Showing 24001 words to 27000 words out of 100763 words

Chapter 9 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2853

iya nutsuwa ya shirya kome cikin dadin rai. Ka koya daga gare shi."
Rintsa idanun yayi yana jin kamar ya fita ta rufe su da duka. "Kai mishi barazana da rayuwarshi? Kasan ko ciwon kai yayi kai ne, idan mun koma gida kayi gaggawar kiran yan jarida ka wanke kanka."
"In sha Allah "
"Na gaya maka, hatta tari idan kayi duniya zata fassara shi da wata manufa ce, baka gane ba, kana kokarin lalata min shiri na."

Hajiya da Yaranta baki daya wucewa gida suka yi, Majid da daman ya rigasu barin wurin taron, sun same shi a dakin shi na Asali , yana kwance. Dakin duhu kamar kullum. "me yasa kake son zama cikin duhu?" Tashi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yayi zaune yana kunna wutar da yake gefen gadonshi. "Hajiya ina jin dadin haka ne, domin yana tuno min da wasu abubuwan da suka wuce."
Murmushi tayi tana kallonshi ya kara girma, ya nutsu ba kamar lokacin baya ba. Ya zama cikakken namiji me cikar halitta, sadauki da duk inda ake nimanshi ya kai. "Abdul Majid maganar aure fa?" Gabanshi ne ya fadi, ya kurawa ?asa idanu. Akwai wani abu da yake rufewa a zuciyarshi baya jin zai iya aure. "Hajiya!" Ya kira sunanta muryar shi tana rawa. "Hajiya auren nan dole ne?"
"Dole ne Majid! Dole kayi aure domin haka ne zai saka ka kara zama cikakken mutum ka zama magidanci."
"Hajiya."
"Akwai yar kawata babanta abokin cinikin mu ne, kaje an jima da yamma ka ganta."
"Hajiya!" "Bana son musu, ai na maka adalci rabonka da kasar nan." Mikewa tayi tare da fita daga dakin. Sai da ta isa bakin kofar ta juya ta ce mishi. "Ka fahimci gatar da zan maka amma ban maka dole ba." Gyada kai yayi yana jin kamar ya fasa ihu.

Hajiya tana fita falon ta Salamatu me aikinta tace "Hajiya akwai baki a falon kasa ." Kura mata idanuwa tayi ta ce mata. "Su waye?" Cikin girmamawa ta ce mata. Hajiya Nana da Hajiya Hadiza!" "Muje!" Tsayawa Salamatu tayi Hajiya ta shiga gaba, har falon kasa suna zuwa suka same su a hakimce. Niman wuri tayi ta zauna tana gaishe su. "Ina Abdul din yake?" Inji Hajiya Nana. "Yana sama!" Kwafa tayi ta ce mata. "Wato har ya kai da ya mai da mutane yan iska ko? Sai yazo gari ya ki zuwa gaishe da Hajiya." Murmushi Hajiya tay ta ce musu. "Na ga dai Abdul Majid Mamman Ba'are, d'ana ne kin manta ne Hajiya Hadiza? Da kika ce Yaransu Hajiya Rabi da Fauziya sune Yaranki, Yaran da suka fito daga jikina Yayan bariki ne, yanzu kuma da wacce kuke tafe?"
Kurawa Hajiya idanu suka yi, Nana ta ce. "Bana son munafurci, kiyiwa jikana magana yazo har gida ya..."
"Tunda kika kasa hakuri kika zo takalata da faWa, kin san dai baki isa na zo har gidanki ba." Ya fada yana gyara hannun rigarshi. Kallonshi tayi wannan yaro yana bata tsoro har cikin ruhinta. Hadiye yawu tayi tana kauda kanta domin tana matu?ar tsoronshi. Zama yayi ya kalli Hajiya Hadiza ya ce mata Mama Barka dai."
Tab'e baki tayi ta ce mishi. "Barka."
"Yanzu Alhaji sai kazo garin nan baka zo ka duba ni ba.? Fisabilillahi." Ta fada kamar zata fashe da kuka.....

#thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*009*
Tamke fuska yayi yana kallonta, domin ba zai tab'a mantawa da izayar da matar nan ta bashi ba, cikin muryar shi mara daWi ya ce mata. "Nana kin ajiye ni ne da zan zo na duba ki?" Shiru tayi tana kallonshi kamar zata mutu, idan ta ga yana nuna mata kiyayya haka. "Alhaji ina laifin Nana don ta damu da kai?" Mikewa yayi bai basu amsa ba, musamman ita Hajiya Hadiza da ya tsani ta mishi magana.
"Kyale shi ai Uwarshi tana gani yake wulakantani." Murmushi Hajiya tayi tana faWin. "kin sha gaya min idan kina magana da ahalinki na daina shiga cikin maganar, kuskure ne don na zab'i yin shiru akan na magantu?"
Cikin borin kunya ta ce mata. "Hmmm! Haka dai kika ce, amma ni yaushe na ce ki daina shiga cikin ahalina. Yanzu dai nazo ne maganar kamfanonin nan, da fatan dai ba za a cire min hannun jarina ba ko?"
"Ni babu ruwana ki same shi." "Tow ta nan kika bullo min Sa'adatu?" A gajiye da halin Nana Hajiya ta ce mata. "Nana meye nawa a cikin wannan lamarin? Yaran nan jikokin ki ne, sannan kuma."
"Kawai dai ki ce mana Yaranki sun fi karfinki, amma taya akan wannan yar maganar zaki ce wai babu ruwanki salon munafurci da nunawa kamar ba ruwanki." Inji Hadiza Abdul Majid ba'are, "Hadiza kin ga babu ruwanki da sha'aninmu, tsakanin Nana da Jikokin ta gata ga su ina ruwana?"

Ta fada tana kallonsu, kwana biyu da suka wuce har cikin gidan suka biyo ta suka ci mata mutunci har da mata gorin a caca aka aurota, haka duk bai isa ba Nana ta gaya mata cewa ta zuba idanu tayi kallo hatta wannan gidan da take ciki sai ta fice daga cikinshi, sai gashi Allah ya raba gardama ya kawo mata shi cikin sauki, don haka ba zata lamunci rainin hankali ba. "Hmm! Nana tashi muje!" Inji Hadiza, haka suka fito a harabar gidan suka same su, a ran Hajiya Hadiza ta ce. *Shaidanun biyu* kallon Nana Aryan yayi, ita hankalinta yana kan hannun Captain yana goge wata sabuwar bindiga. "Captain ni dai ka nima min lasisin rike bindiga!" "Munafiki algungumi uban me zaka yi da bindiga?" Juyawa yayi ya kalli Nana. "Hajjaju laifin me na miki? Uwar Mamman Ba'are!" Ya tambaye ta, yana wasa da katon lion dog Winshi. "Uwarka Sa'adatu gata can a sama." Juyawa yayi ya sumbaci hannun shi ya wurga mata. "Ta iya haihuwa tunda ta haifi Abdul Majid Mamman Ba'are, ta haifi Aryan Mamman Ba'are ba, Uwar Jamilah da Aneesah, Babar Amaan Mamman Ba'are, akwai saura ne?" Ya tambaye ta, cike da takaici ta ce mishi. "munafikin banza." "Da nayi miki me?" "Kai dai wutarka dabance." Sam baya son hayaniya, don haka ya d'anna kunamar ya sake harbi a iska, shiru wurin ya dauka. Musamman Hajiya Nana da ta ji kamar zuciyarta ya harba, kafin su farga daga ita har yarta sun gudu baka ganin alamarsu, sojojin da aka bawa Captain Win suka shigo a guje. "Sir!" Murmushi yayi ya musu alamar su tafi da hannunshi.
Kar'ar harbin Majid Mamman Ba'are, ya karad'e ilahirin gidan baki daya, wanda yasa kowa ya sha jinin jikinshi, lallai Majid ya iso, Gidan Alhaji Kamilu Abdul Majid ba'are, kuwa tab'e baki yayi ya ce. "Kowa ya sayi rariya yasan zata yi yoyo, ai na gaya musu, babu ruwansu da Yaran Sa'adatu amma suka ki, gashi nan sun takalo mana jaraba." Ya fada yana shan tea a hankali, "ni kuwa sai nake ganin kamar da gayya aka takalota."
