Showing 72001 words to 75000 words out of 100763 words

Chapter 25 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2863

wannan wuraren? Akwai kofar da xasu fitar da ke har wani kauye, daga nan zaki wuce bodar Nijeriya da nijar ne da yake dole kaina, mu nan muna yankin River Benin ne.
"Ban gane ba?" Zama yayi yana kara murmushi ya buWe kofar ya shiga shi da Babyn sannan ya mika min hannu na rike shi na sauko. "Kina da saurayi?" "Na'am?" Na ce mishi, ina kallon shi. Murmushi yayi min sannan muka cigaba da tafiya.

"Nace kina da saurayi?" Ya juyo yana kallona." Zare idanuwa na fara, da wasa da ya bakin mayafina. A hankali yake takowa na juya bayana naga ko wani abu yasa yake biyo ni, sai naga haka kawai koda na juya ya matso kusa dani sosai. "Baki da saurayin ne?" Hadiye yawu nayi na gyada kai na, a hankali ya sunkuyo da kanshi a tunanina sumbatar bakina zai yi, da sauri na kawar da kaina. A hankali ya kai hannunshi gefen wuyata ta wurin mayafina ya kad'e min gizo-gizon da yake kaina.
"Ki kula." Ya fada yana kallon kwaron. Hadiye yawun bakina nayi ina kara jin kamar zan saki fitsari.
---
Cikin larabcin da bai gama rike bakinta ba, Addah ta kara gyara zamanta ta ce mata. "Idan nayi miki karya, ki saka a kashe ni a binne gawata, amma yarinyar da Yallabai yake fita da ita yata ce, kuma zaki iya zuwa gidan mu, ki ga irin kyawawan kyaututtukar da yake kawo mata." Mikewa tayi tana faWin. "Muje!" Haka Addah ta mike jikinta yana rawa ta ce mata. "Tow!" Suka tawo har gidan, wato ita Yazid zai ci amanarta. Ita zai tsallaka yana bin karuwa da ta gama yawon karuwancin kafin ta fado hannunshi, bata kara sarewa namiji ba dan goyo da zani ba ne, sai da ta ga katon akwatin kayan da ya kawowa uwar da yar, ciwon bakinta tayi sannan ta juya ta fita cikin nutsuwa Addah kuwa murna kamar zata daka tsalle.
Haka Reshmah ta koma gida, ta zauna tana tunanin me zai faru, me zata aikata da zai bawa Yazid tsoro ita ba kalar Matar da zai ci amana bane . Bai isa ya ci amanarta ba.
---Sai dare muka dawo tun a hanya aka tare shi, ana gaya mishi abin da ya faru cikin wani irin yare, murmushi yayi ya ce musu. "Suwa laula!" (Shi kenan naji) kallonshi nayi domin ban tab'a zatan yana jin wani harshe bayan Hausa da larabci ba.
"Wani yare ne haka?" Murmushi yayi ya ce min. "Harshen darsa, yana da saukin amfani.". "zan koya!" "Zaki iya kuwa?" "Hmm!" Haka ya rako ni gidan sai da na shiga ya ce min. " Za a kawo miki abinci." "Tow na gode!" Daura yatsar hannunshi yayi a baki ya ce min. "Shiiii" hadiye yawu nayi. "Kada ki b'ata min alakata da godiya." "Shi kenan!" Haka ya bani Babyn muka shiga cikin gidan, yana fita yayi waya aka kawo min abinci, muna kwance aka buga kofar kallona Addah tayi na mike na bude kofar na amso abincin na fara ci, tashi tayi zata saka hannu Ummi da take gefen gadona ta doke hannun da wani sanda, sai da kashin hannun yayi ?ara. "Kika sake wani abu ya shiga bakinki sai na shakeki har lahira munafukar banza." Daga haka bata ci ba na kalli ummi ta dauke kai. "Me yasa kika hanata!" "Ba zata ci ba wallahi." Shiru nayi ina kallon Addah da ta koma ta kwanta. Ban kuma musu magana ba, sai da zan fita Addah ta ce min. "Bani Aminatu na taya ki goyanta." "Ba zata baki ba, duk abinda zai faru sai dai ya faru!" Inji Ummi. Fita muka yi, nima na nufi gidan Yallabai. A falon kasa na same ta a hankali naji jikina ya bani akwai matsala. Haka na wuce na fara aiki har na gama. Tana zaune sai da na gama zan fita ta ce min. "Ke jira ni!" Daidai shima yana saukowa daga sama, kenan ta shiga kitchen, kamar ya san nufinta, tana fitowa kawai ta watsa min soyayyen mangyad'a da ta dauko a fry pan.
Rumfa yayi min ta zuba mishi a bayanshi, bata san lokacin da ta saki fry pan din ba, "Yazid!" Ta kwalla mishi kira, bude idanu yayi a kaina."Yallabai!" Na kira sunanshi. "Jeki gida lafiya ta lau." "Yallabai bayanka fa?" "Ba kome, jeki"

