Showing 54001 words to 57000 words out of 100763 words

Chapter 19 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2856

wiwi. "Addah lafiya!"shigowa da Munaisah aka ayi dakin kamar bata da lafiya ko taci duka. "Allah yayiwa Nenne rasuwa?" Tashi zaune mukayi. Murmushi Ummi tayi ta ce mata. "Hankalinku ya kwanta "
"Me kike nufi? Babu kowa a wurinta sai Munaisah naje domin na tayata zama ne!"
"Ya isa Addah" inji Zuzu, wallahi duk sun saka ni cikin duhu. "ina gawar?" "Tana can ana mata sutura" nida Zuzu muka fita, Ummi ta kalli Munaisah ta ce mata. "Daga nan karatun daya ce har birnin lantsandaal, kin biyewa Addah kun kashe Mahaifiyarki, ki rubuta ki ajiye. Addah sai ta ci amanarki wallahi kuwa sai ta saka ki kuka lokacin babu Zahra da zuzu, matukar zata sayar da Yarta ke din banza ce ba zata iya miki butulci ba. Na tausaya miki matuka gayya."
Tun bayan an yi jana'izar aka kaita makwancinta, da zamu koma Balali ya kirani ya ce min."don Allah ina son magana dake."
"Ok me ya faru?"
"Ki saka idanu akan matar da take dakinku da ita wancan me cikin." Hadiye yawu nayi, na ce mishi. "Lafiya kace haka?"
"Kiyi hakuri anan sansanin tunda wancan gayen yazo tow wallahi numfashin ki ma da zai saya tow tabbas zai saya ya samu kuWi."
"Me zan iya yi?" D'ago kai yayi ya ce min. "Jeki zan baki sako!"
Haka na juya na tafi sai lokacin na lura ashe Uwar mugu ya gani. A hankali muka hadu da ita ta ce min. " Me yake gaya miki?" Murmushi nayi nace mata. "Ta'aziya yake min."
"Bayan nan bai ce wani abu?" Girgiza kai nayi nace mata. "Haba bai ce kome ba!" "Zahra'u kenan! Mu shiga ki karya." Girgiza mata kai nayi ina faWin. "A'a na koshi."
"Muje mana, ko an gaya miki wani abu ne?" Ganin tana son daura zarginta akan Balali yasa ni binta har dakinta, muka zauna ta shiga zuba min abinci da kayan ciye-ciye. Duk abinda ta zuba min sai da na raba biyu tana kallona, tana gamawa na ce mata. "Muci tare."
"Kin xata zan saka miki guba ce?" Girgiza kai nayi nace mata."ko daya kawai muci tare wannan zan kaiwa Zuzuna."
"Tow muci" haka muka ci tare da ita, sannan na mike ta kara min abincin. "Kina da wani irin kyau, kiyi amfani da kyan nan mana." Girgiza kai nayi nace mata. "ai kyauwa na muni ne ga wancan abin"
"Kina son zuzu ko????????? "
>??=?D?Me ya kawo irin wannan tambayar... Jama'a me uwar Mugu take nufi.
#Thedambuje
[2/19, 12:21 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTU?ARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....

