Showing 45001 words to 48000 words out of 100763 words

Chapter 16 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2854

kamar zai suma. Tsoro da firgici na Uban ya kara cika zuciyar Yaron, satin su hudu suka bar gidan, shine ya dawo daidai amma kuma sai ya xama ko sauti yaji mai karfi, zai zabura yana niman inda zai boye kanshi. Gashi zama da mutane bai saka ta saki jiki da kowa ba, haka yasa bata mu'amala da kowa.

Wani zuwan Mahaifinta taron Malamai na Afirka, yazo ya ganshi bai tsaya ba, ya dauke shi zuwa gidan Sheikh Muhammad Taj Kalarawi, ya ajiye mishi Yaron yana faWin. " Malam Muhammad ka kalli yaron nan kamar akwai sihiri ko?" "Ikon Allah yanzu dan wannan yaron aka yiwa asiri haka?" Murmushi Sheik Aliyu Wodabbe yayi ya dauki Yaron. "Idan anyi ne don a ga bayan shi, in sha Allah ba zasu ga bayan shi ba. Sai ya zame musu gaggarabadau.." ya dauke yaron yana murmushi, "Alaraini kayi hakuri kada ka mai da musu sharrinsu."
"Ni ban musu ba, kuma ba zasu min na kyale ba. Kasan waye ni kuma kasan daga ?abilar fulanin da na fito, wallahi ba zan bari ba." "Don darajar Ubangiji kayi hakuri amma shi ka tsare shi." Huci yake kafin ya sab'a yaron zai fita Sheikh Muhammad Taj Kalarawi, ya ce mishi. "Kawo shi!" Mikamai yaron yayi, sannan ya tafi ya koma wurin Sa'adatu. Ya tambaye ta meke faruwa da Yaron, amma bata ce kome ba sai kuka. Haka yasa shi fahimtar tana da damuwa amma ba zata fada ba, sati biyu ya yi a garin tare da tsayawa akan Yaron.

Wannan zuwan ya zame musu alkhairi, domin kuwa har makaranta aka saka yaron, bayan tafiyarshi Alhaji Mamman yazo da Tani. Hmmm ganin yaron yana makaranta da nutsuwa. Hankalinta ya tashi a wannan lokacin da ta saka mishi kahon zuka, domin kuwa duka take mishi wani lokaci idan zai tafi makarantar domin har gida ake zuwa daukar shi, amma zata hana a kai shi, duk da Sa'adatu tana son mata magana tsoron abinda zai je ya dawo yasa take rintsa idanunta.
Bata taSa hanawa ba, sai sau daya tana laulayin cikin Aryan da aka zo za a dauke shi, Tani ta hana. Kasa hakuri tayi ta ce mata. "Gaskiya ba zai yiwu ba, ya tafi makaranta domin ba zai zama ya rasa nutsuwa ba, a gida bai huta ba sannan a can inda zai huta kice ba zashi ba, wannan ba yi bane ." Ta kamo danta ta fi da shi. Tana komawa cikin gidan Tani ta saka sakatar gidan zata rufeta da duka, ita dai bata san me ya faru ba, sai dai kawai an balle kofar gidan ne aka d'aga daga kan Tani da ta suma.

Koda Alhaji Mamman Ba'are ya zo don yaji labarin abinda ya faru, shima tsorata yayi da Yanayin Sa'ade, don haka ya tattara kayan Tani da d'anta. Bai kuma takowa gidan ba, har ta haifi Aryan ita da kanta tayi mishi huWuba. Haka tayi ta rayuwa can wurin danginta kamar sun manta da ita, haka shima bangaren mijinta ya manta da ita, sai da ta kai dole ta cire Abdul Majid a makaranta. Dake makarantar Sheikh Muhammad Taj Kalarawi ne,. Ya daina ganin yaron domin Allah ya daura mishi son Abdul din, wani ikon Allah sai kamar an dakatar da shi da zuwa duba su. Haka ya watsar da tunaninsu.. yara uku babu abin da zasu ci, don haka kawai ta fita ta fara aikatau, tana wanke-wanke da abinci, a bakin titi, karshe ma karatun da take ne ya tsaya, akwai wani karamci da kanawa suke dashi, kasancewarta bakuwa kuma daliba, ganin bata zuwa aka tashi wasu daga cikin dalibai suka nimo labarinta, haka yasa makarantar B.U.K suka dauki nauyin sauran lokacin da ya rage mata, wannan karamcin da suka. Mata yasa bata iya mantawa da su ba, sannan daliban tsangayar suka hada mata kudi ta kama sana'a a cikin gidan, ba sai ta fita ba.

