Showing 9001 words to 12000 words out of 81712 words
Chapter 4 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
da Ameer, ya yin da Daneen ke kwance a kan
cinyarta. Runtse idanunta ta yi, ita kam ta rasa me Dada take nufi da ita. Duk salon rashin
ƙaunarta ne yake cigaba da fito wa kusufa-kusufa haka? Ta nuna ba za ta ciyar da ita ba, ta yi
haƙuri ta zauna. Yanzu kuma tana ciyar da kanta ma ba ta tsira ba? Wannan wace irin rayuwa
ce. Sai dai cikin sakannin da ba su wuce biyar ba, ta buɗe idanunta lokacin da ta jiyo muryar
Baffa na faɗin
"Ba kuma zai yiwu ba gaskiya sai dai ki yi haƙuri. Tun da dai sana'a take don ta ciyar da kanta
da 'ya'yanta ba za mu hana ta ba gaskiya." Ya faɗa ba tare da ya kalli Dadan ba, duk da yadda
yake jin wata irin shakkar ta. Amma ya danne, ya cije ya faɗi abin da ke masa yawo a zuciya.
Lumshe idanunta Inna-wuro ta yi tana jin wani irin sanyi na ratsa ta. Wasu hawaye masu ɗumi
suka zubo a kan kuncinta.
"Ya Allah Ka ƙara dawo da hankalin Baffana kaina. Ka kare shi daga sharrin wannan matar." Ta
faɗa a hankali, har lokacin idanunta na a rufe. Buɗe idanunta ta yi lokacin da ya sauka a kan
Daneen da ke ta kallon ta, zuwa lokacin uwar ramar da ta yi duk ta yi nata wajen. Sai ta sakar
mata murmushi tana kamo kumatunta ta ja.
Zaro idanu Dada ta yi zuciyarta na bugawa, cikin matuƙar tsoro ta ce bakinta har rawa yake
"Umar.." Ta ambata tana kallansa, kafin ya ce komai ta sake faɗin
"Ni kake faɗa wa haka?" Ta faɗa har lokacin bugun zuciyarta bai koma daidai ba.
"Toh ai gaskiya ce." Ya faɗa yana juya wa ya bar ta a wajen tsaye kamar wadda aka dasa. Ta
kai wajen minti 5 tsaye a wajen ba tare da ta motsa ba. Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta toshe,
kanta ya kulle. Mai take ganin yana shirin faruwa? Lallai ta yi mugun sake. A daren Dada ta fice
daga gidan zuwa gidan wata 'yar'uwarta. Kuka kawai ta fashe da shi tana faɗin
"Ni kam na shiga uku Hanne, ki taimaka mini kafin rayuwa ta juya mini baya. Umar ya fara juya
mini baya." A ranar suka saɓi jiki zuwa wajen Malamin da ya saba musu aiki faka-faka.
_BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR_
A cikin shekarun nan abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da sauyawar Dada kaɗan,
saboda wani dalili da ita kaɗai ta bar wa kanta sani. Duk da shekarun da suka tafi, hakan be sa
ta watsar da makamanta ba, ko don yadda girma ke ƙara kama su. Domin kuwa daga zarar ta
ga Baffa ya soma ɗan sassautawa, yana ja da abin da ta faɗa za ta yi saurin koma wa wajen
malaminta ya yi mata aiki a kansa. Kai daga ƙarshe ma sai ta nemi a yi mata aikin da har abada
ba za ta sake dawo ba. Nan da nan Malamin ya nemi da ta kawo kuɗaɗe masu yawa, ta kuwa
siyar da saniyarta ta biya kuɗin aikin, domin kuwa abin da take ƙoƙarin aikatawa ta san zai
kawo mata ninkin ba ninkin kuɗin Saniyar da ta kashe. Daga nan kuwa al'amarin Baffa ya sake
rikicewa fiye da da, ya zama shi ma ya koma muzgunawa Inna-wuro a cikin gidan nan.