Kallon Matarshi yayi, kafin ya ce mata. "eh da gayya ce mana, tayi abu ko Yaranta suyi su zama masu laifi ake so." "Amma me yasa suke haka ne?" "Saboda dukiyar Mamman ya raba biyu ya basu rabi, rabi aka yi rabon gado da ita."
"Allah ya kyauta!"
"Kin yi waya da Maisarah?" "Eh mun yi waya, amma tace min idan suka samu hutu zata zo." Shiru yayi yana kara jin ba dad'i. Kowa a duniya yana farinciki da nutsuwa idan yana tare da ahalinshi, amma shi a nashi Sangaren dole ya hakura da Maisarah ta koma wurin dangin Mamanta da suke labenon, tunda a can ya auro ta,kuma ba karamin son Yaransu suke ba. Sai dai tun bayan Mutuwar Mamman Ba'are yarinyar taki zama a wurinshi. "Ina Jamal?" " Ya tafi wurin kallo!."
Gidan Hajiya Tani.
Cikin matsanancin b'acin rai take kallon Sajjid Mamman Ba'are, "kasan yadda na Sata lokaci akan ka samu damar shiga cikin dukiyar Mamman Ba'are?" Girgiza kai yayi yana durkushe a gabanta. "Kiyi hakuri Hajiya!" "Idan ka kuma bani hakuri sai na tsine maka." Ta fada ranta yana suya, "sai da na gaya maka ba zan dauki kuskure ba, kace babu matsala Amaan zai bamu hadin kai, amma sai gashi daga kai har shi kun fad'i." Kasa magana yayi domin yana matukar tsoron kada yayi magana ta tsine mishi.
"Yanzu kana da hanyar da zaka iya dawo min da asarar da nayi?" Girgiza kai yayi, tayi kwafa sannan tacigaba da cewa. "Dake kai lissafinka baya ja, shine ka bude shegen bakinka zaka mishi barazana da rayuwarshi!" "Na tuba Hajiya!" ?aukar glass cup tayi ta jefe shi sai da ya tasa mishi goshi, jini ya shiga zuba a Kyakyawar fuskarshi.
"Ka sake bani hakuri sai na illataka!" Jini da yake zuba yasa shi rike wurin. "?ace min da gani." Mikewa yayi ya nufi dakinshi,ya shiga kallon kanshi a mirror din dakinshi. Wayarshi ce tayi ?ara. Dauka yayi ya ce. "Na'am!" Cizon fatar bakinshi yayi ya ce. "Ban san asara ba, kayan nan Libya zaa shiga da su, ka gayawa Guru ya binciko min duk inda Jaguwa yake a tsakanin sahara da dazuzzukar Kamaru da Nijeriya, idan kuka sake na fita farauta ba zai muku kyau ba." Ya kashe wayar yana me jifa da ita, asara biyu yayi yau baki daya bai tab'a shiga damuwa irin ta yau ba, ban daki ya wuce ya wanke fuskarshi da jikinshi, sannan ya bude first aid kit ya gyara goshinsa. Yana gamawa ya fito yana tsane jikinshi, ya ji harbin bindigar Majid. Datse fatar bakinshi yayi da hakorinshi sai da ya fara jini.
Ya sake bakinshi a hankali, yana jin Idanunshi yana cika da kwalla. Idan yana raye sai ya ga bayan Majid, ya raya a ranshi yana me kara tabbatarwa kanshi, sannan ya shirya cikin kananun kaya, ya dauki madubi ya saka domin ta rufe mishi inda aka jefe shi. A falon ya sami Hajiya Fauziya, tana kasa da murya ta ce. "Wato ban san yadda aka yi wancan dan iskan Yaron ya dawo ba, amma tabbas ita Uwarshi abin ya mata dad'i." "Zan fita." Dauke kai tayi tana faWin. "Hm!" Daga haka ta juya ga Hajiya Fauziya. "Me kika ce?" Cikin tuntuben harshe ta ce mata. "Naga alamar babu nasara." A fusace Hajiya Tani ta watsa mata harara. "Kika ce me?" Hadiye yawu tayi ta ce mata. "Dama nace wannan karon mun fadi ya zamu yi?" Tab'e baki tayi tana faWin. "Ya kuwa zamu yi? Ku je kuyi shawarar makomarku bamu ba."
