Showing 30001 words to 33000 words out of 100763 words

Chapter 11 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2869

mun yi sallar asuba, sai ga wasu mutane uku, biyu maza daya mace. "Zamu mai daku sansanin gudun hijira ne, domin mun samu labarin yadda wasunku suke fita yawon dare." Dukkanmu Addah muka zubawa idanu. Matar nan tayi mirsisi da idanunta, ta nuna ni. "Ga yar iskar da take bin maza, nayi fadar nayi maganar na gaji." Wato wani irin razana muka shiga, domin babu wanda ya kawo Addah zata iya min sharri, ni kuwa banyi mamaki ba, domin fiye da haka idan akace zata min wallahi zan yarda, matukar Hajiya Addah ce kaWan da aikinta, amma kuma abin da tab'a rai.
"Tow koma waye, zamu tafi da ku." "Addah ki fara gina wutarki kafin ki tafi lahira." Inji Zuzu, sake bude baki tayi zata kara magana. Na rufe mata baki saboda ko Munaisah da muke tare itama bata ce kome ba, hakan yasa na gane ni ce bare a cikinsu, dukkansu abu daya ne. Haka na shiga haWa kayanmu. "Muna jiranku."
"Ranki shi dade, akwai yar Uwata da bata da lafiya an kaita ICU ko zan zauna a jikinta?"
"Ba zaki zauna a jikin kowa ba, domin kuwa kika zauna a nan ba jinyar zaki yi ba, yawonki zaki shiga yi." Inji Zuzu. Haka suka fita, ko ya aka yi sai ga Nurse Ali da Rabeka. "Yar fillo, ga wannan katin yanzu na amsa miki keda yar Uwarki. Koda zaku fito daga camp zuwa nan tow ku tabbatar kun rike wannan katin, sannan Fulani zata tsaya tunda Mamarta ce, ke idan an jima yayi sai kizo ki canjeta. inji Doctor Moses."

Ba alfahari ba, haduwa da mutanen kwarai a jinina yake, duk inda na shiga sai na hadu da mutanen arziki, haka muka fito baki Waya, a lokacin da zamu bar Asibitin Dr Moses yaga Yakumbo ya dubata da kyau, sannan ya bamu magani akan muna bata idan ya kare muzo da ita taga likita. Gyada mishi kai nayi, muka tafi inda Nenne take, dake zamu bar Munaisah a wur??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in. Rike hannunta nayi. "Don Allah ki kula kin ji." Gyada min kai tayi, ban san wani irin zuciya nake da shi ba, ni fa bana iya rike ka idan kayi min, ina ji a raina babu amfanin rike mutum araina domin haka ba zai amfane ni da kome ba, sai ciwon rai.
Ni kuma bana son hassada da kyashi ya shiga, zuciyata saboda kai.
Haka muka isa camp din, cikin wani irin yanayi, muna isa Office din shugaban da yake kula da camp din aka kai mu, aka saka sunanmu, da inda muka fito da dalilin fitowarmu. Ana gamawa muka fito daga office din, Mutanen da suka kawo mu, suka raka mu har wani tanti, shiga muka yi baki dayanmu. Ba laifi cikin a rufe yake kasar kuma an lailaye shi da leda, alamar waWanda suka zauna a cikin tantin suna da tsafta. Zubewa muka yi, daya matar ta ce min. "Fillo zamu je ki fara dauko muku kayan shimfidarku." Gyada kai nayi, muka fita da ita,haka nayi ta jido kayanmu. Har da kayan Abincin. Cikin sakin fuska matar ta ce min. "Akwai kayan abinci ku nawa ne?" "Mu bakwai ne." Na fada a sanyayye. "To shi kenan kai kayan ki dawo."
"Amma me yasa za a bamu danyen abinci?" Murmushi tayi tace min. "Danyen abinci shine zamu iya baku, idan muka ce dafaffe ne, a wurin bayarwa aka fara dambe sai an zubda abinciin baki daya."
