Showing 78001 words to 81000 words out of 100763 words

Chapter 27 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2860

had'a kaina da gwiwa ina wani irin kuka na takaici da bakinciki. Cizon bakinshi yayi ya ce min "me kike so?" D'ago jajjayen idanuna nayi ina kallonshi kafin na ce mishi. "Kawai ka rabu da ni." "Ba zan iya ba. domin lokacin da zuciyata ta had'e dake bata yi shawara da ni ba, ni kuma bana jin a raina zan iya rabuwa dake don kawai kin ce na rabu dake, kiyi tunani da kyau."
"Babu inda zan yi tunanin kawai ka rabu da ni!" Na faWa cikin kuka. "Fadimatul Zahra'u, ni fa akan abinda nake so babu abin da ba zan aikata ba. Gaya min me aka miki kike kuka haka.". "ni yaushe nace maka anyi min wani abu, don Allah ka rufa asiri kada ka ja min sabon masifa, kawai ka tafi ka bar ni, idan da hali ka kore ni daga rayuwarka."
Rike hannuna yayi yana kallon kantar hannuna, kafin ya ce min."su waWanda suka miki barazana zasu miki wani abu har suke bautar dake baki gaya musu kina da Sultan Yazid Hamir ba ne?"
"Kai ba iyakata ba ne, su kuma kai ne iyakarsu, ina da tawa rayuwar a wani wurin don Allah ka yi hakuri ka barni." Na fada da ?arfi. Shigowa Aseem yayi d'aga mishi hannu yayi alamar ya tafi ya ce min. "Sun miki barazanar zasu kashe ki ko? Ko sun miki barazanar zasu maki fyade ne? Kai ko sun Miki..." Wani irin zabura nayi tare da kame jikina, da yake rawa sakamakon hada'a idanu da nayi da mutimin da kullum sai ya min kashedi akan Yallabai. Bin inda nake kallo yayi da idanu yaga na sunkuyar da kaina ina kara tattare rigar jikina ina faWin."don Allah ka tafi kaji ka rabu dani." Kusan ban san fuskar shi ba, amma da safe idan na fita ina yawan had'a idanu da shi, haka yasa na karanci kwayar idanuwanshi, ko bai magana ba, nasan shine
.
"Darda!" Ya kira sunanshi, "Na'am Sultan!". Wani irin tsalle nayi na koma ?asar gadon, domin shi din ne fuskarshi da Muryar shi ya tabbatar min da shine, na kame jikina da yake rawa na ce. "Don Allah ka tafi, ka tafi bana son ganinka wallahi bana kaunar ganinka ka rufa min asiri da halin da na shiga." Na fada cikin matsanancin kuka da ihu. Ganin haka ya sashi barin dakin asibitin. Darda ya bi bayanshi. "Aseem ka saka Darda ya gaya maka me suka yiwa Zeehrah!"
"Wallahi Sultan Amiratul ta saka mu, mu mata barazana." Shiru yayi yana zare Idanu, ai yasan matu?ar bai magana ba shine a ruwa. Don haka yayi magana da wuri, koda suka isa gidan yarin. Zubewa Darda yayi ya lissafo mishi wadanda suke da hannu a cikin abin da suka mata. Duk a ka tawo dasu. "Me kuka mata?" Da kanshi yayi tambayar. Jikinsu na rawa suka nuna Darda. "Shi yace zai mata fyade bayan ya mata fitsari kai." Ware manyan idanunshi yayi yana tuno yadda tayi ta kame jikinta. "Abin da ka aikata kenan?" Inji Aseem.