A zunkud'e tace mata. "Ban gane ba?" Gyara zama Hajiya Tani tayi ta ce mata. "Dama da an samu nasara kamar yadda na gaya miki, kina da kaso saba'in cikin dari, ni zan tashi da talatin kuma gashi ya dawo." Cikin tsannanin takaici Hajiya Fauziya ta sauke kanta kasa, "Ban san ta inda aka samu matsalar nan ba, amma tabbas akwai wani abu."
"Idan ma akwai ya dace ki sani kece me yara mata baki daya, gara Rabi tana da Lukman, Harirah tana da Sharif ke fa? Babu ko daya sai Yara mata, kuma kin san koda yau gwanjon kayan ba'are aka yi kasonku bai wuce kason Aryan ba, kai ina ba ma zai kai kason Aryan ba. Duk da yadda muka yi dake na cewa zaki tsayawa Sajjid a wurin sai gashi har aka tashi baki yi kome ba, yanzu zaki zo kice min wani abu." Tana gama fadar haka, ta mike tana me barin Hajiya Fauziya a wurin. A hankali ta fita ta bar gidan, tana me jin takaici me yasa Majid ya dawo daidai wannan lokacin.
Alhaji Haladu.
Tunda ya shiga yake safa da marwa, kana ganinshi kasan lissafi ya kwace masa. Matarshi kuma me bashi shawara ta musamman ta zauna tana kallonshi. "Abban Afiyyah ban ga dalilin d'aga hankalin nan naka ba, ai ja da baya sai raggo, taya zamu zuba idanu Sa'adatu ta ci bulus bayan ka manta a caca aka ciyo ta."
Cikin takaici ya zuba mata idanu, ya ce mata "taya zan manta bayan dan uwana ya ciyo ta ne a caca,a lokacin da yake ?ishirwar d'a namiji a lokacin ya saka kudinshi aka ci kawunta."
Murmushi tayi tana kara jin haka shine abinda take bukata,bata kaunar Sa'adatu ta cigaba, amma dole haka zata hakura.
Shigowar Hajiya Fauziya kamar an watsota daga sama, yasa baki dayansu suka razana. "Ke lafiya?" "Ina lafiya kuwa." Ta fada tana gyara zama, "ya zamu yi Haladu?" Gyara zama yayi ya ce mata. "ya kuwa zamu ban da mu nime wata hanyar?"
"Kamar ya wata hanyar?"
Gyara zama yayi yana faWin. "Dole zamu marawa Tani baya, sai mu san me za ayi kuma."
"Kana ganin marawa Tani baya shine mafita?" Inji Hajiya Turai Matarshi. "Eh mana shine mafita, domin ita ba zata watsar da ra'ayinmu ba"
Dariya tayi tana faWin. "Lallai fa, tow Tani itama hanyar niman shiga take kan dukiyar Yaran Sa'adatu, idan kuka mara mata baya zata iya juya muku baya, idan kuka nime naku na kanku kowa zai kasance a ankare. "
Shiru suka yi kafin kuma suka ce mata. "Bamu fahimci inda kika dosa ba?" A hankali ta gyara zamanta ta warware musu fahimtarta, sannan ta kara musu kwarin gwiwa da cewa dole su kasance masu mika kai domin idan baka iya kama barawo ba tow shi zai kama ka."
Nan suka yi na'am da shawara ta, har Hajiya Fauziya ta fita, Hajiya Turai ta cewa Mijinta. "Bari na gaya maka gaskiya, matar nan munafuka ce ka sani nima kuma na sani, so abin da zan gaya maka. Zata tafi wurin Hajiya Tani da zancen nan, kai ka fara kiran tani ka gaya mata abin da ka yanke. Sai na gaya maka yadda zamu yi"
Ai kuwa kamar yadda ta fada haka ya kira Tani, ya gaya mata kome da kuma yankar bayan da Hajiya Fauziya ta mata, sannan suka dauki laifin kacokan suka daura mata, ita ce ta kawo musu zancen a shiga malamai. Jin shi Hajiya Tani take, sai da ya gama ta ce mishi. "Zan duba al'amarin"
Ta kashe wayar, murmushi Hajiya Turai tayi ta ce mishi. "Ka shirya zuwa bayan Magariba ka tafi gidan Hajiya Sa'adatu ka yi sulhu da ita. Idan ta lalace maka anan a can zaka fita"
Kurawa Matarshi idanu yayi tunda yake bai tab'a zata shaidaniya ce har haka ba. Take ya sake murmushi yana faWin. "Lallai Hajiya ke duniya ce."

