Showing 45001 words to 48000 words out of 81712 words
Chapter 16 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
bayan mai napep ɗin. Har zuwa lokacin da
suka isa emergency. Cikin gaggawa aka karɓi Ameer saboda yadda jikinsa ya yi mugun
tsamari. Daneen ta zube a kan gwuiwoyinta tana sake fashewa da wani sabon kukan. Ta jima a
wajen, ba tare da ta san abin da ya ci gaba da faruwa ba. Ita dai burinta ɗaya ta ji halin da
ɗan'uwanta yake ciki.
"Ki yi haƙuri, In Sha Allah zai samu sauƙi. Addu'a za ki yi masa ba kuka ba." Ta jiyo muryar mai
napep ɗin nan yana faɗa mata. A hankali ta ɗan ɗaga jajayen idanunta ta kalle shi, da ƙyar cikin
dashashshiyar murya ta ce
"Na gode sosai, Allah Ya saka maka da alkhairi." Ta faɗa tana lumshe idanunta.
"Babu komai." Ya faɗa, kafin ya gyara tsayuwarsa ya ce
"Bari na wuce, Allah Ya ƙara sauƙi. In Allah Ya yarda zuwa an jima zan shigo."
"Toh." Ta faɗa a sanyaye. Ko minti 5 bai yi da tafiya ba, aka nemi ganin waɗanda suka kawo
Ameer. Da wani irin sauri Daneen ta miƙe ta shiga office ɗin likitan. Gwaje-gwaje aka ba su
rubuce a takarda. Ita dai Daneen ba wannan take buƙatar ji ba. Don haka ta luma ƙwayar
idanunta cikin na likitan ta ce
"Don Allah ya jikin ƙanina?" Sai da ya kalle ta, ya ɗan yi jimm kafin ya ce
"In Sha Allah zai samu sauƙi. A je a kawo gwajin nan yanzun nan, za mu san abin yi ne bayan
an yi su." Cikin sauri ta jinjina kai, ba ta sake cewa komai ba ta fice daga office ɗin. Sai kuma da
ta fito ɗin sannan ta dakata tana kallan takardar tamkar idanunta za su faɗo. Sai a lokacin
ƙwaƙwalwarta ta tuna mata babu ko sisin kwabo a jikinta, ba kuma ta da wanda za ta tunkara ya
ba ta kuɗin yin gwajin. Ta lumshe idanunta tana ambatar sunan Allah daidai lokacin da ƙirjinta
ya wani irin bugawa. Buɗe idanunta ta yi, ta shiga jefa su cikin asibitin kamar mai neman wani
abu. Cikin rashin sanin abin yi ta shiga taka ƙafafunta, tunani birjik cikin ƙwaƙwalwarta, mafita
kawai take nema, mafita kawai take so. Ameer take so ya sami lafiya, toh amma ta ya ya? Tana
ci gaba da waɗannan tunanukan sai tsintar kanta ta yi cikin harabar asibitin. Ta sake wuwwulga
idanunta tana kallon mutanen da ke zaune, wasu na tsaye, wasu kuma na hira. Kai tsaye ta
soma takawa, ba ta jira komai ba, ta tsuguna har ƙasa lokacin da ta isa dab da wata mota,
wadda wani babban mutum ke tsaye, gefensa kuma wata mata ce, ya yin da wani saurayi da a
ƙalla zai yi shekaru 30, ke kusa da mutumin.
"Don girman Allah ku taimaka mini da kuɗin gwajin waɗannan, ƙanina ne ba shi da lafiya, kuma
ba ni da komai, don Allah ku taimaka mini." Ta yi maganar idanunta a kan mutumin.
"Ka ga halin mutanen koh? Har sun fara." Matar ta faɗa tana jan tsaki a ƙarshen maganar tata.
Kallon Daneen mutumin ya yi, kafin ya maida dubansa kan matarsa ya ce
"Idan ma ba su fara ba ba ni da nutsuwar saurarar kowa a yanzu.. Kai Yohanah ina jiran ka, kar
ka ƙara ko da minti 10 ne a kan lokacin da na ba ka. Na dai faɗa maka, ka kuma kiyaye." Ya
ƙare maganar yana kallon saurayin da ke gefensa, wanda ke sanye cikin wata riga da wando
crazy. Kansa da wani banzan aski, ya yi cibiri-cibiri a tsakiyar kan.