Ya fada min da wata irin murya, da sauri na fita tana rufe da fuskarta tsoro ya kamata, hadiye yawu tayi tana kallonshi. "Me kike nufi?" Jikinta ne ya fara rawa, "don Allah kayi hakuri." Jan iskar bakinshi yayi ya yaga rigar tare da zama a bakin kujerar falon, da gudu ta fita ta kira Aseem ta gaya mishi, shi ya tafi har wurin likitan ya tawo dashi, suna shiga suka same shi a falon. "Garin yaya?" "Nice na zuba mishi ba da gangan ba." Bai ce uffan ba har likitan da Aseem suka yi ta cire mishi rigar da ya hadu da fatar bayanshi, ya zuba mata idanu. Cikin wani irin Imagining da Zahrah zata zubawa man gyadar nan a fuska. Sai lokacin ya iya bude baki ya ce Mata. "Nufinki Zeehra zaki zubawa?" Zubewa tayi tare da rufe fuskarta ta fashe da kuka. "Kayi hakuri sharrin iblis ne." Ta fada tana shasshekar kuka, haka ya cigaba da kallonta tana kuka. Yana wondering yadda zuciyarta ta mutu da tunanin ta nakasa mace yar uwarta, murmushi ya saki a hankali yana kallonta. "Sultan kayi hakuri don Allah!" Ta fada tana waiwayen bayanta. "Aseem!" Da rarrafe ta kama kafarshi. "Don Allah ka rufa min asiri Sultan kishinka ne ya saka na aikata haka, Sultan ba zan kara ba." " A bata abinci dare da rana, ta zauna a wurin sai na warke." Fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita,
"Sultan afuwa!" "Aseem!!" Zubewa yayi akan gwiwarshi. "Uwar Yaranka ce, kuma mace mai daraja a gare ka, kasan haka kuma kai da kanka ka gaya mana babu mace mai darajasama da Reshmah."
"Zeehrah tana da daraja, darajarta me girma ne!" Ya fada yana kauda kai. "Matar da nake aure idan bata ji magana ta ba nawa zata ji? Idan wani abu ne ya had'ata da yarinyar waye zata tinkara? Dole sai ni, wato shine aka gaya mata xata kona musu yar mutane. Idan ta lalata mata fuska fa? Fisabilillahi ace mangyad'a zata zuba a fuskar Zeehrah...
#Mai_Dambu
[2/25, 7:57 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

*Muna da stone Veils da plain,sai hular Yara, masu kyau akwai veil na Yaran shima.*


