Showing 42001 words to 45000 words out of 100763 words

Chapter 15 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2868

ta zuba min shara ta b'ata min safa ta." Dama Hajiya rabi tana cike da ita Harirah ta hana a casata, sai gata ta fito da wani murtikekken bulala. Ta rufe Sa'adatu da duka, tana yi yaranta suna yi. Fitowa Hajiya Fauziya tayi tana faWin. "Shegiya sai kace Mayya idan an gama dukarki wanke -wanke na yana jiranki." Tasan ana dukarta ne babu halin amsa mata, haka ta shige kitchen ta dibo ruwan zafi zata watsa mata sai ga Alhaji Mamman Ba'are da Harirah. "Ka gani ba? Ruwan zafi zata watsa mata bayan sun gama dukarta. Alhaji kaji tsoron Allah Ubangiji ba zai barka ba, kasan zaka kawo ta cikin masifa ka auro ta ka mai da ita wurin danginta."
"Rabi da Fauziya. Na baku nan da minti ashirin ku bar min gidana, idan kuwa na dawo na.same ku wallahi sai na sake ku.". Ya nufi Sa'adatu ya dauketa suka nufi ciki. Goge mata fuska yayi yana son yayi Magana amma ya kasa magana. "Shirya mu bar ?asar."
"Ina zaka kai ni? Wurin Abbati? Ko wurin Baffana?" Ta tambaye shi cikin kuka. "Wani wuri da zaki rayu babu faWa babu tsangwama."
"Tow."
Haka ta shirya kayanta sannan suka fito a lokacin Nana ta fito tana kallonshi. "Ban gane ba, ina zaka kaita?"
"Idan Uwar da ta haife ni, ta gaza taimaka min waye zai taimaka min? Nana ke kika basu damar cutar min da Mata? Nana gani na da kika yi a raye yasa kike cutar da abinda nake so? Nana zan nisantatta da ku ne domin Harirah ta gayawa dan uwanta na auro mace na kawo Matana suna son kashe ta, kotu zata turo min sammaci sai ki san abin da zaki ce musu."daga haka ya riko hannun Sa'adatu suka bar gidan, Marad'i ya wuce da ita suka kwana biyu, a wannan kwana biyun ne, ya mai da ita cikakkiyar mace, cikin alfahari da samun mace irinta, dama an gama.mata kome na makarantar, da shi da Alhaji Abubakar Abzin suka tawo da lta garin kano, inda ya tsaya sai da yaga ta fara karatu. Don kusan watan shi biyu
kafin ya fara shirin dawowa nijar ya rike hannunta.
"Kinsan dalili na na kawo ki nan, kin san kudirina na kawo ki nan. Don Allah kiyi karatu sosai, kiyi abin da ya kawo ki zan na zuwa lokaci zuwa lokaci ina duba ki."
Gyada kai tayi, Washi gari motar shi tazo ta dauke shi, haka ya barta cikin kewa da rashin sabo, ta fara karatu a BUK, a tsangayar tattalin arzikin kasa da kasuwanci. Yarinya me kwazo da hazaka.
Wata ukun farko da fara karatun, kaf tsangayar suka san tana ja,. Ai kuwa shima Alhaji Mamman Ba'are da suka zo da Alhaji Abubakar Abzin, ya ga sakamakon da ta fara samu ya fahimci yarinyar guruwa ce, domin samun irinta a cikin Yaranka ba karamin arziki ba ne.
Haka yayi ta dora Alhaji Mamman Ba'are a kan hanya, yadda zai na kyautatta mata. Har ta samu shekara daya a lokacin ne ta samu cikin Abdul Majid. Cikin tsananin zafin laulayi haka ta haWa karatu da laulayi tana tsoron kada ta samu matsala ya ce tana wasa, a lokacin ta shiga aji biyu. Haka yazo ya samu tana fama da laulayi ga shi suna tsakiyar semester, kanta yayi zafi duk da wannan yanayin bai gaza gaya mata kudirinshi ba, har ya gama kwanakinshi zai tafi ya ce mata. "Idan mace kika haife zan barki ki kara haifar daya, su zama biyu kema ki samu abokan hira, don Allah ya azurtani da Yara mata sun kai goma sha bakwai ga na cikinki ga na cikin Rabi da Fauziya. Don haka kina haifan biyu zan kai ki a cire mahaifar ki huta kinji."

