Showing 39001 words to 42000 words out of 100763 words

Chapter 14 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2865

aka tono da shi, ya tara dukiya me yawan gaske sannan aka fito dashi. Wannan abin ya bawa kowa mamaki, asibiti aka wuce da shi yayi sati biyu aka sallame shi, tare da kayanshi baki daya da ya hako a rami.
Aka dawo da shi Nijar, Aka karrama shi gwamnati ta bashi babban gida da fili anan Niamey. Sannan gwamnatin ?asar ta nemi ya sayar mata da abinda ya zo da su, ya sayar da kadan domin ya gina dukiyarshi saboda kusan rayuwarshi ya saka a hatsari ya samo dukiyar nan.

Kad'an da ya sayar din nan, da ita ya cigaba da gina katafaren kamfanin zinari, har ya kuma haWa gwiwa da kasar Mali ana shigo mishi da zinari, a lokacin bai wani karatun boko ba, amma kuma ya san kan lissafin kome, sai da ya samu shekaru uku da dawowarsa ya tafi ya nimo Danginshi. Ganinshi cikin wadata da nutsuwa yasa suka ta murna, har agadaz ya je domin an san ya mutu dole yaje ya nuna kanshi dan su san yana raye.
Yana zuwa Kanin mahaifiyar shi ya bashi auren Yarshi, Rabi duk da bai so ba amma haka ya amshi auren, domin yana niman macen da tayi karatun boko wacce zai ciccibeta ya dorata akan dukiyarsu, haka aka sha biki.

Tana shiga a burin shi tana fara haihuwar namiji, zai gina rayuwar yaron ta hanyar bashi ilimi me yawa da zai rike dukiyarsu. Sai dai kash tana fara haihuwa ta haifi mace, haka ya kara auro Fauziya itama tana shigowa mata ta fara haifa masa, haka ya hakura ya cigaba da kula da yaran da basu ilimi sai dai iyayen basu wani damu da ilimin ba, ana haka ya hadu da Harirah yar secondry haka yayi ta mata hidima, har ta gama itama dai ba wani abin kuzo ku gani ta yi ba,haka ya aureta.

Alhaji Mamman Ba'are, yana da wata dabi'a ita ce cacca, dake yana yawan shiga libya, a nan ya haWu da Alhaji Nasiru Wodabbe shima rikakken dan cacca ne.

"Yau gidan nan yayi baki,ga Alhaji Nasiru Wodabbe gefe guda Alhaji Mamman Ba'are, yau wasan sai tafi koda yaushe armashi da karsashi" domin kowa yasan kowannensu gwani ne a harkar cacca.
"Idan nayi nasara akanka Ba'are me zaka bani?" Murmushi Mamman Ba'are yayi ya ce mishi. "Wodabbe idan kayi nasara a kaina, ka kwashe kome har da kayan jikina. Idan nayi nasara akanka kuwa zan bika har garin na dauke shanayenka!"

"Na yarda!" Inji Nasiru Wodabbe, shima kuma Mamman Ba'are ya ce mishi."na amince."
Aka shiga buga cacca kamar da wasa, Nasiru Wodabbe ya shiga nasara akan Mamman Ba'are, har dai da ya cinye shi kome hatta wandon jikinshi sai da ya saka a cacca. "Mamman Ba'are kwashe kayanka, idan ka haifu namiji ka saka kamfaninka " kurawa Alhaji Nasiru Wodabbe idanu yayi, kamar ya zagi Uwarshi. "Zan saka amma ka sani idan nayi nasara ba zan maka da wasa ba."

"Na amince," saka kamfanin yayi cikin murna da kwarewa Nasiru Wodabbe ya fara buga wasa, tun a zagaye na farko ya fahimci kamfanin Ba'are GOLDEN EMPIRES ba sa'ar sa bane, domin a wasan farko Ba'are ya dawo da kayanshi wasa na biyu ya dawo da kome hatta zobensa na azurfa sai da ya dawo da ita. Murmushin ya?e yayi suka cigaba da wasa, aka cinye kome cikin takaici ya ce mishi. "Na saka yar Yayana Sa'adatu."
Shiru Mamman Ba'are yayi yana kallon Nasiru Wodabbe,"Me yasa baka saka yarka ba sai yar dan uwanka." "Da ina da Y'ar
ba zan saka Sa'adatu ba, domin darajarta tafi karfin dan cacca irinka,na gaya maka."
Tab'e baki Mamman Ba'are yayi yana dariya,"bari na gaya maka ko gwal ce da kanta, bata fi karfin dan cacca irina ba sai ma tausayinta da naji da ta samu Baffa irinka."
Cikin fushi Nasiru Wodabbe ya kara buga wasan hannunshi, cikin rashin sa'a ya fadi Mamman Ba'are yana bugawa sai gashi yayi Nasara, "Na sameta kana da wani abu da zaka fanshe ta?" Idanunshi ne ya kad'a jajjur. "Kai tsinanne yarinyar da babu ruwanta, yarinyar da gwamnati dauki nauyinta saboda kasancewarta hazika, me ilimin addini da na boko, shine zaka samu a banza ba zan baka ita ba, ni na sakata a cacca amma ka fara ketare ni kafin ka isa gare ta."
"Ba zan ketare ka ba, yadda ka saka ta a cacca haka zaka bani ita har da kome nata." Shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are, bai tab'a zatan Allah zai bashi irin macen da yake so ba, sai da ya buga kamfanin shi na gwal a cacan sai gashi Allah ya bashi ita a lokacin da bai zata ba.