*024*
Kallon Aseem yayi kafin ya ce masa. "Ka fice min da ita ko kuma na had'a da kai." Haka ya saka Reshmah a gaba ya wuce da ita wani gidan da aka ware domin hukunta duk wanda ya ja da Yazid, gidan kamar gidan yari yake, sannan a cikin gidan akwai masu kula da kowa kawai ba zaka fita ba,ba zaka iya kome ba kana zaune a daki guda ga kome amma kuma takure kake.
Ya kaita can wani daki da yafi kowanne kyau, "Aseem don Allah ka roke shi."
"In sha Allah." Ya fada, yana me barin dakin, kuka ta fashe da shi a ranta tana kara shan alwashi sai ta wulakanta Zahrah matukar ta fito.
----- Tun da nake a rayuwata ban taSa cin karo da irin wannan abin ba, domin kuwa ban zaci mangyad'a mai zafi zata watsa min ba, dafe goshina nayi ina mamakin kishinta. Ina zaune har su Addah suka dawo. Muna zaune ana cin abinci kawai muka ga mutanen Yallabai sun shigo cikin dakin, basu yi magana ba suka dauke ni. Zasu fita dani nace musu. "Ina da karamin goyo don Allah ku bar ni na dauke ta." Haka suka fita dani, dariya Addah takamayi tana cin abinci."Allah yasa su mata abinda ya wuce tunaninta."
"Kenan ke ce kika hada mata rigimar?" "Eh nice!" Ummi bata kuma magana ba, tana mamakin Addah.
Da suka wuce dani can wajen garin suka ajiye ni a gabanshi. "Kuje!" Kaina yana sunkuye. "Ke meye ya haWa ki da Sultan?" Da sauri na d'ago kaina ina kallonshi, fuskarshi a rufe sai idanun shi kawai nake gani. Sake daka min tsawa yayi, na fashe da kuka, musamman da ya fidda wuka tsirararta. " Ban san shi ba." Na fada ina ja da baya, "Meye alakarki da Yazid?" Wani irin curewa yayan hanjina suka yi, jikina ya dauki wani bala'in rawa, na ja da baya ina girgiza kai. "Ba zaki gaya min ba kenan?" Ya kara daka min tsawa, kuka na saka mishi me karfi ina faWin. "wallahi babu kome." "Ok tashi ki gudu" da sauri na mike tare da diba a guje, sai dai ko wurin ban bari ba, na ci birki sakamakon kartin mazan da na gani sun tare ko ina. hankali na a matukar tashe na waiga na ga sun zagaye ni. "Daga yau kada na kara jin labarin kin hadu da shi ko kin shiga gidan, idan kuma kika kara sakewa kuka hadu ko?" Ya fisgo ni tare da yaga min riga har kasa, kare kirjina nayi ya saka kafa ya tokare ni sai da na fadi. Ba a tab'a tozarta ni irin na yau ba, domin yana tsaye a kaina ya cire gabanshi ya shiga sakar min fitsari a kaina, sauran suka kwashe da dariya. "Wannan wasa ne, wanda zan miki ba fitsari ba ne, tsakanin cinyoyinki zan raba, nayi sukuwa a akanki yadda zaki ji rad'ad'in haka a ranki, naji labarin baki tab'a karo da namiji ba." Ya maida abin shi ya matsa a kaina, ya d'ago kaina ya dinga marina. Sai da naji kamar fuskar bata jikina, na karshe ne ya mare ni akan idanuna. "na tsane ki daga yadda Sultan yake zubar da kimarshi akanki." Suna gamawa suka watse daga wurin aka bar ni babu kowa. Haka na mike a hankali naji wani abu ya cika min zuciya na kasa kuka, har na kusa shiga gida, tun kafin na isa gidan nake jin Ihun Baby. Har na isa babu wanda ya kulata asalima a duhu suke. BanWaki na Wuce ina ta kwara ruwa, ina wanke jikina sai da na wanke ko ina sannan na koma dakin.
Na dauke ta tare da rungumarta ina sheshekar kuka, daga Addah har Ummi babu wanda ya ce min, nayi shiru a hankali barci ya dauke ni, ga ciwon da idanuna suke domin ina ga da wani abu ya mare ni ba da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hannu ba. Sai asuba na tashi nayi alola nayi sallah, ina idarwa na juya na kwanta sai dai kamar yadda nake saka raina zan yi barci, ashe abin ba haka ba ne,. Wasu kartin maza ne suka kuma zuwa suka tafi da ni wannan karon ina ganinsu na dauki Babyna muka tafi, tun daga ranar ban kuma zama ko na minti biyar ba tare ina aiki ba, wahalace ta karu min kamar na mutu na huta, haka nake fama da aiki babu dare babu rana, sannan abinci sau biyu ake bani sai yanzu na fahimci akwai iyakata akwai iyakar wasu, Yazid iyakar wasu ne, shi din duniyar wasu ne da zarar na sake wani abu ya kara had'a ni da shi tabbas zan iya fuskantar mutuwa. Haka yasa nake addu'a ba dare ba rana, ina gayawa Ubangiji ya kawo min mafita da karshen wannan halin da nake ciki.
-----
A bangaren Yazid babu ranar da ba zai tambaye su Zeehrah ba, an kai mata abinci Ya Baby take, babban burinshi ciwonshi ya warke ya tafi ya ganta, domin baya iya fita ko waje ne, yana cikin gida yana fama da ciwon.
Akwai wani abu da dayawanmu mata bamu gane ba, shine idan har namiji ya lakato batun dating da wata mace mafi alkhairi mu kyale shi, mu zuba mishi idanu. Idan kuwa muka ce zamu yi magana. Tow kuwa ya dinga abun da zai b'ata mana rai.