Kwata-kwata babu sauƙi ita kam a kowanne ɓangare sai a wajen Allah. Sai kuma idan ta kalli
'ya'yanta da take fata nan gaba su zame mata sanyin idaniya, kamar yadda tun yanzun su kaɗai
take kalla ta ji daɗi. Daneen da Ameer sun taso ne tamkar 'yan biyu. Don kuwa tun da Ameer ya
fara girma sai da ya kamo Daneen, sai ya zamana idan ma ba ka sani ba kana kallan su za ka
kira su da 'yan biyu, saboda tsananin kamar da suke, uwa uba kuma kansu ɗaya. A tare suka
taso da wata irin muguwar shaƙuwa, da tsananin soyayyar junansu. Ɗaya ba ya son abu ya
samu ɗaya. Idan ɗaya ba shi da lafiya ba za ka taɓa gane waye bai da lafiya ba, saboda gaba
ɗaya haɗuwa suke su yi jinyar tare. Wanda hakan ba ƙaramin tada wa da Inna-wuro hankali
yake ba. Ta rasa inda za ta jefa kanta, har sai mara lafiyar ya warke kafin take samun nutsuwar
zuciya, ita da mai taya jinyar. Har zuwa lokacin tana siyar da abinci kala-kala, har ma da wasu
abubuwan buƙata. Da wannan sana'ar ta yi amfani wajen saka 'ya'yanta a makarantar da ke
nan bakin kasuwar da take siyar da abinci. Nan suke zuwa su same ta idan an tashi kafin idan
ta gama abin da take su tafi gida. Da daddare kuma su je makarantar dare, wadda take babu
nisa daga gidansu. Duk wannan abubuwan har zuwa lokacin Dada ba ta canja ba. Sai dai wasu
abubuwan sun ɗan yi sauƙi saboda gajiya. Uwa uba kuma da ya kasance watarana ma idan ta
ga Inna-wuron da safe sai dare sannan za ta kuma sanya ta a ido. Dalili kenan da ya sa ta ɗan
yi sanyi tana jira lokacin da Malam ya ce mata ta jira ya yi. Sai dai kuma maimakon haka sai ta
ɗauki rabin tsanar da ta yi wa Inna-wuro ta maida ta kan Daneen da kuma Ameer, ba su da
damar su fito tsakar gidan yin wasa, ko wani abun sai ta hantare su. Har gwara ma Baffa, duk
da shi ma ba ya wani kula su, amma dai ba ya hantarar su kamar yadda Dada take.
Da ma kuma tun da suka taso suka fara wayo suka fahimci ko ma wace ce Dada ba ta ƙaunar
su, don su ɗin yara ne masu matuƙar wayo. Don akwai ranar da suna kasuwa siyar da abinci,
Ameer ya kalli Inna-wuro ya ce
"Inna.."
"Na'am Ameer." Inna-wuro ta faɗa bayan ta juyo ta kalle shi da murmushi ɗauke a kan fuskarta.
"Wai me ya sa Dada ba ta sonmu?" Ya yi tambayar da ta sanya Inna-wuro janye murmushin
fuskarta.
"Ameer?" Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan fuskarta a haɗe. Ba ta taɓa zata ba, ba ta taɓa kawo wa
tun a yanzu za su fahimci cewa Dadar ba ta ƙaunar su ne ba. Sai dai ga shi sun shammace ta.
Kafin ya ce komai ta ɗora da faɗin
"Waye ya ce maka ba ta son ku?" Ta tambaya a sanyaye. Ɗan ƙaramin bakinsa ya buɗe ze yi
magana, sai kuma ya juya ya kalli Daneen da ke zaune suna kallan juna. Dara-daran idanunta
farare ƙall ta ɗaga ta zuba wa Ameer ɗin su tana jira ta ji me ze ce. Ganin yana shirin buɗe baki
ya yi magana ya sanya ta soma girgiza masa kanta, ƙasa-ƙasa da siririyar muryarta mai daɗin
saurara take faɗin
"Inna ba ni ce ba."
