Showing 12001 words to 15000 words out of 81712 words

Chapter 5 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

amsa yana ɗaukar wayarsa da ke ajje a gefen sa. Daidai lokacin da Hidaya ke
faɗin

"Yaya tun jiya duka gida sun damu da ganin ka, ni ma kasa jurewa na yi shi ya sa na sake zuwa
in duba ka. Please ka je ko za su ji daɗi." Jinjina kai ya yi, har lokacin idanunsa na kan waya.
Miƙewa Hidaya ta yi ta ce a nutse

"Bari na je Yaya, na ga kamar aiki kake yi." Sai a lokacin ya ɗaga idanunsa a nutse ya kalle ta.
Ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe, ya buɗe bakinsa kamar wanda ba ya son yin maganar
ya ce

"Olright, take care of ur self soulsis. Zan shigo zuwa an jima In Sha Allah." Ya ƙare da ɗan
gajeren murmushin nan nasa da ya kasance na dabi'a. Yana matuƙar ƙaunar er uwar tasa,
kasancewar ta mace ta farko da ta fi kowa damuwa da damuwarsa, ta fi kowa fahimtar sa idan
yana cikin damuwa. Ta fi kowa shiga damuwa idan ta gan shi cikin rashin walwala. Shi ya sa
duk lokacin da take kusa da shi, ya kan yi ƙoƙari wajen wanzar da murmushi ko da kuwa yana
da damuwa don kar ma ta fi shi shiga damuwa.

"In Sha Allah Yaya. Amma don Allah ka cire Diyana a ranka, ka manta da rayuwarta.." Hannu ya
ɗaga mata alamar ta dakata kar ta ƙarasa maganar da ta fara. Tuni annurin fuskarsa ya ɗauke.
Shi haka rayuwarsa take, idan dai har ya bar abu toh ya bar shi har abada. Shi ya sa ma ba ya
saurin yanke hukunci har sai ya tabbatar da abu. Ganin tana shirin ɓata masa rai ne ya sanya ta
faɗin

"Don Allah Yaya ka yi haƙuri.." Ta faɗa tana kama kunnenta. Ɗan sauke gajeriyar ajiyar zuciya
ya yi kamin ya ce bayan ya ƙaƙalo murmushi a kan fuskarsa

"Kar ki ƙara." Girgiza kai ta yi tana faɗin

"Ba ma zan ƙara ba har abada." Ta ƙare tana murmushi. Daga haka ta yi sallama da shi ta fice
daga ɗakin. Ya ja laptop ɗin gabansa ya cigaba da abin da yake yi a ciki.


.. Sanye take cikin doguwar rigar atamfa mai matsakaicin kyau, tana sanye da hijabi dogo
wanda ya wuce gwuiwarta. Tafiya suke yi tare ita da wani ɗan saurayi wanda kusan tsayin su
ɗaya, sai dai kasancewar namiji ya sa ya fita tsayi. Jefi-jefi su kan ɗan yi magana, har zuwa
lokacin da Ameer da ya kalli Daneen ya ce
"Adda wai kin ma san wani abu kuwa?" Girgiza kai ta yi tana ɗaga manyan fararen idanunta ta
kalle shi sannan ta ce

"A'ah." Ta yi maganar tana cigaba da tafiya.