A bangaren yaranta ta saka su a wata makarantar gwamnati. Haka suka ta rayuwa da dadi ba dad'i. Har suka gama ta cigaba da xama a Kano, a hankali ta rungume Yaranta, ta cigaba da sana'a idan suka cinye jarin, sai ta nemi aikatau a gidan mutane.
Abdul Majid tun yana primary yake da kokari, sai dai daga lokacin da aka mishi tsawa, zai birkice ya koma kamar dolo, haka yasa wani lokaci yake hakura da makarantar ya zauna a gida.

Akwai gidan da take aiki, Yaron gidan ya nimeta da lalata, ita kanta bata sani ba. Sai da ta ganta a Office din yan sanda, an rufeta, tayi tayi ta musu bayani amma ina sharri aka mata, haka ta bar Yaranta a gida ,babu kowa sai Allah, tayi kuka tayi bakinciki har cewa take ita da ganin wannan rayuwar da mutuwa tayi ya fi mata, akan wannan rayuwar domin tana cikin tasku. Tun safe da Yaran suka karya har rana bata dawo ba, har dare babu labarinta, haka Abdul Majid yake goyan Aryan idan ya gaji ya sauke shi. Kwana suka yi babu kowa a gidan sunyi kuka har sun yi shiru. Washi gari da safe suka tashi babu Mamansu. Har rana bata dawo ba, dalilin da yasa Abdul Majid ya fita bakin shagon unguwar kenan ya sato bread,. Babu wanda ya lura da halin da suke ciki.


Haka aka rufe shi da duka yana rungume da bread din, yaki sakewa sai dukan shi ake yi, makocin sune ya ga ana ta dukar shi, shine ya karbe shi. An farfasa mishi jiki. Mutumin da yake lura da shige da ficen su, yaga yau bai ga Mamansu ba. "Abdul Ina Mamanku?" Yana sheshekar kuka ya ce bata dawo ba, har lokacin yana rungume da bread din,. "Me yasa ka daukar musu bread." "Aryan da Amaan yunwa suke ji Hajiya bata dawo ba." Jikin mutanen da suka dake shi ne yayi sanyi. "Nawa ne kudin bread din?"
"Dari ce!" Biyan kudin yayi ya saka yaron a gaba har gida, "ina mamarku take aiki?"
"Ta can ne?"
"Tow ka jira ni ina zuwa." "Tow!" Gidan shi ya koma ya amso musu kunu da dumammen tuwo, ya kawo musu Aryan da Amaan suka ci sai da suka kusan cinyewa sannan suka koshi, Aryan ya koma ya kwanta sannan Abdul Majid yaci kadan ya bar musu, yadda Mamansu take yi ta ci kadan ta bar musu sauran....
~~~~~~~~~~~~~~
```Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136```

#Mai_Dambuje.
[2/17, 5:06 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*016*
Mutumin nan bai yi kasa a gwiwa wurin neman Mutanen unguwar tare da mai unguwa, ya zauna a tsakiyarsu ya ce musu. "Akwai matar nan yar kasar Nijar, tow gaskiya a da ina ganin mijinta yana zuwa, amma a yanzu an dauki shekara biyu ban ga mijin yazo ba, sanan ita kuma tana yawan fita aikatau domin ina yawan ganinta ta fita da sassafe ta dawo da la'asar lis, tow kada na kaiku da nisa Matar nan dai jiya bata kwana a gida ba, sannan ku yi nazarin idan mune ya zamu ji? Sannan yarinya ce domin bata kai talatin ba, don Allah ku duba lamarin."
"Hmmm! Waye ya sani ko yawon bin maza ta tafi." Inji wani mutum a wurin, tsawa limamin unguwar yayi mishi. "Mene ne hujjarka?" Sunkuyar da kai yayi, kafin liman ya ce. "A yanzu muje gidan, ko akwai yaron da zai fada mana inda take zuwa aiki." Haka suka mike bakiWayansu, suka tafi har gidan, sun samu Aryan yayi kashi ya b'ata jikinshi. Haka Mutumin farko ya kira Matarshi ta wanke su, sannan ta dauko musu kayan Yaranta, suka kasa sannan ta riko hannun Abdul Majid suka fito. "Abdul Majid!" "Hmmm!" Ya fada yana komawa gefe, domin har yau yana fama da rashin sakewa. "Kasan gidan da Mamanku take zuwa aiki?" Gyada kai yayi. "Ok Maman Luba tafi da sauran, bari ya kai mu inda take zuwa aiki."
Haka suka saka Abdul Majid a gaba, har gidan dake tana zuwa da shi yana taimaka mata da Aryan yana wasa da shi, koda suka zo gidan babu wanda ya yarda yayi musu maganar Sa'adatu, sannan babu wanda ya kula su, sai da yan unguwar suke gayawa musu ai tun jiya da hantsi yan sanda suka tafi da ita office dinsu.