"Toh sai na ƙaraso." Ya faɗa da gurɓatacciyar hausarsa, da tun daga fara maganarsa za ka
fahimci ba bahaushe ba ne. Ko da yake fuskarsa ma kaɗai ka kalla za ka iya fahimtar hakan,
daga zarar kuma ya yi magana shi ne za ka tabbatar. Bai jira wani ya sake cewa komai ba ya
faɗa cikin motar, matarsa na gefensa ya ja ya fice daga asibitin. Daneen ta bi su da kallo tana
jin wata faɗuwar gaba na kama ta. A hankali ta ɗan sake runtse idanunta tana miƙewa a kan
ƙafafunta, har lokacin idanunta na bin ƙurar da mutumin nan ya bari.
"Nawa kike buƙata?" Ta ji an ambata daga bayanta. Da sauri ta juyo har tana ƙoƙarin yin
tuntuɓe ta kalli matashin saurayin da a kira da 'Yohana'. Kawai sai ta miƙa masa takardar.
Maimakon ya kalli takardar, sai ya ci gaba da bin ta da kallo, tun daga sama yake kallon ta har
ƙasa, wanda har hakan ya ɗan so ya sa ta tsargu, har ta kai ga ta soma janyo addu'a cikin
zuciyarta. Sai ya maida dubansa kan takardar ya shiga karantawa.
"Mu je." Ya ambata yana yin gaba. Babu musu Daneen ta soma binsa. Hausarsa kwata-kwata
ba ta da daɗin saurara, saboda yadda bai iya ta ba, kawai dai yana kwaɓawa ne. Dukkan kuma
wasu alamu sun nuna yarinyar nan da ke gabansa ba lallai ta iya turanci ba. Don haka suna ci
gaba da tafiya ya ce
"Kina son taimako a kan duk abin da kike so na yi miki?" Duk da ya yi maganar a juye, amma
tabbas ta fahimce shi, dalili kenan da ya sanya ta jinjina kai tana faɗin
"Ehh don Allah." Ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya ce
"Alright, I will help you, but ke ma za ki taimaka mini a kan wani abu. Get it?"
"Zan taimaka maka idan dai har ka taimake ni, ni dai burina kawai ɗan'uwana ya samu lafiya."
"Ohk don't worry, he will be fine soon." Duk da ba wani turanci ake yi musu a makarantarsu ba,
amma tabbas ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta jinjina kai kawai.
Har bayan shuɗewar wasu awanni Daneen na tare da Yohana, bayan an yi wa Ameer
gwaje-gwajen da likita ya buƙata. Kuma da taimakon Ubangiji, taimakon gaggawar da aka ba
shi ya taimaka masa matuƙa, wanda har bayan dawowarsu daga gwajin ya samu wani
wahalallen bacci ya ɗauke shi. Sosai Daneen ke ci gaba da jajanta kirkin Yohanah, don duk
wasu alamu sun nuna ba musulmi ne ba. Abin da ya sa kuma ta ƙara tabbatarwa, shi ne da
lokacin Sallah ya yi ba ta ga ya tashi ya yi ba. Sai dai taimaka matan da ya yi, ya matuƙar yi
mata daɗi, ta kuma gode wa Allah da ya kawo mata shi a irin wannan lokacin da ta ke buƙatar
taimako.
.."Zuciyarsa ta yi raunin da ana buƙatar a yi masa aiki, idan ba haka ba a kowanne irin lokaci za
a iya rasa shi." Likitan ya faɗa yana kallan Yohanah. Dama ya san da wuya idan ba haka ne zai
faru ba, saboda yadda shi kansa da ba likita ba ya ga yanayin Ameer ɗin, da kuma gwajin da
aka masa. Hannu ya miƙa wa likitan suka gaisa kafin ya fita daga office ɗin. Kamar yadda ya
tsammata kuwa, Daneen na ƙofar tana jiran sa. Kallon sa kawai take yi, tana jira ta ji abin da zai
ce. Fahimtar hakan ya sanya shi faɗin
"Ana buƙatar a yi masa aiki a zuciya." Wani irin jiri ne ya kwashi Daneen, lokaci guda wani duhu
ya zo ya mamaye ganinta. Ta yi gefe za ta faɗi, duk da yadda take ƙoƙarin ganin ba ta zube ba.
