Showing 3001 words to 6000 words out of 100763 words

Chapter 2 - BAƘIN HAURE BOOK COMPLETE BY MAI DAMBU.doc

02 Nov 2025

2847

muryar da tayi kama da mai shirin mutuwa, azabar da ta ratsa ni lokaci guda........
*Gamu nan mun dawo*
1/3/2024...
#Mai_Dambu
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA?IN HAURE....=?>?=?>?*

{Greed for Money is the roots of all evils>???}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*002*
_Ban zan yi tafiya mai nisa ba, ba tare da na tsaya na miki fatan Alkhairi Hannatu Idris Allah ya shiga cikin lamarinki, ya saka da alkhairi na gode sosai_

Operation Anaconda
***
A daidai lokacin da nake tsammanin mutuwata, ta zo gare ni domin nasan abubuwa dayawa sun faru a cikinsu har da rashin ganawa da mahaifiyata, wanda tana raye amma bamu san a wata duniyar take ba, iya hakan idan aka barshi a rayuwata na azabtu da rashin Uwa, nasan duk laifin na Baffa ne da Addah at least ya dace a gaya min inda mahaifiyata take. Soka min wukar a gefen cikina, yayi dai-dai da dawowata daga duniyar tunani da mafarkin zahirin da nake bayan na ga mutuwa. Sake caka min wukar yayi cikin tashin hankali ina kara jin abin da yake fada.
"Sai na kashe ka, idan ka kuma tab'a min Mamana!" Ya kara d'aga wukar zai soka min kamar wanda aka mishi wani abu, haka ya zube a jikina. Azaba da rad'ad'i yasa na kasa aikata kome, ina kwance kasarshi da alamun suma yayi domin ina jin dan bugun zuciyarshi. A hankali na tattara karfin da yaymin saura na tunkud'e shi gefe can, ina jin yadda jinin yake zuba. Ga zafi gashi yana zuwa da sauri da dumi, a hankali na fara sauka daga bisa gadon sai dai na kasa, komawa nayi ina jin wata iriyar azaba ga zufa da gajiya me haWe da jiri kamar xan yi aman kayan cikina. Haka na koma tare da kame wurin ina kwance, nayi ta kokarin niman wani abu na rufe ciwon. Na rasa a wurin lalube na tabo fuskarshi. "Tashi ka taimaka min kada na mutu,ka tashi don Allah zan mutu ka ji." Na fada ina jijjiga kafadarshi. Kamar a mafarki yayi ta jin muryata, haka yasa shi bude manya idanunshi da suke cike da barci, "Tashi ka taimaki rayuwata mutuwa zan yi." Na fada da asalin karamar muryata.