A haka idan ka kalle su za ka iya cewa Ameer ne babba, sai dai nutsuwa da yanayin yadda
Daneen ke abubuwanta da suka wuce na shekarunta, ya sa ake gane ita ce babba. Kyawun
nan da ta taso da shi tun yarinta, har yanzu babu abin da ya ragu. Sai ma ƙaruwa da ya yi, ta
ƙara zama wata irin kyakykyawa, don kaff rigarsu tana sawun farko cikin kyawawan 'yan matan
ƙauyen. Idanunta manya ne, kamar yadda tun yarinta suke, sai dai yanzu asalin kyawunsu, da
kuma yadda suke a halitta sun ƙara bayyana. Tamkar idanun mage haka suke, masu kyau da
kuma ɗaukar hankali. Wani irin shape na da su na musamman, wanda ko iya kyawun idanunta
aka tsaya an gama tashi. Siririn hanci gare ta, wanda ta gado shi daga wajen Inna-wuro. Don ko
kaɗan, daga ita har Ameer ba su ɗauko ko abu ɗaya daga wajen Alhaji Baita ba. Bakinta kuwa
ƙanƙantarsa kaɗan ne ya ƙaru tun yarinta. Haka yake ɗass a bakinta, ja ne matuƙa, irin jan nan
mai ɗaukar hankali. Don sau da dama idan ta je makaranta a kan ce sai ta goge jan bakin da ta
shafa a bakinta kafin ta shiga aji. Idan ta ce ba ta shafa ba, wasu ba sa yarda, har sai ta saka
gefen hijab ɗinta ta goge bakin nata, sai dai maimakon janbakin da suke iƙrarin ta shafa ya fita,
sai bakin ya sake ɗaukar ja saboda gurje shin da ta yi. Duk wani abu da ake buƙata a jikin
kyakykyawar mace Allah Ya ba wa Daneen. Ƙarancin shekarunta ba su nuna wa a jikinta
saboda tarin nutsuwa da take da ita. Sai dai idan fuskarta ka kalla shi ne za ka gano zallar
yarintar da ke tattare da ita. Sanyi ne da ita tamkar me, ba ta da hayaniya ko kaɗan. Ko da
kuwa a cikin jama'a ne, za ka same ta shiru babu hayaniya, idan dai har ba tare da rabin jikinta
Ameer take ba, toh shi ne za ka ji bakinta sosai. Shi ma Ameer kyakykyawa ne, don kamar su
ɗaya ma da Daneen ɗin, sai dai duk kyawunsa ta fishi, musamman kuma don kasancewarta
mace.

"Mutumin nan fa yau ma sai da ya." Tun kafin ya ƙarasa ta katse shi da faɗin

"Kaa ga Ameer na faɗa maka ka fita harkar wanda ba ka sani ba koh? Wallahi ba ka jin
magana." Ta ƙare maganar tana hararar sa. Dariya ya yi, yana so ya ga Daneen ɗin na masa
faɗa, sam ba ma ta iya haɗe ran ba. Kuma ma wani idan ya gan su tana masa faɗan zata zai yi
rashin kunya take yi wa yayanta. Tun da dai a tsaye ya fita girma, dan ma dai ba shi da ƙiba ne,
haka yake siriri sai tsayi.

"Toh Adda na dena." Ya faɗa daidai lokacin da suka iso ƙofar gida. Da sallama suka shiga cikin
gidan, Dada na zaune kan kujera tana cin gyaɗa marau, ya yin da Baffa ke zaune kan tabarma
yana saurarar Radio. Dukansu girma ya bayyana sosai a jikinsu, sun sake zama dattijai matuƙa.
Tun da suka shigo gidan sai suka kama kan su, don sanin halin masu gidan.
"Baffa barka da wannan lokacin, Dada barka da wannan lokacin." Suka haɗa baki wajen faɗar
hakan. Ba tare da sun jira jin cewar wani daga cikin su ba suka wuce ɗakinsu, ɗakin da yanzu
Inna-wuro ta yi masa dabara ta samu ta fitar wa da Ameer inda yake kwana. Don sun san in dai
Dada ce ba amsa wa za ta yi ba, shi kuma Baffa ko ya yi niyya idanun Dada ba za su bar shi ya
amsa ba.

"Sai da na ce miki mu tafi wajen Inna ba ta dawo ba, ni na ji hakan a jikina." Ameer ya faɗa
lokacin da suka gama shiga ɗakin nasu babu Inna-wuro a ciki. Ita ma Daneen ɗin tura mitsitsin
bakinta gaba ta yi kafin ta ce

"Allah na ɗauka ta dawo fa."

"Toh mu koma mana." In ji Ameer. Girgiza kai ta yi ta ce

"Dada na tsakar gida shi ne za mu fita, chaɓɓ.. Ba inda za mu je." Ta ƙarasa maganar tana
neman waje ta zauna.

"Kai Adda."

"Na gama magana." Ta faɗa tana jefa masa harara.