*018*
"Na'am me kike ce?" Na kalleta cikin son fahimtar me take nufi, murmushi tayi tana kallona. "Kawai naga yadda kike damuwa da ita ce ko mahaifiyarta bata damu da ita haka ba, kin ga wannan wuri da kike kowa ta kanshi yake, ki ajiye wata Zuzu ki kama Harkar gabanki yafi miki."
"Ban damu da ko waye bai damu da zuzu ba, amma ni a raina na damu da zuzu. Sannan ba zan dauki wani ya dora ni akan hanyar da ba zata bulle min ba,, idan Addah ta gadama ta kula da rayuwar Yarta idan bata gadama ba, ta barta tai yadda take so. Ke da ita baku isa tilasta ni yin abin da ban shirya ba, idan kuma kina ganin zaki iya Bismillah. Har karshen rayuwata ba zan daina tsayawa a bayan zuzu ba kin ji na gaya miki sai ki san nayi." Daga haka na juya tare da barin mata dakin ko abincin ban dauka ba.
"Abincin da kika bar min fa?" Ban juyo ba, na ce mata. "Kece idan baki ci ba zaki mutu, ni kuwa ko banci ba zan rayu matukar Allah shine rayayyen nan da baya mutuwa."
Sannan na sa kai zan fita, ta kuma ce min. "Kada ki d'aga kafarki domin zan iya aikata kome." Juyawa nayi na kalle ta dariya nayi nace mata. "Ni ban san tsoro ba, ki gaya min taya zan san tsoro bayan akan idona aka kashe min dangina? Gaya min tsawarki bai wuce haushin dan kwaikwayo ba. Ni gurnanin fitar rai naji kin ga kenan babu abin da zai bani tsoro bayan nasan ina raye ne ko na mutu don Allah, ko a kashe ni don niman duniya." Daga haka na bar mata gidan, Yana kwance yana jin duk abinda suke fada, a ina aka samu yarinya me zuciya haka, Aina'u ya kalla da take ta sharar bacci, ya mike zaune yana mika, kirjinshi cike da gargasa ya dauki dogon wandonshi ya saka. Ya fito inda Uwar mugu take zaune tana mamakin maganganun Zahrah. " A ina kika samo jar wuya haka?" "Yan gudun hijira ne da suka taso daga Nijeriya, za akai su sansanin gudun hijirar hadin gwiwa da na Nijeriya yaranmu suka karkato mana da su nan, Yaran jiya da ka gani duk daga can suke."
Shafa kanshi yayi yana faWin. "Yarinyar ta iya jefa citta a bakin mutane, ban tab'a jin yarinyar da ta gaya miki gaskiya haka ba." Sosa kanta tayi tana murmushi ta ce mishi. "Eh ai bata da kunya ko kaWan. Haka yar Ubanta take fama da ita, taurin kai ne da ita kamar arnan dutse."
"Nawa aka samu domin ina son wucewa da shi kafin lokaci ya kure min." Sunkuyar da kai tayi tana faWin. "Ba a wani samu dayawa ba, amma zaka iya zuwa wurin ajiyar zaka ga iya wanda muka samu." Gyada kai yayi yana faWin. "Duk bayan wata shida nake zuwa amma ace iya wanda na samu kenan? Babu waWanda suke jinya ne?" Kasa tayi da murya tana faWin. "Allah ya baka hakuri, akwai Aina'u anan!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "A nemo min nan da sati xan wuce na gaya miki."
"In sha Allah, amma akwai yaron nan Balali da Dilla ya kawo mana shi, yana son ballo mana ruwa."
"Ki saka a kawo min shi naji hujjarshi na lalata min dagiya ta."
"Yarinyar da ta fita suna tare."
"Nace a dauko min shi, ita kuma a tadata tabar min daki kafin fushina ya sauka har kanta." Da sauri ta nufi dakin ta tada ta, suka fito domin idan ya fadi haka rashin Imanin ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????shi ya motsa kenan. Tana fita ta nufi kofar da su Balali suke aiki, ta ce. "Ku rufe kofar nan." " Tow!" A take suka rufe ta ce musu."ku kama min dan iskan cen ku kaiwa yallabai."
Bai gudu ba, ya tsaya suka kama shi har gidanta, ajiye shi aka yi gaban shi. Kanshi a sunkuye. "Kai me ya haWaka da yan matan da suke wannan sansanin?"
"Ayi hakuri yallabai ba zan sake ba." "Hmmmm ba zaka sake kula su ba ko ba zaka sake wani abu ya fita daga bakin ka ba." "Dukka biyu yallabai." Gyada kai yayi yana faWin. "Idanuna yana kanka, nan da sati biyu zan bar nan ka sake wani abu ya faru." Wata ?atuwar wuka ya ciro, yana wasa da ita kafin ya ce mishi. "Da shi zan kashe ka."
"In sha Allah, ba zaka kara kama ni da wani laifi ba."
Haka ya bada hakuri sannan aka kyale shi, wani abin mamaki murmushi mutumin yayi bayan ya fita. "Me yasa baka kashe shi ba?" "Akwai abin da na karanta shi me dabi'ar Dilla ne bada hakuri akan kuskure wanda ya aikata da wanda bai aikata ba, wannan yaron dila ne. Kin san dai wannan wurin an gina shine da ra'ayin mutane mabanbanta, shi kin san aikinshi da abinda yake so, ni kin san aikina da abinda nake so, idan na ce zan kashe shi. Zan lalata goma daya bata gyaru ba, madadin na kama shi sai nayi rashin sa'a.