"Subhanalillahi!" Na fada ina Waukar katifa da ta daura min, har tantin mu ga nisa. Ina kaiwa na kuma juyowa zan koma muka hadu da wata yarinya. Itama budurwa ce. "Barka mai kyau!"
Murmushi nayi mata sannan na ce mata. "Ai kema mai kyau ce." Juya idanu tayi, "Hmm!" Ai ban tsaya bin nata ba, na wuce abina domin ina da abin yi. Tass na kwaso kayan har da kayan abinci, ina tsaye ina haki Zuzu ta ce min. "Yanzu ya zamu yi idan aka fara ruwan sama?" Juyawa nayi na kalleta. "Kamar ya?" "Wurin girki. "Ok na fahimta. Kamar an wurgo ta,ta shigo cikin ba sallama. "Batun girki kuke? Akwai inda ake sayar da itaccen da gawayi, har gas akwai me sayarwa." Ta fada tana rangwad'i da yauki. Da fulatanci Zuzu ta ce min "Zahra a ina kuka kwaso mana Zee yauki?"
"Ande!" Ita kuwa sai yauki take, wato ko Allah ya shirya zuzu. "Dukkanku masu kyau ne, wow." "Yanzu ya zamu yi kenan mu sayi gawayi kawai domin zai fi gas din nan, ko?" Na tambayi Zuzu. "Tow ya zamu yi da kudin nan na naija ne da" "ai duk suna amsa, kasancewar garin nan yana kusa da boda, zaku iya sayayyarku da shima."
"Mun gode amma meye sunanki?" ."Aina'u suna na!" Gyada kai mukayi, muna kallonta kafin Zuzu ta ce . "Kina da kyau!" Ai kuwa kamar an kunna radiyo, ta fara zuba. "Zahra'u dauke kawarki ta rakaki, ku nimo mana abinda zamu ci bamu isa da surutun ta ba." Inji Addah ta faWa da fulatanci, haka na jata muka tafi har inda zamu sayi kome,, dake a cikin kayan da aka bamu har da kayan miyar gwangwani kifin gwangwani, da sauran tarkacen irinsu garin kunu, shinkafar ci da ta tuwo garin madara, burabisko, mangyad'a da man ja, magi ma ban tab'a ganin irinshi ba, sai a wurinsu, haka muka siya har da tukunyar hannu da kwanuka. Anan wurin take cewa. "idan ba zaku yi amfani da kayanku ba, ku bamu zamu baku kuWi." Murmushi nayi mata nace mata. "Bamu koshin da zamu sayar da abinci ba, ki jira idan mun koshi zamu kawo mu sayar."
........
08130269641
*Mai_Dambu*
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*011*
Bige hannuna Aina'u tayi cikin rangwad'a ta ce min. "Ba a fadar haka, Uwar mugu bata lamuntar cika baki" sannan ta kalli matar cikin fara'a ta ce mata. "Uwar mugu muna neman yafiyarki domin bakuwa ce daga Nijeriya bata san kome akan gurin nan ba." Murmushi matar tayi tana kallona cikin wani irin kallo kafin ta juya ga Aina'u tana murmushi ta ce mata. "Ya sunanta?" Cikin kad'adi irin na wanda ya saba ta ce mata. "Zahra!" Rike baki Uwar mugu tayi tana cewa. "Mai Babbar suna kenan, kun ga uwata takaina, maza ku je babu komai ai Uwata ce bata laifi."
Aina'u kamar ta zube kasa, tayi ta godiya har da cewa. "In sha Allah zaki same ta mai biyayya." Idanunta kyam a kaina, ni kuwa ko dar ban ji ba, domin matar asalima kawai bata kwanta min a rai ba, haka muka bar wurin ko inda take ban kuma kalla ba, babbar mace ce amma yanayinta zaka kalla kasan bata da mutunci. "Amma matar nan bata da mutunci ko?" Da sauri Aina'u ta rufe min baki, ta juya tana kara gaida matar, wacce da na juya na kalleta ni take kallo."Uwar mugu bata da matsala, kuma bata da abokin tarayya a cikin sansanin gudun hijirar nan, mace ce da tasan kan duniya idan taso zata iya janyowa a Kore ki, ko kuma a kwace muku kayan abinci. Tana da Yaro Waya baya cikin sansanin nan, yana tafiya farauta ne, sai dare ya ke shigowa. Matar tana da matu?ar hatsari idan ka nuna mata kai ma dan duniya ne, idan kuma ka bita a hankali zata iya sakawa kowa ya kaunace ka, idan ka nuna mata baka da mutunci zata iya sakawa a tsane ka. Uwar mugu mace ce da take hada mutum da mutane masu arziki na wajen nan. Nima ba karamin arziki na samu a ta sanadinta ba."

