Showing 48001 words to 51000 words out of 100763 words

Chapter 17 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2861

Haka tayi ta kokarin lallai sai yaron, ya zama wani abu kai babu wanda ya isa yayi mishi fada balle tsawa. Ga rashin kunya da fitsara.
****
Tunda suka dawo ta fara laulayin cikin Jamilah don ma babu wani wahala, amma kuma tana yawan kwanciya. Saidai da sauki,haka taci gaba da rayuwa har Allah ya sauketa lafiya, ta samu yarta mace, Kyakyawa da ita, haka yasa ta saka sunan Yafendo Jamilah.

A lokacin ba laifi abinci da sakon yana samunta, haka tayi ta renon Jamila, amma ta turawa Alhaji Abubakar Abzin sakon ta haihu, shi kuma ya turawa Alhaji Mamman Ba'are, bai bi ta kanta ba, sai bayan shekaru biyu, rabon Anisah ya kaishi Kano, a lokacin Abdul Majid ya kusan gama primary, a wannan zuwan da yayi ne. Ya kama yaron ya mishi mugun dukar da ya suma saboda kawai an kawo kararshi wai ya dauki kudin wani me shago, ya mishi wannan dukar, ya tura shi gidan horar da kangararun Yara,. Wani abin tashin hankali ya dauke Hajiya da sauran Yaran suka koma Niamey. Suka bar Abdul Majid, da yayi fama da jinya ga cutarwar yan gidan, duk wanda ya fika ?arfi zai zalunce ka, sannan yara ne masu banbancin hali, har da marasa jin magana masu luwadi, sai dai tunda suka barshi Hajiya ta bar amanarshi a hannun Maman Luba. Tana can amma addu'arta bai daina sauka a kanshi ba,

Sai da ya kwashe shekaru goma har ya zama kaman dan gida, anan ya gama primary school da secondry school, yayi jarabawar shiga jami'a, ?o?arinshi yasa shi samu tallafin karatu a wurin gwamnatin Kano, anan ya tsaya ya karanci bangaren likitanci, tsawon wannan lokacin, Hajiya tana marad'i, tunda Alhaji Mamman ya zubasu yayi tafiyarshi, Alhaji Abubakar Abzin shine kome nasu, har ta haihu.

Dukkan Yaran sun san Majid amma Anisah bata san shi ba, sai labarinshi. Zamanshi a gidan horan Yara, ya kara maida shi wani irin mutum mai murdadden hali, sannan baya hmm baya Humm. Dole yasa yake zama a cikin aji, amma baya son hayaniyar mutane ko kaWan. Idan dare yayi kuwa baya barci domin idan ya fara barci zai ta mafarkin Babansu yana dukar Hajiya. Haka xai bude idanu, sau biyu yana faduwa a aji, a duk ranar da yayi mafarkin tow zai fadi ya suma sai washe gari don bai samun isasshen barci.

