Showing 69001 words to 72000 words out of 100763 words

Chapter 24 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2858

haka gaban ya mutu."
Rufe baki Aryan yayi da karfi jikinshi yana rawa, hawaye na zuba mishi kamar mace haka yake kuka yana kallon dan uwanshi. "Hammayo ba xai tab'a zama da mace ba kenan?"
"Gashi nan dai, bamu sani ba ko Ubangiji zai yi ikonshi, amma Abdul Majid yana cikin jarabawa." A hankali ya fashe da kuka, yana jin wani irin tausayin dan uwanshi. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Ubangiji mun gode!" Ya fada Aryan akwai karyayen zuciya, haka yake ga saurin kuka kamar mace, gani yake kamar dan uwansa zai mutu da damuwar lalurar.
Shi yasa yake nisanta kanshi da mutane, baya yarda ya zauna da kowa rayuwarshi cikin duhu, akwai wani irin shakuwa tsakaninshi da duhu tun yana Yaro, gashi ya girma da wannan trauma Win. A rayuwar Abdul Majid bai san soyayya ba, bai samu soyayya ba, ita kanta Hajiya ta haifi Majid ne amma bata damu da damuwarshi kamar yadda ta damu kanta da yayi aure ba.

Duk laifin abinda ya same su, laifin Alhaji Abbati ne, da bai saka Hajiya a cikin caca ba da babu yadda zata hadu da mahaifinsu ya kashe rayuwar dan uwanshi haka,. Sai yanzu yake fahimtar me yasa Majid ya tsani dukiyar Mamman ba'are, asalin don a gina duniya da dukiyar aka lalata musu rayuwarsu. Cikin shashekar kuka yake faWin. "Saboda hab'aka dukiyarshi ya lalata rayuwar wanda babu ruwanshi."
"Asibiti muke kayi hakuri ka bar wannan zancen." Haka suka cigaba da zama har wani lokaci kafin Alhaji Abubakar da lauya suka bar asibitin tare da Mahdi,. Suka tawo da Hajiya tare da abinci, mika mata kome Aryan yayi sannan ya koma gefe yana kallonta, ajiye takardar tayi ta zauna tana kallon Majid. A hankali hawaye yake zuba mata, wannan wacce irin rayuwa ce? Me yasa kome yake zuwa mata haka? Me yasa daga wannan sai wannan? Shin anya bata yi wani laifi Ba tare da ta saninta ba.
Su da suka zo da zimmar kwana Waya, sai gashi sun kare da dibar kwanaki har sama da biyar, a na shida aka sallami Majid din, ba laifi ya Wan samu sau?i. Kuma dama yanayinshi ba mai yawan walwala bane, sai abin ya kara yawa. Ita kanta Hajiya ta damu sosai kamar ta cire ciwon. Haka suka tawo Niamey zuciyarta babu dad'i.
Lokacin da suka isa gidan A tsakar gida suka hadu da Nanah, tana jin rigima. "Ya zamu yi da wannan tsohuwar?" A hankali ya fito yana tafiya, kamar ba zai taka kasa ba, saboda rashin karfi da kuzari. "Kai Alhaji!" Ta fada tana mikewa tare da dogara sanda har inda yake ta ce mishi. "wallahi ka sake ka mutu sai Allah ya mana hisabi. Kai ma mutuwa zaka yi?" Ta faWa, yadda tayi maganar zaka fahimci bata cikin nutsuwarta. "Munafukan can ne suka kaika zasu kashe min kai ko?" Kasa magana yayi yana kallon yadda take fada. "Nana likita yace a barshi ya huta." "Muje daga yau ni zan yi jinyar shi " duk da bata kaunarsu amma a lokacin da takira Hajiya take fadan ba zasu dawo bane, an barta kamar ba a damu da ita ba, gashi kayan abincinta ya kare, babu nama babu kome Haladu da Kamilu sunki saya mata, me take nufi na dauke mata Aryan shi ko zata mishi meye baya fasa saya mata kayan abincin.