Ba karamin kaduwa suka yi ba, domin kuwa har an rasa me magana, haka suka mai da Abdul gida, sannan wasu suka wuce kasuwa, wasu kuma suka hakura da kasuwa suka nufi Office din yan sanda nimanta. Musamman Baban Luba mutumin nan yayi halacci musamman da yake makocinta, haka suka yi ta yawo kafin Allah ya gajarce musu wahala, suka same ta goshin Magariba a wani Office din yan sanda.
A lokacin da suka je a bada belinta, kin sauraronsu aka yi, da suka nace aka kawo laifin da ake tuhumarta da shi na sata da yunkurin kisan kai. Shiru kowa yayi kafin, suka roki a basu ita tana da Yara kanana. Amma aka hana su, sai dai sun fito da ita, suka ga ko tsayuwa bata iyawa ga yunwa ga tashin hankali, haka Baban Luba ya tafi ya sayo mata tuwo hannu baka hannu kwarya haka take cin abincin.

Tana ci a lokacin hankalinta ya dawo jikinta, duk yadda suka so jin me ya faru, kunya da zurfin ciki ya hanata magana. Haka suka maida ita hankalin kowa ya tashi, sai da aka mai data ta zauna tayi ta kuka tana jin me yasa ta kasa magana. Haka ta kwana kuka.

Washi gari..
Gidan mutumin da take aiki suka je, dakyar da sannu sannu aka bawa mutumin hakuri sannan ya janye karar domin yace kotu ce zata raba su da ita, daga taimako zata kashe musu d'a da sata. Su dai tunda aka janye karar, suka yi godiya suka bar gidan. A can office din yan sanda, aka bada belinta, aka dawo da ita gida, Baban Luba shi ya fita can sai gashi da kayan abinci, ya kawo mata da dafaffen har da Yaranta. "Idan kina da matsala ki yi magana da Maman Luba, Allah ya tsare na gaba."
"Allah ya biya maka bukatarka na alkhairi, na gode." Ta fada tana kuka, haka ya bar gidan, sai da tayi wanka tare da sauke sallolin danke kanta, ta samu wuri ta zauna ta sakawa yaran abinci, suka ci banda Abdul Majid da yake manne a jikinta, yana kallon yadda take sharar kwalla. "Hajiya kici abinci man." Ya faWa kamar zai fashe da kuka. "Na koshi Alhaji!" Ganin taki ci yasa shima yaki ci. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, Washi gari ta tafi har gidan Baban Luba tayi godiya, sannan ta ce mishi. "Ina son zan fita da yaran, ga gidan."
Kafin Baban Luba yayi magana Maman Luba ta yi maza ta karSe zancen. "Ina zaki kuma?" "Ina son zuwa nijar ne, shine nake son fita muyi Bara ko za a samu kudin mota." Ta fada cikin matsanancin kunya, "Bara?" Suka hada baki, "ki je gida ki shirya gobe in sha Allah sai ku tafi, yau zan samu abokina Hamisu bazabarme na gaya mishi akwai fasinjar marad'i ko?" Gyada kai tayi, ya jinjjina kai ta koma gida, haka ta dawo gida, bayan fitar shi ta koma gidan ta cewa Maman Luba."idan kina da aiki kawo na rage miki."
"A'a Maman Abdul barshi." "Don Allah kawo ko wanki ne." Haka matar ta fito da wankin. Kafin azahar ta gama wanki, kuma kayan sun fita tass, ta shanya mata sannan ta basu abinci suka dawo gida, ita kan Maman Luba wani irin son Sa'adatu take, shi yasa take tsananin tausayinta. Tasan yarinya ce. Da dare Luba ta kawo musu abinci har gida, washe gari da sassafe makocinsu ya sakata a gaba, bayan ya gayawa me unguwa da liman, aka kaita tasha sannan suka bata guzuri me yawa, ta baro Kano zuwa marad'i. A lokacin da ta isa ta samu Alhaji Abubakar Abzin, baya gari a gidan ta zauna na tsawon sati daya, kafin ya dawo. Duk da tazo wurin shi da damuwa amma kuma tana ganinshi sai ta kasa fadar kome, ta koma kuka. Yana rike da hannun Abdul Majid, yake tambayarshi sai ya kalli Mamansu kafin yake magana, amma yaki fadar abin da ya faru. "Hajiya baki ce kome ba, sai kuka." Girgiza kai kawai tayi. Haka ya mike ya ce ta koma can wurin uwargidansa tunda dama a can ta sauka, Mutumin kirki, Washi gari ya tashi wani yaron shi ya je har Kano aka duba mutumin da ake bashi aika ya kai mata, ashe ya rasu, sannan dan aikan ya tafi har unguwarsu, anan yaji labarin abin da ya faru, kwana biyu tsakani sai gashi nan ya dawo da bayani, Alhaji Abubakar Abzin ya yi shiru. Sannan ya kira ta. "Me ya faru har aka rufe ki na tsawon kwana biyu?" Kanta a sunkuye ta ce mishi. "Babu kome Abba." Don a haife ya haifeta.

