Showing 1 words to 3000 words out of 81712 words

Chapter 1 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 01

مسب الله نمحرلا .ميحرلا


__ Sassanyar iska ke tashi, wadda ke haɗuwa da ƙamshin jar jiƙaƙƙiyar ƙasar da ke malale a
tsakar gidan. Hakan ne ya sa iskar da ke shiga hancin duk mahalukin da ya shaƙe ta, ta
kasance daddaɗa. Ruwa ne kwance a wani gefe na tsakar gidan, ya yin da wani wajen ƙasar ce
kawai a jiƙe. Wanda hakan ze alamta maka cewa ba a daɗe da ida ruwan sama ba. Tana zaune
a kan kujera 'yar tsuguno, gaban murhu da tukunya ke ɗore a kai tana fifita wutar da ke ƙoƙarin
mutuwa. Sautin sauke numfashin da ta soma jiyowa daga cikin ɗaya daga cikin ɗakunan da ke
gidan ne ya sanya ta dakatawa daga fifita wutar da take. Ta sake ƙanƙance idanunta da suka
ɗan sauya kala saboda yajin da ke shiga cikin idanunta, na icen da ke ci cikin wuta.

"Wayyo Allah! Wayyo.." Ta sake jiyo sautin a wahalce. Ba ta san lokacin da ta jefar da mificin
hannunta ba, ta miƙe da sauri har tana ƙoƙarin tuntuɓe, ba ta tsaya ba ta yi gaba kai tsaye zuwa
cikin ɗakin. Hannu ta saka ta yaye yalolon labulen da ya hana ta ganin abin da ke faruwa cikin
ɗakin, har sai da ta shiga. Ta sauke idanunta a kan motsatstsiyar katifar da ke cikin ɗakin.
Matashiyar budurwa ce zaune a kan katifar tana sauke numfashi a wahale, hannunta ɗaya dafe
da turtsetsen cikin da ke gabanta, ya yin da ta yi amfani da ɗayan hannunta wajen damƙe gefen
katifar da wani irin ƙarfi da ba ta san tana da shi ba. Idanunta a rufe suke gam tana jujjuya kanta
cikin tsananin azabar naƙuda. Jin alamar an shigo cikin ɗakin ne ya sanya ta buɗe jajayen
idanunta ta yi ƙarfin halin kallon matar da ta shigo. Cikin raunanniyar murya ta ce

"Dada marata, Dada zan mutu.." Ta ƙare maganar tana yarfe hannunta da ta ɗauke daga kan
cikinta. Duk da ba ta da tabbacin ko Dadar za ta taimaka mata, ko za ta bar ta ne ba tare da ta
yi yunƙurin taimaka mata ba. Murmushi wadda aka kira da Dadar ta yi tana faɗin

"Alhamdulillah!" Ta ƙare maganar tana maida idanunta kan Inna-wuro. A ranta tana ji kamar ta
taka rawa don tsananin murna. Cikin ƙarfin hali tare da danne duk wani abu da take ji tace

"Sannu Inna-wuro." Ta faɗa tana ƙarasawa kan katifar. Duk da tsananin azabar da Inna-wuro ke
ji hakan be hana ta kallan Dadar ba, ta lumshe idanunta tana jin wata ƙwalla na tarar mata a
cikin idanunta. Duk wani ƙoƙari da za ta iya dan ganin Inna-wuron ta haihu lafiya Dadar ta din
ga yi. Kasancewarta Ungozoma ya sa ba ta nemi wani taimako ba, ko yunƙurin kiran wani dan a
kai ta asibiti ba. Ita dai burin ta kawai Inna-wuro ta haihu lafiya, ko da abin da ke cikinta be fito

lafiya ba wannan ba damuwarta ba ce. An kwashe wajen minti 30 kafin wani dattijon bafulatanin
mutum ya shigo cikin gidan da sallama ɗauke a bakinsa. Dada ba ta iya amsawa ba saboda
cigaba da taimakawa Inna-wuro da take.

"Kina ina ne Uwar gida." Ya faɗa yana zame hular kansa. Shirun da ya ji ya sanya shi ƙarasowa
cikin gidan, yana dab da ƙarasawa Dada ta fito. Ya kalle ta sosai yana nazarin yanayinta. Tun
kafin yace komai ta ce

"Naƙuda ce ta tasowa Inna-wuro." Zaro idanunsa ya yi, da sauri ya kai hannunsa yana lalubar
aljihunsa.