Ganin haka zai shafi karatunsa, yasa shi fara ganin likitan kwakwalwa, aka fara duba shi, domin har dawanau aka tura shi. Lokacin da suka samu hutu, ya shirya ya tafi marad'i da tambaya da kwatance yaje gidan Alhaji Abubakar Abzin, Aryan yana kofar gidansu na maradin ya hango Abdul ba zai manta da shi ba, da gudu ya tafi ya rungume shi." Hammayo;" murmushi yayi ya kara rike shi suka nufi cikin gidan, ya kawo musu tsarabar Kano. Hajiya da ta ganshi, juya baya tayi tana kuka. Murmushi yayi bai ce mata kome ba. Ya zauna kanshi a sunkuye. Haka ta shiga daki Jamilah ta fito ta ce. "Hammayo kai ne" ta zauna a kusa dashi tana washe baki . "Yafendo kin zama yan mata " "sai buhun rashin mutunci." "Hammayo kaga Hamma Aryan ko?" Tashi yayi ya shiga dakin Hajiya, ya same ta a can kuryar dakin tana kuka. Zama yayi gabanta. "Hajiya ko daidai da rana daya ban manta daku ba."
"Amma ai na manta da kai!" "Hajiya nasha mafarkin kina sallah kina min addu'a da wannan na yarda a zuciyarki ina tare dake."
"Alhaji baka yi fushi ba?" Girgiza kai yayi yana murmushi. "Hajiya kina karkashin mijinki, a kaina ba zaki kashe auren da na bude idanu na gani ba." Hawaye ne ya zubo mata danta dan kimanin shekaru goma sha takwas. "Gobe zamu je Niamey."
"Hmm! Allah ya kai mu!" Ya fada.
Haka ya fita ta kawo mishi abinci, kannen suka zagaye shi, suna bashi labari can sai ga Anisah ta shigo tana kuka."Hajiya!" "Na'am Auta."
"Hajiya Hamma Amaan ya kwace sauran canjin."
"Allah ya shirya min ku baki daya." Ta amshi sakon, ta ajiye a kitchen. "Hajiya Ina hamma Aryan?" "Suna cikin daki Hammayonku ya dawo." Da sauri ta shiga Dakin, ta d'aga labule. Kura mishi idanu tayi idanunta cike da kwalla. "Hammayo!' bude mata hannu yayi, da sauri ta isa gareshi tana kuka. "Hammayo ban sanka ba, amma Hamma Aryan kullum sai ya bani labarinka." Murmushi yayi yana kallon Aryan. "Ya ce miki ina sat.." rufe mishi baki Aryan yayi. "Alkhairi nake gaya mata, yarinya ce bata san sharri ba please."
"Hamma Amaan yake gaya min wai sat..." Rufe mata baki Jamilah tayi. "Ke dai akwai bakin allatsine, idan kika bi na wancan sakaran sai an daure ki igiya tayi saura."

Domin daga Jamilah har Aryan basu shiri da Amaan,.kamar wuta da auduga. Mikewa yayi suka tafi masallaci, suna dawowa suka samu Hajiya tana kokarin tuka tuwo.. "Hajiya bani na miki?" "Yau.girkin maza zamu ci?" Ta tambaye shi, "zamana a gidan Horon kangararrun Yara, yasa na rike bangaren girki har gasar girki muke " ya faWa a sanyayye, Duk da cikin raha yake maganar amma fuskarshi bata nuna haka ba, yanayinshi babu yabo babu fallasa, suna zaune ya tuke tuwon ya kwashe tas, yana gamawa wata mata ta shigo kawo kar'ar Amaan. "Maman Jamilah ina jin kunyarki, ki jawa danki kunne wallahi ya fita harkata da yarinya ta."
"Kiyi hakuri;" shine abinda Hajiya ta faWa, sannan matar ta fita tana zage-zage. Can kafin magariba sai ga Amaan, ya shigo yana zage zage da rashin kunya. Kallon Abdul yayi ya ce mishi. "Barawo ka dawo ne?" "Hammayo muje masallaci!" Inji Aryan, domin a cike yake da Amaan babu ranar da zata waye ba a kawo ?arar shi ba, "Kai dan shegiya da kai nayi?" Wani irin mari Abdul ya kifa mishi, a wurin ya zube yana nishi, "kayi yadda kake so, idan kaso ka fadi abinda yayi maka. Amma ka sake ka zagi wani cikinsu sai na cire ma hakori."
"Hajiya k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ina ganin barawon danki zai kashe ni." Alola yayi ta wuce daki, shima ya wuce dakin. A masallaci Aryan yake bashi labarin abinda yake faruwa, sannan wani abin tashin hankalin shine duk bayan wata biyu Hajiya xata kwashe su har Niamey, su je can ayi ta wulakanta su ana ganawa Hajiya azaba da masifa.