"Adda Neen." Ya faɗa yana nuna ta, lokacin da ya turo bakinsa. Don babu yadda ze yi, ba ya so
Innar ta kama shi da laifi kwata-kwata musamman da ya ga ranta ya ɓaci. Sai dai in da a waje
ne, ko ma wane irin laifi Adda Neen ɗin tasa za ta yi ya gwammace ya ɗauki laifin. Shi ya sa
sau da dama ko a makaranta sai dai a yi faɗa da shi ba dai da Daneen ba. Don kuwa zama
yake tamkar shi ne yayan ita kuma ƙanwar. Maida duban ta Inna-wuro ta yi kan Daneen da ta yi
rau-rau da idanunta kamar me shirin saka kuka, ta buɗe baki za ta yi magana Daneen ta ɗaga
yatsanta guda ɗaya ta kai saitin bakinta tana faɗin
"Inna na rantse ba haka ba ne." Dariya ta ba ta, don haka ta sanya hannu ta janye hannun tana
faɗin
"Ya isa haka, kar na sake jin wani a cikin ku ya ce haka. Dada tana son ku sosai Uhmm?"
Jinjina kai kawai suka yi suna murmushi.
"Ya yi kyau. Abin da nake so da ku kawai ku dage ku yi karatu, ina so ku zama wasu, ku zama
waɗanda kullum zan din ga alfahari da su."
"Inna da ma muna ƙoƙari ai ko?" Ameer ya faɗa yana murmushi.
"Kuma dai na fi Ameer ƙoƙari." Daneen ta faɗa tana rausayar da kai, sassanyan murmushi na
fita daga kyakykyawar fuskarta.
Haka suke yini cikin farin ciki idan suna tare, sai dai daga zarar sun koma gida sai farin cikin ya
gushe, musamman idan halin Dadan ya motsa. Haka za su yi gum a ɗaki ta yi ta jarabarta ita
kaɗai. Idan Inna-wuro ta tanka ta ce za ta mata rashin kunya. Idan kuma ta yi shiru ta ce ta
maida ta mahaukaciya tana magana ta mata shiru. Wannan dalilin ne yake sanya Inna-wuro
kasa sanin takamaimai abin da za ta yi. Sai kawai ta haɗa kan 'ya'yanta ta rungume cikin rashin
sanin abin yi.
Wannan kenan.
*** *** ***
__ Ƙaton palour ne da ya amsa sunansa palour. Haɗaɗɗe, me ɗauke da zafafan kujeru masu
ɗaukar hankali, kyau da nutsuwa. Ƙatuwar T.V ɗin da ke gefe, inda take zaune a tsare babu
hayaniya ce ke ta aiki. Sai dai ga dukkan alamu babu wanda ya damu da abin da ake haska wa
a ciki. Wata dattijuwar mata ce zaune a kan ɗaya daga cikin lausasan kujerun da ke zagaye da
ɗakin, ƙafarta ajje a kan wani tattausan pillow, wata matashiyar budurwa na matsa mata ƙafar.
Can gefe kuma wata kyakykyawar mata ce zaune, sanye cikin atamfa doguwar riga ɗinkin
kaftan, ta yi ɗauri wanda ya dace da shekarunta. Har bayan wajen mintuna biyar babu wanda
ya ce ko uffan. Zuwa can wata matashiyar budurwa ta shigo cikin ɗakin da sallama ɗauke a
bakinta. Hannunta ɗauke da tsadaddiyar wayarta, tana sanye cikin wata doguwar riga da ta
matuƙar karɓar jikinta. Neman waje ta yi ta zauna gefen wannan dattijuwar fuska a narke tana
kallanta. Girgiza kai dattijuwar ta yi kafin ta ce
"Toh.. za a yaudare ni ne?" Ta ƙare tana taɓe baki. Turo baki matashiyar ta yi kafin ta ce
"Babu wata yaudara fa Dadaji. Allah kuwa magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci." Jin
hakan ya sanya wadda ke yi wa dattijuwar tausa miƙewa, don ba hurumin su ba ne jin wata
maganar da ta shafi 'yan gidan. Don haka ta ce cikin girmamawa.
"Rankiyadaɗe bari na je." Amsa mata Dadaji ta yi tana maida dubanta kan Hidaya ta ce
"Me kuma ya faru?"
"Dadaji har zuwa yanzu fa Yah Tareeq bai fito ba. Na yi wa Maama magana ta ce na bar shi
zuwa an jima, na kikkira wayarsa ya ƙi daga wa kuma Aminu ya tabbatar mini da ya ga
shigowarsa cikin gidan nan, ni kuma na kasa haƙuri."