"Tuba nake a yafe min ba zan kuma ba. Wallahi saka ni aka yi, ba zan kara ba " murmushi yayi sannan ya ce mishi. "ka yanke mishi hukunci daidai da laifinshi. "Sultan ka yafe masa, ba zai kuma ba." "Ita yarinyar bata da gata ko? Babu wanda ya damu da ita tunda uwarta da Ubanta sun watsota duniya basu san dajararta ba ko? Gaya min abin da yayi mata akwai adalci a cikin shi, itama mutum ce fa. "
"Bai kyauta ba "
"Aseem ina son Yarinyar shi yasa bana kaunar kukanta, idan har ban bata tsaro da kulawa ba, taya zan ji da abinda yake raina "
Haka ya mike yana faWin. "Ka hukunta shi nace." Ya fita, gidansa ya wuce yabar shi ya samu Reshmah. Share ta yayi bai kuma kulata ba, domin idan yayi magana zata kuma fitar da hanyar da zata kuntattawa Zeehrah. Lokaci yayi da zai koma aljeria. Dama rabon ya hadu da ita yasa ya kasa komawa, a yanzu kuwa babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu koda kuwa mutuwa ce sai dai ta dauke su tare. Haka ya gama tsara yadda zai tafi da komin shi Addah kuwa, sakawa yayi aka mata duka, har sai da suka tab'a mata lafiyar idanunta Waya.
Koda aka dawo da ita kallo Waya Ummi ta mata ta ce mata, "Kina tsammanin daga nan zaki kara samun sukuni ne? Kamar yadda kika saka rayuwar wacce bata ji ba bata gani ba a gaba haka zaki rasa kome naki."
Addah bata yi Magana ba, sai dai dukarta da tab'a mata idanu ya kara haifar mata da bala'in tsanar Zahrah. Sai ta ga bayan Zahrah, sannan abinda ta fahimta Yazid niman kuWinshi ba don ya cutar da kowa ba ne, niman kuWinshi akan kanshi yake daukar kasada, ba kamar wancan mutumin da yake sayan Sassan dan Adam tare da sayan yan mata domin karuwanci ba.
*** Sati biyu nayi sannan na dawo, a lokacin naga idanun Addah yayi wani bala'in girma gashi jini ya kwanta a cikinshi. "Addah baki je asibiti ba?" "Na je asibiti kika tambaye ni? Nace na je asibiti fa? Sai na illata rayuwarki Zahra matukar ina numfashi."
"Baki illatata ba ma an kashe miki idanu, idan kika lakace ta sai dai lahira tayi bako."
"Ban yi dake ba!"
"Dama baki isa kiyi dani ba Addah."
"Mara kunya kawai "
"Marasa kunyar suna dayawa!"
"Addah ki kyaleta muyi maganar idanunki."
"Kinci Ubanki shegiya munafika."
"Kayya da ina nufinki da sharri da kullum kaina zai tsaya, amma dake zuciyata daya ba zan iya nufarki da sharri ba." Na gaya mata, domin zuwa yanzu addah ta fara isata, ban san yadda zan yi da itaba amma na gaji da halin ta, "idan kina son idanunki,ki shirya gobe ki ga likita."
D'ago kai tayi tana kallona, "Annamimiya kina min haka ne don na yafe miki!" Inji ta.
"Idan kin so kada ki yafe min Addah wallahi babu abinda zai tsaya, bakya gabana asalima tausayi kike bani, daga lokacin da ?addarar Allah ta rabamu wallahi billahi azim sai kin yi fatar da ina tare da ke. Ba zan ce Hakkina yayi ta bibiyarki ba, amma nasan zaki so ina tare dake domin ni daya ce kawai. Zan tsaya a gefenki ki tuna da kin haifi Zuzuna, sannan ba zance nayafe muku ba daga ke har ita sai ranar da muka hadu ta gaya min dalilinta na cutar dani babu hujja. Idan yayi miki muje a duba idanun idan bai miki ba, ki zauna da shi Allah ya ba?i lafiya." Daga haka na kyaleta ina zan iya da bakin hali, bakiWaya bata kanta take ba, hanyar da zata cutar dani kawai take nima sai kace na tare mata wani abu.
***
Niamey.
"Alhaji gaya min ina ke maka ciwon?" Kasa d'ago kai yayi ya kalleta. Kuma yayi shiru kamar baya wurin.