"An gama The Babbar Yaya." Ya ƙarashe maganar yana dariya. Shi ma neman waje ya yi ya
zauna, sai suka shiga bitar littafan makaranta. Don ko a makarantar ma ajinsu ɗaya har
islamiyya. Sai dai ko minti 10 ba su yi ba muryar Dada da ta ke magana cikin ɗaga murya ta
katse su.
"Ina waje ina aiki kuna cikin ɗaki koh? Toh ku fito kai ka je mini gonar Habule ka tsinko mini
zogale. Ke kuma ki zo ki je ki ɗebo mini ruwa..
Za ku fito ne ko sai na ci uwarku." Ambatar sunan uwar da ta yi ya sanya duk jikinsu ya yi sanyi,
ɓacin rai ya taso wa Ameer da yake ya fi Daneen zuciya. Shi idan ta shi ne in da ubansu ta ce
toh da sauƙi. Tun da dai be san waye uban nasu ba, abu ɗaya ya sani kawai duk lokacin da
suka yi wa Inna-wuro zancen wani abu da ya shafi mahaifinsu ranta kan ɓaci. Wannan dalili ne

ya sa suka jefar da maganar tasa gefe suka dena yi. Girman mahaifiyarsu na ƙaruwa a
zuciyarsu, domin su a wajen su ita ce uwa, kuma ubansu. Miƙewa Daneen ta yi, ganin Ameer
be ko da motsawa ba ne ya sanya ta faɗin

"Ameer tashi mu je."

"Ni ba inda zan je." Ya faɗa yana ɗauke kai. Hannunta ta kai ta dafa kafaɗarsa a sanyaye ta ce

"Don Allah ka yi haƙuri Ameer ka tashi mu tafi, idan Inna ta ji Dada ta saka mu aiki ba mu yi ba
ba za ta ji daɗi ba. Ka yi haƙuri ka ji?" Shiru ya yi na tsawon sakanni kafin ya miƙe ba don ya so
ba. Ya haɗe fuska don ba kaɗan ba ransa ya ɓaci. Kuma sanin kanta ne ita Dadar Habule ya
hana mutane shigar masa gona tsinkar wani abun, don ba shi da mutunci ko kaɗan, a kan ko da
ganye ɗaya ne be ƙi ya ya ci maka mutunci ba, ya zage kaff danginku hankalinsa kwance. Ɗebo
ruwa kuma da ta aiki Daneen ta yi ta san sarai an hana mata zuwa rafin, saboda gurɓatattun
samari da ke zama a wajen. Ko kuma su laɓe, ba sa tashi fitowa sai 'yan mata sun zo ɗibar
ruwa. A can aka kama wasu samari su huɗu sun yi wa wata yarinya fyaɗe, kafin a kai ta asibiti
ta rasu. Wannan dalilin ne ya sa aka hana mata zuwa ɗibar ruwan, aka kuma samar da rijiyoyi
don abin ya zo da sauƙi.

"Kar ka sake ka siyo mini na siyarwa ba na so, idan ma shi ka siyo zan gane. Ni ba sa'ar ka ba
ce, don haka inda na aike ka can nake nufi ka je. Ke kuma sauri nake na ba ki mintuna biyar ki
kawo mini ruwa in ɗora tuwo kar ya min dare. Idan kika sake kika wuce billahillazi sai na ci
ubanki a cikin gidan nan." Dada ta faɗa lokacin da suka fito daga ɗakin. Ba su ce komai ba, sai
ficewa da Ameer ya yi, ya yin da Daneen ta ƙarasa ta ɗauki wani tulu ta yi waje da shi. Baffa da
tun da ta fara magana be ce komai ba, sai a lokacin ya bi su da kallo, har lokacin kuma be ce
komai ba. Dogon tsaki Dada ta ja tana ƙarasa jefa gyaɗa guda ɗaya da ta yi ragowa a
hannunta, sannan ta miƙe don iza wutar girki.