Ware idanu nayi na kalli Aina'u, "yanzu Aina'u harkokin bin maza ta dauraki a kai?" Murmushi tayi irin bai dame ta ba, ta ce min. "Kai ji wata magana sai kace wani saSo nayi, ai wannan rayuwar idan baka iya d'aga kafa ba, ba zaka huta ba, abincin da aka baku kin zata zai kai wata ne? Bari ki ji, daga zarar kun kai sati biyu nan ne idanku zai raina fata." Baki daya naji hankalina ya tashi, bamu rabu da bukar ba an haifi Habu, wato mun yi gudun gara mun tadda zago. Ban kuma magana ba, haka dai na barta tayi ta surutu domin ban san me take fada ba, haka muka isa, na ajiye kayan na shiga daki na samu wata mata suna ta hira. "Laaa Mamata itama tazo kenan." Ta shigo, "Tumba!" Ta kira sunanta. "Na'am Aina'u." Zama tayi a jikinta tana murmushi. "Kin samu kawa daga zuwa kenan?" Mamar ta tambayeta. Juya idanu tayi tana faWin. "Eh Tumba." "Dama Yarki ce?" Gyara zama tayi tana murmushi ta ce mata. "Y'ata ce, na tafi Saudiya na barta ina dawowa rikicin boko haram ya koro mu nan Kamaru." Shiru tayi kanta na kasa kafin ta ce. "Sai da muka yi kwana talatin a hannun Yan boko haram, suna gana mana azaba, ga cin zarafi da fyade." Ta rungume Aina'u, itama yarinyar k'amk'ame Mamarta tayi, alamar har yau idan suka tuno abin yana musu zafi da ciwo. "Sun ci zarafinmu." Mikewa nayi na fita waje, kallon sama nayi domin bana son hawayen da ya taru a idanuwa na su zubo. "ku shiga da kayan ciki domin za a sace." D'ago kai nayi muka yi ido biyu da shi. Security ne domin naga sanye ya?e da Uniform. "Tow!" Nace mishi. Na shiga da kayan cikin tantin mu, "Aina'u a ina zan samo ruwa?" Mikewa zumbur tayi tana faWin. "Muje!" Ta dauki daya daga cikin langar da ta sani na saya. Muka fito ban ga mutumin ba, haka muka ratsa ta dakinsu, da mutane a ciki. Guga ta dauka, dakin ban da warin sigari baka jin kome. Kafin ta dauki gugar daya daga cikin mazan dakin ya fisgota. Tana dariya ta ce mishi. "Meye haka, Faruq?" Da sauri nayi baya, na tsaya a waje, ina jin mazan dakin suna ta dariya, har da ita ganin xata bata min lokaci na juya na bar wurin, haka kawai naji jikina yana bani kamar ana bina, juyawa nayi naga mutumin dazun ne. Mutanen da na gani a dakin suma irin kayan jikinsu Waya, tsayawa nayi naga ko zai wuce, abin mamaki sai naga ya tsaya. A hankali wani sabon tsoro ya kamani na juya . "Me kake so?" ."raka ki kawai zan yi, don naga kina da nutsuwa. " Ya tawo ya amshi bokitin hannuna, yayi gaba ina bayanshi, har bakin inda zamu d'ibi ruwan.

