Showing 15001 words to 18000 words out of 100763 words

Chapter 6 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2875

wasa da sallah, koda na idar addu'a nayi sosai sannan na tashi zuwa bakin gadon. A hankali nake jin wani irin kamshi yana tashi me matukar dad'i da sanyi, ware ido nayi ina kallon Zuzu. "Zuzu kamshi me nake ji?" Kamshi kuma?" Gyad'a kai nayi ina kallonta. Itama ni take kallo, dube dube muka shiga yi, a hankali Zuzu ta d'aga pillow da yake gadon, wani ?aramin hanky ne yake wannan azabebben kamshi.
"Mtsew ji abin da yake kamshi." Na ja tsaki, ina kokarin gyara zama, fari ne kal a hankali na warware. Gefen zanen wani babban gida ne kamar masarauta gashi nan kamar castle. An rubuta BGE.
"Mene ne ma'anar wanan kalamar?" Na tambayi Zuzu. "Adda mai tuwo tuwo!" Ta fada min hankalinta kwance. "Amma dai ke dai anyi yar banzar Y'a."
"Tow shi kenan sunanshi Fadimah Zahrah Buba Shad'ari." "Bana son b.... uba." "Na waye? Nawa ko naki ko najin dadin bakinki?" Abinci ta saka min kaWan, duk da dama aikin ai ba wani aiki na tashin hankali ba ne, a hankali nake kurbar shayi, ina kallonta. "Zuzu!" "Na'am!" Ta amsa tana kallona. "Kinyi al?awari ba zamu tab'a cutar da juna ba?" Na mika mata hannuna, "Me yasa kika bukaci haka?" Ta tambaye ni, murmushi nayi ina kai abinci bakina, a hankali na d'ago kai ina kallonta. "Ban sani ba, amma kuma nasan dai wata rana zamu iya cin amanar juna."
Amsar kofin hannu na tayi da plate Win,ta ajiye, a duk lokacin da tayi haka nasan me take nufi. "kin san an min aiki." Na faWa idanuna rau-rau. "Mtsew! Kin ci sa'ar ciwon jikinki da kin sha mamaki."

Dariya nayi mata, sannan na cigaba da karyawa ta, har na gama ta balla min maganin da na gani ta Ciro a lock din gadon ta mika min. Da ruwan tea na sha ina son tmbayarta Addah amma nasan halinta bai zama dole ta bani amsa ba.
"Ya Addah take?"
"Lafiya lau!" Kallon fuskarta nayi naga kamar a dakile. "Wani abu ya faru ne?" "A'a." Ta fada tana leka wayarta, kawai na sha jinin jikina haka kawai Zuzu ba zata sauya ba. Sai na share kawai ban ce mata kome ba.
Tuna abin da ya faru a komawarta gida yasa baki daya, ranta ya kara b'aci da maganar Zahrh
Lokacin da ta koma gida, ta samu Addah tayi bakon wani mutum, tunda ta gansu a dakin Addah tasan mutumin ba na alkhairi ba ne, duk da ba yau din ya fara zuwa ba, sai dai kuma zuwan shi na yau kamar niman shi aka yi, shi din d'an bori ne. Haka yayi ta tsalle yana ihu, kafin can ya fara gyatsa. Ya fashe da dariya, yana nuna Addah da hannu. "Tabbas baki da arziki a jikinta a yanzu, sai gaba zaki ci arzikinta sama da yadda kika zata. ?addara ta hadata da shi, maza ki nisanta ta daga wannan duniyar zuwa wata duniyar, domin kuwa kika sake suka kuma haduwa ba zaki kara morarta ba har abada."
"Nazimu ya zanyi? Ita Zulaihah bata da gobe ne?" Ta faWa a hankali. Gyatsa ya sake yana dariya. "Gobenta yana manne da yarinyar da take asibiti." A dame ta kalli Nazimu ta ce mishi. "sauran yan matan fa?" "Hmmmm! Itace inuwarsu."
"Babu yadda za ayi a mallake min ita?" Shafa gemunshi yayi ya ce mata."ba zan iya wannan aikin ba,lokaci na zuba da zaki amfana da rashin haka, idan aka mallaka miki ita ba zaki tab'a samun biyan bukata ba."
"Nazimu kace na dauketa daga nan?" Gyad'a kai yayi yana gyatsa. "In sha Allah wani sati zamu wuce Taraba!"
"Dakyau. Ki nisantatta da nan domin zai bincikota."yana gama fadar haka ya fara kwara amai, nan Addah ta fito ta gaya musu zasu tafi Taraba, shiru kowa yayi a cikinsu. "Addah kinsan muna zuwa za a fara maganar munki aure fa."
"Ba zamu wuce kwanaki uku ba, tunda zamu bi motar dauko shanu ne,iya kwanakin da zamu yi uku ne, idan kuma kuna son zama anan shi kenan "
"A'a zan tafi naga Yakumbo na kwana biyu ban ganta ba."inji Ummi,
"Nima zan je na ga Nenne na!......
#Thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

