Showing 36001 words to 39000 words out of 100763 words

Chapter 13 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2855

idanunta ya sauka akan Addah zata shake mata uwa, da wani karfi ta bangaje Addah ta fadi can. Ta shiga dukarta kamar Allah ya aikota.

Dake yarinya ce kuma da sauran kuruciya a tare da ita, da kuma a fusace take da Addah haka ta rufe idanunta tayi ta dukar Addah. Ganin da gaske zata kashe ta yasa ta saka ihu da kururuwa tana niman ceto. Amma ina zuciyar Ummi ta kai iya wuya, domin ta gama sarewa matukar basu nan Addah kashe mata uwa zata yi, tunda ta iya sayar da Yarta Uban waye ba zata kawar don cimma manufarta ba, Ihun Addah yasa mutane suka farga aka kawo mata dauki. "Ke ba Babarki ba ce!" Aka shiga d'aga ta dakyar. "Da wannan ta haife ni gara ban zo duniya ba, in sha Allah Addah mushe sai yafi ki daraja." Ta fada tana kuka me ciwo, ta d'ago kai tana kallon yadda kowa yake bata laifi. "Wannan da haihuwarki gara b'arinki, sam baki cancanci zama uwa ba, Allah ya isa tsakanina da ke, Addah In sha Allah lahiranki sai tafi duniyarki muni." Ta fada cikin kuka domin bata san wani level zata ajiye Addah ba, domin matar bata bu?atar addu'a sai Addu'ar iftila'i da masifa da jafa'i. Sai da Uwar Mugu ta shigo ta zubawa Addah idanu. Kafin ta ce. "Me ya had'aki da ita?"
"Eyeee! Hmm kawai don."
"Karya take zuwa nayi ma same ta, zata kashe min Yakumbo." Harara Uwar mugu ta watsa mata tana faWin. "Ka da na kuma jin makamancin haka."
"Naji Hajiya haka ba zai kuma faruwa ba," inji Addah da kumburaren bakinta, kallon Ummi tayi ta ce mata. "Kema wannan ya zama na karshe ki kula da Mamanki. A wannan duniyar mutane na iya kome saboda kuWi kiyi tunani dakyau...
#money
#evilalive
#trueordare
#mai_dambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

*Ni ban san me Adda tayi aka tsane ba, salon ku saka mata ido da baki ta lalace =?9?=?!?
'?? da alamu Adda tana girgiza ku=?9? mutuniyar kirki saura ku ji ban dadi =?!?=?9?>?#?*
___________________________________________
```Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTU?ARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....```

*013*

"Babu abin da kudi basu saka mutum ya aikata, rayuwar mahaifiyarki ko kuma ki wayi gari babu labarinta shine gaskiyar da zan gaya miki." Daga haka ta juya ga Addah, "Ba kowa yake da hakurin da zai ga kina shirin lalata mishi goben???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? shi ya iya hakuri ba, don haka sai a kula." Daga haka ta fice a dakin, ita kuma Ummi ta koma gaban Mamanta, tana shafa fuskarta hawaye na zuba mata, a duniya idan akwai abin da ta tsana shi ne ka tab'a mata Yakumbo, haka yasa ta kece da kuka me ban tausayi, gani take kamar duk abin da ya faru Addah ce sababi domin da bata yi shawarar kawo Zahrah Taraba ba, da basu faWa wannan bala'in ba, bakiWaya ta tattara laifin kacokan ta aza bisa kan Addah, tsanarta da wani sabon kiyayyar Addah take ji, a hankali ta juya tana kallon Addah kafin ta ce mata. "In sha Allah sai na gayawa Zulaihah kin sayar da ita, sannan abinda baki sani ba, Zulaihah ciki ne da ita, don haka ki saka a ranki bakin ciki da goyon shege yana wuyarki. Mu dai duk lalacewar da muka yi bamu daukowa iyayenmu shege ba, kinci ribar bariki da hujja." Ta fada tana sakin wata dariya me daukar hankali ta cigaba da cewa. "Ni dake shege ka fasa, idan baki ga bayana ba, ni sai naga naki wallahil azim ki ajiye a ranki daga yau na fara farautar rayuwarki. Ba iya ke ba, hatta ta Zulaihah sai na saka ta tsane ki sama da yadda kike tsammani."