Kafin wani lokaci rikici ya barke a tsakaninsu, sai ga manyan maza da bawa hammata iska, dakyar aka raba su domin har jami'an tsaro sun shiga lamarin, Alhaji Mamman Ba'are da yaga samu zai ga rashi ya daka tsalle ya ce ai ta zama tashi tunda wasa aka buga, wasa gaske dai yaki karbar kome ita Sa'a kawai yake so. Ganin haka yasa Alhaji Nasiru Wodabbe ya amince da shawarar da aka bashi a office din yan sanda aka daura auren Sa'adatu Aliyu Wodabbe da Alhaji Mamman Ba'are, a Office din yan sanda, da sadakinta aka bashi yana ji yana gani Alhaji Mamman Ba'are ya wuce tare da Waukar yan rakiya har gidan Nasiru Wodabbe, ganin kamar Mamman Ba'are bai da hankali yasa shi isa gidan kafin su isa, yana shiga kamar wanda aka wurgo shi, dama a Libya yake da zama da Matarshi da yar rokonshi. Sakamakon wani karamin abin da bai kai ya kawo ba, ya baro kasarshi.

"Sa'ade ki yafe min, na miki rashin adalci. Kiyi hakuri in sha Allah gobe zaki yi dariya." Ya fada yana dauke kanshi ya kalli Matarshi, Raliyah. "shiryata za a zo Waukarta na aurar da ita " "ka me?" Ta tambaye shi jikinta yana rawa. "Eh na gaya miki na aurar da ita, ina ga ai da Hausa na fada ba larabci ko fillanci ba."
"Amma me yasa? Kasan Lamido yana can yana jiranta."
"Haka Allah ya nufa ita ba matar shi ba ce." Ya dawo kan Sa'aden ya riko hannunta. "Kinsan ba zan tab'a cutar dake ba ko?" Gyada kai tayi kanta a sunkuye. "Tow kiyi hakuri kin ji." Ya fada yana Hadiye kukan da ya zo mishi, haka ya hada har da kome nata, ya tsaya Raliya ta shiryata.........
(Hmmmmmmmm ku bi alkalamin ?addara)
#Mai_Dambu
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTU?ARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....

*014*
Tana fito da ita ya kalli yarinyar, kafin ya riko hannunta har waje. Ya ja Alhaji Mamman Ba'are gefe. "Gata nan, ka da ka duba lalacewar da nayi ka hukunta ta da shi, wallahi billahil azim mahaifinta shahararren Malami ne kuma attajiri ne, soyayyar da take min tun tana yarinya yasa ni tawowa da ita yawon bariki, Sa'adatu bata rasa kome ba, hatta abinda zata ci Ubanta ya tanada mata, wallahi rashin ji ya sani fitowa da ita, Ba'are don Allah kada ka cutar da ita babu ruwanta."
Duk da zuciyarshi ta motsa akan yadda ya mishi da farko amma kuma yadda yake gaya mishi inda yarinyar ta fito sai yake ganin kamar bai mata adalci ba, amma halin Nasiru Wodabbe yasa shi jin ko kad'an baya tausayin yarinyar domin baki daya bata wuce shekaru goma sha shida ba, haka ya kad'e babbar rigarshi ya ce mishi. "Nasiha kake min ko me? Ka sani babu abinda ya dame ni, daga yau har zuwa ranar da zan gama amfani da ita a caca na ciyo ta."

"Na roke ka kada ka cutar da ita, don Allah. Ita bata maka kome ba ni nayi laifi." Ya fada yana niman durkusa mishi. "Abbati kada ka durkusa mishi, Indai akaina ne wallahi bana tsoron duk abinda zai faru kuma bana fatan naga hawayenka. Duk abinda kayi a kaina Abbati daya ne, ba zaka tab'a cutar dani ba." Cikin wani irin tashin hankali ya riko hannunta. "Ba zaki fahimci me na aikata ba, sai dai duk rintsi kada ki manta da Allah." "Ke muje, na gaji da wannan wasan kwaikwayon naku, sai kace uban wani ne yasaka shi saka ki a caca." Haka Alhaji Mamman Ba'are ya sako ta a gaba har inda motarshi take. A lokacin yana da wani aboki wanda suka taso tun suna agadaz daga baya shi da iyayenshi suka koma marad'i da zama. Wato Alhaji Abubakar Abzin.