"Bari na kira..."

"Ka kira wa?" Ta katse shi da faɗin hakan bayan ta tattaro girar sama da ƙasa ta haɗe waje
ɗaya. Dakatawa ya yi daga ƙoƙarin lalubo wayarsa da yake, cikin 'yar rikicewa ya ce

"A'ah.. wai da a kira shi a sanar da shi ta soma naƙuda." Numfashi Dada ta sauke har lokacin
ba ta saki fuskarta ba, ta ce

"Toh ga ka ga wayar nan ai sai ka kira." Daga haka ta juya ta koma cikin ɗakin. Fahimtar gatse
take masa ya sanya shi bin ta da kallo kawai ba tare da ya sake yunƙurin taɓa aljihunsa ba.
Daidai lokacin da ta saka ƙafarta cikin ɗakin, ya yi daidai da lokacin da kukan jariri ya cika cikin
ɗakin. Da sauri ta ƙarasa, cikin mamakin yadda haihuwar ta zo wa Inna-wuron a sauƙaƙe duk
da kasancewa ta fari ce. Kukan jaririn da take ji be sanya ta kula inda yake ba. Sai ƙarasawa da
ta yi cikin tashin hankalin da ya rufto mata lokaci guda. Ta sanya hannu ta riƙo Inna-wuro da tun
da babyn ya fito ta zube a wajen ba ta sake motsawa ba. Idanunta da ke motsawa a wahalce ne
ya sanya Dada sakin ajiyar zuciya. Sai a lokacin sannan ta miƙe ta saka hannu ta ɗauki babyn
da ke ta rusa kuka. Ta sanya shi cikin zani ta ajje gefe. Farawa ta yi da gyara Inna-wuro, cike da
kulawa kamar wani ƙwai haka take kula da ita. Abin da ya saka Inna-wuro sakin baki tana
kallanta cike da maɗaukakin mamaki. Sai dai ba ta ce komai ba, ta cigaba da bin komai da ido.


.. "Zan iya sanar da shi abin da aka samu?" Baffa da ke zaune a kan kujera ya faɗa yana kallan
Dada da ta fito daga cikin ɗakin.

"Hohoho.. Wai ni kam Malam me ye damuwarka da wannan haihuwar ne? Yoh har wani ma
abin alfahari ne a wajenmu da yarinyar nan ta haifi mace? Ka dai san a kan yarjejeniyar da aka
rabu, saboda haka don Allah ka dena mini maganar nan. Ka bar ni in ji da abin da nake ji."

Lumshe idanunta ta yi lokacin da kunnuwanta suka gama jiyo mata maganganun Dada. A
hankali ta kai kyawawan fararen idanunta kan babyn da ke kwance cikin zani tana bacci.
Hannunta ta kai ta ɗauke ta, ta ɗan gyara zamanta tana runtse idanunta. Murmushi ne ya
suɓuce mata a kan fuska lokacin da idanunta suka sauka a kan kyakkyawar farar fuskar jinjirar

da ke bacci cikin kwanciyar hankali, tana sauke numfashi a hankali. Kafe ta ta yi da idanunta
tana jin wata irin ƙaunar ta na ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci
idanunta suka fara juyewa zuwa ja. Ƙalubalen da ke cikin rayuwarsu shi ya soma faɗo mata.
Shin ko ita ɗin mahaifinta ze yi farin ciki da zuwanta duniya? Shin mahaifinta ze karɓe ta kamar
yadda kowanne uba ke karɓar ɗan da ya haifa? Shin akwai mutanen da ke farin ciki da zuwan
wannan halitta duniya ko kuwa ita kaɗai da ta haife ta ita ke farin ciki da zuwan ta? Sabuwar
ƙwallar da ta tarar mata a idanu ita ce ta sanya ta lumshe idanunta, tana jan kyakykyawar
babyn ta rungume a ƙirjinta. Wani irin sanyi na ratsa ta. Soyayyar ɗiyarta na shigar ta.