"Kace jibi zaka tafi ko? Idan ka tafi zaka ga likita a can ko?" Duk ta uzirawa kanta, gani take kamar laifinta ne da sakacinta. "Alhaji" can kasan makoshinsa ya ce . "Hajiya lafiyata lau."
"Ina lafiya mm, zan zo na ganka."
"Assalamu alaikum!" Afiyyah ta shigo cikin nutsuwa domin duk rawar kanta da iyayinta, tana shakkar Majid da Aryan. "Wa'alaikimus Salam!" Hajiya ta amsa tana kallonta cikin kulawa. "Hajiya wai kizo keda Hammayo inji Nana!"
"Tow shikenan ki ce mata gamu nan!"
A hankali ta fita cikin wani irin taku me tab'a zuciyar yan maza, tunda ta shigo kallo daya yayi mata bai kuma kallon ko inuwarta ba, harkar gabanshi ya ishe shi. "Muje Alhaji."
Me yasa Nana ta kira su bayan abinda ya faru kwanakin baya bata kuma shiga harkar su ba. Tashi yayi ya haura sama ya sako wasu kayan shadda ce skyblue, anyi mata Winki yar shara. Ta cikin rigar wata farar riga ya saka me dogon hannu, sai hular da ya saka ta amshi fatarshi sosai. Turaren pure oud ya fesa, bakiWaya dakin ya hargitse da kamshinsa me dad'i......
#Mai_Dambu
[2/27, 10:56 AM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price
Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au >?#?=?9?=?? kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au =??>?#?=?9? baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida =??=?9? atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne```
*TUNTUBE WANNAN NUMBER 08130269641*


*026*
Yadda ya karya hula zaka rantse cikakken bahaushe ne, amma yanayin fatarshi zai nuna maka cewa bai da alaka da hausawa. Lokacin da ya fito daga dakin shi, Hajiya tana kallonshi daga kasa, kamilalliyar fuskar shi, me cike da kamewa ta kalla sannan ta shiga tasbihi ga Allah madaukakin sarki. "Ya Allah ka tsare min bawan nan naka." Ta fada tana cigaba da tasbihi har ya iso inda take, takalmin kafarshi kawai abin dubawa ne. Haka ya wuce ta suka fita tana bayan shi yana gabanta, sai da suka isa wurin kofar ya bude mata, sannan suka shiga bangaren Nana, haka suka iske falon a cike, gaban Hajiya ne ya fadi, tunda ta gan su tasan Babu alkhairi a wannan zaman nasu, don haka ta shiga da addu'a a bakinta.

"Assalamu alaikum jama'a, Barkanku dai."
"Wa'alaikimun Salam, barkanki Sa'adatu." Yadda suka amsa mata, yasa jikinta ya kara bata akwai wani abu. Zama tayi a daya daga cikin kujerar falon, Shi kuma ya zauna a kasar kafarta. Sai da aka yi gaishe gaishe hankalinshi yana kan wayarshi. Kafin aka bude taron da addu'a. Shiru falon ya Wauka aka rasa wanda zai fara magana, Hajiya Fauziya ta ce. "Nana kinyi shiru abin arziki ya tara mu ba na tsiya ba"
"Eh wallahi fa, dama Sa'adatu." D'ago kai Hajiya tayi tana kallon Nana, baki daya sai ta cika mata idanu. "Na'am Nana!" "Hmmm dama dama!" "Dama me Nana?" "Wai cewa nayi a cikin yan matan gidan nan ya duba daya ya zab'a."
"Ai shine maganar? Tow ai Nana na gaya miki tsakaninku ne na Familyn Ba'are, ni a caca aka ciyo ni gaki ga Majid din Allah ya baku sa'a."
"Ashe akwai babban Al'amari Hajiya shine baku gayyace ni ba?" Inji Aryan yana shigowa falon, yadda yake tafiya zaka tabbatar da iskanci yake ji A ranshi. Domin kuwa bai kawo haka ba, shi dai yana shiga gidan ya ga basu nan, har zai fita yake tambayar Lawe yake gaya mashi ya fito ban daki ya ga fitarsu ta kofar Nana. Zama yayi a stool bakinciki ne ya kama Nana, tasan da babu Aryan zata iya rarrashin Majid,. Amma da Aryan yazo ko ta kulla sai ya kunce mata.