Dalili kenan da ya sanya Yohana kai hannunsa ba tare da wani tunani ba ya riƙo ta. Wani irin
runtse idanunta ta yi, tana komawa kan ƙafafunta, ta yi maza ta buɗe a kan hannunsa da ke kan
nata hannun, sai kuma ya yi saurin janyewa yana furta
"Sorry girl, Sorry please." Ya faɗa saboda yadda ya ga tana bin sa da wani irin kallo. Ba tare da
ta bi ta kan abin da yake faɗa ba, ta zube a kan ƙafafunta tana jin yadda bugun zuciyarta ya
ƙaru. 'Aiki a zuciya?' Shi ne abin da take ta maimaitawa, hawaye tuni sun cika mata idanunta.
"Stop crying Cutie. Ki tashi mu samu mafita." Ya faɗa yana kallan yadda take kuka kamar Baby.
Duk wasu alamu sun nuna yadda take matuƙar ƙaunar ɗan'uwanta. Gaba ɗaya aikinta da kuma
maganganunta sun nuna shaƙuwa da kuma tsananin ƙaunarta da ɗan'uwanta. 'Me hakan ke
nufi?' Ya tambayi kansa. Sai kuma ya yi gefe, ya fito da wayarsa daga cikin aljihu ya danna wa
wata number kira.
"What's going on?" Ya faɗa bayan an ɗaga wayar. Shiru ya yi na ɗan wasu sakanni, yana
saurarar abin da ake faɗa masa daga can ɓangaren, kafin ya ce
"Ya yi, send me the address now! I will call you later."
"Ohk." Ya sake faɗa bayan wasu sakanni. Jefa wayar ya yi cikin aljihu kafin ya koma inda ya bar
Daneen, da ke zube a wajen tamkar wadda aka dasa.
"Tashi mu tafi." Da sauri ta ɗaga idanunta ta kalle shi. Ya jinjina mata kai kana ya ce
"Ehh, asibiti za mu sauya.. Za ki iya sadaukar da wani abin da kika mallaka saboda
ɗan'uwanki."
"Matuƙar dai zai samu lafiya." Ta faɗa tana jinjina kai.
"Ohk let's go. But let me go and meet the doctor, I will explain everything to him. Wait for me
here." Daga haka bai jira ta ce komai ba ya faɗa cikin office ɗin. Wajen minti 20, sai ga shi ya
fito, tana tsaye kamar yadda ya bar ta. Ya miƙa mata takardun hannunsa kafin ya wuce ɗakin da
Ameer yake.
Runtse idanunta Daneen ta yi tana sake gode wa Allah. Ba don Allah Ya kawo mata Yohanah
ba, da ba ta san yadda za ta yi ba. A bayan motar Yohanah ɗin aka kwantar da Ameer, da
na'ura ke taimaka masa wajen numfashi. A gaban motar Daneen ta zauna, ya yin da shi kuma
ya zauna wajen mai tuƙi. Babu ɓata lokaci ya ja motar suka fice daga cikin asibitin. Suna tafiya
Daneen na juya wa baya ta kalli Ameer, sai kuma ta dawo ta ci gaba da kallon titi. Ganin abun
take tamkar a mafarki, tamkar ba Ameer ɗinta ba. Har suka yi tafiya mai nisa ba ta daina
tunane-tunane ba. Tun daga bakin asibitin za ka fahimci lallai babban asibiti ne, babban ma irin
babban da ya amsa sunansa babba. Hamshaƙi, haɗaɗɗe wanda kallo ɗaya za ka masa, ka san
ya lamushe kuɗaɗe da yawa wajen gina shi. Idan kuwa aka shiga ciki ba za ka taɓa zata a cikin
Nigeria kake ba, saboda matuƙar haɗuwa da ya yi. Kai tsaye a inda aka tanada don ajje motoci
Yohanah ya yi parking na motarsa, Daneen kuwa ban da ci gaba da kallon cikin asibitin babu
abin da ta yi, mamaki take toh me ya kawo su nan ɗin? Saboda yadda duk wasu alamu suka
nuna nan ɗin bai yi kama da inda za a taimaka wa talaka ba. Ita tun da take ma, ko kuma ta ce
tun da suka shigo garin Kano ba ta taɓa ganin waje mai kyau da tsaruwa irin wannan ba. Sai
dai da yake gaba ɗaya hankalinta yana kan Ameer ya sa yana ida yin parking ta sauka daga
motar ta koma inda Ameer yake. Shi ma saukar ya yi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka shigar da
Ameer cikin asibitin, da cikinsa ya fi harabarsa tsaruwa nesa ba kusa ba.
