar da nake, domin idan na bude baki zan yi magana kuka ne zai kwace min. Haka na dauki lalita ta, ina kallo. "Zahrah ya dai?" Idanuwa na da suka cika da kwalla na kalleta."Ashe Sabiru yayi aure bai gaya min ba?" "Mtsew sai kace autan maza." A hankali na fashe da kuka, ina jin wani irin abu yana taso min, kamar kukan nan saka ni ake yi, har sai da nayi na gaji, tana kallona taci abinci ta koshi, ta mike ta daura ruwan zafi, ta fita tayi wanka sannan ta shirya zuwa gidan Babanta, koda ta je can faWa yayi mata me yasa zata zo, gari ba lafiya. Hakuri ta bashi tare da mishi zancen ta hadu da wani tana son ta turo shi,ta kira saurayin ta hada su, sukayi magana ta roki Babanta kada ya bari Addah ta sani. Ya mata al?awarin ba zata sani ba.

***
Karfe biyar ina wurin dabobbi, ina taya Baffa'm tatsar madara. Wayarshi tayi ?ara dauka yayi yana me sallama. " Alhaji Abubakar ko?" "Eh ni ne?" "Okay ko zaka fita kai da wani naka, domin mun samu labarin za a."
"Anan aka haife mu, anan muka girma bamu da inda yafi nan, sai dai mu mutu, Yallabai mun gaya musu, bamu ne muka musu barna ba, taya zamu cigaba da amsar laifin da bana mu ba, a matsayinku na jami'an tsaro hakkinku ne kula da rayuka da dukiyoyin mu."
"Shi kenan, kada kace ban sanar maka ba, na gaya maka gaskiya kuma ba a bamu umarnin kare kowa ba, don Allah ka fita daga cikin Jenuwa."
"Shi kenan!" Baffa'm ya faWa yana kallona, taya zai fara. Haka ya wuce ni ya saka aka kira mishi sauran mutanen rugar ya gaya musu abin da ya?e faruwa. Shiru suka yi kafin aka samu wasu tsagera suka kama dariya."Baffayo kana nufin Mu bar rugarmu saboda kada mu mutu? Kusan kai ma kana da shanun nan,don haka babu inda zamu ai wannan maganar karya ce wallahi babu wani! Harin da za a kawo mana, da alamu tsufa ya fara kama baffayo." Kiri-kiri matasan nan suka ?aryata shi, haka yasa shi komawa gida da tarin takaici da bakinciki.
Koda ya dawo ana kiraye-kirayaen sallar Magariba, a masallaci ma yayi magana dayawa suka karya tashi sai yayi shiru, koda ya dawo bayan isha muna cin abincin, ya shalenta abin yake faruwa a cikin gidan, Babangida ya ce mishi. "Baffa taya zasu kiraka su gaya maka, kawai dai wannan zance ne. "Bai fito ya ?aryata baffa ba, amma maganarshi sak ce da ta sauran mutanen, ban san me yasa ba ko don a gabana aka yi wayar sai naji zuciyata tayi sanyi, kuma wani irin tsoro da fargaba, ya shige ni Zulaihah ma ta shiga haWa duk wani abu me muhimmanci akan mu bar garin cikin daren nan, amma wani abin mamaki kana naka, Allah yana nashi, wurin karfe tara na dare, muka dinga jin ?arar harbe-harbe, hankalin Baffanmu ya tashi, yana shigowa dakinmu ya ce min.."taso Fadimah." Tashi nayi a rikice ya cewa Zulaihah. "Kema tawo!" Dakinshi ya wuce damu," kada ku sake ku fito matukar bani na bude muku kofar ba, da izinin Allah babu abinda zai faru." Ashe ya tafi har dakin Nenne ya kwaso yaranshi, Yar matan nan tace ta adana Yaranta, domin mugun nufinsa ya janyo wannan tashin hankalin,da bai fada ba ai da babu abinda zai faru. Bai mata magana ba ya dawo duk inda ya nime su bude kofar ya kwaso yaran sunki,.haka yasa shi dawowa ya dauki addarshi ya tsaya a kofar gidanmu.
Ban tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba,domin kuwa kana d'aga kai zaka ga yadda garin yayi jajjur da wuta da hayaki. Baka jin kome sai karar bindigu da kukan dabbobi.

Ban san me yasa idan wani abu ya faru mutane ke huce takaicinsu akan shanu ba, shanu suna da daraja a rayuwar Bafulatani, domin zai iya hakura da rayuwarshi akan dabbarshi, amma mutane basu ganewa. A cikin yan dakikai nayi wannan nazarin, "Tau!" Muka ji kar'ar harbi kamar a cikin gidan anan aka yi,kuma babu karya a cikin gidan aka yi. "Malam Buba yau addarka ba zata amfane ka, da kome ba, domin kafin ka kai sara mun tashe ka aiki." Jijjiga kofar nayi ina hango Baffa'm a kwance, domin sun haska mishi katon torchlight dinsu mai shegen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login