Kallona yayi ya ce min."Idan muka karasa wurin zaki iya ganin maza suna wanka, zaki iya ganin su babu kaya?" Sunkuyar da kai nayi na juya bayana, ilahirin jikina rawa yake, "bana fatan kara ganin wani babu kaya" na juya kamar zan fashe da kuka. Abin da ya faru yana dawo min, a hankali naji kirjina yana min ciwo, ban san tafiyarshi ba, sai ga shi nan dauke da bokitin da jarkar ruwan, haka muka tawo, ina share hawayen da yake zuba min. "Idan zaki dauki shawarata, ki hakura da tarayya da yarinyar nan, sannan idan dare yayi ki kula da kanki da yan uwanki."
"Wani abu yana faruwa ne?" Murmushi yayi irin wanda yafi kuka ciwo, ya ce min."ki kula da kanki." Sai lokacin na hango Aina'u tana rungume da wani mutumin. Tana hango ni ta ture shi, ta iso wurina. "Balali meye haWinka da Kawata?" Bai tanka mata ba, ya saka ni gaba muka wuce ta, shiru tayi har taga wucewar mu, sannan ta biyo mu, a bakin kofar tantin mu, muka hadu da Zuzu ta fito da wutar tana gani na, ta ce. "Zahra'u hala kin mai damu kazar turawa zaki saka mana wuta a daki?" Murmushi nayi nace mata. "matar Babban sakataren gwamnati yi hakuri bari na mai da shi waje, kada ki narke domin da kitse aka yi ki " na ajiye ruwan ina kallonshi. "Na gode Yayana " na fadi haka ina jin kwalla yana cika min idanu. "Ni ne da godiya, amma bana son yaya nan". Zuba ruwa a tunkuyar zuzu tayi, tana faWin. "Love at first sight!" "Yes haka ne, yar uwa." Ita kan aikinta ta cigaba da yi, dakyar na sallame shi ya tafi. Yana tafiya Aina'u tana zuwa. "Zahrah kin ga mutumin nan dan iska ne, kada ki bashi fuska." Kallonta nayi na wasu dakikai, kafin na ce mata. "Na gode." Tow me zance mata? Ni dai nasan idan karuwanci bai zama abincina ba, ba zai tab'a zame min guba ba, tunda mutanen da suke zagaye da ni kusan ?addararsu ta haWa da wannan sana'ar.
Ganin naki kulata, ta ja ta zauna domin na fahimci abincin take bukata, don haka Zuzu tayi uwa tayi makarbiya, ta tsaya kan abincin, ganin nima bani da katabus akan abincin ta koma tantinsu, domin yadda Zuzu ta haWe rai ko ni a dakile take amsa min magana, don haka tana gama abincin, ta zuba kwanon asibiti sannan ta zuba mana a wani kwano, muka hadu har da Addah muka ci. Alhamdulillahi ba laifi mun tashi komad'a, sallah muka yi, sannan na shirya tare da kwanon abincin ni da Zuzu muka nufi Asibitin, ba a hana mu fita ba, amma sai da muka bi kofar uwar mugu, haka Balali ya gaya min ya ce na gaya mata zamu tafi asibiti. Lokacin da muka isa tantinta wanda yafi na kowa kyau, domin kamar gida yake, buga mata kofa muka yi, ta ce. "Waye?" "Zahra'u ce." "Shigo abinki!" Bude kofar nayi na tura kaina da sallama, dakin sai warin wiwi yake, durkusawa nayi na ce mata. "zamu tafi duba Mamana a asibiti ni sai gobe zan dawo, yayata zata dawo da yar Uwata."
"Ai naji labarin Yadikonki ce, mahaifiyarki yar kasar nan ce, baki son a nima miki ita ne?" Idanuna ne suka cika da kwalla muryata a sanyayye na ce mata. "ba a bukata, waWanda suke wani hali nake son su samu lafiya tukun nan."
"Sai kin dawo, ga abinci ko zaki ci." Da sauri na ce mata. "A'a na gode!" Na mike na fito, Zuzu da Balali suna waje, ina fitowa ya kalle ni. " Me yasa kace mu gaya mata?" "Domin ina son ki samu kusanci da ita, yadda babu me iya tunkararki da mugun nufi, idan har kika iya kiyaye abin da bata so, cinnaka bai isa ya cijeki bata saka an ga bayanshi ba."