Lashe baki yayi yana jin daci a ranshi, haka sukayi sallah sai bayan Isha suka dawo, tun a kofar gidan suke jin muryar Jamilah, Hajiya tana gefe bata yi magana ba ta xuba musu idanu Amaan sai dukanta yake. A fusace Aryan ya nufi Amaan Majid ya rike shi, "sake ta!" "Idan naki fa?" "Aryan wuce da hajiya Wakinta!" Ai dama ganin hajiya a wurin zai saka ya kyale shi, sai gashi cikin fushi ya kai mishi wani irin duka a kafa, dauke wuta yayi wato Majid zama gidan horon nan ya koyar da shi mugunta sala sala. Targad'a shi yayi ya ce mishi. "Kafin ka warke ka fara fita zaka fahimci muhimmancinsu, idan ma baka horu ba, akwai hanya dayawa da zaka nutsu."
Haka ya wuce da ita daki, yana faWin. "Kin mishi rashin kunya ne?" "A'a Hammayo, kiranta yayi tana sallah shine tana idarwa ta fita ya kama dukanta da hajiya tai magana yace babu ruwanta."
Cizon fatar bakinshi yayi yana jin tafasa a ranshi, a daren Aryan ya gyara dakinsu, da Inda Hammayo zai kwana. Haka suka kwana suna hira, sai asuba suka yi barci.. wurin karfe goma motar kai su Niamey tazo, suka tafi sai cika Amaan yake yana batsewa. Har suka isa gidan, wanda daga kofar gidan zaka fahimci ana sha'ani ne.

Lokacin da suka isa gidan, ba laifi ana ta hada-hada, falon Alhaji Mamman suka nufa suka gaishe shi sama sama ya amsa. "Kai me yasa meka?"
"Ba Barawon can bane ya dawo ya targad'a min kafa ba."
"Waye barawo!"
"Abdul Majid!" Wanda ya shigo falon, mikewa Alhaji Mamman yayi ya ce. "Sa'a me yasa kika kawo min shi gidana!" Juyawa yayi ya bar falon. Ai kuwa garin bashi hakuri ya rufeta da duka, har waje. Wannan abin ko a jikin Amaan domin shi gani yake Hajiya ta rabasu da jin dadin gidan Ubansu ta kawo su wata duniya suna wahala. Shi yasa duk abinda Alhaji Mamman zai mata baya tausayinta ko kaWan.
Da gudu Anisah ta fita waje, "Hammayo kazo Alhaji xai kashe Hajiya." Sun saba duk lokacin suka zo haka xai mata duka a gaban jama'a. Amma na yau ya wuce tunaninsu domin biki ake yi a gidan, kuma ga mutane babu wanda ya damu sai ma tsayawa da suka yi suna kallon abin. Haka ya ratsa taron ya shiga. Ya rike hannun Alhaji Mamman Ba'are da yake zuba mata duka. "Ya isa haka!" D'ago kai yayi yana mamakin waye ya isa ya dakatar dashi daga dukar Sa'adatu. "Ya isa haka Alhaji Mamman Ba'are!" Ya sake hannun shi yana kallon cikin idanunshi. "ya isa haka nace!" Ya fada yana me dago kai yana kallon Hajiya Nana. " Na rantse da Allah,duk ranar da danki ya kuma d'aga hannu ya tab'a min Uwa, sai na hauro sama na bugaki da kasa daga saman zan wurgo ki billahi azim, Uwa bata fi Uwa ba duk sunansu Uwa." Ya faWa yana d'ago Hajiya. ""Kai waye ya baka damar shigo mana gida?" Inji Sajjid Mamman Ba'are, cikin wani irin fushi, ya juya ga Sajjid wanda ganin idanun Abdul ya bashi tsoro. ?wayar idanunshi a fusace yake fushinsa daga zuciya take kunno kai ga idanunshi, kamilalliyar fuskar shi bata nuna fushin ba..
"Kace me?"
Hadiye yawu yayi, ya juya ga Alhaji Mamman Ba'are zai magana Hajiya ta ce mishi. "Kul ka kara magana!" "Hajiya idan ya kuma dukanki sai kashe shi, Nana kin ji me nace." Ya fada da karfi, juyo shi hajiya tayi ta watsa mishi mari, ta kuma marin shi. Jikinshi ya hau cira kamar zai tashi sama. "Ban doraka akan haka ba,me yasa zaka min haka?" Inji Hajiyar tana kuka."Mahaifinka ne me yasa zaka mishi haka a gaban jama'a?" Zube gwiwarta tayi ta ja hannun Majid din, sai yaki. "Ki cewa danki ya fita na tsame shi cikin zuri'ata."
"Haka yayi ai dama kafin yau ni ba danka bane."
"Ba zai fita ba, rashin kunyar da yayi sai Uwarshi ta biya akan idanunshi." Jin Nana tana saukowa. A fusace yayi kanta tare da tsare ta da idanunsa masu Bala'in ban tsoro. Da gudu Hajiya ta rufe shi da duka, "ka bar tashin hankalin nan, ka koma inda ka fito na roke ka, don Allah na roke ka ka tafi ka yi nisa da mu na yafe maka zuwan."