Kwana 5 da haihuwar jikinta ya soma komawa daidai. Ta ji daɗin jikinta ainun. Babynta ma da
yake tana samun isasshen abinci ya sanya ta yi kyau abin ta. Duk a tsawon kwanakin nan ta
ɗauka za ta ji Dada ko Baffa wani ya ce mata Alhaji Baita ya kira ta a waya dan jin lafiyarta. Sai
dai har aka shafe kwanaki ba ta ji daga gare shi ba, duk da dai ta san da ma hakan kan iya
faruwa.


... "Ya ce a ɗauki kuɗin rago cikin kuɗaɗen da yake turowa, sannan ya kuma ba ki wuƙa da
nama a kan zaɓar wa 'yarki suna. Ba shi da matsala da hakan, saboda haka wane suna za a
raɗa mata?" Baffa ya faɗa yana kallan Inna-wuro. Wani irin yawu me ɗaci ta haɗiye, karyayyiyar
zuciyarta na sake karyewa. Tausayin rayuwar ɗiyarta na sake kama ta. Kenan har rashin
muhimmancinta, da kuma son nuna be damu da abin da ta haifa ba ya kai ya kasa sakawa
'yarsa suna? 'yar da ya haifa da cikinsa? Ta ja wani numfashi da ƙyar kafin ta ce

"Baffa ka saka mata duk sunan da ya maka." Ta faɗa cikin ƙarfin hali, tana jira ta ji amsar da za
ta fito daga bakin Baffan. Kamar yadda ta tsammata kuwa sai cewa ya yi

"A'ah, kin ga ni fa cewa na yi ki faɗi sunan da za a sanya wa yarinya. Me ye garin gamina da ita
kuma? Ubanta ma be saka mata suna ba sai ni karan kaɗa miya?" Ya ƙare yana nuna kansa.
Daidai lokacin da Dada ta fito daga cikin ɗakinta tana kallan su. Ta taɓe baki kafin ta wuce
banɗaki. Dalili kenan da ya sa ba ta son cika magana da Baffan nata, don abubuwa da dama
kan zo cikin ƙwaƙwalwarta, tana sake ji duniyar na mata zafi, komai yana sake juye mata
saboda halin da Baffan ke nuna mata. Baffan nata da be daɗe da sauyawa ba.

"DANEEN, Allah Ya raya ta da imani." Ta faɗi abin da daga shi har Dadan suka kasa faɗa tun
da ta haihu. Tana gama faɗa ta miƙe.

"Ameen." Baffa ya faɗa. Ita kuma Inna-wuro ta wuce cikin ɗaki. Daidai lokacin da babyn ta soma
kuka, ta ƙarasa da sauri tana sakin murmushi ta ɗauke ta. Ta yi amfani da hannunta ɗaya wajen
ɗauke ƙwallar da ta sakko mata a kan fuska.

"Ya isa haka Shalele." Ta faɗa tana ƙarasawa ta zauna, ta shiga shayar da yarinyar tana kallan
kyakykyawar fuskarta da kullum kyawunta sake fitowa yake yi. A duk lokacin da za ta kalli
fuskarta sai ta tuna abubuwa da dama, abubuwan da suka faru a baya, da ma waɗanda take

hasaso tabbas za su faru nan gaba, idan dai ba Allah ne Ya taƙaita ba.

A ranar aka yanka rago aka kuma sanya wa yarinya suna DANEEN. Haka Inna-wuro ta cigaba
da kula da ɗiyarta cikin kulawa, so da kuma ƙauna. Ta gefe guda kuma Dada na sanya ido a
kan duk wani motsinta, sai dai ga mamakinta ba ta taɓa damuwa da ya Daneen ta tashi ba, ya
ta kwana, kullum burinta ta san lafiyar Inna-wuron. Dalili kenan da ya sa ta maida hankali sosai
wajen kula da 'yarta, tun da dai ita kaɗai ce ke son rayuwa da kuma lafiyarta.


.. Cike da damuwa ta ɗauki Daneen ta taɓa jikinta da ya yi zafi zau kamar wuta. Ta runtse
idanunta tana jin duk jikinta babu daɗi, ƙirjinta har wani bugawa yake saboda tsoro. Kuka
yarinyar ke yi sosai, Inna-wuro na rarrashinta. Tun tsakiyar dare har sai wajen asuba kafin
zazzaɓin ya sauka. Sai a lokacin sannan wani wahalallen bacci ya kwashe ta. A hankali ta
sauke ajiyar zuciya tana kafe Daneen da idanunta. Tausayinta na kama ta. Addu'a ta karanto ta
tofe ta da ita, ta ɗan ja zani ta sake lulluɓe ta da shi tana addu'ar Allah Ya sa kar zazzaɓin ya
sake dawowa.