"Alhajina Maisarah ko Afiyyah." Ajiye wayar shi yayi yana kallon yadda ta ririta fuska. Alamar tana son kada ya bata kunya. "Ni ba zan aure su ba, matar da zan aura Hajiyata ce zata nima min, sannan Nana na gaya miki ki daina shiga harkana baki ji ko."
"A'a Alhaji!" Ta faWa tana ware idanun tana kallon yadda ya saka hannu a cikin aljuhun rigar shi. Tasan bindigarshi zai ciro "Alhaji Fauziya uwar munafukai ce ta ce na had'aka aure da Maisarah da Afiyyah, wallahi ba tunanina ba ne, tunaninta ne."
"Hajiya tashi muje!" Ya fada yana mikewa, "Kenan idan baka amshi auren nan ba yana nufin kai ba cikakken namiji ba ne? Ko dai baka da lafiya ana boye mana ne, aeeeeh da alamu mutumin hotiho ne, babu karfin da zai raxana mace, koda yake kai idan aka baka mace karshe a shiga hakkinta aikin sojan shi ya kamace ka."

Inji Sajjid da ya fito tare da Amaan.
"Idan hakan ce zata saka ya zama cikakken namiji, tow ba zai amshi auren ba. " Inji Hajiya ta juya tana kallon Tani. "Da alamu bata gaya maka cewa shi aure da Yaron ciki aure darajarsu ba daya ba ne, shi dan aure yana da wata isa da kamala da duk inda ya shiga sai an girmama shi domin iyayenshi sun san cewa ba zasu?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? b'ata mishi gobenshi ba, duk da a caca aka ciyo ni, ban yi zaman dandi ba, zaman aure nayi na haifi kyawawan irin da babu irinsu." Sannan ta juya ga Amaan da yake zare idanu. Takawa tayi har inda yake ta ce mishi. "Kayi kokari muje!" Ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, ita kuma shi ne jarabawar ta, ace yaro baka isa kayi kome ba sai ya gayawa kowa. Kowa ma abokan gabanka waWanda basu da buri sai ganin bayanka.

"Hajiya ni fa ban gaya musu kome ba." Bata ce mishi cikanka ba, har suka isa falonta. Sakin hannunshi tayi ta zube a kujerar , tana kallonshi ranta a b'ace yake kuma abinda zuciyarta ke son faWa zai iya saka ya kara lalacewa sama da yanzu, "Hajiya na rantse da Allah, ban fadi kome ba." "Gaskiya baka fadi kome ba, sharri aka maka ko? Taya wancan tsinannen ya san matsalarshi? Wato kai dai ina ga baka da banbanci da jaki, domin kwanyarka bata daukar lissafi."
"Meeting din da za ayi gobe ka soke sunanshi a cikin board director." Inji hajiya ta kara kallon Aryan, "akai shi matsayin karamin ma'aikaci kamar kowa jahilcinshi ba zai bashi damar aiki ba."
"A'a Hajiya, tsanar da Amaan yayi min ni ba zan tab'a mishi ba, tayiyu shi yana da dalilinsa, amma ni bani da hujjar tsanarshi. Don haka ki kyale shi a matsayinsa, haka da yayi min yana kara min son shine, domin akwai wani abu da yake boyewa sama da tsanar da yayi min ba iya tsana ce take fitowa daga kalamanshi ba, har da kauna da bai san yana min ba. Shi yasa nake mishi uziri.". Ya faWa, kafin ya wuce dakinshi, rufe kofar dakin yayi ya jingina a jikin kofar. Yana jin kamar ya fashe da kuka, me yasa shi yake jin ciwo sama da kowa? Me yasa yake jin zafin haka? Da yana da wata hanya da ya nisanta kanshi da kasar nan bakiWaya.