Shi ne ta bata hakuri da gaya mata ai Majid bai da lafiya ne, bata san lokacin da ta rikice ba, tayi ta sumbatu tare da dorawa Hajiya laifin abinda ya faru gani take kamar Hajiya ta kaishi aka mishi wani abu, sannan ga Amaan da dama can tasan munafuki ne. "Ina gaya maka kada ka sake kana yarda da mutane, domin kuwa wasu ba imani a cikin zuciyarsu. Sun sayar da imanin su ga duniya, Gara ka yi nisa da su domin kada a wayi gari babu magajin Abdul Majid ba'are. Sannan kasaka ayi ta maka addu'a da saukar Alqur'ani domin nasan makiya ba zasu Barka haka ba, li'ilafi aniyar kowa ta bishi daga yau har Sa'a ban yarda da ita ba. Domin dankareren dukiyarka yawa ce da ita a tow zamani na masu iya kashe mutum, waye ya sani ko shima Muhammad kashe shi aka yi!" Zama yayi a daya daga cikin sofa, yana haki yana kallon agogon hannun shi. "Nana zan huta kiyi shiru." "Alhaji duk abinda kace ai shi zan yi." Ta zauna tana kaskantar da kanta tana faWin. "Ahtow nayi shiru, amma ina ga hatta Salamatu ban yarda da ita ba, waye ya sani ko har da ita ake shirya maka kitimurmura." "Nana jeki gida, an jima zan shigo duba baki." Ya fada yana daure fuska, domin idan ba haka yayi ba, ba zata kyale shi ba.
Sannan ya san halinta sarai sai ta kara mishi wani sabon ciwon kan. "Tow Allah ya baka lafiya, zan damo maka kunu na kawo maka." Yasan sarai idan yace mata ba zai sha ba, zata yi tsammanin bai yarda da ita ba ne. Haka yasa shi rufe idanunshi ya d'aga mata kai, domin kuwa baki daya bayan son magana. "Sa'adatu ki saka idanu akan shi domin ba zan yardaba idan wani abu ya same shi." Ta futa tana faWin. "A kula da shi don wallahi zan iya shiga kotu da kowa." Tana fita ya kalli Hajiya ya ce mata. "don Allah a gyara min dakina." Daga haka ya juya musu baya, don baya son magana, Hajiya da kanta ta wuce dakin, ta gyara baki daya, sannan ta fito tana faWin. "Na gyara maka" dakyar ya mike ya haura sama, koda ya shiga kashe wutar dakin yayi ya kwanta.

A hankali labarin matsayin da Abdul Majid ya bawa su Aryan ya zagaye cikin gidan, bakiWaya suka taru a falon Nana suna mitar abin da ya faru, da akan me Majid zai yanke hukuncin babu shawara da su, musamman su da suke Yan uwan Babanshi. Yadda ake masifar Nana ta zuba musu idanu, can da suka ishe ta mike tana faWin. "Yayi yadda yake so kamfanin nasu ne ba na wasu ba. Don Allah ku sakar musu mara na gaji da fitinarku, kada na kuma jin wata magana." Ta wuce dakinta bata kuma kula su ba, haka ta shiga ta bar su nan suna mita.

Wannan fitinar ta dame ta, kowa yasaka musu idanu. Kowa ya saka buri akan abinda ba na shi ba, sannan baki daya kowa burinshi ya mallaki abin da yafi na dan uwanshi, a kan wannan zasu iya kashe junansu akan abin da ba nasu ba,
***
*Zahrah*
Bana ce rayuwa tana da sauki a wurin Uwa irina ba, domin baki daya na susuce akan Babyna, zamowa uwa ba abu ne mai sauki ba. Haka na nakoma kome kamar mahaukaciya, bana barci da zarar naji motsinta duk barcin da nake na daina Kenan xan tashi daga barci har sai ta koma, wani abin da na kasa sabawa da shi, shi ne, da zarar na saka abinci a gaba Baby zata fara kuka, ba zata kuma shiru ba sai na hakura da abincin............
#Mai_Dambuje
[2/24, 2:51 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

_Hodjam Fire to fire Fitilar hikayar Dambuje, BA?IN HAURE comments. Wannan Pagen na kune yan arzikinsssssssss zaku sheke min dariyata >?s?>?p? Irin wannan comments a kwana a hantse sai Kyakyawa =?? Baby Aminatu sai tasha Baloon din nan fa >?#?=??Baby bata mutuwa fa sai hakuri_



Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTU?ARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....

*023*
Ko don na taso a tsakar gidanmu ne, ban tashi gaban Uwa ba, ban san yadda Uwa take handling yara kmr Babyna ba, akwai wani abu da na fahimta da zarar gari ya waye zata wuni barci, sai dare garinta zai waye duk da haka bai hana da zarar na saka abinci a gabana zata bude idanunta ta fara rigima ba, sannan baki daya a girman dakin da muke babu me iya tunanin ya taimaka min, Ummi da Addah kowa harkar gabanshi yake, sannan basu da lokacin da zasu tsaya lallai sai sun taya ni kula da yarinyar.
Bakidaya sai na kasa sabawa, da zarar dare yayi zan goyata ina yawo da ita har daren yayi nisa tayi barci. Na kwanta da ita a bayana, sannan zamu yi barci idan kuma sanyi ya dame ta hana kowa barci take, haka zasu yi ta tsaki suna mita. Gari na wayewa kowa zai kama gabanshi. Suna tafiya suna mita, ban tab'a fushi akan hakan ba.