Murmushi tayi tana faWin "taya ba zan kasance haka ba, ina tare da dai ga makiya sun rufa maka baya ta ko ina, ai lahu a gare ni na tsaya maka, don haka kada ka ji kome mijina."
***
Wurin karfe biyar na yamma Hajiya Sa'adatu tana kan abin sallah, tana lazimi Nabeeha matar Aryan ta shigo hannunta dauke da katon tire, bayan ta Aryan ne dauke da Kwando, "Assalamu alaikum Barka da maraice Hajajju." Sallamewa tayi tana kallonsu fuskarta dauke da murmushi ta ce musu. "Amin wa'alaikumus Salam, barkanku mutanen kirki." Gyara zama tayi tana faWin. "Nawa ne ko na Hammanku?" Dariya sukayi. "Hajiya naki da nashi ne, muka ce bari a kawo mishi, duk da ban gaya mata da wuri ba." " Hajiya kinji ba yaki gaya min zai tawo da hamma kawai sai gashi nan yazo da zancen akwai bako." Nabeeha ta faWa tana tura baki. "Baka kyauta ba, maza jeka dakinshi ka taso min shi."
"Tow Hajiya." Haka ya fita zuwa dakin Majid din da yake kwance, ya lullube kanshi da mayafi, dakin ya bada wani irin duhu. Kunna wutar dakin Aryan yayi, ya hango shi zaune ya jingina da allon gadon. Amma kanshi a lullube yake. "Baka da lafiya ne?" Janye lulluben yayi yana kallon Aryan. Dauke kai yayi yana me sake lullube kanshi. "Kazo falon Hajiya da yake sama Please."
"Me zan yi?" A yanayin rayuwarshi matukar ba'a wurin aiki ba,baka tab'a ganin fara'arshi, tashi yayi ya sauka daga gadon ya nufi ban daki. Sai da ya gama uzurinshi ya fito ya saka hula a kanshi ya fita. Zuwa falon hajiya domin sun fito daga Wakinta, yana shiga ya same su a kan kafet sun baza abinci. "Matar Aryan ce ta maka abinci."
"Nagode sosai!" Ya fada yana gyara zamanshi a kafet Win, Aryan ya zuba mishi yana jan shi da hira. "Amma shirun da Hajiya Tani tayi babu magana a kasa?" "Allah yana sane kuma yafi mu sanin abinda yake zukatansu."
Inji Hajiya, tana cin abincin itama don ta lura Majid yaki cin ko loma daya ne, har yau yana shakkar cin abincin kowa, domin rufawa rayuwarshi asiri yasa ban da girkin Hajiya kai ko tea bai yadda ya ci wani abu daga wani wurin ba. Shi yasa a duniyarshi yake shakkar kaidin mace. Saboda kaf duniya babu wanda yasan cewa sanadin jinyar Mahaifinsu guba ce. A hankali ya tura abincin yana murmushi. "Bana son abincin da aka saka citta da tarfarnuwa, domin ina da allergy."
Sanin ba zai ci bane Aryan yayi maza y kare dan uwanshi. "Wayyo kayi hakuri, na manta na gayawa pretty baka cin citta da tarfarnuwa." Murmushi yayi ya mike, karshe abincin da bai ci ba kenan. Kuma ai Hajiya tasan ba zai ci ba. Ita tana ganin har yau Majid bai warke ba, pretend yake kamar mai lafiya amma a zahirin gaskiya bai da lafiya. Shi yasa take son yayi aure ko zai samu wacce zata jure matsalarshi,

"Kiyi hakuri haka yake, baya cin citta da tarfarnuwa ne, tun yana Yaro." Itama Hajiya ta fadi haka, shi kuwa gogan naku yana shiga dakin drower yaja ya Ciro kudi me yawan gaske, ya fito daga dakinshi kenan suka hadu da Amaan Mamman Ba'are,. Kallon kallo suka yiwa juna kafin kowa ya kame kanshi, akwai wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login