"Oh ni 'yar nan. Toh ni kuma meye nawa a ciki Hidaya? Ke ɗin da kuke ɗasawa ma da shi bai
ɗaga kiranki ba me zan yi masa? Da ma ya aka cika ballantana kuma wani abu ya faru? Ni kam
ban san me zan masa ba kuma." Dadaji ta faɗa.
"Kai don Allah.. Wallahi dai ya kamata a tausaya wa Yaya.. Ni fa ina tsoro wallahi, kin dai san
shi da saka abu a rai. Maama don Allah ki saka baki kin ji?" Ta ƙare maganar tana juyawa ta
kalli ɗayar matar da ke cikin ɗakin.
"Hidaya na faɗa miki ki bar shi yana buƙatar kaɗaici koh?" Maama ta faɗa tana kallan Hidayar.
"Ah toh." Dadaji ta faɗa tana jinjina kai. Jiki a sanyaye Hidaya ta ce
"Tohm." Daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta, har lokacin tana sake kiran number Yayan nata
amma be ɗaga ba.
... Bayan tsawon mintuna masu yawa da ya kwashe a toilet ɗin, inda ya sakar wa kansa ruwa
me sanyi. Ɗaure da towel a ƙugunsa ya fito daga toilet ɗin. Nannaɗaɗɗen gashin kansa jiƙe
sharkaf da ruwan da ya daɗe a cikinsa. Farar fatarsa ita ce ta tona asirin baƙar gargasar da ke
jikin gaɓɓai da yawa na jikinsa. Musamman ma dai ƙirjinsa zuwa kan hannunsa, wadda duk da
yadda take a jiƙe hakan be hana ta miƙewa ba. Be yi tunanin duk daɗewar da ya yi cikin ruwan
nan zai cigaba da jin ɓacin rai ba. Sai dai yadda zuciyarsa ke tafasa, tana sake yin zafi ya sa
hatta numfashinsa yake fita da sauri. Tsigar jikinsa har lokacin ta ƙi dena tashi, wadda ita ta
taimaka wa gargasar jikinsa wajen ƙin lafe wa a kan faffaɗan ƙirjinsa. Cikin takun nutsuwa ya
ƙarasa bakin mirror ya tsaya, daidai lokacin da kyakykyawar fuskarsa ma'abociyar wani
sassanyan kyau ta bayyana. Kyakykyawa ne na gani na faɗa, irin kyan nan me ruɗar da duk
wanda ya yi tozali da shi. Fari irin farin nan me mugun kyau, wanda ƙasumbar da ke zaune ras
a kan fuskarsa ta ƙara ƙawata kyawunsa da kuma farin nasa. Wasu idanu ne da shi na
musamman, farare masu ɗauke da baƙa wuluk ɗin ƙwayar ido. Ɗan ƙaramin baki ne da shi
tamkar wata mace, ja kamar wanda ke shafa wani abun. Yadda kwantacciyar ƙasumbar
fuskarsa ta zagaye fuskarsa har tana ƙoƙarin rufe mitsitsin kyakykyawan laɓɓansa. Hannunsa
ya kai ya ɗan shafa saman girarsa idanunsa a lumshe yana ɗan fidda numfashi a hankali ko zai
samu ɓacin ran da yake ji ya tafi, ya manta da abin da ya faru, ya ɗauka ya jefa shi cikin
kwandon sharan abubuwa mara sa amfani, amma ya kasa, ya kasa kwata-kwata. Daidai lokacin
wayarsa da ke yashe a kan gado ta ɗauki ƙara. Be ko motsa ba, ballanta ya yi yunƙurin ɗaukar
wayar. Wani kiran ne ya sake shigo wa bayan wancan ya tsinke. Duk da ba a ɗaga ba, hakan
be sa an dena kira ba, ya lumshe idanunsa yana jan ƙaramin tsaki, sabon ɓacin rai na taso
masa. A nutse ya juya ya ƙarasa kan gadon ya ɗauki wayar, yana shirin kashe ta gaba ɗaya
sabon kira ya sake shigo wa. Ya dafe kansa da yatsu biyu kafin ya kalli me kiran nasa. Sauke
ajiyar zuciya ya yi har lokacin kyawawan idanunsa ɗore a kan wayar. Dab da za ta tsinke ya
ɗauka. Daga can ɓangaren aka ce
"Tareeq.. Me ya sa za ka yi haka ne?" Ya faɗa a gajiye. Maida wayar ya yi ya riƙe da ɗayan
hannunsa kafin ya gyara tsayuwarsa, kafin ya kai ga cewa komai aka sake faɗin
"Don Allah ka fito. Wallahi ka ɗaga mini hankali." Ya faɗa dan ya san halin abokin nasa da saka
abu a zuciya, ƙaramin abu ma idan ya saka a zuciyarsa an banu, ballantana wannan lamari da
dukkanin su babu wanda ya taɓa tunanin hakan za ta iya faruwa.