Yazeed Hamir.
Asalinshi dan kasar aljeria ne, mahaifinshi babban attajiri ne sannan Basarake ne a babba a kasar , kuma Balaraben aljeria. Suna da kudi sosai sai dai shi Yazid ya lalata rayuwarshi ta hanyar shaye-shaye. Mutum ne da bai da yawan magana ko hayaniya, sannan akan abinda ya shafi sayar da kwayoyi baya da wasa. Domin ya bar ?asarshi ta haihuwa ne yazo wannan wurin ya kafa inda zai na fitar da shu'uman kayan maye yana rabawa tsakanin kasashen Afrika. Shaidani ne na gayawa Sarkin gari, yana da wani irin sirrin da duk inda ya shiga sai ya fitar da kaya, zai yi wuya ya shiga wuri bai fitar da kayanshi ba, sai dai yana da rauni sosai matarsa da Yaran shi, biyu dukkansu mata ne yana matukar kaunarsu. Yazid ya bar gidansu ne tun yana shekaru ashirin da biyar a duniya, domin yana da matukar kiyayya da sarauta, domin a sanadin mulkin da za'abawa Babanshi Mahaifiyarshi ta rasa rayuwarta kuma dama ana ta faWan cewa ya sadaukar da ita ne ga mulkin shi, shi yasa ranar da ya fara jin labarin ya sami mahaifinshi da maganar, ?aryatawa yayi shi kuma ya ce matu?ar ya tabbatar da haka sai ya bar mishi kasar da kome yaje yayi rayuwarshi,. Dake akwai mutanen da basu son Babanshi, sai suka yi amfani da haka suka tabbatar da cewa sadaukar da Amiratul Aminat aka yi, duk yadda Uban yaso mishi bayani amma ya?i fahimta. Don haka ya saka kafa ya bar kasar da dukiyarshi a lokacin ya gama karatunshi a bangaren had'a magunguna.

Wannan abin yayi matukar yiwa mahaifinshi ciwo, har kwanan gobe yana zuba idon ganin shi, Yazid yana matukar tausayin mata da Yara, akan mahaifiyarshi ya kara jin tausayin Yaya mata, kuma wani abin da yake kara saka shi tausayinta, ita sikila ce. Sai akayi dace shi bai da shi, haka yasa yake son Reshmah kamar zai haukace da ta fara haihuwa ma bai tab'a ce mata ga zab'in shi ba, sunan da takeso take sakawa. Tozali da yayi da Zahrah yaji duniya bai tab'a tausayi da son wata Y'a mace ba kamar ta, sannan baki daya sansanin da suka zauna mutanen Yazid ne, hatta Uwar mugu dalilin da yasa Nawwas yazo nimanshi wurinta kenan, sai gashi kuma Nawwas din jin kamar Yazid din yana zuwa yasa shi guduwa da yan matan.
Matarshi itama balarabiya ce, Reshmah mace ce mai tsananin kishi da saurin fushi, sannan shima Yazid yana matukar kiyayye abinda zai saka kishinta ya fito har ayi tunanin wani abu. A wannan dajin idan kana son ka fita sai ka je an saka maka wasu kwayoyin da zaka masa safara da shi idan ka sha zaka je a cire maka, sannan kayi tafiyarka daga nan ka samu yanci, ba kuma zai barka ba domin abin shi kamar da siddabaru domin ko ka bar dajin ka manta kenan. Ba zaka kara tunawa ba, da haka Yazid yafi karfin abokan gabanshi, domin yana fito da kayanshi ta kowace fuskar ya sayar a waje.
Lokacin da muka zo garin ina cikin waWanda aka rabawa aikin shara da goge gogen gidanshi, idan har Matarshi ta rigashi tashi hatta bango sai na goge, sannan babu ruwanta da ina da baby ko bani da Babyn, matar nan yar bala'i ce. Kafin Yazid ya fito na gama kome na bar gidan. Sai yamma kuma na koma.
Ban san me yasa ba ko yana sane da yadda matarshi take saka ni a gaba da fitinar aiki, ranar ina zaune a kofar gidan da muke sai gashi ya zo ina jijjiga Baby. "Babyn Zahran bata yi barci ba ne?" Juyawa nayi zan yi magana domin ban zata shi ba ne. Sunkuyar da kai nayi na ce mishi. "Yallabai kai ne?" Na fada ina jijjiga ta, ajiye wata jakar takarda yayi ya ce min. "Kawo min ita." A hankali na mika mishi ita har hannunmu yana gogan juna. Da sauri na janye nawa hannun, shi kuma ya cigaba da kallona. Yana me kallon inda kwanon abincina yake, na bude zan ci ta fara rigima. "Ki ajiye abincin anjima sai ki ci ga wannan ki ci." Ya nuna min jakar da idanunshi. Sai gashi na rikice baki daya, domin ina jin yadda yake bina da idanu, ban saba ba sai nake ganin kamar ba zan iya tsayawa da kafata ba. Jingina nayi na dauki jakar na bude, madara ce a kwalba sai gassashen nama, hadiye yawu nayi duk da ba laifi tunda muka zo ba laifi abincin mu yana da kyau, sannan a wadace muke samu. A hanya muka fuskanci matsala amma tunda muka zo abincinmu babu laifi. A hankali na fara bude takardar da ya nad'e namar, kamshinsa kawai yasa na hadiye yawu yafi sau goma. Na d'ago kai naga yana hidimar baby da sauri na fara ci, ban sani ba ko yana kallona domin ganin nama yasa ni jin duk wata yunwar da nake ji na tsawon watanni bakwai ta dawo min sabo fil, "ki ci a hankali." D'ago kai nayi naga Babyn yake wasa da ita, goge bakina nayi na cigaba da cin namar, har na koshi. "Zan tafi!" "Allah ya saka da alkhairi." Na faWa ina sunkuyar da kai, koda su Addah suka dawo a gajiye, idanunta ya sauka akan jakar takardan, dauka tayi zata buWe Ummi ta fauce. "Dalla bani." Dama kuma na rage musu ne, ganin kowannensu ya samu ba zai bawa dan uwanshi ba. Yasa na amsa. "Idan kuka yi hakuri na ku ne, idan kun yi faWa ma naku ne." Na fada ina ciro musu na mika musu, faucewa suka yi suna jan tsaki.
"Wani dan iskan kika samu ya kawo miki?" Inji Addah, ban bata amsa ba na gyara mana kwanciyarmu da Baby. Washi gari da na shiga gidan aiki naga Matarshi sai hawa da sauka take, har na gama aiki zan fita ya fito dauke da Yarshi. Murmushi yayi min na sunkuyar da kaina, na fita da sauri.