"Amma ya naji Wakinta yana warin wiwi?" Murmushi yayi yana faWin, "muje zaki fahimci wani abu nan gaba." Da muka fito mun haWu da wasu zafafan motoci guda biyar, mutanen da suke jikin motar dauke suke da manyan bindigu. "Tambayarki ga amsarta." Shiru nayi ban san dame zan lissafa abinda nake son ganewa ba, haka muka isa bakin hanya ya saka mu a mota, ya dawo. "Zahrah bayan tafiyarki diban ruwa, matar nan dai Addah ta bata labarin mu, sannan ta amince zata shiga sana'arta."
"Yanzu don Allah ita Addah meye abin burgewa a wannan sana'ar? Gaskiya gara na mutu da nayi wannan sana'ar." Murmushin takaici tayi ta ce mata. "gara ke, kina da taurin kai, ni Addah tana cewa zata tsine min nake amincewa. Ki godewa Allah babu wani mai mugun nufi a rayuwarki." Ta fada tana kuka, rike hannunta nayi ina faWin. "Ya isa haka!" Itama rike hannuna tayi tana wani irin kuka, wanda na fahimci ba kukan abin da yake faruwa damu ba ne, akwai wani abu a ranta. "Zahra'u Alfarma nake nima daya tal?" Rike hannunta nayi, hannuna ta ja cikin rigarta, ta daura a saman cikinta. A razane na cire hannun ina toshe baki. "Idan ya rayu, zan so ki rike a matsayin naki don Allah bana son ya bata min gobe na. Idan na mutu ki rike shi har abada." Wani irin rawa jikina ya dauka, ban taSa kawowa a raina haka zai faru da Zuzu ba, "Me yasa kika bukaci haka?" "Babu wanda ya sani sai ke, don Allah." A daidai isar mu asibitin, sauka nayi na bashi canjin da Balali ya bamu. Koda muka isa asibitin Munaisah tayi kuka har ta godewa Allah. Tana ganinmu ta faWa jikina, tana kuka tana faWin. "tun tafiyarku sai tashi abin yake ana ta niman wanda zai nimo ki, tana son ganinki." Bubbuga bayanta nayi, na ce mata. "Ya isa!" Dakyar ta daina kuka na ajiye mata abinci, ta fara ci zata cire hannu na cigaba da bata, tana ci tana kallona. "Kiyi hakuri.!" Ta ce min, ni na saba da wannan kalmar bata wani hana ni sakat, haka ta ci abincin sosai, sannan na tafi inda zan sauya kayana, na nufi dakin da Yadikko take, an zuba mata na'ura kanta da kirjinta. Ina zuwa na rike hannunta. Kafin na shafa kanta bude idanu tayi tana kallona. Hawaye ne yake zuba mata, ta rike hannuna da babu kome. Ina murmushin karfin hali nace mata. "In sha Allah zaki tashi kin ji Nenne na, zaki tashi da kafarki da karfinki."
Kallona kawai take har na wani lokaci, kafin Munaisah da Zuzu suka shigo. Kallonmu tayi tana kallonmu bakidaya, "bari na rakasu," na janye rikon da tayi min, na tafi na rakasu. "Balali yana jiranku zai kai ku har har tantin in sha Allah."
"Tow shi kenan!" Haka suka hau mota na dawo dakin Nenne, ina rike da hannunta, tunda ta bude idanu ta ganni, ta lumshe idanunta, wato ko? Wannan yanayin Allah kadai yake da ikon jarabtarka a zauna lafiya. Nenne tana cikin wani irin yanayi, domin kuwa tasan kai ne akanta amma babu bakin magana. Can kuma zuzu ta fado min a rai. *Yaushe tayi cikin?* Wannan shi ne tambayar da nayiwa kaina, kuma nasan bani da me bani amsar sai ita, haka yasa nayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login