Juyawa yayi zai tafi Nana ta dauki sandarta ta shiga bugawa Hajiya, "Hammayo tana dukan Hajiya" bai ce kome ba, ya nufi falon Alhaji Mamman ya ce mishi. "Ka fita ka jawa Mamarka kunne ko na kona gidan nan baki Waya wallahi billahi azim." Ya fada a haukace, zuwa yanzu shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are tsoron Majid ya darsu a zuciyarshi. Ganin yadda ya fita da gudu, inda motar gidan take ya nufa, ya cire rigarshi ya bude wurin tanki, ya saka rigar sai da ya jike da fetur, ya Ciro yana watsawa a kan kome na gidan, "Hajiya kyale ta don Allah." Alhaji Mamman Ba'are ya fada, sannan ta tsaya tana hakki. "Me yasa ka dakatar dani?"
"Saboda d'anta zai aikata kome don mahaifiyarshi."
"Kenan idan aka dake ta zai dau mataki?"
"Zai aikata kome.ma". Ya faWa yana kallon yadda Majid din ya d'ago Hajiya suka dauki kayansu, suka nufi gidan. " Ita da Yaranta su zauna a gidan shi ya bar magana gidan mu!" Inji Nana domin ta shirya sai Hajiya ta biya abinda Abdul Majid ya aikata musu.

Suna da kudi suna da karfi, Majid ba xai zubda musu kimarsu ba. Don haka suka hana Hajiya tafiya, suka sakata a gaba. Shima Majid din kin tafiya yayi yana tsaye a kofar gidan, yana jiran ganin ko Aryan ne, suna can Alhaji Mamman yasa Hajiya a gaba da cin mutuncin, har aka gama bikin cikin kuka take, karshe ma turawa maradi yayi aka rufe gidan wai kada Majid ya tafi can ya zauna.

Shi kuwa rubuta wasika yayi ya bada aka kaiwa Hajiya da ban hakuri,

Bayan tafiyarshi da wata biyu, Alhaji Mamman ya yanke mata rabin wahala ya sakata a gaba ta fara zuwa aikin kamfaninshi. Da iliminta da kokarinta ta fara aiki inda ta fahimci wasu na azurta kansu da dukiyarshi, don haka ta fara aikin binciken anan ta gano har da hannun Alhaji Haladu da Kamilu. Ta mika mishi duk wani abinda ta tattara, sannan ya ce mata. "Ki saka Yaranki a gaba su koma makaranta, naji ance wancan dan mahaukaciyar, likitanci yake karantawa. Tow sai ya cigaba amma ya sani ko ya gama karatun anan zai yi aiki xa a fara gina mishi asibiti."
Zuwa yanzu baya shakkar mutuwa dama abinda yake so ya samu, Yaran hajiya zasu iya tsaya mata, duk da yasan yayi kuskure amma a yanzu yana da damar barin mata kome domin shima yanzu ya san girma ya cimma shi.
Majid da y koma sai da yayi jinya, a haka yake karatu, bayan wata uku aka kawo shi har marad'i, don bai san waye akanshi ba, abu daya yake faWa sai na kashe ka idan ka tab'a min Mamata. Hajiya bata iya ganinshi a wannan halin ba, kamar an mata bushara ta wuce da shi wurin danginta,. A can ya zauna har ya samu lafiya sannan aka yi cuku-cuku ya dawo nan da karatu, amma abin ya zame mishi cutar damuwa dan mental health Winshi ya tabu, don ma Kakanshi yana tsaye akanshi da sauran dangin Mamarshi haka yasa shi ya boye yadda yake shan wahala, ya cigaba da karatunshi....
Bayan shekaru bakwai.....
#Dambuje
[2/18, 11:33 AM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*017*
Bayan shekaru bakwai.
Duk da wannan shekarun zaka dauka Hajiya ta huta daga jidalin dangin Alhaji Mamman Ba'are, amma ina domin bala'in ya kara hauhawa ne bayan Alhaji Mamman Ba'are ya nad'ata sabuwar shugabar kamfanin ya sauke wanda yake kai ya dorata, ai kuwa sai gashi fitina ta kunno kai, daga kamfanin har gida bata da sukuni.

