Showing 21001 words to 24000 words out of 100763 words

Chapter 8 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2850

haske, Baffa'm a kwance jini na zuba ta gefen cikinshi.
"Kai ku shiga ku fito mana da yaran da suke cikin gidan, matan ku ware mana manya da kanana, mazan a musu yankan raggo a gaban Malam Buba da yace basu ne suka mana barna ba." Inji mutumin, "tow;" dakyar Baffa'm ya mike yana rike kafar mutumin. "Don Allah dan ladi kada ka cutar dasu, wallahi bamu bane. Akan me zamu cutar da zaman da muka yi na amana da ku?" Shure Baffa'm suka yi tare da take mishi wurin ciwon, suna murtsukawa. Haka suka fito da kowa na gidan, har da Baffa Modibo. Babangida da Habibu. Sa'idu da su Aminu. Dukar kofar da nayi yaja hankalinsu ba zan iya ganin wannan cin mutuncin ba, gara na mutu da Mahaifina. "Aiho boye wasu kuka yi?" Ya dokawa Baffa'm gindin bindigarshi akan ciwon, "ku balla kofar ku fito da su." Haka suka nufi kofar da gudu Baffa'm ya tashi yana me tare kofar. "Ku min kome na yarda, don Allah ku kyale mata da yaran basu yi kome ba." Rufe shi da duka suka yi, tare da janshi daga kofar dakin suka Salle kofar, tare da finciko mu. Suka yi waje damu. Ganin suna dukar Baffa'm babu me cetonshi na nufe shi, tare da fara ture su, haka aka fisgo ni suka bugani da kasa, tashi nayi da rarrafe kafin na isa sun mishi wani irin duka tare da cin zarafinshi suka tube mishi suturarshi. Rike gashin kaina mutumin yayi yana dariya. "Ke me baba ko? Maza jeki, Malam Buba idan kana son mu kyaleka dole sai ka amince kayi tarayya da Yaranka mata. Su kuma Yara mazan su kwanta da iyayensu Mata ko kuma mu,mu kwanta da su."
Suka fada suna dariya irin abin ya musu dad'i. "Ku kashe ni ba zan iya ba, ba zan iya kallon wannan kazantar ba." "Ashe? Tow kai daure min hannun mazan a musu yankan raggo su kuma matan ku ware min yan matan manya kuma su raba su." Har zuwa wannan lokacin yana rike da gashin kaina. "Dan Ladi kada kayi abin da zai dame ka, don Allah kada kaci zarafin Musulunci mana, addinin Kirista bai baka damar cin zarafin mata da yara ba." Amma mutanen nan suna dariya suka d'ago Babangida. "Kaje ka kwanta da uwarka kacita kamar yadda namiji yake cin Matarshi a gadon auren, kada ka biyewa Ubanku ba zai tab'a barin ku tsira ba, kana gamawa ga kofa ka fita ba zamu tab'a ka ba." Kusan yadda dan Adam yake da buri, kuma a ran Babangida gani yake idan ya aikata haka zasu barshi ya rayu, Baffa'm yasan yaudara ce kawai. Rike hannun Babangida yayi ya ce mishi. "Idan ka sake ka aikata haka, zasu kashe ka Allah ya saka hijabi a tsakaninku har abada ba zasu kasance a shimfidarka ba, Mahaifiyarka da yan uwanka, haramtattu ne a gare ka. Don haka kada ..." Dauke kan Babangida suka yi da harbi, sai gashi a jikin Baffa'm. Wani irin ajiyar zuciya Baffa'm ya sauke ya ce musu."Gara ku kashe mu da ku kasance kuna saka mu,aikata barna."
Wurgar da ni Mutumin yayi na na rarrafa wurin Baffa'm, na mika mishi kayanshi. Ina durkushe a gabanshi. "In sha Allah duk tsanani yana tare da sauki, kada wani abu ya ba?i tsoro gwagwarmayar...." Sake mishi harbi suka yi a gadon bayanshi. Ya fadi a jikina. "Kada tsoron mutuwa yasa ki ki tserewa da zaki rayu. Kiyi iya yinki Allah yana tare da mai gaskiya da takawa." Wani Harbin suka yi mishi sai da jin ya wanke min fuska. Har lokacin bai cika ba, babban burin shi yaga mun tsira ba tare da sun ci zarafin mu ba.