Gyada mishi kai tayi tana jin duk abinda ya ce, domin ita ba zata tab'a bijire mishi ba, shi din kamar waliyi ne a gare ta, haka yasa ta ke daukar duk wani abin da ya ce da muhimmanci. A hankali ya shafa kanta yana rungumeta. Abu daya yasa yake sonta, ilimi da kokarinta. Kuma yaranta zasu banbanta da Yaransu rabi haka yasa yake kara jin dadin ganinta tana kara mishi biyayya.
**
Ya dawo da su Hajiya Rabi, suka nime saka Harirah gaba, danginta suka ce basu san da zancen ba, kada su fara saka yarsu a gaba ba yarda zasu yi ba. Haka ba karamin ja mata mutunci yayi ba. Bayan shekara daya ne Alhaji Nasiru Wodabbe da Mahaifin ta suka zo mata da kayan aurenta, kayan alfarma na yar gata, da wasu daga cikin yan uwan Mamanta,. Dake Alhaji Mamman Ba'are har kasarsu ya tafi ya je suka ganshi ya tabbatar musu tana lafiya, sai gashi sun kawo mata kayan aurenta da duk abind??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ake na al'adar kasar nijar. Shima ganin ya auri yar babban gida, basu bar kasar ba, sai da ya ajiye musu kayan auren da ake a cikin kayan har da zinari babba tukwaicin budurcinta.....
#past
#entangled
#revals
#lovers
#Dambuje=?9?
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

_=?D? Wai page biyu kuke so, Yasin kuyi maneji mana=??? masoyan Addaririya_

Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTU?ARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....

*015*
A bangaren Nana ta dai sassauta kiyayyar ta ne don, iyayen Sa'adatu babu wanda ya isa ya kawo musu raini sannan daga mazan dangin har matan kana ganinsu kaga wadanda suka san ciwon kansu, ga wanka da matan suka yi na arziki zaka fahimci sun tashi cikin arziki da wadata domin gwala-gwalan da sukayi kwalliya da su, bayan tafiyarsu ne ya fara ginin part din Sa'adatu ya zuba mata kome nata, da zai tafi wurinta ya dauko mata yan kunnenta babban set da karami ya kai mata,
A lokacin da laulayi nata yayi sauki kenan, haka ta rike shi da daraja, bai gayawa kowa Sa'adatu tana da ciki ba, amma yadda yake lissafin zata haihu bayan sun gama jarabawa zai kaita wurin danginta ta zauna sai tayi arba'in ya dawo da ita. Haka kuwa aka yi domin suna gama jarabawa, ya zo ya zauna ko zata haihu amma ina shiru haka.yasa shi daukarta suka tafi kasar Iyayenta. Lokacin da ta ganta a cikin danginta. Ranar kwana tayi tana kuka tana jin wani irin son danginta..ga iyayenta ga Abbati sai shiga da fita yake yana kawo mata abinci da ta ce tana so.

Shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are sai da yaji wani iri domin kuwa yarinyar ba tsarar shi ba ce, don Abbati ya nuna mishi wanda aka so ta aura, yaro ne Matashi amma haka ?addara da rabo ya shiga tsakani. Ranar da suka isa a daren ranar ta haifi d'anta namiji, babu wanda yasan tana nakuda, tsabar kunya da wauta.
Yafendo mahaifiyarta tana dakin Mallam mahaifinsu, suna sallar nafilla da mallam wanda suke kiran shi Babaji, taji kukan jariri, bata yarda kunnenta ya jiyo mata ba, sai can ta kara jin kukan. Ai sallama tayi ta nufi dakin ta, anan ta samu Sa'adatu da Kanwarta Kabo, an rasa wanda zai yi wani abu, sun saka Baby a gaba. Dariya abin ya bata ta ce. "Danejo jaririn kuka kasa a gaba. Keda kabo shine baku fita kun kira Sumai ba?" Tana jingine da gadon, tana sauke ajiyar zuciya. Bata ce kome ba, itama Yafendo fita tayi ta kira Sumai, Uwargidanta kenan, ita tazo ta gyara Babyn tsaf, ta wanke Sa'adatu a lokacin, sannan suka saka turaren wuta, domin ita Sumai fulanin chad ce, tana harkar turaren wuta. Kafin wani lokaci gidan ya cika da kamshi, Sa'adatu ana kiranta danejo, Babaji yana kiranta da Hajiya. Kasancewar sunan Mahaifiyarshi ce kuma Hajiyar ce da gasken gaske.

Da asuba aka gayawa Alhaji Mamman Ba'are, Hajiya ta haihu.don da fari bai fahimci wacece Hajiya ba, sai da Alhaji Nasiru Wodabbe ya zauna ya mishi bayani, sai ya gane ya kuma ce musu. "In sha Allah Hajiyarta za a kirata.". Haka ya fita Masallaci, ya shiga gidan don ance mishi ta haihu amma basu gaya mishi me ta haifa ba, sai da ya shiga Sumai take murmushin farinciki ta ce mishi. "An samu da namiji, ango ba cefane." Zubewa yayi a kasa ya zuba sujudul shukur, kafin ya fashe da kuka, aka mika mishi Yaron, jikinshi yana rawa ya fito da yaron har gaban Babaji, ya ce mishi."ka saka mishi sunanka." Murmushi Babaji yayi ya amshi yaron ya mishi huWuba, a madadin yasaka mishi Aliyu, sai ya saka mishi Abdul Majid. Ya mika mishi. "Gashi nan Abdul Majid, kukan ya isa haka. In sha Allah zai zame maka fitila a duk wani Mabudin alkhairinka." "Mallam baka saka sunanka ba?" Ya faWa hawaye na zuba mishi. "Suna na ba shine mai muhimmanci ba, sunan da zai zame mishi alkhairi ake bukata."
Malam yaji dadin wannan kara da Alhaji Mamman Ba'are ya mishi, shi kan kuka yake tayi, don gani yake kamar ba dan shi bane, har asibiti aka kai Yaron aka duba lafiyarshi. Sannan suka dawo kwanan shi biyar ya dawo Nijar ya gayawa Nana ai Sa'adatu ta haihu, bata wani damu can ba, sai da ya ce mata namiji ta haifa shine bayan suna suka je ita da Hadiza da Harirah. Ba karamar hidima aka musu ba, duk iskancin Nana da wulakanci sai da ta rena kanta, domin tazo inda ake magana ta arziki wato kudi kumbar susa. Domin su suka je Barka, sai gashi sun dawo da kayan arziki niki-niki. Madadin haka ya janyowa Sa'adatu farinjini sai tsanarta ya kara cika zuciyar Hadiza da Nana, ita kan Harirah tun farkon ganin Sa'adatu da hakorin hajji jikinta ya bata daga babban gida ta fito, shi yasa bata wani takurawa kanta wurin kishi me zafi ba.