A lokacin ko barci neman gagararta yake, wata irin wahala take sha da kamfanin Mamman Ba'are, gashi yadda ta tsaya ba ?aramin bun?asa kamfanin tayi ba, domin idan har kana son gane yadda kamfanin ya cigaba tow ka shiga office dinta, ita da Aryan suke tsara duk wani cigaba dake Allah ya taimaka shi mutum ne mai kwazo kamar Abdul sai gashi ya hada karatu da aikin da yake taya mahaifiyarshi, duk da wannan jigilar bai hana idan ta koma Nana ta sauko ta shiga gaya mata magana marasa dadi ba, ana cewa idan duka yayi yawa na kai ake karewa tow ita Hajiya baki daya da ta ko ina kare dukan take, sannan Yaranta tsayawa tayi akansu, domin idan ba haka tayi ba Yaran so ake a lalata mata rayuwarsu.
A cikin shekaru bakwai din nan, suka tafi bikin gama makarantar Abdul Majid, wanda kana ganinshi kaga babban mutum, sai dai har yau yana nan babu sakewa kamar baya, ga shi nan dai amma yanayinshi zai nuna maka yadda yake jin babu dad'i a cikin mutane. Haka aka gama a hanyarsu ta komawa gida ne, Hajiya ta amshi takardarshi. "First class, Alhaji ka fito da shi amma baka farinciki." Yake yayi ya ce mata. "Ya Amaan yake?" Ajiyar zuciya tayi tana kallon Aryan da Jamilah da kowannensu yayi tsaki. "Yana lafiya." Ta fada tana son ta manta da abinda Amaan din yake mata. "Hammayo yaushe zaka dawo gida?" Shafa kan Anisah yayi yana faWin. "Zan dawo." "Ka dawo ko Hamma Amaan zai daina saka Hajiya magana, shi ba karatun ba, shi ba aiki yake ba. Sai dai kullum a bashi kuWi. Hajiya tayi magana har ta gaji "
Bai ce mata kome ba, shi dai ba zai je Nijar ba, wallahi ko a kai za a kai shi ba zai je ba. "Hmm tayi hakuri ta cigaba da addu'a."
"Ba zaka dawo gida ba!" Shiru yayi bai ce mata kome ba, zata kuma Magana Aryan ya ce mata. "Nisah ya isa haka, Hammayo ya gaji." Ya faWa yana kallon Abdul Majid din, dake su sun iya turanci duk haka suka juya harshen turanci. A hankali Aryan yake tambayarshi me yasa ba zai dawo gida ba.
"Kawai ba kome, zan tafi karatun sanin makaman aiki a Nijeriya ne "
"Amma.". "bana son hayaniya don Allah." Hajiya tasan halin Yaranta, kowa da irin nashi hakurin, amma hakurin Majid daban ne, haka fushinsa daban ne kuma zai iya hakura da kome musamman idan akwai wulakanci da cin mutuncin. Haka suka iso gida, Innarsu kanwar Hajiya wato Kabo wacce aurenta ya mutu take gida dauke da karamar yarta mai suna Zaytoonah. Yarinyar suna shiri sosai da shi, yana shiga ta tare shi da kyaututtuka masu yawan gaske. Tana murmushi ta ce mishi." Hammana ina tayaka murnar kammala karatun ka!"
Amsa yayi yana faWin. "Na gode dear!" Daga haka suka wuce ta tsaya tana kallon Aryan da yake mata dariya. "Hamma Aryan dariyarka kamar gwalo kake min"
"Tow Allah ya ba?i hakuri, ina Nabeeha?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Ka bani cin hanci dai na kira maka ita."
"Ok idan na shawo miki kan shi fa?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Karya kenan domin kuwa zuciyarshi da kiyayya ta ginu, duk macen da zata samu damar kutsa kai cikin zuciyarshi mace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login