"Shi kenan, amma Mamman yana zuwa?" Hawaye ne suka zubo mata, ta girgiza kai. "Shi kenan." Haka ya fita a ranar ya bar marad'i, wato koda ya isa Niamey. FaWa suka shiga yi shida Alhaji Mamman kamar zasu yi doke-doke, kafin suka dawo Alhaji Abubakar Abzin ya gaya mishi halin da iyalinshi suke ciki. "fisabilillahi yara maza har uku fa, gasu nan duk da rashin kulawa amma yaran sun samu tarbiyya kaji tsoron Allah kafin ya tsayar da kai."
"Naji zan zo amma gaskiya Ya fada kuma sai yayi shiru, kafin yayi kwafa. Kwanan Alhaji Abubakar Abzin daya, suka juyo tare. Cikin farinciki yaran suka ga Babansu, sai dai Majid ya koma jikin Hajiya ya lafe, saboda kallon tsanar da Alhaji Mamman yake mishi.

Tambayoyi har da takardun ta, duk ta bashi sannan ya kalleta cikin isa ya ce mata. "gobe zaki koma Kano, ki sani ban baki damar kiyi karatu don jin dadinki ba, ban tara dukiya don yaranki su ji dadi ba, na tara su ne, don amfanin gobensu. Dole ki jajirce ki kuma koyi boye damuwarki, sannan kiyi hakuri da abinda kike da shi. Wannan shine abin da zan gaya miki ".
"Mun gode sosai hakan ma" ta faWa muryarta a raunane. "Kada ki kuma kawo karana." "Allah ya huci zuciyarka, in sha Allah haka ba zai kuma faruwa ba."
Haka ya kwashi Amaan da Aryan, ya tafi da su yawo, sai dare ya dawo dasu. Duk abinda ya kawo musu haka yace kada ya bawa Abdul, amma abin ka da Uwa. Sai da sauran suka yi barci ta tashe shi ta bashi ya ci, sannan ya kwanta. Tausayin Abdul take ji, gani take kamar tana da laifi wurin duk abinda ya same shi. A hankali take shafa kanshi har barci ya dauke shi, tana zaune a wurin Alhaji Abubakar ya shigo ya cewa Matarshi ta turata wurin Mijinta, haka ta shirya ta tafi, za a iya cewa wannan karon rabo ya kawo ta, domin kuwa washi gari ya juya ya koma ya bar kome nasu a hannun Alhaji Abubakar Abzin. Ita kuwa a ranar ta dawo kano da tsaraba me yawan gaske. Ta kaiwa gidansu Baban Luba, sannan ta kai na gidan Mai unguwa da Liman, don sune iyayenta.

Bayan tafiyarta da binciken da Alhaji Abubakar Abzin yayi, ya ji gaskiyar abinda ya faru. Ai kuwa ya maka mutumin da yasa aka rufeta a kotu, rikici babba aka yi ta yi kamar me, sai da dattawan unguwarsu suka saka baki, haka ya sama mata yanci, suna dawowa ranar Monday aka zo aka kwashe Abdul da Amaan suka tafi makaranta. Ba laifi zuwa yanzu ta samu dan nutsuwa, tana dan sana'a kuma abincinsu yana nan.
***
A can kuwa Tani tana zuba mulkinta yadda take so, bata yarda ta kuma cewa tana son zuwa ganin halin da Sa'adatu take ciki ba, domin tsoron abinda ya faru kada ya kuma faruwa, haka ta zauna tana zuba musu isa da mallaka.

Sannan a gefe guda ta mallake Nana sai yadda tayi da ita, kuma bata da katabus sai Abinda Tani ta ce, ana haka ta saka Alhaji Mamman a gaba ya saka mata danta Sajjid a makaranta tare da gaya mishi duk abinda yake so Sajjid zai mishi, ba sai ya damu da Abdul ba, fatanta kawai ya saka Sajjid a cikin Yaranshi. Amma mutumin nan yaki kula zancen. Idan ta dauko zancen zai ce mata yaji kawai don ta rabu dashi amma a ranshi baya jin zai yarda ya amshi Sajjid domin ba jininshi ba ne.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login