*ZINARIYAR MACE?&*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo=?? Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
*006*
Juyawa tayi ta kalli Zulaihah,kafin ta ce mata. "Baki da ra'ayi ne mu barki anan?" Murmushi tayi iyakarshi lebbenta. Ta ce mata. "Ina da ra'ayin idan na tafi nima ba zan dawo ba, aure zan yi domin na samu mijin aure " dariya Addah tayi sannan ta ce mata. "Ta yaro kyau take bata karko, Allah ya kai mu zulai." Har ta juya zata tafi ta ce mata. "Ki sani matukar muka tafi kika zauna a can, duniya sai ta san me kike aikatawa balle mijin da nake da yakinin shi kike hari." "Addah barazana kike min?" Itama ta mike tsaye, tana kallon Addah. "Kashedi nake miki, kuma idan na miki barazanar ai ba laifi ba ne. Saboda ai da kome nawa kika kawo haka, sannan idan nace zan miki barazana ba laifi ba ne." sannan ta juya ga Ummi ta ce mata. "Ko nayi laifi a cikin wannan maganar?" Girgza mata kai suka yi, domin Allah ya zuba musu shakkar Addah idan ka cire Zulaihah, da sam bata shakkarta, Wakinta ta koma ta kalli Nazimu. Kamar zata fashe da kuka. "Yarki bata da matsala, halayyarku ce da bambanci, ita ba zata iya abin da kike yi ba, domin tana da kirki da nutsuwa shi yasa halayyarsu da jininsu ya hadu da Yarinyar can, don haka ina baki shawara da kada ki sake, ki takura Yarki domin duniya ki sarara mata."
Gyad'a kai tayi tana faWin. "Itama tana da farin jini fa." "Eh mana, amma kuma kila yawan takurar da kike mata zaisa ta iya rabuwa dake na har abada."
Dafe kirji tayi tare da cewa. "Don Annabi?" Wannan ne karon farko da Addah ta kira sunan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama,domin ba dabi'arta ba ne kiran sunan Allah. Yadda Nazimu yayi kasa da murya yasa ta nutsuwa tana sauraron shi, sannan can yana gamawa ya mike ya fita, Munaisah ta shiga dakin ta gyara, "Ya gaya min maganar chef yace wai yau ki saka wannan turaren zaki samu alkhairi sosai a wurin shi."
"Kai Addah ni ai mota nake son ya saya min." "Banza sakarya motar kaniya, idan kika samu kudi saniya zaki saya da shi a fara ajiye miki."
"Kuma haka yayi fa, Addah ya batun Zahrah?" Tsaki tayi tana tab'e baki, zata tafi can ta hadu da wancan dan iskan Yaron, su kare kalau ni ina zargin anya Yaron nan bai gama lalata Zahrah da take jin ba zata iya wani abu sai da shi ba." Addah ta faWa tana kallon Munaisah, "Uban waye ya sani, shegiya munafika ni ban son tayi aure domin haka zai saka a samu a gaba da munki aure sai zaman bariki." Shiru Addah tayi tana kallon Munaisah ta sake murmushi ta ce mata. "Da ni kuke zancen, ki bar kome a hannu!"
Daidai shigowar Zulaiha. "Wa makaru wa makrallahi wallahu khairar makiri." Tana fadar haka Addah ta zuba mata idanu, "zan tafi asibiti."
"Allah ya tsare." Juyawa tayi ta fita, amma ranta soye yake...
"Ke tunanin me kike yi ne haka?" Tab'e baki tayi tana faWin. "Babu kome!" Ta fada tana kallon wayar. Ba zan iya ganinta cikin wani yanayi na Kyaleta ba, don haka na ce mata. "Zuzuna gaya min!" A hankali ta d'ago kai tana kallona kafin hawaye ya zubo mata."Zahrah kin ji dadinki,tunda kike baki tab'a zina ba, sannan baki tab'a yarda kin lalata tarbiyyar da Kawu shad'ari ya miki ba, Zahrah wani sakayya zan bawa mijin da ya aure ni?" A hankali ta fashe da kuka, sosai tana yi tana karawa. "Kada ki manta Allah xai baki mijin da zai kauna ce ki a duk yadda kike, kin ga yanzu da kin yarda kin amince kin koma diplomar nan, ai da yanzu saura watanni zamu gama, na gaya miki ba zina yake bada abinci ba, a'a yarda da Allah, Zulaihah kin bi na Addah kina lalata gobenki, bayan su mazan abin da yake jikinki suke bi idan suka gama dake zasu gudu."
"Ya zanyi?" Ta fada cikin kuka, tana kara jin tsanar kanta. "Kiyi hakuri kawai." Na fada mata, a hankali ta warware min tafiyarmu taraba, amma kuma tana jin addah tana kulla min sharri. Murmushi nayi na ce mata. "duk abinda Addah zatayi, ba zata hana Allah ikon shi ba, don haka ta gama abin da zata yi saura ta barwa Allah ikonsa."
Daga haka muka cigaba da hirarmu.
**
Kwana biyu mai kyau aka yi ana bata kashi a tsakanin, Captain da yan tada kayar baya, kafin aka fitar da su Commodore Magaji Abba, wanda yaci bakar wahala. Sannan sojojin ruwa da na kasa suka kame sauran yan tawayen aka tafi da su, a daren ya dawo gida a gajiye anyi anyi ya tsaya a asibiti amma ina, domin shima akwai rauni a jikinshi, yana shiga ya samu Aryan yana kwance a falon. Wucewa dakinshi yayi ya nufi ban daki ya shiga cire kayanshi, yana gamawa ya ga inda aka harbe shi biyu saboda bullet proof da ya saka ne basu ji mishi rauni ba, wanka yayi ya fito ya sha magani, ya sauke salolin da yake kanshi. Sannan ya fito ya hada tea ya sha, kafin ya dawo daki ya kashe wutar gidan baki daya, akwai yarda da Amana a tsakaninsu da duhu.