Bayan barin Majid falon, Hajiya ta kalle shi, "ka ji dadinka wallahi, Allah ya shirye ka" tsaki Aryan yayi ya bar falon, hatta Matarshi sai da ta fahimci ranshi ya b'aci, don har dare bai da walwala.
Sai lokutan sallah yake fito da shi, bakiWaya sai ya tsangwame kanshi. Da dare Hajiya da kanta ta kai mishi ruwan tea, yana cikin duhun shi na fama dama tasan za ayi haka, "tashi ka sha ruwan zafi!" Tashi yayi zaune, ya amshi kofin tana tsaye akanshi ya sha ya ajiye kofin a gefen gadonshi, "Zaka yi aure!" Da sauri ya d'ago kai. "Eh zaka yi aure koda kuwa babu wani tarayya, idan kayi auren ka tafi da matarka."
"Hajiya!"
"Maisarah ta bar gidan nan tun kafin rasuwar Babanku, Sannan mahaifiyarta kawai take mu'amala da ita, sau biyu muna haduwa a Saudiya, tana son yin magana amma tana ganin Mahaifiyarta zata yi shiru mu gaisa."
"Hajiya idan ta san ba zan mata..."
"Kada ka damu, dazun na kira Hajiya Sanah na tambaye ta, ko tana da saurayi ne? Ta ce babu hankalina ya fi kwanciya da Maisarah domin Afiyyah suna tare da Sajjid, duk abinda zai haWaka da Tani ina avoiding Winshi."
"Hajiya!"
"Kada ka ce min kome!"ta faWa tana barin dakin, zuwa yanzu Hajiya tana son fitar da wani abin da ba kowa ya sani ba, daga ita sai Majid dangane da Mutuwar Mamman Ba'are, idan har tayi hi jack points, tow ba makawa zata iya saka wanda yayi kisan motsi. Duk da bata san meye ake shiryawa ba, sai dai tafi tunanin ana shirin da bata san ta inda xa a fito mata ba.
***
Monday.
A yau monday akwai batutuwa da yawa da ake son aiwatarwa a kamfanonin BA'ARE GOLDEN EMPIRES, sai dai wani abin da ya tab'a zuciyar al'umma shine tashi da samun labarin mutuwar babban manajan kamfanin.
Daga Hajiya har yaranta hankalinsu a tashe yake, kuma abin tambayar anan shi ne, waye ya kashe shi? Shin kashe kansa yayi ne? Tow akan me?
Majid kan kin saka kanshi yayi cikin maganar, kuma bai da niyyar haka kuma har Hajiya ta fahimci haka, shi yasa ta tsaya ita da Aryan suka yi ta shige da fice. A cikin kwanaki uku sun jigata, jinin Hajiya hawa yake yana sauka, dole Aneesah ta tsaya a gefen Aryan, ga sintirin yan sanda a kwanakin.
Sai da aka kwashi sati daya ana abu Waya, karshe tafiyar Majid da bai samu yayi ba kenan, ya kara niman excuse.
A cikin sati biyu da yin abin, aka ga wasu mutane haka kawai suka rufe Kamfanin. Tsawon awa takwas aka dauka, kafin aka bude kamfanin kamar babu abinda ya faru.

Washi gari.
Aka kai sakamakon office din Aryan suna tattaunawa da Majid da ya kawo mishi, "Yallabai gashi nan, sakamakon binciken da muka yi." Ya mikawa Aryan kallon Majid yayi kafin ya dauke kai, yana amsar takardan. Mikawa Majid yayi ya ajiye, yana kurbar coffee. "Mun gode!" Sannan mutumin ya fita, zama Aryan yayi ya fara bude takardar, mikawa Majid yayi, "ban fahimci abinda suke nufi ba."
A hankali ya amsa yana faWin. "Kiran da yayi kafin faruwar lamarin, sai sakon da aka turo mishi aka goge na barazana, sannan a daren da abin zai faru kamar bibiyar shi aka yi. Ka duba ka gani"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login