Watansu guda suka dawo kano da kaya niki -niki, suka cigaba da zuwa makaranta. Da dattijuwar da tazo da ita daga garinsu me suna Inno, ita tayi ta renon Abdul Majid har suka yi arba'in da wasu satika sannan Inno ta koma ita kuma ta cigaba da karatunta, sai da suka yi wata hudu sannan suka tafi marad'i, kwanansu uku suka wuce Niamey. Wayyo rawar kai a gurin Alhaji Mamman Ba'are ba acewa kome, haka tayi musu sati Uku. Don zasu koma makaranta kuma har cikin azumi suna karatu. Haka da zata dawo Alhaji Mamman Ba'are yayi ta mata hidima.
Har suka dawo, kaunar da yake nuna musu ya janyo mata bakin jini, haka suka yi ta jigilar karatu ga danginta daga garinsu ana yawan mata aike, lokacin da Abdul Majid ya cika shekaru biyu, suka tafi Umara da shi, Abbati ya biya mata da Abdul Majid. Lokacin sun samu hutu koda suka dawo, Nijar suka sauka a can ta huta domin lokacin zata shiga aji hudu ne, ga zata tafi IT, wannan zuwan ta fahimci kamar bayan son ganinta har ta gama hutun zata koma, ya zo domin sau biyu suka hadu, da zata koma ya mata kome, ya ce kada ta kuma zuwa Nijar.
Tunda ta dawo bai kuma waiwayonta ba, Allah ya so Abbati baya wasa da zuwa ganinta duk bayan wata uku, bata taSa gaya mishi tana cikin matsi ba, ba kayan abinci shima Abbati idan yace zai zo Mahaifinta zai cika mota da kayan abinci akawo mata . Sannan Yafendo tana turo mata da kayan sayarwa turaren wuta da wasu abubuwan da babu anan, haka yasa ta samu damar tsayawa da kafarta.
A can Nijar kuwa, Alhaji Mamman ne ya hadu da wata mata sun haWu tun a lokacin zuwan shi Mali, sun dan tab'a soyayya sai gashi ta kuma dawowa rayuwarshi,. Bayan da ta fahimci ta kare mata, tun da suka hadu ta kara jan ra'ayinshi suka fara soyayyar bariki, kuma dama can yar barikin ce shima ba zai ce ba yar barikin bace domin bai san.yadda aka yi ya fada tarkonta ba.

Tunda ta dawo rayuwarsa tayi bincike a cikin matansa wacece yafi so, a binciken ta gano Sa'adatu da danta. Anan ta fara shige da fice, sai da ta cire mishi su a ranshi, sannan ta aza mishi kiyayyar Abdul Majid, idan ya ga yaron kamar zai kashe shi. Don haka yace kada ta kuma zuwa gare shi, don yaron.
----- Bayan ta gama IT, ta koma makaranta Allah ya taimaka akwai kudi a hannunta dasu ta biya kudin makaranta, ta cigaba da karatu, suna cikin karshen zangon da zasu gama makaranta, yazo a lokacin Abdul Majid bai wuce shakara biyu da rabi ba. Da murnar yaron ya tawo gare shi, Alhaji Mamman yasa kafa yayi kwallo da Yaron, tana wanka ta ji ihun Abdul Majid, da sauri ta fito daga ban daki, ganin Alhaji Mamman Ba'are ya rufe yaron da duka, yasa ta isa wurin ta dauke shi, tana faWin. "Yaron da babu ruwanshi me yayi da zafi?" Kame gashin kanta yayi ya rufeta da duka, har da kwallo da ita, wulakancin da yayi mata Allah kaWai ya sani, ya kuma jan ta har cikin Wakin, haka Abdul Majid ya tafi bakin kofar yana buga kofar yana kiran sunanta "Hajiya!" Yana buga kofar, Alhaji Mamman Ba'are kuwa, ya kwana biyu bai tab'ata ba, haka yayi ta sukuwa akanta kamar ya samu jaka. Yana gamawa ya tashi yayi wanka ya gyara jikinshi, ya saka aka sauke musu abincin yayi tafiyarshi,

Bai kara waiwayarta ba, sai bayan sun gama exam ana batun zuwa bautar ?asa, ya samu tana fama da laulayi, lissafi yayi kafin ya sakata gaba suka je asibiti aka duba lafiyarta, sannan suka dawo ya kuma rufe Majid da duka, ya kara saka mata doka. Tana gama bautar ?asa Masters zata wuce. Haka yasa suka zama kamar bayi, a wannan zuwan da yayi har da Hajiya Tani da ya mai da ita yar gida. Amma idanuna Harirah yana kanta, domin bata yarda da ita ba, koda tayi magana akan hakan sai da suka kwashi yan kallo. Tana ji tana gani Tani ta samu damar k'amk'ame kome a cikin gidan.