.. "Akwai wani cikin asibitin nan, mahaifinsa mugun mai kuɗi ne. Ƙodarsa ce ta lalace, ana
buƙatar a sauya masa wata. Saboda haka idan dai har kika sadaukar da ƙodarki ga ɗansa, toh
tabbas ko ma nawa ne, ko nawa ake buƙata, zai biya a yi wa Ameer aiki. Zai iya fitar da shi ma
waje ƙwararrun likitoci su yi masa aiki. Ƙodarki guda ɗaya kawai za ki bayar, daga nan ki saka a
ranki ɗan'uwanki ya samu lafiya." Tun da Yohanah ya fara magana Daneen ke kallonsa, tana
rarrabe duk wata kalma da ya faɗa. Har bayan kusan minti ɗaya da gama maganar ba ta ce
komai ba. Sai zuwa can sannan ta ce
"Ka tabbatar zai biya a yi wa Ameer aiki? Ko da an yi aikin kuma na mutu idan na bar Ameer a
hannunka za ka kai mini shi wajen mahaifiyarmu?" Daneen ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta.
Murmushi Yohanah ya yi, yana ɗan shafa gefen kumatunsa. Sai da ya soma girgiza kai sannan
ya ce
"Nothing will happen. Just pray as much as you can, za a yi komai cikin nasara. Za ki samu
lafiya, ɗan'uwanki ma haka." Ya yi maganar a nutse saboda ya ba ta ƙwarin gwuiwa. Ganin ta
sake yin shiru ne, ya sanya shi faɗin
"Za ki iya zuwa ku yi magana da doctor, zai yi miki bayanin komai himself." Ajiyar zuciya
Daneen ta sauke, kafin a hankali ta buɗe baki da ƙyar ta ce
"Na amince." Ba ƙoda ba, ko da zuciyarta ce za ta iya sadaukar wa a kan ɗan'uwanta, matuƙar
zai samu lafiya. Ballantana ƙoda da aka ce mata guda biyu ce. Ubangiji Allah Ya dubi zuciyarta
Ya ba wa ɗan'uwanta lafiya, da ita kanta da za a ciri wani abu daga cikin jikinta. Shi kuma
wanda zai siya ƙodar tata Allah Ya sa ya ji tausayinsu, ko da kuɗin da ake buƙata wajen yin
aikin, ya fi kuɗin da ya yi niyyar bayarwa, ya taimaka ya biya gaba ɗaya. Ya kuma saka a yi
aikin cikin nasara.
Wani irin murmushi Yohanah ya saki, yana sauke ajiyar zuciya. Kai tsaye ya shiga office ɗin
likitan don yi masa bayanin abin da ya kawo su cikin asibitin. Duk da da farko ba su nuna ba,
don sai da ya bari aka karɓi Ameer tukunna, bayan ya ajje kuɗi masu ɗan tsoka kamar yadda
yake a tsarin asibitin.
A sanyaye Abeey da ke sanye cikin wata bluen shadda, ɗinkin babbar riga, ya ke takawa zuwa
cikin ɗakin. A hankali ya ɗora hannunsa kan hannun ƙofar ya tura. Har lokacin Maama na zaune
kusa da ɗanta hannunta na cikin nasa. Yana kwance kan gadon, rabin jikinsa lulluɓe da bargo,
ya yin da idanunsa ke a lumshe tamkar mai yin bacci. Ɗaga idanunta Maama ta yi ta kalli
Abeey, bayan ta amsa sallamarsa. Ya ƙarasa cikin ɗakin, idanunsa na kallan fuskar ɗan nasa
da ta yi fayau, ya ce
"Sannu Tareeq." Ya faɗa yana kallansa cike da tausayawa. A hankali ya shiga buɗe idanunsa
da suka masa nauyi. Ya sauke su a kan Abeeyn, yana sauke numfashi a hankali kamar wanda
ya yi aikin wahala.