Karfe biyar na asuba ya farka, ya nufi ban daki yayi wanka da alola ya fito falon suka yi sallah,a lokacin an fara ruwan sama. Kitchen Aryan Mamman Ba'are ya wuce ya hada musu abin karyawa. "Kasan yau zamu bar garin nan." "Eh! Amma ai ana ruwa." Kallonshi Aryan yayi kafin ya ce mishi. "Zamu wuce Enugu a can muke da jirgi zuwa kano."
Haka ya zauna ya ci abinci, suna hira sama-sama. "Ya Amaan?" Tab'e baki yayi yana faWin." Yana nan." Daga haka dukkansu babu wanda ya kara cewa Uffan. Har suka gama, Aryan ya shiga dakin Majeed yayi wanka ya shirya sannan ya zo ya kwashi kayansu, yafita da su. "kana nufin kwana biyu da kayi baka fita ko ina ba?" Tab'e baki yayi irin abin ya zame mishi jiki ya ce mishi. "Ina zan leka? Gari kullum ruwa, da nasan haka ne, ai da na tawo da Sanayah!" Shiru yayi yana kallon yadda yake shirya kome. Bayan ya gama shima ya koma ya shirya tsaf cikin Kananun kaya, suka rufe gidan bayan ya kwashe kayan abincin ya rubutawa Emmanuel, yayi amfani da shi. Sai da suka fara zuwa headquarter yayi sign sannan ya leka asibiti ya duba Magaji Abba Chindo, da yake zaune ana wanke mishi ciwon shi, zama yayi bayan an gama nurse din suka fita ya amshi sauran kayan aikin ya cigaba da gyara mishi ciwon. "Ba na son na kuma maimaita maka abin da ya wuce, amma zan gaya maka gaskiya yarinyar nan da ka saka a bi sawunta ni na taimaka mata, ba don kome ba sai don na kubutar da kai daga sharrin zina. Nasan kayi nisa amma ka gwada barin shi zaka fahimci abin da nake nufi. Ni zan wuce ?asarmu, ka sani ba wai bamu da inda zan yi aiki ba ne, sai dai wannan karon idan na tafi ba zan dawo ba,na bar maka ?asarku na koma aiki a babban headquarter Naval na French." Daga haka ya mike zai fita daga cikin dakin. " tow sai me? Bayan sai da na zama nakasashe zaka gaya min na daina zina? Sun kashe min gaba wadancan karnukan."