Cikin da Ummi ta faWa mata, bai bata mamaki ba. Kamar yadda take ji take gani zata rasa Zulaihah. Murmushi tayi ta ce mata. "Ai ciki na san da shi, sai me? Kuma ki saka a ranki cikin ya kusan b'arewa matukar ina raye. Na gama magana sayar da ita zan yi idan ma suna sonta da cikin jikinta shi kenan, idan har zan sayar da d'iyar cikina Wacece ke da bazan iya cusawa a tashin hankali ba? bakya gaba na domin ina da abin da ya fiki daraja." Shigowar Munaisah ta kura musu idanu, "ba sai kin zuga Zulaihah ba, Addah sayar da ita kika yi ra?" Ta tambayi Addah dafe da goshinta, "Addah na zata duk abin da zamu yi miki akan kuWi iyalinmu da mu kanmu mun tsira." Dariya Ummi tayi, ta ce mata. "Baki san wani abu ba, tow ina kallon lokacin da Addah ta danne Nenne har dai da ta shiga wannan halin."
Cakume wuyar Ummi Addah tayi. "Munafiki algunguma me nayi miki?" "Addah ba zamu kara miki biyayya ba ne, na gaya miki kuma sai na rabaki da duk me shirin yimiki biyayya." Ummi ta faWa tana dariya. "Domin idan ta kashe iyayenmu, bamu da kowa bayan ita, zata saka mu lallai mu amshi ?addarar da bata rubuce cikin littafin mu, wallahi ina gaya miki sai na ga bayanki"
"Ummi kina tsammanin don kin gaya min Addah tayi yunkurin kashe Nenne zan yi mamaki ne? A wannan takin ni kaina na samu damar zan kawar da Nenne domin matukar tana raye ba zan samu yadda nake so ba, don haka ki ajiye a ranki mutuwarta shi ne tashina."

Wani abu ne ya tsaya a ran Ummi wato, ita ta ma lura duk wanda ya zauna da Addah sai ya zama mara mutunci, fisabilillahi uwar da ta haife ka, zaka nuna bata da amfani a rayuwarka. Komawa jikin Yakumbo tayi, tana jin kamar ta goyata su gudu, domin kuwa tana hango rashin imaninsu kada ta matsa jikin Mamanta a kashe mata uwa. Tana jin yadda suke shewa da ihu, kudi suke kirgawa tun daga lokacin bata tashi a gaban Yakumbo ba, sai da taji sallamar Zalaihah. Sai lokacin kunya ta kamata, tabbas bata kyauta ba amma kuma babu wanda zai so a tab'a mishi uwa. Abin da ya fara fitowa bakin Zulaihah shi ne. "Addah hatsari kika yi ne?" Ta tambayi Addah hankalinta a tashe. Kallon Ummi Addah tayi, ta fashe da kuka tana nuna Ummi. "Ban gane ba, kina nuna Ummi gware kuka yi da ita?" Girgza kai tayi ta fara magana. "Kashi ta bani." Juyawa Zulaihah tayi ta kalli Ummi, bata ce mata kome ba, ta wuce ta zauna tana nishi. "Ashe dama zulai har zaki yi ciki ba zaki gaya min ba?" Da sauri ta kalli Ummi, eh Ummi tasan da cikin, kallon Addah tayi kafin ta ce mata. "Ina son cikina ne, domin ba don naci abinci na same shi ba, domin ina son Ubangiji ya gafarta min ta sanadin cikin."