A harabar gidan naga alamar zasu fita ne, haka yasa na bar gidan domin yau bata min kakale-kakale ba, asalima kamar sauri suke. Ina dawowa nayiwa baby wanka. Sannan muka kwanta bayan mun karya.

12:30pm,
Ji nayi kamar ana tsaye a kaina a hankali na bude idona, ya sauka akanshi yana bakin gadon Ummi yana latsa wayarshi, da dan sauri na tashi zaune ina kallonshi. "Yau Baby bata yi rikici ba kenan?" Ya ajiye min irin jakar jiya.
"Wai ya sunan Babyn?" Tiririn da nake ji na kamshi yasa ni rikicewa domin yunwa nake ji, kuma sai karfe biyu za a kawo mana abinci. "Ban mata suna ba, baby muke kiranta."
"Ya sunan Mamanta?" D'ago kai nayi ina kallon shi, kawai sai ya cika min idanu. Sunkuyar da kai nayi ina faWin. " Zulaiha!" Na zabi na fadi haka ne domin ya min kwarjini. "Ok bani ita!" A hankali na mika mishi ita, kamar mai tunani sai kuma ya ce min. "Hmmm! Ba zan saka mata sunan Uwarta ba, domin zata iya gadon halinta."
"Ka saka mata sunan Addah." "Ita criminal ce zata tashi da shaidancinta."
"Tow ka saka mata sunan Mamana!" "Ya sunan yake?" "Aminatu!" Murmushi yayi ya ce "sunan Kakata ce da tasoni sama da kanta." Ya fada yana shafa kan Babyn yana me mata huduba. "Maman Aminatu!" Murmushi nayi, tare da Mikewa zan karbeta ya ce min. "Ci abinci" ba musu na zauna na ci grill fish da chips a gefenshi. Sai da na gama ci ya mike, ya ajiye min yarinyar.
Ya tafi, lokacin sallah yayi na mike na wuce ban daki nayi alola sannan.na dawo nayi sallah, sannan muka kara kwanciyarmu, domin kifin akwai maiko. A hankali wata irin shakuwa da bansan daga inda ya samo asali ba, ta shiga tskanina da Yallabai Yazid, da farko sau daya yake zuwa, daga baya ya koma yana zuwa sau biyu. Da rana da kuma Yamma, a hankali idan yazo shirya Baby Aminatu, Addah kamar zata rufe ni da duka da taji sunan har da Min Allah ya isa, bata yafe ba don na saka sunan Mamana.

Da yamma idan ya zo Waukarmu yake muna zaga cikin garin, gonarshi da lambun shi har da gidan dabbobin shi. Yau ma haka ya saka ni a gaba, bayan ya kawo min wata doguwar riga da mayafinta. Muka shiga wani yanki ta Cikin gonar, mun yi dogon tafiya kafin ya kawo mu wani wuri a ?ar?ashin ?asa, ya ce min. "Kin ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login