"Wai ana sallama da Baffan Inna-wuro." Wani yaro da ya shigo gidan bayan fitar su Daneen ya
faɗa yana kallan Dada. Juyawa ta yi ta kalle shi kafin ta maida duban ta kan Baffa, ba ta ce
komai ba, sai sake mayar da idanunta da ta yi kan yaron ta ce

"Je ka ce yana zuwa." Fice wa yaron ya yi daga gidan, ya yin da Dada ta ɗaga murya tana faɗin

"Ai dai kana ji ana sallama da kai." Miƙewa Baffa ya yi yana faɗin

"Naa ji kam." Daga haka ya fice daga gidan. A bakin mota ya hango wani mutum tsaye, sanye
cikin babbar rigar shadda, da hula zannabukar a kansa. Tsayawa ya yi da mamaki shimfiɗe a
kan fuskarsa yana kallansa, don kwata-kwata bai shaida fuskar ba. Ganin fitowar Baffa ya saka
mutumin ƙarasawa cike da girmamawa ya miƙa wa Baffa hannu yana faɗin
"Salamu Alaika.." Karɓar hannun nasa Baffa ya yi yana amsa wa a hankali kamar wanda ke jin
tsoro. Cikin girmamawa mutumin ya sanar da shi shi ne wanda yake sallama da shi. Gyara

tsayuwa Baffa ya yi kafin ya ce

"Sai dai ban shaida fuskar ba." Sauke numfashi mutumin ya yi kafin ya soma faɗin

"Da farko dai sunana Abubakar Bashir, ni ɗan kasuwa ne, wanda ke harkar siye da siyarwa a
cikin garin Kano har ma da wajen ta. Matata Allah Ya Yi mata rasuwa, ina da 'ya'ya waɗanda ke
tare da ni. A taƙaice dai na ga 'yarka ne, wadda aka tabbatar mini da nan ɗin nan ne gidan
mahaifinta shi ya sa na zo don neman izini." Cike da mamaki Baffa ya ce
"Wace 'yar tawa kenan?"

"Fatima!" Ya faɗa kai tsaye.

"Ikon Allah." Baffa ya faɗa cike da mamaki, don kuwa zai iya cewa a tsayin shekaru sha biyar
da suka gabata, babu wani da ya taɓa zuwa ya ce yana son Inna-wuron. A hankali Baffa ya
ɗaga kansa ya dubi kamilallen mutumin, bai san me ze ce masa ba a yanzu dai kam. Domin
kuwa tamkar ba shi ne uban ba, ba shi da ikon yanke hukunci sai abin da Dada ta faɗa. Don ko
ya ce zai yanke ma, idan Dada ta faɗi saɓanin abin da ya yanke dole ne ya bi. Shi ya sa ma ba
zai yi gaggawar yanke hukuncin ba, saboda kar mutunci ya zo ya zube daga baya. Dada da ke
leƙe daga soro, ta sake leƙo da kanta don sake tabbatar da da gasken mota take gani zaune a
ƙofar gidansu, kuma mallakin mutumin da ya zo neman auren Inna-wuro??

#MAFARI..


Na gode sosai da addu'oinku. Waɗanda suka kira ni, waɗanda suka mini gaisuwa ta DM, har
ma da waɗanda suka mini cikin group. Thank yhu all for your kind words and condolences. I do
appreciate, Allah Ya bar zumunci.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 06

__"Shi kenan, In Sha Allah zan neme ka zuwa gobe. Zan ɗan yi tunani sannan na yi shawara
da matata, duk yadda muka yanke gobe sai ka dawo ka ji." Maganar da ta ji Baffa ya faɗa ita ce
ta ta sanya ta ji tamkar ta daka tsalle don farin ciki. Da alama lokacin da ta daɗe tana jira ya zo.
Ba ta sake jiran komai ba ta koma cikin gidan tana jiran dawowar sa. Kwata-kwata ta kasa tsaye
ta kasa zaune, ji take kamar ta fita kawai ta sanar da mutumin cewa an ba shi auren Inna-wuro.

Sai ta shiga zagaye tsakar gidan, tana ta saƙe-saƙe a cikin ranta. Babu dadewa sallamar Baffa
ta ratso cikin gidan. Ta juya da sauri cikin farin ciki, abin da ya manta ma da mata tana faɗa wa
mijinta, yau ɗin sai ga shi ta furta

"Sannu da zuwa." Ya kalle ta, sai ya ji daɗin hakan. Saboda haka ya saki murmushi yana
ƙarasowa cikin gidan.