"Shi yasa Uwar da ta haife ki, ta sayar da ke ba." Inji Ummi, sannan ta cigaba daga inda take cewa. "Babu wanda zai yarda yana ji yana gani don biyan bukatar wani a kashe mishi Uwa, kama wannan tsohuwar kilakin nayi zata kashe min mahaifiya, kuskure ne don na kare rayuwar Mahaifiyata? Nayi laifi kenan?" Girgza mata kai Zulaihah tayi, tana jin zuciyarta kamar zata buga, ta kalli Addah . Gyara zama Ummin ta kara yi ta ce mata. "Ta sayar da ke. Idan kina da yadda zaki yi kafin su bukaci Waukarki da cikin jikinki sai ki sani." Daga haka ta mike ta suri gwangwani. "Zan tafi sallah ga Yakumbo, idan wani abu ya same ta, Addah ce." Daga haka ta fita daga tantin, Zuzu kan bata ce kome ba,.domin kuwa tasan idan tayi magana ba mamaki zucuyarta ta buga, haka ta zauna shiru har Ummi ta dawo. "Ki duba tana raye?" Zuzu ta tambayeta.b'ata Yakumbo Ummi tayi ta cewa Zuzu. "Eh tana raye." A hankali ta juya ta fara sallah, tana idarwa ta fara addu'a a lokacin Munaisah da Addah suka fice a dakin, ita kuwa ta cigaba da musu munanan addu'a da tsinuwa. Duk wanda ya jefa rayuwarta cikin hatsari.

"Ya isa haka, kada garin fushi ki jefa rayuwarmu cikin tsinuwa. Tunda Yakumbo tana raye, ki saka idanu akanta. Kuskure daya kika min, na bayyana zancen cikin jikina ko Zahra sai yau na gaya mata. Addah kuwa ba zan yi mamaki ba, idan ta nuna bata san da zancen cikin ba, ai ba laifi ba ne, to amma kada ki kara min haka." Itama Ummin cikin kuka ta ce mata. "Wallahi na gaji ne da halin Addah, a can idan ta ce ta dauki nauyin mu da na iyayenmu ba laifi amma a wannan lokacin da muke, cikin tsaka me wuya ta ce zata saka mu, karuwanci ai babu kanta sannan haka bai ishe ta ba, sai da na kamata zata kashe min Uwa, gaya min Zalaihah me ya dace nayi?"
"Kare mahaifiyarki;" inji Zuzu, "Gaya min ta ina nayi kuskure? Akan addah wani irin bala'in rayuwa ne ban gani ba? Kafin na waye a harkan sai da aka zubda min ciki sau uku, ya take son nayi? A haka ta haWa ni da mutumin da ya goga min infection da kyar na rabu da ciwon. Haka kawai sai ta nime kashe min uwa? Duk abin da nayi fama da shi addah bata bani kudin magani ba, ni daya nayi fama da kaina.

Allah ba zai tab'a barin addah ba, domin daga duniya zata ga sakamakon abinda ta aikata. Wallahi nayi dasananin abin da na aikata, Zuzu akan idonku aka keta alfarmar Mahaifiyata, aka keta nawa maza sun fi shida akan Yakumbo, Zuzu Gaya min har zan ji wani d'a namiji ya burge ni? Gaya min anya akwai adalci a cikin wannan yanayin? Mahaifiyata fa suka lalatawa farinciki bayan sun kashe kannena da mahaifina da kowa nawa.

Zuzu me Addah take so nayi? Bayan na gama ganin masifa da idanuna zata bukaci na kara hada shimfida da wani d'a namiji, tsoro nake ji Zuzu ina tsoron Allah kada ya kona ni." Rungume juna suka yi. "Babu wanda zai kuma saka ki dole, koda bana nan kada ki gayawa Zahrah kome ki barta ta fahimci abinda ya faru da kanta, kada ki gaya mata don Allah."
"Wallahi ba zan iya ba, matukar na ganta cikin wani yanayi zan gaya mata. Amma zuzu me yasa kike gaya min haka?" Murmushi tayi tace mata. "Ba kome kawai dai na gaya miki ne kada ki gaya mata kome."