"Zina ya janyo maka haka." Daga haka ya juya ya fita, bai samu Dr Umaima ba, sako ya bar mata tare da tura mata kuWi, sannan ya fita daga asibitin suka bar garin ma baki daya.
***
Ranar da na cika kwana shida, aka sallame, Doctor Umaima tazo tare da mika min jaka. "Gashi akwai ticket na jirgi zuwa Yola, daga can zaki samu motar taraba. Don Allah ki koma gaban Iyayenki ga wannan kuWin inji Captain ya ce a baki kuma yana bada hakuri da abinda ya faru. Shima ba a son ranshi ba ne."
Murmushi na sakar mata, ina faWin. "Duk wannan kuWin?" "Akwai matsala ne?" Girgiza kai nayi, sannan na ce mata. "Ko zamu je banki a tura min kuWin." "Wani bank ne?" "Ecow bank!" "Me yasa sai bank din?" Saboda idan na koma zan tafi niman Mamana ne ne a Kamaru.". "ok muje!" "Gaskiya kin yi dabara, yadda Adda ta shirya wulakanci tana ganin kudin nan zata raba ki da su."
Murmushi nayi na wuce muka fita, da taimakon Aunty Umaimah muka tura kudin account dina, sannan suka sa ni lallai sai na yi welcome back din layina. Bayan nayi na sayi wata yar ?aramar wayar bani da buri akan babbar waya. Haka yasa nake rayuwata da yar karamar waya abina.

Lokacin da muka zo gida, na samu su Addah sun gama shirin tafiya. Koda na gaya musu ni jirgi zan bi sai suka yi shiru, Zulaihah itama ta kira wani sugar daddy dinta ya tura mata kudin ticket, sai gashi baki Waya sun biya har da Addah da Ummi. A daren muka bar garin fatakwal. Muka wuce garin Yola. Mun isa wurin ?arfe daya na dare, don haka muka kwana a masallacin da yake cikin airport din, gari na wayewa muka fito tare shiga kasuwa muka yi sayayyar tsaraba, sannan muka dauki hanyar taraba.

A hankali muke tafiya, hankalina yana kan wayar hannuna, na turawa Sabiru sakon gamu nan muna hanya, amma shiru bai dawo min da ansa ba. "Ya dai Zahrah?" Tsaki nayi ina yatsina fuska."Sabiru bai kira ni ba." Juyawa Addah tayi tana kallonmu, fuskarta dauke da murmushi. "Allah ya sa ba halin yan maza zai miki ba." Shiru nayi ban iya magana ba, amma tabbas akwai wani abu a kasa, haka kawai Sabiru baya kin daukar kirana ko sakona ya gani.
Wai ma kun san wacece Ni?
Fadimah Zahrah Buba Shad'ari, shine cikakken sunana. Mahaifina Bafulatanin taraba ne daga karamar hukumar Takum. Gari ne da ya hada makiyaya da manoma.
Alhaji Shu'aibu Jauro shine kakanmu dattijon arziki, mutumin kirki da babu biyun shi, Allah ya mishi rahama. Domin ya rasu tun ina da shekara shida a duniya, amma ba zan manta alkhairinshi ba.
Addah ita ce Babbar yarshi, kuma kangararriya mara jin magana. Wato ana cewa albasa batayi halin ruwa ba, hakan ce ta faru da Addah domin bata dauko halin iyayenta ba dukka biyu, sai Baffa'm wanda shine d'a na biyu da yake bin Addah, mutum ne me hakuri kawaici da Dattaku. Baffa'm yasan darajar kanshi da rayuwarshi. Mutum ne da yake da ilimin addini sosai, sai dai bai samu halin yin ilimin boko ba, sai ya saka a ranshi matukar yana raye Yaranshi sai sun yi karatun boko, wani abin haushi. Nenne Matarshi kuma uwargidansa, babu ruwan ta domin har wurin ardo ta kai Baffa'm don yace sai yaranshi sun yi boko.
Haka ya hakura dake yana tafiya da shanu cirani, musamman yankin Gyambu da yake da yalwataccen yanayi me kyau, yana zuwa yayi watanni sannan ya dawo da su. A irin wannan tafiyar ne ya hadu da Mamana domin tafiyar ta kaishi har kamaru, a can ya aurota ya kawota. Lokacin Munaisah tana da shekaru biyu a duniya.

Tunda Baffa'm ya auri Mamana, mutanen gidan suka sakata a gaba, wai ita Rumada ce wato bayin fulani, duk da kana ganin Mamana kasan yar babban gida ce, domin duk rugar mu babu macen da take sanye da zinari a kunne sai ita, sannan take gaya min ina Yarinya su Mahaifinsu kana cika shekaru goma a duniya kake fara zuwa aikin hajji, daga nan duk Shekara kana tafiya Umara. Wannan yasa duk yan gidansu suka je aikin Hajji.
Baffa Modibo shine ke bin Baffa'm, sai dai mutum ne mara kirki,haka yasa har da shi a cikin masu musgunawa Mamana. Haka tayi ta rayuwa a kuntacce, a lokacin da aka haife ni kuncin yayi yawa, domin a lokacin Addah sun dawo da Mijinta ya saketa, haka ta zo ta saka Mamana a gaba da fitina da tashin hankali. Har zuwa lokacin da ta samu wata kaw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????arta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login