Duk da shi yayi karatun boko, can marad'i yayi tunanin kai Sa'adatu domin a can zata fi sakewa. Haka kuwa ya faru domin daga Libya kai tsaye marad'i ya wuce da ita, a lokacin da Alhaji Abubakar Abzin ya ganshi da ita, ya sha mamaki amma sai ya nuna ba wani abu bane, domin yasan kulafuncin niman haihuwar d'a Namiji da yake, bai kai burin shi na niman mace mai ilimi ba, sai gashi ya samo yarinya karama me ilimi da nutsuwa.

Bayan sun kebe da Alhaji Mamman ya labarta mishi duk abinda ya faru. Sannan ya mika mishi takardunta, ya duba sosai ya ce mishi. "Kai ne dan boko, duba min ta ina yarinyar nan zata tayani rike kamfani na?" Ya tambaye shi yana leken takardar.
Gyaran murya yayi kafin ya ce mishi. "Yarinyar bata da matsalar kome, sai dai tana da fahimta ta bangaren kimiyya, idan da a zabinta zaka tambaya ba zai wuce ta ce zata karanci likitanci ko unguwarzoma. "

"Tow ina niman wanda zai rike min kamfani ina zan barta ta tafi asibiti, duba dai da kyau." Ture takardar Alhaji Abubakar Abzin yayi ya ce mishi. "Maganar gaskiya, idan har kana son ta zama yadda kake so, dole sai ka nisantatta da wannan rayuwar, ka kaita wani wurin ta rayu tayi karatu. Domin idan tana cikin matanka da danginka kishi da damuwa ba zai barta ba, sannan ita ce karama kowa zai zo mata da fitina da ba?in kishi. Don Allah ka nisantatta da gidanka ban ce kada ka kaita ba, zaka iya kaita amma kuma dole ka rabata da su. Domin kuwa matu?ar tana cikinsu ba zata yi karatun ba, kuma ba zata baka abin da kake so ba, karshe ta haifa maka yaran da kake so babu ilimin da kake bukata, zaSi yana gare ka." Ya faWa mishi yana gyara zaman shi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mishi. "Kana nufin na dauketa daga cikin gidan kenan?"
"Duk yadda yayi maka."
"Shi kenan zan d'auketa amma ina zan kaita?"
"Nigeria, kano idan ka kaita can in sha Allah zata dawo maka da abinda baka zata ba."
Shiru yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya, "ya zan yi da Nana?" Shiru Alhaji Abubakar Abzin yayi kafin ya ce mishi. "Nana ka Wauke kai akan wani abun da take amma batun yarinyar nan ka tsaya kai da fata ka bata ilimi idan ba haka ba, gidanka duk jahilai za a ayi ta haifa maka. Karshe ga hanyar da za a ci abinci amma kuma babu damar cin abinci, sai dai a kashe kamfanin a zauna a haka. Amma a ?alla aka samu mace daya da maza biyu zasu jagoranci kome da yardar Allah."
"Shi kenan in sha Allah haka za ayi." Ba don Allah ya bashi aboki na gari ba, tabbas Alhaji Mamman ba'are haka zai kaita cikin iyalinshi babu wani tsari ko plan. Sannan Alhaji Abubakar Abzin ya kara mishi kwarin gwiwa na ya tsaya akanta kai da fata, domin yasan Mahaifiyarshi ba karamar shu'umar mace ba ce, idan bata son mutum. Sannan yana son yadda yarinyar take da nutsuwa koda Allah zai bata haihuwa da Alhaji Mamman Ba'are, ya kasance Yaran sun fita daban.

A wannan takin Amaryar Alhaji Mamman Ba'are ita ce mace mara yara dayawa, amma daga Rabi har Fauziya, a ?alla suna da yara kowaccen su shida zuwa bakwai , domin gidan gasar haihuwa ake kamar yadda suke hango iyakar kokarin mijinsu.
Sannan Nana ta kara musu zafin kishinsu, ta hanyar gasa musu magana da cewa "Ni duk macen da bata haifa min jika namiji ba, ai tayi a banza tunda mace bata gadon arziki." Wannan ya kara musu kwarin gwiwa daukar ciki suna haihuwar yara rututu, don ma Uban yana tsaye akan Yaran. A gefe guda ga kannenshi da suke hararar dukiyar, wanda ya sani sarai kawai dauke kai yake akan su, fatanshi kada ya bar duniya bai samu wanda zai rike kamfanin ba.
Haka ya tawo Niamey da Sa'adatu. Asalin Bafulatana, kana ganinta kasan Bafulatana ce kasancewarta doguwa sirirya. Ga kyau ga farar fata gata da wata irin kunya da kamun kai. Haka yasa Alhaji Mamman Ba'are, kware mata daga yan kwanakin da suka yi a hanya, ya fahimci yarinyar mace ce guda, haka yasa yayi ta nan nan da ita har suka iso gida.