Suna zaune addah suka shigo da kayan ciye-ciye, itama Zuzu ledar da tazo da shi, ta bude suka ci abincin da Ummi. Sai da ta gama cin abincin, ta kalli Munaisah. "Ita baiwarki da kika bari a can Asibitin me kike nufi?" Kallon Addah tayi, tana son tayi magana amma ganin har lokacin Zuzu bata yi magana ba, yasa Addah kasa da kanta. "Zaki tashi ko sai naci Bu..... Ubanki." Inji Zuzu tana mikewa. "Doluwa jaka!" Mikewa Munaisah tayi kamar zata mutu, ta dauki kayanta. Itama zuzun ta mike tana bayan Munaisah, tana kare mata zagin kare dangi, har asibitin don masifa Zuzu ta kawo ta, ina zaune kamar wata mara galihu, sai ga su nan mikewa nayi ina kallon yadda Munaisah take share kwalla. Domin a duke zasu daku da Zuzu, amma kuma Zuzu irin mutanan ne masu matukar kwarjini domin yar bala'i ce.
"Meye na kuka?" "Rabu da shegiya ba zata zo ba, wai har tana kuka yar iska Uwarki ce, ba Uwarta ba."
Girgiza kai nayi na cewa Zuzu. "Tunda bata son zama ta koma, ke mu kwana dake." "Wallahi ba zata koma ba, idan ta koma ma wurin wani shegen zata kwana." Sake baki nayi ina kallonta, "wurin wani shegen zata kwana?" "Wallahi na rantse miki da Allah, kwana zata yi a wani wurin."
Mikewa nayi ina karkad'e jikina na ce mata. "Ok sai ki zauna. Ai kin san yadda ake kome ke muje!" Daga haka muka bar asibitin, raina yana b'aci. "Kin san Ummi da Addah sunyi faWa?" "Ina zan sani, tunda ina asibiti."
Murmushi tayi tace min. "Hmmm! Allah abin tsoro rayuwa abin tsoro, yau wai Ummi ce take gaya min Addah ta sakata aiakata abubuwa masu kazanta, yanzu ta tuba ta bi Allah ba zata kuma bin maza ba, asalima tsoron mazan take "
"Alhamdulillahi Allah ya amshi addu'ata, akanta kenan, tunda gashi nan tana faWin ta tuba."
Murmushin karfin hali tayi ta fara bani labarin yadda aka yi, ware idanu nayi ina mamakin yadda ta iya dauke kai kamar babu abinda ya faru. "Me yasa baki damu ba?" "Kawai ba zan tab'a damuwa ba, domin kare rayuwar Mahaifiyarta tayi, kuma ko kashe addah tayi bata da wani hukuncin." "Amma!" Rike hannuna tayi tana faWin. "Addah tayi kurakurai, kada haka ya zama abin da zaki bi bayanta, barta da halinta bata ga kome ba." Ta fada tana sauke ajiyar zuciya.

Ban san me yasa haka yake faruwa ba, amma nasan Addah tana da kaso mafi girma na lalacewar rayuwar Ummi, lokacin da muka isa da Balali muka haWu tunda ya ganni yake murna, sama sama na gaishe su, muka wuce koda muka isa kallona Ummi tayi ta ce mana."me yasa kuka bar ta a can Asibitin?." "Mahaifiyarta ce duk abinda ta gadama tayi, rayuwar Nenne yana hannunta, ta ce ko ta samu damar kawar da ita, zata yi ga damar nan na bata na dauko Zahrah da ta tare mata damar." Inji Zuzu tana dafa kafadana. "Ban gane ba?" "Ba zaki gane ba." Hadiye yawu nayi wato idan na fahimta akwai abin da ake boye min, kura musu idanu nayi da na fahimci basu son na fahimci kome, sai na zauna ina faWin . "Yau baku mana abinci ba ne?"