Janyo shi suka yi, akan idanuna kamar wata gaula ina kallonsu, suka shiga bude mishi wuta har sai da ya daina shure shure yana kalmar shahada, ban san ya aka yi ba amma ihu da karar harbe-harbe nake ji amma ban san me yake faruwa ba..haka suka yi ta bin Yaran nan suna harbinsu har da Baffa Modibo, akan idanun Nenne suka kashe mata Yaranta maza biyu, Yakumbo Sa'idu, Amaryar Baffa Modibo kuwa a wurin ta samu tab'in hankali domin kuwa ganin jinin yaranta yasa ta kama dariya. Bayan sun kashe mazan baki Waya, haka suka yi ta bin iyayenmu mata suna kwanciya dasu, ko nace Fyade. Hawwa'u da Hadiza kan, ko taron da mazan suka musu ne, amma ban san kome ba, sai da naji an rufe mu da duka ni da zalaihah. Ni dai naji kamar an suka min wani abu ban kuma sanin kome ba.
Bayan sun gama ta'aadacinsu, suka sakawa gidan wuta, kafin wani lokaci rugar mu ta zama makabarta domin babu inda babu gawarwaki. Sannan yadda suka tozarta mu haka suka bar mu a wulakance. Bayan tafiyarsu Addah da duk rashin imaninta yau sai da tayi kuka, Ita ta tashi da gudu tana shiga dakinta ta Ciro kaya tana daukar zanuwa da zanin gado, ita da Yakumbo. Dukkan iyayen nan kana ganin yadda suke abu kasan karfin zuciiya ne domin Nenne da suka mata wulakancin bata iya tashi ba, haka aka yi ta lullube gawarwakin da sauran mu, ita kan Amaryar Baffa Modibo, bayan sun gama mata fyaden, kasheta suka yi sannan suka barta a wurin. Zama Addah tayi a gaban gawar kannenta ta fashe da kuka. Sai lokacin kuka ya zo mata, har gari ya waye sai lokacin yan agajin gaggawa suka kawo mana taimakon gaggawa. Aka wuce damu asibiti sai dai kuma babu gado domin kuwa asibitin cike yake.

Wani abin da nake son ku sani, Taraba tana kudu da kasar Kamaru, sannan koda aka bamu taimakon babu wani abu, tura mu camp na yan gudun hijira aka yi, muna zuwa can,aka ce babu wuri dole aka hada mu da hukumar gudun hijira aka mana takardu aka wuce da mu Kamaru....
This is the beginning.....300? ..
#thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

*Wato jiya an yi kuka, hmm ayi hakuri na kara bada hakuri. Abin labarin a sannu =?
? wannan naku ne masu bibiyata. Allah ya saka da alkhairi =?
?d'?>????#?=?9? Na gode sosai*

*008*
Saboda azabar ciwo da muke fama da shi, bama fahimtar juna ko me yake faruwa, iyayen mu mata kawai zaka kalla ka fahimci suna cikin wani yanayi amma gudun kada su sare a gaban idanuwan Yaransu yasa suke fakar idanunmu suna kuka. A haka muka isa har Kamaru tafiyar kwana biyu,
Adamawan Kamaru aka kai mu, anan babban camp na yan gudun hijira ya?e. Sai da muka je asalin headquarter aka mana takardu, sannan aka wuce da mu asibitin da ya?e asalin garin, anan aka shiga bamu taimakon gaggawa.