Sannan itama bata takura kanta ba, tunda tasan ba zata iya sauya ?addarar da ta same ta ba. Haka suka isa kantamemen gidan alfarma. Wanda ya gaji da haduwa kamar ba gobe, suka shiga cikin gidan motar tayi parking ya fito itama ta fito. Cikin gidan ya nufa da ita, tana baya yana gaba duk inda ya wuce gaisuwa ake mika mishi har ya nufi falon Nana, zama yayi a saman daya daga cikin kujerun falorn, ita kuma Sa'aden ta zauna a kasa, kanta a kasa. "Ka dawo Mai Babban suna, ya hanya ya kasuwar?"
"Alhamdulillahi! Kasuwa tayi albarka tunda har da mata na samu." Ya fada yana dauke kai yana kallon Sa'adatu. Kalman Alhaji Abubakar Abzin yana dawowa mishi. "Don Allah kada ka zubar mata da mutunci ta hanyar gayawa mutanen gidanka a caca ka samo ta."
"Ban gane ba?" Ta tambaye shi.da alamar bata ganen ba, gyara zama yayi ya gaya mata kome amma ya roketa da don Allah kada sauran matanshi su sani, Sa'adatu a caca ya samota. Kuskuren shi kenan bayan Alhaji Abubakar Abzin ya roke shi, shi kuma yana tunanin Nana Uwa ce da zata iya rufa mishi asiri, sai dai yayi kuskuren domin Nana bata cikin irin wadannan iyayen.
Kiri-kiri ta shafawa idanunta toka, ta shiga bala'i da hayagagga. Akan me zai auro mata mugun iri, maza ya fice mata da ita daga gida, kada bala'i ya fado musu cikin dukiyarshi mai tsafta.
Fadar Nana da ihunta yasa matan gidan sanin Alhaji Mamman Ba'are ya karo aure kuma matar Nana bata yi na'am da ita ba. Haka sukayi ta bala'i a gidan, ya wuce da Sa'adatu bangarenshi, ya zuba mata idanu.
"Kiyi hakuri laifina ne, da ban gaya mata ba da haka bai faru ba." Dake tana da hakuri haka ta sunkuyar da kai ta ce mishi. "Ba kome Uwa ce bata laifi." Wannan abin da tayi ya kara mishi kaunarta da bai san lokacin da ya faWa ba,
Haka zaman gidan ya kasance, idan ta fita tsakar gida, Hajiya Rabi da Yaranta su rufeta da duka, koda kasheta zasu yi idan Nana ta fito cewa take. "shegiya jinin matsiyata, Ubanta da tsiya ya masa katutu a caca ya sakata. Ku kashe banza da haihuwar su gara mutuwarsu."

Harirah wacce ta kasance itama yar babban gida ce, sannan Yayanta babban lauya ne, yasa take iya shiga fadar Sa'adatu, sau biyu tana kwatarta a hannun Hajiya Rabi da Yaranta. Sun mata dukar kawo wuka, ta suma ta ce musu. "Wallahi idan yarinyar nan ta mutu sai na gayawa Yayana ya nima mata hakkinta kuma daurin rai da rai za a muku kun san dokar Nijar ai." Jin haka yasa suka rage dukanta, aMma hantara da wulakanci ayi abinci a hanata. Karshe ma sai wanda yaran suka jagwalgwala shi za su bata, ga bakar magana idan ta bukaci wani abu.

Shi Alhaji Mamman Ba'are bai san me ke faruwa ba, domin bata tab'a gaya mishi halin da take ciki ba, amma kuma tana matukar cutuwa, sai Harirah ce ta gaya mishi abin da suke mata, ta ce mishi. "Idan baka yarda ba, ka tafi ka dawo idanunka ya gane maka, nima don ina gidan ne aka rage dukanta amma matukar bana gidan tow sai abin da ya karu "
Haka ya kwana cikin mamaki, domin koda ya tambaye ta, shiru tayi mishi kanta sunkuye tana wasa da yatsunta. Washe gari da safe, suka fita daga shi har Harirah.

Lokacin har Sa'adatu ta fito tana share gidan, Yar Hajiya Rabi Babban wacce bata wuce shekaru goma ba, ta zo wucewa ita Sa'adatu bata sani ba, ta zuba mata shara. Ai kuwa yarinyar ta daddage ta zuba mata dundu a baya, tana ihu. ""Mama Mama kin ga wannan matsiyaciyar da aka auro a caca

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login