A ɓangaren Daneen da Amir kuwa, ko da suka fito kallan Amir Daneen ta yi ta ce

"Toh yanzu ya za mu yi?" Shiru ya ɗan yi na wasu sakanni kafin ya ce

"Kawai ki je rijiyar majalisa, nan ne mata suke zuwa."

"Ba ni ba Amir.. Kai kuma ya za ka yi?"

"Adda in dai ke kin yi sauri kin dawo ai ni babu matsala." Ya faɗa a nutse. Girgiza kai Daneen ta
yi ta ce

"Ba ka tsoron faɗan Dada koh? Idan ma ta kama ta haɗa da duka ko?" Ta ƙare a sanyaye. Shi
ma girgiza kan ya yi kafin ya ce

"Amma dai Adda kowanne duka za ta mini ba za ta kashe ni ba ai dai koh?" Harara Daneen ta
jefa masa, don har ta haddace wannan maganar tasa. Daga zarar ta masa maganar Dada,
kullum amsar sa kenan, ai dai ba za ta kashe shi ba.

"Adda kar fa ki wuce mintunan da ta ba ki. Ki tafi ki je ki ɗebo. Ko kuma ki kawo in ɗebo kafin na
je na siyo mata zogalen." Ya faɗa yana ƙoƙarin karɓar tulun hannunta. Janye wa ta yi ta ce

"A'ah, ka yi sauri ka je ka siyo. Ni kuma bari na je na ɗebo ruwan."

"Toh shi kenan." Ameer ya faɗa yana yin gaba. Ita ma hanyar da za ta sada ta da rijiyar ta yi da
sauri saboda gudun kar ta ƙara lokacin da Dada ta ba ta. Duk da mawuyaci ne ma hakan ba za
ta faru ba. Saboda ko daga fitowar su daga gida sun ci wajen minti nawa.

Tun daga nesa ta soma hango bokitai, robobi ajiye a gefen rijiyar. Wasu a hannun
mamallakansu wasu kuma sun ajiye. Mutane da dama zagaye da rijiyar kowa na ɗiba da gugan
da ya zo da shi.

"Wayyo Allahna!" Ta ambata cikin sanyayyiyar muryarta tana lumshe idanunta. Sauke wani
nannauyan numfashi ta yi, tana rasa yadda za ta yi. Ta yi shiru tana tunanin ta ina za ta fara
jiran wannan layin har ya zo kanta? Anya kuwa ba ƙundunbala za ta yi ta nufi rafin nan ba?
Kawai sai ta buɗe idanunta, ta sake kallan inda mutanen ke tsaye suna cigaba da ɗibar

ruwansu, babu alamar za su ragu. Soma takawa ta yi tana barin wajen, kai tsaye ta nufi rafi,
cikin zuciyarta tana karanto duk addu'ar da ta zo mata. Duk da yadda take jin tsoro, amma ba ta
sare ba, ta dogara da addu'ar nan da take yi, ta san in Allah Ya yarda babu wani abu da zai
faru.
"Daneen.." Ta ji an ambata lokacin da take dab da ƙarasawa rafin. Da sauri ta juyo cike da
mamakin jin muryar Innarsu. Da mamaki Inna-wuro ke kallan ta. Fasa tafiya Daneen ta yi ta
dawo da baya zuwa wajen Inna ta ce a mamakance

"Inna.."

"Na'am, ina za ki je?" Ta ƙare tambayar tana kallan tulun hannunta. Ita ma Daneen ɗin kallan
tulun ta yi kamar wadda ta manta da wanzuwarsa a hannunta. A narke ta soma faɗin

"Inna, Dada ce ta ce na je na ɗebo mata ruwa.. Kuma ta ba ni ƙididdigaggun mintuna. Na je
rijiyar majalisa mutane sun fi nawa, shi ne zan je na ɗebo a rafi. Amma ina tafiya ina addu'a." Ta
ƙare maganar tana kallan fuskar Innar don ganin yanayinta.

"Ya ilahy." Inna ta faɗa tana dafe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login