"Sannu." Maama ta faɗa a hankali. Sai ya jinjina kai yana ƙaƙalo murmushi ya wanzar a kan
fuskarsa kafin ya ce
"Yawwah." Ya ƙare har lokacin da murmushin ƙarfin hali a fuskarsa.
"Yanzu dai ba ka isa ka ce mini ka warke na yarda ba. Ka ma daina mini wanna yaƙen. Ni na fi
so ko me kake ji ka sanar da ni Tareeq. Ba garin wannan ɓoye abin da ke damunka ɗin ba ne
ya janyo haka ba. Ni dai Abeey ka faɗa masa ya daina wannan ɗab'iar tasa, idan da wani abun
ya same shi kafin mu ankare fa? Ko kuma abin da ke damun nasa bai fito fili ba ya ci gaba da
cin sa a cikin jikinsa fa?" Ta ƙare maganar tana kallan Abeey. Murmushi Abeey ya yi kana ya ce
"Ya isa haka, shi kenan faɗan ya isa haka. Yanzu dai ki yi haƙuri ki.." Kafin ya kai ga ƙarasa
maganar, wayarsa ta ɗauki ruri. Ya zube idanunsa a kan wayar, ganin doctor ke kiransa ya
sanya shi saurin ɗagawa. Shiru ya yi na tsawon mintina yana saurarar abin da likitan ke faɗa.
Suka ɗan yi magana kafin ya ajje wayar. Ya kalli Maama murmushi na tashi a kan fuskarsa ya
ce
"Tun kafin a je ko'ina, har an samu yarinyar da za ta sadaukar da ƙodarta gun yaronki." Da
matuƙar mamaki Maama ta ce
"Da gaske Yallaɓai? Ita kuwa me take buƙata a rayuwarta wanda za mu iya biyan ta da shi?" Ta
tambaya wani irin murmushin farin ciki na tashi a kan fuskarta.
"Abin mamaki, Likitan ya sanar da ni ba ta buƙatar komai." Shiru Maama ta yi tana kallon Abeey
cike da mamakin jin furucinsa.
"Ba ta buƙatar komai kuma?" Jinjina kai Abeey ya yi kafin ya ce
"Ya ce ta bayar da ita ne saboda a yi wa ɗan'uwanta da ke kwance cikin asibitin nan addu'ar
Allah Ya ba shi lafiya. Ban da wannan ba ta buƙatar ko sisi."
Littafin DANEEN na kuɗi ne, a kan 500. Sai dai daga farko har ƙarshen Book 1 free ne, Book
2&3 shi ne na kuɗi kuma duka a kan 500. Har yanzu kuma muna cikin Book 1 ne, wato (Free
pages). Waɗanda za su fara payment yanzu, su tuntuɓe ni ta 08124818273. Waɗanda kuma sai
mun gama Book 1 ne za su yi payment, zan saka muku yadda za ku yi a last page na Book 1.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 19
Jinjina kai Maama ta yi cike da mamakin jin abin da Abeey ya faɗa. Ta sauke ajiyar zuciya kafin
ta ce
"Allah Sarki! Amma abin kam da mamaki. Allah Ubangiji Ya saka mata da alkhairi, Ya ba wa
ɗan'uwanta lafiya."
"Ameen." Abeey ya amsa da hakan, har lokacin annurin fuskarsa yana nan. Tun da Abeey ya
fara magana Tareeq yake kallon sa har ya ƙare. A hankali ya ɗan gyara kwanciyarsa lokaci
guda yana lumshe idanunsa. Da sauri Maama da ta lura da shi ta taso tana faɗin
"Me ya faru?" Girgiza kansa ya yi lokaci ɗaya yana buɗe idanunsa. A hankali ya soma faɗin
"Abeey wace ce ita? Ina son ganin ta tukunna." Ya faɗa cike da ƙarfin hali.
"Oh Yah Ilahy Tareeq, ka samu ka samu ka yi bacci kafin mu ji abin da Likita zai