.. Dada na tsakar gida tana dama kunu lokacin da ta fito daga cikin ɗakin, Baffa kuma na kan
kujera suna hira da Dadar. Ƙarasawa ta yi a hankali ta tsuguna, ta gyara kwanciyar Daneen da
ke hannunta ta ce

"Baffa don Allah alfarma nake nema a wajen ku." Ta faɗa tana jin ƙirjinta na bugawa, duk wani
fatanta a ce su amince da abin da za ta faɗa. Ba tare da ya ce komai ba ya ɗaga kai ya kalli
Dada da ta juyo tana kallan Inna-wuro.

"Me ya faru?" Dada ta faɗa cikin tsare gida. Sauke numfashi ta yi tana tunanin ta inda za ta fara.
Sai dai ta yi ƙarfin halin soma faɗin

"Don Allah Dada ku taimaka ku kira mini shi a samu a kai yarinyar nan asibiti. Wallahi kullum da
zazzaɓi take kwana cikin dare. Kun ga har ta fara ramewa wallahi." Ta ƙare tana sauko da
Daneen daga kan kafaɗarta. Ba tare da kowannen su ya ce komai ba, Dada ta kai hannu
goshin yarinyar ta taɓa. Ta ja tsaki kafin ta soma faɗin
"Maƙaryaciyar banza, ina zazzaɓin yake a nan? Kina jin jikin yarinya sanyi ƙalau ki ce zazzaɓi?
A'ah asibiti ne a kanta." Girgiza kai Inna-wuro ta yi ba tare da ta kalli Dada ba ta ce

"Wallahi da gaske nake Dada. A kwanakin nan kullum cikin dare da shi take kwana, ko bacci ba
ta iya wa sai ya sauka. Toh ina tsoron kar wani abu ya faru kuma."

"Ki ji nemawa kai bala'i kuma.." Dada ta faɗa tana riƙe haɓa.

"Kin ga ke.. Inna-wuro, maza koma ɗaki ki zauna tun da dai babu zazzaɓin. Yoh ki je ma ki
cewa likitocin me tun da babu zafi jikinta? Ki zauna duk sanda zazzaɓin ya dawo sai a san abin

da za a yi." Baffa da tun ɗazun be ce komai ba ya faɗi hakan. Ba ta sake cewa komai ba, sai
miƙewa da ta yi a sukwane, jikinta a matuƙar sanyaye ta saɓa Daneen a kafaɗarta ta wuce
ɗakinta.

"Ko dai a kira shi a ji ta bakin nasa ne?" Baffa ya faɗa bayan ya ga shigar Inna-wuro ɗaki. Da
sauri Dada ta juya ta kalle shi

"Wai ni kam manta yadda aka yi da shi ka yi? Dududu kwana nawa ya rage ta bar gidan nan?
Idan mun yi haƙuri da kansa fa ze zo ba sai mun kira shi ba. Kamar yadda aka yi da shi wata
biyu ciff bayan haihuwar, ina da tabbacin ba ze ƙara ba. Toh ni dai kar na sake jin kana wani
zancen kiransa. Mu kira shi mu masa me? A'ah don Allah."
"Toh shi kenan Uwar gida, ai komai kika ce ya zauna." Ya ƙare yana murmushi. Ita ma
murmushin ta yi tana maida hankalinta kan kunun da ke hannunta a cikin kofi.

.. Cikin ikon Allah kwanakin da suka biyo baya Daneen ba ta sake kwana da zazzaɓin ba. Farin
ciki kamar me haka Inna-wuro ta ji, ta din ga gode wa Allah tana cigaba da kula da 'yarta. Bayan
wasu kwanaki ga maɗaukakin mamakinta sai ta ga Dada da kanta ta soma gyara ta.
Magunguna kala-kala, da na sanyi da na gyara jiki haka ta din ga ba ta. Ita dai jiki a sanyaye
haka take bin Dadar, don ba kirki ne da ita ba. Ba ta ƙi ta ci mata cin mutunci ba a kan ko mene
ne.