"Abdoul don Allah ka ƙyale ni, zuciyata na buƙatar hutu, idan har ba so kuke ta tarwatse ba." Ya
ƙarasa maganar a gajiye, yana fesar da wani huci da ya fito tun daga ƙasan zuciyarsa.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 05
__ "Tareeq!" Abdoul ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya. Bai ce komai ba sai ajiye wayar da
ya yi, ya koma ya zauna a gefen gadon hannunsa ɗaya cikin sumar kansa, idanunsa a lumshe,
zuciyarsa na sake cunkushe wa waje ɗaya.
A ɗaya ɓangaren kuwa kallan Abdoul Maama ta yi ta ce
"Ya katse ne?" Ta tambaya tana kallan sa. Gyara zaman wayar ya yi a hannunsa kafin ya jinjina
kai, a nutse ya buɗe baki ya ce
"Ehh, amma dai sauƙin ta ɗaya yana cikin gidan nan." Ajiyar zuciya Maama ta sauke kana ta ce
"Ku bar shi, kar wanda ya sake kiran sa don Allah, ni da kaina zan je na same shi zuwa gobe,
na san kafin nan In Sha Allah zuciyarsa ta yi sanyi."
"Toh shi kenan." Abdoul ya amsa da hakan. Daga haka ya yi sallama da su ya fice daga ɗakin.
... Tura ƙofar ɗakin ta yi, cikin sa'a kuwa sai gashi ta buɗe. Ta sauke ajiyar zuciya tana saka
kanta cikin ɗakin da sallama ɗauke a bakinta. Yana zaune a kan haɗaɗɗiyar kujerar da ke cikin
palourn, sanye cikin ƙananan kaya da suka matuƙar yi wa jikinsa kyau. Laptop ce gabansa yana
dannawa cikin ƙwarewa, gaba ɗaya fararen idanunsa na kai, da alama wani aikin yake mai
matuƙar muhimmanci. Duk da kusan duk hankalinsa na kan laptop ɗin, hakan be hana shi jin
lokacin da aka turo ƙofar ba. Ya ɗaga manyan fararen idanunsa ya kalli ƙofar a nutse. Daidai
lokacin da Hidaya ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin, kamar koyaushe babu abin da ke tashi sai
sassanyan ƙamshin jikinsa da kuma na cikin ɗakin. Wanda suka cakuɗu suke bayar da ƙamshi
me daɗin gaske. Rufe laptop ɗin ya yi kafin sassanyan murmushin da ya ƙawata fuskarsa ya
bayyana a kan laɓɓansa. Sai dai yadda tsagoron kyawunsa ya sake bayyana, ga duk wanda ya
kalle shi zai so a ce ya zauna a hakan ne ko da yaushe. Ita ma murmushin Hidaya ta yi tana
ƙarasawa ta nemi gefensa ta zauna ta ce a narke
"Kai Yah Tareeq, da ma ka gama fushin amma shi ne ba ka nemi kowa ba?" Kallan ta ya yi,
kafin cikin er basarwa ya ce
"Ni na faɗa miki ina fushi?" Ya ƙare kamar da gasken ba shi ne ya yi mugun fushi jiya ba. Sanin
halinsa ya sanya ta yin murmushi kafin ta ce
"Yah Tareeq.."
"Uhmmm." Ya