Ina jin wani uban tsallen da ya buga, yasa ni ?ara ware idanuna, ina nishi idanuna a rufe naga kamar an haska fuskata. Bude idanuwan da zan yi hasken wuta ya gauraya dakin, sai dai abin mamaki shine bana gani sai dishi-dishi. Lumshe idanu nayi a hankali naji kamar barci ne ko wani abu ne yake faruwa da ni, na dai san ban kuma fahimtar duniyar da nake ba. Wani irin rikicewa yayi wanda yasa shi gaba-daya rud'ewa, wayarshi da yake gefen gadonshi ya dauka, tare da duba lokaci. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!" Ya iya furtawa domin kuwa yasan yayi abinda ya dame shi, ya kuma rasa wanda zai kira ya gaya mishi halin da yake ciki. Sake wucewa yayi ban daki ya kalli wandon shi bai ga alamar manhood Winsa tayi wani abu ba, amma kuma hannunshi kaca-kaca da jini. *Doctor Umaima!* Abin da zuciyarshi ta ambato kenan, da sauri ya fito tare da Waukar wayarshi. Jikinshi na rawa ya kirata.
"Assalamu alaikum!" Ya faWa ta d'aya bangarenta. Ina bai samu arzikin amsa mata ba ya jifa mata tambayar. "Kina asibiti ne?"
"Yes ina Night ne!"
"Alhamdulillahi! Umamai don Allah ina cikin tashin hankali ne, na yi attempt kisan kai. Please ki taimaka min gani nan."
"Ya Rahaman,tayah hakan ta faru?"
"Ba lokaci gani nan." Ya faWa mata, sannan ya koma kan gadon ya dauki wani towel ya daure inda jinin yake zuba, sannan ya dauko zanin gado ya nad'e ta da shi, kafin ya kuma Waukar bargo ya dunkule ta a cikin, sannan ya dauke ta, ya nufi hanyar waje, ta falonshi ya shiga gareji.
Ya ajiye ta bayan motar, ya koma ya dauko key, yana zuwa ya bude a cikin motar ya sakata, ya koma ya gyara dakin shi tas, yana jin zuciyarshi kamar zata buga, yasan halin Commodore Magaji Abba Chindo, yana samun labarin ya kashe yarinyar kwanar shi ya ?are. Haka yasa shi kara rud'ewa domin wannan aikin shi ne farincikin shi, shine kome na shi idan ya sake ya rasa shi tabbas sai yayi matukar danasani. Haka ya gama goge dakin ya saka kome a wancan dakin duhu, sannan ya nufi gareji a lokacin Dr Umaima ta kira shi ya kai sau uku, yana shiga motar ya kirata. "On my way!" Ya kashe ya kunna motar sannan ya fito ya bude get din, ya koma ya fitar da motar, sannan ya sake dawowa ya rufe get din ta ciki ya koma ta fito ta kofar gidan.
Har ga Allah ya tsani kanshi, wannan lokacin ya dace ya rabu da wannan laluran, amma ina kamar kara cusa mishi abin ake, kara ji yayi ya tsani ahalin shi idan aka cire Hajiya. Itace har abada ba zai tsaneta ba, tunanin shi ne ya katse lokacin da ya iso bakin get din fita. Ya nuna ID card Winshi, haska motar suka yi, sannan suna ga normal bargo ne. "Oga ina zaka?"
"Zan shiga clinic ne an kira ni."
"Ok Oga kayan cikin motar nan fa?" "Idan na gama aiki xan kwanta ne, bargo na ne."
"Ok ku bude mishi kofar!" Haka suka bude mishi kofar, ya fita yana sauke ajiyar zuciya. Da gudu ya nufi titi tare da Waukar hanyar asalin cikin barrack din, yadda yake gudu kadai zai tabbatar maka, yana biyayya ne ga zuciyarshi da take bugawa.


Koda ya isa asibitin dake d'an tafiya ne ya raba su, yana isa bakin get din aka tsare shi, mika musu ID card Winshi yayi, suka bude mishi domin sun san likita ne, kuma babba, yadda yake tukin har ya isa bakin Asibitin zai saka ka gane Allah kaWai ya kawo bawan Allah nan asibitin. Yana shiga harabar asibitin Dr Umaima da wasu Nurse biyu suka fito, zasu amshi mara lafiyar, suka ga ya bude motar ya dauko ?unshin bargo. "Jeed Ina mara lafiyar?"
"Ba lokaci mu wuce ciki " ya dauki bargon suka wuce cikin asibitin. Kai tsaye emergency room ya wuce da ita. Ya kwantr da ita a saman gadonsu na marasa lafiya. Sannan aka shiga bude ta, har aka bude ta gaba-daya. Har lokacin jini yake zuba.

"Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Tana zubda jini" Doctor Umaima ta faWa da sauri tana danne wurin. "Ki taimaka min kada ta mutu."
"Kayi wani abu, a tsayar da jinin nan, a shiga da ita tiyata."
Cikin abinda bai wuce minti ashirin ba,suka nemi yin tiyatar . "We need blood?"
"Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!;babu a bank ne?"
"Ban sani ba!"
Da sauri Nurse Biodun ta bude blood bank, ta ce musu ."Daya ne ba zai wadatar ba."
"Za a samu mutane a lab?"
"Bana tunanin sun tashi,saboda aikin su ba dare ba rana ne." Da sassarfa ya fita ya nufi can wurin lab din, ko minti talatin ba ayi ba, ya isa sun rufe da kyar aka samu wanda yake kwana a wurin. "Duba jini na, group O+ ne" Ciro wayarshi yayi ya kira Doctor Umaima. "Leda nawa ake so?" "Ina ga hudu zai yi, don yanzu na samu an tsayar da jinin."
"Ok ki kokarta gani nan zuwa." Ya faWa, kallon mutumin yayi, bai mishi magana ba, ya dauki duk wani abun bukata, ya fara aikinshi, cikin ikon Allah dake mutumin yasan shi, kuma yana tambayar shi, sannan yana duba medical records dinshi a computer Winshi, sai gashi Allah ya takaita da sai anyi ta tests. Aka dibi leda daya, can aka kuma diban na biyu, a lokacin aka barshi ya huta. Kiran Doctor Umaima ya shigo mishi lokacin ana diban na uku. Cikin tsananin gajiya ya Wauka. "Saura leda daya, a zo a karbi sauran"
" Captain!"
"I'm okay!" Ya faWa cikin karfin hali, can kuwa sai ga nurse da wani soja, aka zo aka amsa. Yana isa wurinta ta ce mishi. "Baka saka hannu ba a Matsayin."
"Umaima rayuwar yarinyar ne mai muhimmanci, ba saka hannuna ba."
"Ok"
Haka suka shiga da ita aiki, yana kwance ana diban jinin karshen.
Wurin karfe biyar na Asuba ya fito a hankali yana jin jiri na dibanshi. Dakyar ya isa emergency room. Zama yayi a kujerar da ke cikin dakin, jin kiran Sallah yasa shi nufar masallaci, yana sallah a nan ya kwanta domin wani irin jiri da zazzaSi yaje ji.
Karfe shida na safe Doctor Umaima ta fito, a matukar gajiye domin babu inda baya ciwo a jikinta. Sannan aka turo yarinyar a gadon marasa lafiya. Aka kaita ward, wucewa daki tayi ta gabatar da sallar asuba, sannan ta shiga hada kayanta. Tana kokarin kiran wayarshi amma ba a dauka ba. Sai da ta cire kayan jikinta sannan ta wuce dakin da aka kwantar da yarinyar, bata ga wani fuskarta sosai ba, ta juya ta fita wurin seven ta bar asibitin. Yana barci a cikin asibitin yaji kiran da wayarshi keyi, kamar a tsakiyar kanshi. Bude idanu yayi da suka yi wani irin fari da ja. Yasa a kunne. "Sir kana ina ne? Za atafi teku."
Wani irin jiri ne ya kwashi Idanunshi ya ce. "Ok gani nan" kashe wayar yayi ya sauke ajiyar zuciya, kafin ya hada karfinshi wuri guda, ya tashi tare da Waukar kome na shi ya fita daga Masallacin domin yasan team lead Winsu Commodore Magaji Abba ne, haka yasa ya boye ciwonshi domin ya san halinshi sarai, and yaso ya kuma ganin yarinyar nan, haka ya kwashi motarshi a guje. Sai community dinsu na sojoji. Yana isa a daddafe ya shigar da motarshi, sannan ya wuce kitchen ya haWa tea me kauri ya sha, kafin wani lokaci ya fara zufa kamar me. Wanka ya shiga yayi sannan ya kimtsa ya fito daga gidan ya turawa Doctor Umamai kudi tare da short Note.
*Yarinyar nan idan ta farka please ki bata wannan! Thank you da abinda kika min!*
Daga haka ya fita bayan ya dauki duk wani object na aikinsu.
Operation Anaconda plan.