... Tana zaune a cikin ɗakin, hannunta ɗauke da Daneen da ta yi wayo sosai. Ta ƙara kyau,
jikinta ya murje matuƙa. Ita kanta Inna-wuron ta ƙara wani irin kyau, don sosai jegon ya karɓe
ta, ta murje ta yi kyau abinta. Tun ɗazu take jiyo hayaniya daga tsakar gida, sai dai ba ta yi ko
da yunƙurin fita ba ne, tana cikin ɗakin tana hira da ɗiyarta.
"Inna-wuro! Inna-wuro." Ta jiyo muryar Baffa daga tsakar gida. Da sauri ta miƙe, sai dai cike da
takatsantsan, saboda Daneen da ta fara bacci. Ta kwantar da ita a hankali tana sake jin kiran da
Baffa ya yi mata har cikin kanta. Cikin ruɗewa ta amsa tana miƙewa ta fice, hannunta ɗauke da
ɗankwalin atamfar jikinta.
"Na'am Baffah." Ta sake faɗa daidai lokacin da gama fitowa daga ɗakin. Mummunan ganin da ta
yi, shi ne ya sanya ta dakatawa. Take zuciyarta ta soma harbawa lokacin da idanunta suka
sauka a kan Alhaji Baita, da ke zaune kan wata kujera, ya yi shirim. A ƙalla a shekaru ya ba wa
40 baya. Don a haife ya haifi Inna-wuro, wadda take da shekaru 18. Sai dai ba kowa ba ne shi,
face mijinta, mahaifin abin da ta haifa. Mutumin da kwata-kwata ba ta so ƙara ganin fuskarsa a
rayuwarta ba, ko don saboda nunawa da ya yi ƙiri-ƙiri ba ya son abin da ta haifa. Sauke
idanunta ta yi ƙasa, tana ji duk jikinta na yin sanyi, ko'ina na jikinta ya ɗauki rawa. Ba ta san
lokacin da ta zube a wajen ba, tana jin wata irin ƙwalla na taruwa a cikin idanunta. Shi kuwa
Alhaji Baita, tun da Baffa ya soma kiran sunan Inna-wuro ya kafe ƙofar ɗakin da idanunsa, har
zuwa lokacin da ta fito. Ya kafe ta da jajayen idanunsa, gaba ɗaya hankalinsa na tafiya kan

jikinta. So yake ya ga ko akwai wani canji da ze gani a jikinta. So yake ya ga ko ta sauya daga
ainahin Fatima, me kyau, me diri, wadda ta haɗa duk wani abu da yake buƙata a wajen mace.
Don kuwa ko daidai da canji ɗaya ya gani a jikinta, ko raguwar kyawunta, ko kuma yamutsewar
wani sashe na jikinta, toh tabbas a wajen zai sakar musu 'ya ba tare da an je ko'ina ba. Wannan
rawar jikin da duk wani abu da suke ba ze yi tasiri a wajensa ba...



Toh Alhamdulillah, bayan wani lokaci yau Allah Ya sake haɗa mu cikin wannan tafiyar, fatan za
ku karɓi wannan labarin da hannu bibbiyu kamar yadda kuka saba. Ina faɗa muku zazzafar
tafiya ce, me tsaya wa a rai. í ½í¸�❤️

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 02

__ Sai dai ga maɗaukakin mamakinsa, sai idanunsa suka ganar masa tamkar ma sauya masa
Fatiman aka yi. Ta ƙara kyau, ta wani irin murje. Duk da da ma Fatiman ba baya ba ce wajen
kyawun jiki, amma yanzun ta ƙara cika ta ko'ina. Ya saki murmushi har lokacin ya kasa ɗauke
idanunsa daga kanta. Hannunsa ya kai ya shafa kumatunsa kafin ya lumshe idanunsa yana
sauke wani gajiyayyen numfashi.

"Ina kwana?" Inna-wuro ta yi ƙarfin halin faɗin hakan, saboda wata uwar harara da Dada ke jefa
mata kamar idanunta za su faɗo ƙasa.

"Ahh lafiya ƙalau Fatima." Ya faɗa yana murmushi, kafin ya ɗora da faɗin

"Ya kamata mu tashi mu tafi koh?" Ya ƙarasa maganar har lokacin yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login