****
*Niamey: Niger republic*

Ranar zaben.
Wato wannan ranar abu biyu za a gabatar na farko yadda suka shirya idan har suka fi su Aryan Mamman Ba'are yawan vote. To zasu amshe BA'ARE GOLDEN EMPIRES daga hannunsu Hajiya da Yaranta, na farko kenan, na biyu zasu sayarwa mutanen kasashen waje, sannan su zare hannun jarin Hajiya da Yaranta.
Sai dai wannan lokacin al'amarin daga ita har Yaranta sun sadakar musamman da suka ga Aryan Mamman Ba'are ya dawo babu Majeed, sai jikinta yayi sanyi a matsayinta na Uwa ya zata yi? Hawaye ne ya zubo mata tana kallon Aryan Mamman Ba'are.
Tasowa yayi ya mika mata hanky yana faWin. "Kukan me kike yi?" "Na hango faduwarmu ne, burinsu idan muka fadi hatta gidan BA'ARE housing estate zamu bari, duk wani abu da ya shafi BA'ARE zamu bari." Dariya yayi yana faWin."haka muke so sannan a wannan karon za a sake gwanjon kome har da estate kenan?" Ya fada yana mikewa daga inda ya zauna ya koma wurin shi, masu hannun jari da matsayi a board din kamfanonin BA'ARE mineral oil and gas, amma babban al'amarin da wannan rikicin yana kan GOLDEN EMPIRES ne.
Hajiya Nana ita ce a sawun gaba, sai Hajiya Tani da d'anta Sajjid Mamman Ba'are, sai Hajiya Rabi Mamman Ba'are, sai Hajiya Fauziya Mamman Ba'are, can sai ga Hajiya Harirah Mamman Ba'are, dukkansu da yaransu mata da maza.

Dukkansu nan babu wacce za a nuna mata takarda ta karanta, kawai kishin jahilci ake yi, Hajiya Sa'adatu Mamman Ba'are, ita ce Hajiya mahaifiyarsu Captain. Kuma ita ce Amaryar Alhaji Mamman Ba'are,sannan ita ce take da Yara maza uku cif. Su Majeed suna da yayu mata manya, amma kusan da yake akwai kishi da hauka yasa kowa yake rayuwarsa a inda ya?e.
Idan ka cire Hajiya Harirah da take da abin bata yarda ta kashe kanta da kishi ba, domin sai da ta nime ilimi, saboda ta fahimci wani abu da sauran suka gaza fahimta.
Can Alhaji Haladu Abdul Majid Ba'are sai
Alhaji Kamilu Abdul Majid ba'are, kafin Hajiya Hadiza Abdul Majid ba'are.
A bangaren Hajiya Sa'adatu Mamman Ba'are, Akwai Amaan Mamman Ba'are, sai Aryan Mamman Ba'are, sai Jamilah Mamman Ba'are, sai Aneesah ita ce auta.

A hankali wurin yayi ta cika, kuma a wannan zaman babu bare amma kuma wani abin mamaki shine zuwan wasu daga cikin turawa da yan siyasar da Sajjid Mamman Ba'are ya gayyato, ya tashi ya taro su. Har wurin Nana suka gaishe ta. Kafin suka gaida kowa sannan suka koma wurin zamansu, Abdul Majid dan Hadiza Abdul Majid ba'are, ya mike tare da nufar wurin Hajiya suka gaisa. "Hajiya Abdul Jeed ba zai zo bane?" Idanunta da suka cika da kwalla ta ce mishi. "Ban sani ba, na dai tura Aryan bai ce min kome ba."
"Lallai Jeed dole ya bayyana anan. Domin an shirya makirci na bala'in fitar hankali."
Duk wahala da ta sha, da iya azabar da ta sha, wai karshe abin da ta samu shine ya tsonewa kowa ido. Suna da nasu amma ita nata da na Yaranta ya tsone musu ido. Hajiya Hadiza Ba'are watsawa danta Abdul Majid harara tayi, ita kan bata san wani irin d'a ta haifa ba, ko a gidan Ubansu haka yake makalewa ya'yan kishiyoyinta yana basu kulawa kamar wani son shi suke.
Komawa wurin zamanshi yayi yaki yarda ya kalli Hajiyarsu, da Nanah kakarsu kenan. Kanshi yana can bakin kofar aka fara taron tare da zab'en ra'ayi akan matsayin BA'ARE GOLDEN EMPIRES. Abin dai ba a cewa kome.