Kai tsaye headquarters dinsu ya nufa, anan ya hadu da Commodore Magaji Abba Chindo, kanshi ya sunkuye yana kallon kasa. "Kun san abin da ya tara mu, mun samu labarin za a fitar da mai ta ruwa. Aikinku shi ne ku dakushe yunkurin yan tada kayar baya shine aikinmu,mu mazaje ne a fagen yaki idan kunso idan kun koma cikin matayenku tow ku daura zanin matayenku,kune kuka sani ba mu ba ku ajiye personal emotion dinku domin dakile aikin yan ta'adda. Muna da Kyakyawar yakinin duk wani sojan kasar nan yana tsaye ne domin bawa al'umma kariya da taimakon gaggawa. Yan kasa ne kaWai zasu fahimci yadda tasirin kishin kasa yake kun ji ko? Kada wani yayi harbi idan muka kama su, aikin mu shine mu kawo su headquarter ba kashe su ba, domin suma fararen hula ne."
"Yes Sir!" Suka fada da karfi. Sannan suka wuce inda aka ajiye mota, suka shiga shi kam bai wani damu da ya shiga gaba ba, yafi damuwa da baya, haka wani sub-Lieutenant ya bude mishi gaban mota ya shiga, har zai zauna Magaji Abba Chindo ya zo daidai kunnen shi. "I hope kayi ban kwana da danginka! Domin bana fatar ka dawo a raye."
D'ago kai yayi yana murmushi, ya ce mishi. "Kai ne bakon mutuwa!" Ya faWa yana murmushi. "Wannan murmushin sai ya zame maka mutuwa." Yar dariya yayi ya ce mishi. "Ban sani ba, idan akan aikin da kasan idan na bari ba zai kare ni da kome ba, domin kuwa hmm!"
"Domin me? Kai da aka watsar da kai." Juyawa yayi ya kalli MAC. A fusace yake amma kuma baya jin zai yarda su yi faWa. Sai ya dauke kanshi yana me kallon gefen driver. "Muje ko!" Wato daga cikin abin da Allah ya hore mishi iya sarrafa fushinsa.

Zai yi wahala ka ga tunzurar shi, idan kuwa ya tunzura yana zame mishi mugun yanayi ne mai matukar tsoratarwa, shi yasa baya son fushi baya son fada, baya son hayaniya, yana ajiye kanshi da yanayin shi a wani aji na musamman. Fushinsa ba haka kawai yake yin shi ba. Maganar Magaji bai dauke ta a bakin kome ba. Har suka bar headquarter suka nufi bakin ruwa. A ka'idar operation Anaconda, kome suka hadu da shi, lakwame shi zasu yi amma daga abinda Commodore Magaji Abba Chindo ya a gaya musu ba a basu damar harbi ba, ba a basu damar kome ba sai dai dakile fashin da za ayi, a motarsu na tafiya kai tsaye ya kira Admiral shugabansu.
"Sir wannan mission din yana da matukar hatsari, idan muka samu kanmu cikin tarkon makiya ya zamu yi? Kasan masu wannan aikin suna dauke da miyagun makamai, sir a bamu damar kare kanmu da rayuwarmu don Allah a tura wannan sakon zuwa ga Oga!"
Admiral duk da ba musulmi ba ne, yana matukar ganin girmanshi, musamman yadda yake da jajjircewar aiki, daukar kasada a kan kowani aiki. Infact shi yana cikin SISA, wato (special intelligent Soldier Agent) sannan ya ajiye haka a matsayin personal life din Yaron, ko wannan operation Anaconda plan din yana cikin sojojin da suka kirkirota musamman yakin south south. Sannan asalin labarin daga bakinshi suka jiyo shi, haka yasa suka kara bincike aka tabbatar za a fita da mai ta teku. Shi yasa aka tura su.
"Ku kare kanku, idan kuka faWa tarko!"
"Yes Sir!"
Commodore Magaji Abba Chindo, kiran wasu sojoji guda uku, ya umarce su da su je har gidan da ya dauko yarinyar nan, su ci uban Uwarsu, kada su d'aga mata kafa.

**
Unguwar hausawa.
Koda yake ana kiran unguwar ce da sunan unguwar hausawa, amma a zagaye yake da Musulmai da kiristoci, musamman inyamurai. Tun karfe shida na safe ya dace a ce an dawo da ita, amma shiru har karfe takwas.
"Ada wetin happen? I see you dey pass up and down, shebi your Ethiopia girl neva come back?" Inji wata Beyarabiya, cikin takaici da bakinciki Adda ta ce. "Bise kyale ni da yar iska haihuwar asara, me aka yi da haihuwar bakinciki, shad'ari ya haifa mana irin masifa, kaf cikin al'ummar fulani babu miyagun iri kamar anagamba." Ta faWa tana watsa hannu. Fitowar wata budurwa daga wani daki tana yatsina fuska ta ce mata. "Addah hala irin masifa bata dawo ba ko? Kowa na fitowa bariki arziki ita wannan a barikin ma tsiya da masifa take kara janyowa kanta. Kuma wallahi sojan nan bai da mutumci, ba lallai ya saka condom ba, a tsarinshi baya saka condom. Shi yasa lokacin da ya tab'a daukar Ummi ta dawo tana ta mita, domin tace bata da infection dan shegiya ya zuba mata, mugu. Tow gashi ya dauki Zahrah."
Kwafa tayi tana faWin."ai ni ban ga amfanin haihuwar Zahrah ba, shegiyar yarinya ta dauko bakin jinin Uwarta. Ke kan ai Munaisah kyanki jarinki gaki tabarkallah, ita waccan yar iskar."