"Tun tafiyarki jiya babu wanda ya kara abinci sai Zuzu." Inji Ummi, mikewa nayi na dauki sauran kayan abincin, na fara kokarin daurawa, sai ga Uwar Mugu da wasu matasa uku, kallonta nayi kafin na mike ina son nayi magana. "Ina Munaisah?" Tana asibiti wurin Mamarta. "Me yasa bata zo ta gaya min ba?" Daga ciki zuzu ta leko tana faWin. "Bata zo ba, domin can ya dace da ita ba nan ba." "Ke waye ya saka ki?" Daya saurayin zai shiga cikin tantin na tare shi, "wai meye haka ne?" Na tambaye ta. "Kyale su ku tawo da Aina'u " haka suka wuce ina kallonsu, juyowa Uwar mugu tayi tana kallona, fuskarta a sake. Ta bar wurin a can kuwa tana shiga dakinta, ta ce . "Yallabai yarinyar tana asibiti wurin jinyar Mamarta, amma na saka a kawo min Aina'u."
Gyad'a kai yayi yana kallon wayar hannunshi. "Me yasa bata gaya min Uwarta bata da lafiya ba?" "Afwa Yallabai."
Haka aka tawo da Aina'u da ta cab'a kwalliya kamar zata wurin gasar kyau.
&&&
Niamey. Niger republic
*Familyn BA'ARE*
Alhaji Muhammad Dan Ba'are, su Win dangi suke da Ibrahim Khalil Dan Ba'are (na cikin Bororoji) kakansu daya, kasancewar sun jima da barin agadaz, haka yasa su sai suke amfani da Ba'are zalla, yayin da Khalil yake amfani da Dan Ba'are.(zaku iya bincikar Bororoji duk da ban fito da nasabarsu ba, amma labarin BA?IN HAURE da Bororoji yana da nasaba da juna)
Alhaji Muhammad Dan Ba'are, ya baro gida agadaz domin karatun addinin Muslunci, ba don kome ba sai don yadda Mahaifinsu yake fifita wasu Sangaren na gidan da su, shine d'a na farko a gidan, sai Alhaji Ibrahim Dan Ba'are d'a na biyu, sai Hajiya Latifa, Mahaifiyar Mohan.

Kasancewar su dakinsu Ibrahim sun maida hankalinsu akan karatun boko, yayinda Mamman Ba'are yaki boko ko kadan, haka yasa shi ganin ai ana fifita yaran dakinsu Ibrahim, mahaifiyasu an maida ta kamar saniyar ware. Dalilin haka ya bar gida, ya tafi karatu a can ya hadu da wani abokanshi. Suka wuce kasar mali.

A can suka shiga harkar hako ma'adinai, har na tsawon shekaru biyu, ana haka wata rana, kasa ta rubta musu sai da suka kwashe wata goma sha huWu, kafin aka fito dasu, a kasar nan shi daya ya rayu sun kai su goma sha takwas da suka shiga amma shi daya ya rayu, a lokacin da aka kai labarin Mutuwarshi, Nana sai da ta kwanta jinya da tsanar kishiyarta Hajiya Balaraba, da ganin kamar ita ta mata hanyar da d'anta ya mutu, gaba da kiyayya me zafi suka kara ruruwa a Familyn Dan Ba'are dalilin da yasa suka bar garin agadaz kenan.
Shi kuma a can ya rayu cikin amincin Allah, domin a tsawon watanni nan. A ramin nan da suke hako kuza, a nan yayi katarin haduwa da dutsen zinari, haka yayi ta hak'a, bai fasa ba Abinci sai beraye su yake kamawa ya buga gwal da kuza, wuta ta kama, ya gasa beran da ya kama. Ruwa yana samun shi ne ta wata jijiyar bishiya da ta ratsa karkashin kasa.
Haka yayi ta rayuwa, kwatsam sai ga shi ana tono, inda cikin hukuncin Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login