Haka aka fara voting, jikin Yaran Hajiya yayi sanyi ban da Amaan Mamman Ba'are, dan shi dama yasan haka zata faru, kuma shi yana tare da su, babu me kaso mafi girma da yawa a kamfanonin kamar Majid, don haka gara ayi uwar watsi kowa ya rasa, Aryan Mamman Ba'are kuwa ko a jikinshi domin bai tashi ya kada kuri'ar shi ba, kallon shi Alkalin yayi ya ce mishi. "Malam Aryan Mamman Ba'are, shin baka ga kowa ya kada kuri'a ba ne?" D'ago kai yayi yana yak'e ya ce mishi. "Alkali kayi shiru yanzu zan kundume wasar domin uban gayya ya bayyana." Ya cigaba da danna wayarshi alamar game yake yi, "Malam Aryan kuri'arka ake jira fa." "Ba iya nawa ba, har da na wancan da yake tsaye a bakin kofar." Ya nuna musu Majid Mamman Ba'are sanye da kayan turang. Shadda ce skyblue, yasha babban riga da takalmi halfcover, kanshi sanye da rawani ya rufe fuskarshi da ita, yadda yake tafiya kasan cikakken jarumi ne. Mikewa Aryan Mamman Ba'are yayi ya tafi can bayan kujerar da aka ware babba kuma an lullube shi da mayafi, Hajiya ya dace ta zauna a wurin amma saboda fitina ta hakura, sai gashi Aryan ya janye lulluben da aka mata, sannan ya jata baya, Majid Mamman Ba'are ya isa wurin y zauna, dukkansu sai da suka mike tsaye. Yadda ya zauna sai da ya jingina da kujerar sannan ya aza kafa d'aya kan Waya, ya janye mayafin da yake fuskarshi. Yana bin ilahirin mutanen wurin da rikitaccen Idanuwan shi me dauke da wutar takaici da b'acin rai. "Amma taya dan iskan Yaron nan ya dawo?" Cikin kwafa Hajiya Tani tayi magana tana kallon Majid da ya daura daya kan Waya, yana sakin wani murmushi yana kallon Aryan da ya koma wurinshi da zama. "Alkali Bismillah!" Inji Aryan ya faWa yana murmushi. "Tow Malam Aryan kuri'arka da ta Abdul Majid Mamman Ba'are ya rage, akan sikeli" hannu ya kai aljuhun rigar shi ya Ciro wasu zinarai manya guda uku, sai na shi daya yana zuwa ya saka nashi, yana kallon kowa a wurin sannan ya saka daya na Majid Mamman Ba'are, tuni hannun ya rinjayi daya hannun cikin tsokana da niman magana ya ce. "Alkali idan na saka sauran biyu ina cewa Ba zaku ce nayi son kai ba?"
"Baka da matsala Malam Aryan" cikin wani irin juyi ya ajiye dayan, sai ga shi bakidaya ya rinjaye gefen. Kafin d'aga dayan sama ya ce musu. "Kun ganshi nan kuri'ar Majid Mamman Ba'are na karshe kenan!" Ya ajiye . Shiru wurin ya Wauka. Babu wanda ya kawo Majid zai bayyana, balle a kawo zancen kuri'arshi, sannan babu wanda ya kawo wannan al'amarin haka shi daya kuri'arshi daya ta mutane goma ce ukun baki daya ta mutane talatin ne, domin kuwa asalin zinarin na Alhaji Mamman Ba'are ne, da kanshi ya ajiye wasiyya har kotu aka kai banki aka ajiye, asalima ba a kasar ya ajiye ba. Sai aka zo rabon gado aka gani. Ya narka ta zuwa na Majid Mamman Ba'are kuma ya saka sunanshi a jikin zinarin.
"Kuri'ar Hajiya Sa'adatu da Yaranta sune masu rinjaye, sannan suna da damar fadin yadda suke so ayi da BA'ARE GOLDEN EMPIRES."
A hankali Aryan ya mike ya ce. "Alkali dama ai idan aka yi rinjaye a kan mu gwanjon kamfanin za ayi ko?" Kallon Alhaji Haladu Ba'are da Sajjid Mamman Ba'are alkali yayi, suma kura mishi idanu suka yi.
"Alkali ni nake magana ba Sajjid tani ba, ba Haladu Ba'are ba, Aryan Mamman Ba'are yake magana."
"Eh Malam Aryan."
"Kawai a saka a kasuwa!" Ya fada yana me komawa wurin zamanshi ya daura daya bisa Waya.
Ajiyar zuciya Alkali yayi ya fara karanto ka'idodin sayar da kayan.
"Doka ta farko waWanda suka fadi basu da hurumi akan kamfanin dole suyi hakuri da duk abin da zasu ji ko zasu gani. Doka ta biyu idan aka sayar ga duk wanda ya saya hurumin shine cire sunayen wasu da baya ra'ayi a board meeting, doka ta uku iya waWanda suka saya suke da ikon tafiyar da kamfanonin baki Waya."