Gashi ko sati ba ayi ba, Aseem da Sharif suka saka dakyar ya fito Reshmah, amma abin da tayi ya tab'a zuciyarshi, sannan ba karamin hakuri da juriya yake da shi ba, domin da mace ce aka watsa mata mai da ba karamin jinya zata yi ba. Amma dake akwai kulawa kwanciyar hankali da nutsuwa kuma ana mishi kome ko wurin had'a magungunan shi baya fita anan ake mishi kome, tun ranar da abin ya faru Reshmah bata kwana a gidan da akai ta ba, amma kuma zaman babu dad'i. A wannan daren da sukayi abin da ya faru duk shirinsu ne. Ita da Yaranta shi Aseem yana tare da Yazid babu abin da ya sani.

***
Niamey.
Tunda farko da ace ta san matsalar nan na shi tabbas ko zata rasa rayuwarta ba zata tab'a barin shi da ciwon ba, "Hajiya!" Salamatu ta kira sunanta. "Na'am!" Ta amsa a sanyayye, "Shayin yayi sanyi." "Tow!" A hankali ta dauki kofin ta kurba kana ta d'ago kai tana kallon Salamatu. "Hmmm! Alhaji ya tashi ne?" "Eh yana dakin motsa jiki." Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce mata. "Shi kenan jeki." Juyawa tayi zata fita Hajiya ta ce Mata. "Salamatu Aryan fa?" "Tun dazun ya shigo suna tare da bakon Marad'i." Murmushi tayi sannan ta ce mata. "Shi kenan na gode." Tana fita magani ta dauka ta sha, sannan ta dan kishingid'a tana kallon gefe guda. Wani irin sakaci tayi da rayuwar Majid ya lalace haka. Hawayen da ta gaza tare shi yake zuba mata, tana jin kamar tadau ciwon a jikinshi ta dorawa kanta, bata son ta ce bata yafewa Alhaji Mamman Ba'are ba, amma tabbas shi ya lalata mata nata rayuwar da har haka ya shafi na wanda bai ji ba bai gani ba.