Dilla baya shan ruwa haka kawai sai da wutsiyar shi, idan har zai ajiye wani abu nashi tow duk yadda akayi ina iya jiyo kamshinsa domin yana nan kaWan damu."
"Kana nufin yana kusa kenan?"
"Kin san waye Dilla?" Girgiza kai tayi ya ce mata. "Dilla ita ce dabbar da bata kwana a ko ina sai a tsakiyar busashen ganye, domin ko fara ne ya fada kan ganyen zata farka, Dilla bata kamuwa ta dadi sai da tarko. Don haka maharba basu iya kamata sai sun saka mata tarko."
"Tarko kuma?"
"Eh tarko ita ba a kamata da nama, ko abinci duk abinda tasan baya samuwa a daji bata cin shi, tarkon dilla na musamman ne domin raga ake watsa mata."
"Na gamsu Yallabai, amma taya zamu iya kama shi?" "Ai shi baya bu?atar tarko."."ban fahimta ba?" Mikewa yayi ya nufi dakin, ya watsa ruwa ya fito yana me zama ya ci abinci, bai kara magana ba kuma ita Uwar mugu tana son jin shirin Yallabai akan Dilla ne, tasan su basa shiri amma kuma bata zata al'amarin zai kai har haka ba.
-----
Lokacin da na iso tantin mu, tsayawa nayi a waje ina jin shewar Munaisah da Addah, d'aga labulen nayi muka yi ido biyu da ita, gimtse dariyar tayi tana faWin. "Allah sarki Nennena." " Ba sai kin yi min wasan kwaikwayo ba!" Na fada ina kallonta, shiru tayi tana kallona. "Wacce ta tsare miki gaba ta tafi, sai me? Daga nan sai ki daura daga inda aka tsaya." Na fahimci abu daya, daga Addah har Munaisah babu ruwansu matukar kudi zai zo musu wallahi zasu bada kome suka mallaka, kai hatta rayuwarsu da zasu iya sallama ta, tow kuwa zasu samu kudi da ita.
Sannan wani abin mamaki shine kudin nan gashi nan amma ban san me suke da su ba, zuzu tana kwance nace mata. "Yan mata kina jin yunwa ko?" "Jiranki nake ai ki zo kaina, Zahra'u yunwa nake ji." Mikewa nayi na hada wuta, sannan na yan yanka kayan miya, na soya shi sama sama."
"Zahra'u a saka kifi!" Duba wurin kayan nayi naga babu kifi."Zuzu bari na amso mana kifin!" Na karbi jakar kudina na dauki abinda nake da bukata, na fito waje. Gidan Uwar mugu na nufa, har na isa ban hadu da kowa ba, sannan kowani tanti shiru ya dauka, buga kofar nayi, ta bude. "Zahra'u me ya dawo dake?" "Kifi nazo saya." " Kin ga kuwa jiya da daddare Addah ta kawo min shi na bata kuWi!"
"Ta kyautawa kanta!" Na mika mata kudin iya wanda nake so, ina jin Muryar shi me cike da Amo ya ce mata. "A maida mata wanda aka kawo a sayar a hada mata da kayan abincin."
"An gama Yallabai!"
"Kuma kada ki sake ki kara amsar kayan kowa inji ni!".
"Tow yallabai, maza ki mishi godiya." Ta ce min, "iya na kudina nazo saya." Na fada ina juya fuskata. "Ba zaki mishi godiya ba!" "Ni ba rokonshi nayi ba, shi yayi niyya kuma nace bana so dole ne?" Na fada Ina kallonta. "Yallabai!" "Bata abin da take so!"

Ya fada yana me juyowa yana kallona, nima kallonshi nayi na dauke kaina. Ban san yadda zan muku bayanin yadda yake ba, amma Kyakyawa ne dai-dai misali, sannan yana da sura irinta sadaukan maza. Amma abu daya da kwakwalwata taki mantawa shine yanayin surar Aminin duhu, har yau ina jin haka a raina. Domin kirjinshi a wani murde yake, tsokokin da suka cika kwanjin shi kadai abin burgewa ne. Dafe kaina nayi sakamakon jin kaina yana wani irin kuwwa. Sai yau na tuna da shi sosai, duk da zuciyata bata samu zarafin hasasho min shi ba, sai yau. "Baki da lafiya ne?" D'ago kai nayi na kalle shi, kafin na dauke kai ina amsar kayan hannunshi. "Mai kyau!" Ya faWa kamar rad'a.
Juyawa nayi na bar wurin, ko ina da kyau Allah ya min tsari da hada shirgi da wannan abin kamar dodo. "Amma kada ki sake fitowa, domin tsarina ne." Shiru nayi ban ce kome ba, domin kuwa ba zan iya cewa komen ba, don naga yadda sansanin yayi kamar an yi shara. Haka yana nufin yana da karfin faWa aji, ina isa tantin mu na ce musu. "Ashe yau ba a fita?" Sai lokacin Addah ta ce min. "Eh an gaya min jiya doka ce idan yana nan ba a fita." "Kuma Adda sai kika barta ta fita?" Zuzu ta mike dakyar cikin takaici. "Waye ya sani ko an shirya haka ne don a dauke Zahra din tunda yanzu anyi walkiya kowa yasan kowa."
"Allah ya tsare mana ita." Inji Zuzu, ina ga cikin nan ya karawa Zuzu masifa, domin faWa tayi ta cigaba da yi, tana hararar Addah. "Na gaya miki ban da fada." "Ke kyale ni nayi magana, me aka yi aka yi son zuciya."
"Tow Allah ya baki hakuri!" Daga haka na tafasa mana taliyar da miya, na zubama kowa zan zauna uwar mugu ta shigo ita da Balali. Ajiye mana kayan yayi ya juya ya fita. "Daga yau kada wani ya kara kawo mana kayan Abincinsa."
"Hmmmm!"
"Inji yallabai ne, ba inji ba!"
"Tow ai bin na gaba bin Allah, ina zamu samu wannan kayan dadin naga har da madara."
"Na Zahra'u ce, ba na ku bane."
"Ikon Allah Zahrah an fara dan waken zaga ye ne?" "Ita ba haka take ba, domin har yau bata dagula kuruciyarta da sabon Allah ba " inji Ummi tana tattara kayan, wato na fahimci a dakinmu akwai wani irin ya?i dake tsakanin Ummi da Addah, tsakanin Adda da Zuzu, sai suka saka ni a tsakiya, duk yadda aka kawo min duka zasu kare min, "kinji dadi Zahra sai ki saka idanu akan yan uwanki. Domin kada su kawo mana hayaniya."
Ta fada tana kallon Zuzu da Ummi da Munaisah da addah, ban san me yasa take yawan gaya min haka ba. "Na yarda da yan uwana, don haka ba zan sakawa kowa idanu ba. Kawai duk abinda kika ga ya faru tun can rubutacciyar al'amari ne."
"Gaskiya kan!" Inji Addah tana kasa da kanta, domin wani lokaci idan addah tayi wani abu yadda kasan mutuniyar kirki. Fita tayi ta barmu a wurin, na zauna naci abinci nima,