Fitowar wasu yan mata da kayan barci, yasa tana kallonsu. "Zully kin tashi?" Dauke kai tayi kamar bata gansu ba, ta koma dakin ta dauko brush da marclean, ta kuma fitowa. Bakin magudanar ruwan ta tsuguna tana wanke bakinta. "Zulaihah hala laifin tura Zahrah kwanan waje ko?" Nan ma bata tanka mata ba. "Daurawa kai jaraba, wai tana jin haushin abin da ya faru ne?"
"Munaisah babu ruwanki da ni, domin zan ci mutuncin ki." Inji Zully din. Kumshe dariya tayi tana faWin. "Bani na kar zomon ba, yau wata yarinya zata sha wutsiya gatar gato!" A fusace Zulaihah ta wuce bata kula su ba, sauran yan matan suna mata dariya, domin a duniya rayuwar Zulaihah idan za a ce ta bada shi domin ta kare Zahrah zata bada. Ta tsani irin rayuwar da mahaifiyar take daura yan mata a kai, suma dake son abin duniya da kwadayi yasa suna bada jikinsu me daraja, suna fadawa bariki.

Tashi Addah tayi ta nufi banWaki ta kama ruwa, sannan ta fito domin ka'idar kiran wayar Mahaifin Zahrah karfe goma na safe, ji tayi kamar zuciyarta zata buga domin karfe goma saura. Wannan wacce irin masifa ce Zahra zata cillata cikinshi? Tunda take kawo yara babu wacce ta tab'a wuce shida na safe bata dawo gida ba, sai Zahrah. Abin karyawa suka yi baki daya taliya da mai da yaji, sai Zulaihah da ta fasa kwai da sadine ta soya da yar attarugu da tumatiri sai albasa, ta shiga daki ta ajiye musu tasan idan ba wani lalura ba, babu yadda zaayi Zahrah ta kai wannan lokacin, idanunta yana kan wayarta, duk wani motsin lokaci tafiya yake da sautin bugun zuciyarta.

A hankali ta kara rike wayar, goma tana cikawa wayar Addah tana kara. Jikinta na rawa ta fado dakin. "Zulaihah ban san me zan gayawa Shad'ari ba, don Allah taimaka ki mishi karya wallahi nayi danasanin turata."
Amsar wayar tayi cikin sanyin murya ta ce. "ina kwana Kawu?"
"L??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????afiya lau Zulaiha, ya kwananku da na Addah?"
"Lafiya lau Kawu!"
"Ina kawarki?"
"Baffa yau makaranta sun tura su, wani nazari sai nan da kwana uku zasu dawo in sha Allah."
"Tow Masha Allah, Ubangiji ya dawo da su lafiya, Zulaihah don Allah ki kula da Zahrah kin san yadda take bata ji, sai anyi da gaske." Murmushi tayi tana faWin. "Kawu Indai akan gaskiya ne, ba zan gushe bata goyan baya ba, har sai na koma ga Allah."
"Allah ya muku albarka!"
"Amin Ya Allah, Kawu har yanzu babu labarin Ammynmu ne?" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Na tafi har ye'ude ban samu wani labarinsu ba."
"Allah sarki Ubangiji ya bayyana ta!"
"Amin Ya Allah, ya Munaisah ita ko wayar ba zata yi da ni ba ne?"
"Bari na mika mata." Ta mike zuwa waje, ta mikawa Munaisah. "Baffanku!" Amsar wayar tayi ta saka a kunnenta. "Barka dai Baffa."
"Hmm! Ke Wato sai na nime arzikin magana dake, amma ina jin kina kiran Innarki ko?"
"Kayi hakuri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login