Yadda take kuka kamar karamar yarinya, domin Majid yana matukar bata tausayi, idan ta cire Matsalar Amaan tow Majid ya sauke kaso mai nauyi a zucuyarta. BakiWaya ta rasa inda zata saka hakkin Majid domin abin da ya same shi kamar laifinta ne, da bata yarda ta bi Alhaji Mamman Ba'are a lokacin ba tow da wannan abin bai same shi ba.
---
Amaan Mamman Ba'are.
Kallon juna suka yi, kamar zasu cinye juna kafin murmushi ya kwace mishi ya ce mishi. "Ban yarda da abin da kake faWa ba." Lumshe idanunshi yayi ya bude a kan fuskar Sajjid. "Baka yarda ba kenan?" Dariya Amaan ya saka yana faWin. "Lallai kuwa, hmm dukiyarshi bata da wani amfani tunda babu me ci haka zata yi ta habbaka yadda zamu san me zamu yi mishi."
"Hmm! Ban yarda Abdul Majid bai da lafiya ba. Na fi yarda da cewa bai da ra'ayin aure amma ace bai da lafiya ai maganar kawai tatsuniya ce." Mikewa Amaan yayi yana faWin. "Zan tafi idan lokacin da ka sani sai ka tsaya muyi magana." Sajjid bai ce mishi kome ba, har ya bar gidan. Wani irin murmushi Sajjid din yayi, ya kira Mahaifiyarshi ya gaya mata, shiru tayi, yanzu ne ya dace ta tashi ayi ta ta kare ko kuma ayi ta kasa. Idan Majid bai da lafiya kason shi Hajiya da Yan uwanshi ne zasu more tunda mutuwa zai yi a wurin aikinshi.
"Mutuwar Abdul Majid Mamman Ba'are baya hannuna, amma nasan dukiyarshi zata iya dawowa hannunmu idan har aka bi a sannu. Kana jiye mana abin da zai kai Sa'adatu lahira."
"Ba iya shi ba, akwai labarin da nake son nasani amma yaki gaya min. Ina son idan na samu labarin zan gaya miki."
"Wane labari ne haka?"
"Ya ce min a sanadin haka aka kai, Majid gidan kangararun Yara, domin fitar da Hajiya tayi. A wannan ranar shi ya saka Majid ya fara sace-sace har aka kai shi gidan horar. Idan ya tuna abin yana jin tsanar Hajiya."
"Kai haka ya ce? Lallai nayi babban kamu. Tow kada ka sake ya fahimci cewa kana son jin lallai ya baka labarin, zan cigaba da aikina anan da kanshi zai baka labarin."
"Shi kenan, amma ni gaskiya na gaji da wannan harkar." Shiru tayi ta ce mishi. "Na dan lokaci ne, ka saka idanu yadda zan tarwatsa Sa'adatu."
"Yawwa Hajajju sabuwar Chairwoman ba BA'ARE GOLDEN EMPIRES!"
Murmushi ta saki ya sauke wayar yana faWin. "Hajiya Tani, kifi na ganinki mai jar koma. Ina harinki kina harin Hajiya Sa'adatu."
---
Hajiya Tani.
Jikinta ne ya bata ana tsaye a falonta, ta kashe wayar ta fito, ganin Hajiya Fauziya Mamman Ba'are yasa ta sha jinin jikinta kamar babu abinda ya faru ta kakaro murmushi ta ce mata. "Kina son wani abu ne?" Girgiza kai tayi ta ce mata. "Naji kin ambaci sunan Sa'adatu ne akwai abinda ya faru ne?" Wani sirrintaciyar murmushi tayi tana faWin. "Hajiya Fauziya taya zan yarda na gaya miki gaskiya, bayan kema idan kin samu yakata zaki yi." "Haba wani yakarki? Kawai gaya min zan taimaka miki da yad'a shi." " Ba yad'awa ba ne, so nake ki saka ya Haladu yabawa Abdul Majid auren Afiyyah."
"Kina ganin haka mafita ne?" Girgza kai Tani tayi tana faWin. "Haka shine zai bamu damar fitar da abinda kike son faWa." "Akwai labari kenan!" Murmushi Tani tayi tana faWin. "Mai girgixawa."
Daga haka suka fita, kamar yadda suke son sanin me ya janyowa Majid ya samu wannan matsalar duk yadda aka yi Hajiya tana da wani dark secret da take boyewa idan haka ne kuwa tow tabbas Hajiya ta kusan mutuwa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login