Haka muka ci muka koshi,bamu fita ba sai can yamma da aka ce mana zamu iya fita wanka, Zuzu da Ummi da Addah suka tafi, ya rage daga ni sai Munaisah, yadda bata ce min kome ba nima kuma ban saka ran xan yi mata magana ba, yadda take rayuwarta cikin nutsuwarta ba zaka ce uwarta ta mutu a ranar ba, domin ta warware kamar ba ita ba. Lashe bakina nayi ina gyarawa Yakumbo kwanciyar ta.
"Zahra'u!" Na juya a hankali ina kallonta. A hankali ta matso kusa dani. "Don Allah idan kin samu damar fita daga nan, ki nemi wannan number please Zahrah." Cike da Mamaki nake kallonta. "Murmushi tayi tana faWin. "Zan fita mana, zan tafi nesa dake idan ina ganinki zan iya aikata mugun abu akan ki. A wannan wurin ba uwa ba d'a, kowa ta kanshi yake kuma zaka iya aikata kome saboda kuWi. Fatana daya ki fita daga nan sansanin domin ba sansani ba ne, wuri ne na biyan bu?atar kai."

Baki daya sai ta kara min rud'ani, sama da wanda nake ciki ina muka kawo kanmu? Ina muke raye? "Munaisah me yasa ba zaki min bayani a nutse na fahimta ba?"
"Idan na miki ma ba zaki gane ba!" Muna zaune a wurin har su Addah suka dawo, Nima da ita muka fita, muka je wurin wankan, baki daya sai na kasa wanka na saba sai dare nake wanka,.don haka na juya ina faWin. "Ke bani iya wanka sai dare yayi." "Tow ai shikenan, ki je abinki." Haka na dawo na barta a hanya na hadu da Aina'u. "Naji ance yallabai ya tura miki da abinci, tow wallahi na rantse da Allah ba zan dauka ba, itama wancan me kama da zabiyar sai naci B... Ubanta, domin ba zata kwace min masoyi ba, shegu Mayun kudi. Ki saka idanu ki ga abinda zai faru."
Rab'ewa nayi na wuce ina xan iya da haushin ta, don haka na koma tanti na kwanta. "Baki yi wankan ba!" "Wurin cike yake da mutane ba zan iya wanka a gabansu ba."
"Kuma dai!" Inji Addah.
Haka na kwanta muka yi ta hira har lokacin sallah yayi, sai lokacin Munaisah ta dawo. Kusan ma rikota akayi . "Me ya faru?" "Ita da Aina'u suka yi faWa suka fada wuri me zurfi, ita kan ba a same ta ba. Sai Munaisah aka samu." Hadiye yawu nayi cike da tsoro domin nasan karshen mu yazo. Ihun Tumba muka ji tana faWin. "Wayyo Allah na, kun kashe min fitilar dake haska min gabana wayyo Allah ka dawo min da Yarinya ta. Me tayi muku." Yadda take ihu yasa kowa jikinshi yayi sanyi.

"Me ya haWa ku?" Kuka ta saka tana faWin. "Ita ta tura ni wurin zurfi, kuma wallahi ban san cewa idan muka fada ba zata iya fitowa ba. Wallahi ban kashe ta ba"
"Hakkin uwa wasa ne?"
"Ummi ki daina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login