Wato tani wata irin Shaidaniyar mace ce, da ta gallabi kanta da duk wanda yake kusa da ita. Musamman ta kananaye kowa har da kannenshi da Nana, babu wanda ya isa ya d'aga mata murya. Domin idan kayi magana Alhaji Mamman Ba'are zai ce ka fita ka bar mishi gida, haka yasa kowa ya sha jinin jikinshi. Kowa ya rufawa kansa asiri, kuma ai wargi wuri yake samu. Akwai wani lokaci da Hajiya Rabi ta rufe ta da duka, ai kuwa Alhaji Mamman Ba'are yana shigowa ya samu Tani a inda Hajiya Rabi ta dake ta, babu bin ba'asi ya rufe Hajiya Rabi da duka, sannan ya kwaso mata kaya ya watsa a waje, da guzirin sakinta.

Wannan abin ya tashi hankalin mutanen gidan, domin saura igiya daya a tsakaninsu, haka sai da aka yi da gaske ya dawo da ita, ya kuma kafa mata doka, tun daga ranar Tani take zuba mulki kuma babu wanda ya isa magana, sannan itama Tani tasan cewa yana biye mata amma mafi yawan hirarsu zai sako sunan Sa'adatu. Hankalinta a tashe ta nufi wurin Malaminta ya rufe mishi baki da zuciyarshi.
***
A Kano tayi bautar ?asa, kasancewar Abbati yazo, tana gamawa ta wuce kasarsu a can ta haifi Amaan aka turawa Alhaji Mamman Ba'are sakon haihuwarta, dake a can kamfanin labarin ya same shi, Kuma dayake aikin bai shafi jaririn ba cikin farinciki ya tsayar da dan aiken ya bashi sako ya kai musu, amma shi dai bai taka har can ba, har tayi arba'in ta koma Kano. Dan abin da taxo da shi suka cigaba da rayuwa, bai kuma zuwa ba sai da Amaan ya cika wata takwas, ya turo Alhaji Abubakar Abzin, ya kara biya mata masters ta cigaba da karatu, haka tayi ta fama da Yara biyu ga karatu, koda Alhaji Abubakar Abzin bai zo ba, akwai mutumin da yake kawo mata sako.

Lokacin Abdul Majid yana da shekara uku da rabi, Amaan yana da shekara daya da rabi, domin har ta yaye shi. Sai ga Alhaji Mamman Ba'are da Tani dauke da d'anta karami da ta haifa bata jima ba, kuma abin mamaki shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are ya kasa cewa kome akan dan na farko shi bai ce dansa ba ne, sannan kuma bai ki yaron ba, a wannan zuwa da yayi, rayuwar Abdul ta fara fuskantar matsala, abin da ya kawo haka, shine tunda suka zo gidan suka saka shi a gaba da duka, na safe daban na rana daban, idan suka mishi wannan dukar, zasu saka shi a daki a rufe shi, a manta da shi ita kanta Sa'adatu bata da ikon ciro shi, idan ta ciro shi kuwa Tani ta sakata a gaba da masifa sai kace ita ta haife ta, idan Alhaji Mamman Ba'are ya dawo kuma ta gaya mishi ya rufe ta da duka, ita uwar a wahale yaron a wahale.

A hankali Abdul Majid ya zama kamar dolo matukar Alhaji da Tani suna gidan zai na wani irin sizing

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login