Wannan shine shirinsu idan Majid Mamman Ba'are bai zo ba,tow abin da za ayi kenan. Mikewa Aryan Mamman Ba'are yayi ya mikawa alkali kudin da aka sakawa kamfanonin. Hajiya tasan ba wayonta bane, ba Kuma iyawarta ba ne kawai wata falala ce daga rabbul alamin, ya bata yara maza biyu masu matu?ar zuciya da son cigaban juna. D'aga takardar kudin alkali yayi, nokewa kowa yayi babu wanda yayi kuskuren tashi domin kuwa basu da kwatar kudin da aka nima balle rabi. Haka yasa Majid Mamman Ba'are mika hannu. "Na saya!" Shine dama me hannun jarin da ya wuce misali. Yana fadar haka ya mike, tare da barin taron. "Alkali kaji ya saya, ko akwai wanda zai ja ne?"
"Babu Malam Aryan!" A hankali ya taka gaban kujerar Hajiya Tani ya zuba mata ido. "kun shirya wasa, ba tare da kun san waye dan wasan ba, ya dawo har na tsawon lokacin da ya dibawa kanshi."
Daga nan ya nufi wurin Hajiya ya daukar mata jaka, suka nufi hanya Jamilah da Aneesah suna biye da su. Lokacin da Amaan ya isa wurin Nanah kasa magana yayi. "Munafiki ba kace mana Aryan bai same shi ba? Ko dama munafurci ne yasa kazo don kasan sirrinmu!"
"Nana!" Alhaji Haladu ya kira sunanta, "shima bai san kome ba, babu babban shaidanin kamar Aryan yaron nan "
"Wai ku yaushe zaku daina faWa akan abin da ba naku ba? Dukiyar nan da bakin Ya Mamman ya mallakawa Sa'adatu da Yaranta, musamman Majid don Allah ku kyale su mana."
"Ai kai ban san wani irin haihuwa nayi ba, baki daya baka da kishi da kishin yan uwanka, ban da jaraba irin ta Mamman ai shi kenan."
Hajiya Tani bata ce kome ba, domin dama ba zata tab'a cewa ba, amma zuwan Abdul Majid Mamman Ba'are ya kashe mata kasuwa, domin duk burinta ya lalace. Juyawa tayi ta futa bata musu magana ba, ta nufi hanyar waje ita da d'anta. "Hajiya!" Hannu ta d'aga mishi. A waje suka same su, musamman Aryan."Hajjaju! Ki kara shiri da kyau."
"Kana wasa da rayuwarka." Inji Sajjid Mamman Ba'are. Ai kamar jira ake Sajjid ya fadi haka sai ga Press sun shiga daukar hotonshi a bakin kofar kamfanin. "Taron da aka shirya domin ruguza kamfanonin BA'ARE, ya tashi cikin wani irin juyin juya halin, domin kuwa ana cigaba da taron Majid Mamman Ba'are ya bayyana sannan ya saye kamfanin da kaso daya na cikin dukiyar shi, abin da ba a saba gani ba domin duk taron da ake Majid bai tab'a halartar taron ba, amma wannan karon ya tawo cikin ban mamaki " can wani dan jaridar ya amsa da cewa. "A wani abin da ba a san mafarin shi ba, Sajjid Dan wurin Hajiya Tani da ta likawa Marigayi Mamman Ba'are, yayiwa Aryan Mamman Ba'are barazana da rayuwarshi."

Jikin Hajiya Tani ne ya dauki rawa, ta juya tana kallon Sajjid da ake ta daukar shi, da sauri ta fada cikin Motarsu, suna shiga ta juya a fusace . "Ina ruwanka da shi? Idan ma wani abu ya maka sai ka yi shiru meye na tanka mishi? Ga ka nan kato amma tunaninka na Yara ne, bakasan ka girme shi ba ne? Amma ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login