Showing 57001 words to 60000 words out of 81712 words
Chapter 20 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
jiri na shirin mayar da ita, hakan bai sanya ta komawa ta zauna ba, ta soma takawa a
hankali tana runtse idanunta lokaci bayan lokaci.
"Amma kar ki sake ki sanar da su kina da iyaye a can wani waje. Ka da ki sake ki nuna musu
kina da iyaye, na sake maimaita miki. Idan har da gaske a kan ɗaukar fansar ɗan'uwanki za ki
je gidan yi, toh kar ki sake su san da wannan maganar. Ki bari tukunna sai bayan komai ya
kammala sai ki koma wajen mahaifiyarki da zancen mutuwar Ameer, sai dai kuma tare da
kyakykyawan labarin kin ɗauki fansa a kan wanda ya yi sanadin mutuwar ɗan'uwan naki."
Maganganun Yohana suka daki dodon kunnenta. Ta ɗan dakata kaɗan, amma ba tare da ta
juyo ba. Kenan hakan na nufin za ta ci gaba da zama tare da su ba tare da ta koma wajen
Innarta ba? Ko da yake lokaci ne ƙanƙani, daga zarar ta samo wa Yohana abin da yake so, shi
kenan Tareeq ya shiga hannu, kamar yadda ya sanar da ita, ta kuma san lokacin ne hukuma za
ta ƙwatar wa Ameer haƙƙinsa. Don haka kawai ta jinjina kai, a kan laɓɓanta ta furta.
"Toh." Wanda ita kanta ba ta da tabbacin ya ji ta ko bai ji ta ba, don ita kanta ba ta ji sautin
maganar tata ta fita ba. Tamkar wata er maye haka ta ci gaba da takawa don isa ɗakin da aka
kwantar da ita. Duk kuwa da irin yadda jiri ke ci gaba da kwasarta, yana ƙoƙarin kifar da ita
hakan bai sanya ta dakatawa ba. Gaba ɗaya zuciyarta ta bushe, ta ƙeƙashe, Fansar nan dai ita
kaɗai ke yawo a cikin zuciya, ruhi da ƙwaƙwalwarta.
Numfashi Yohana ya fesar lokacin da ta ida ficewa daga cikin ɗakin, ya fito da wayarsa yana
sake fesar da iska daga bakinsa, har lokacin idanunsa a kan wayar.
"Kai baba shege ne wallahi, ka fiya takura. Toh yanzu ga shi garin abin da na yi da kake ta
kushewa ya janyo mana wata hanyar mafi dacewa. Ga shi nan yanzu mafita ta same mu cikin
sauƙi. Ya kamata ka sara mini, don wallahi kaina na wuta, ka jira ni gani nan zuwa, idan na zo
zan yi maka bayani." Daga haka ya katse wayar yana miƙewa, ba tare da ya bi ta kan kowa ba
ya fice daga asibitin.
... Sun fi awa cikin asibitin, amma ta kasa matsa wa ko nan da can ne daga kusa da Tareeq ɗin.
Duk da wanzuwar Maama, Ummanta har ma da Abeey hakan bai dame ta ba.
"Ya kamata fa a yi maganar auren yaran nan Yaya." Umman Jawahir ta faɗa daga inda take
zaune tana kallon Jawahir. Shi ma Abeey kallon su ya yi kafin ya ce
"Kar ki damu, daga zarar yaron nan ya samu lafiya, za mu yi magana da mahaifin Jawahir a
tsayar da ko sati ɗaya ne. Ban ga amfanin ɓata lokacin ba, saboda haka ku ma ku fara shiri."
Cikin wani irin farin ciki Umman Jawahir ta ce
"Alhamdulillahi, Allah Ya ƙara girma Yaya, Ya kuma tabbatar mana da alkhairinsa." Murmushi ya
yi kafin ya amsa da
"Ameen." Daidai lokacin da Dada ji ta shigo cikin ɗakin, Maama da ba ta daɗe da fita ba na bin
bayanta. Ta nemi waje ta zauna lokaci ɗaya tana amsa sannu da zuwan da suke mata.
"Alhassan har yanzu fa sau ɗaya matarka ta zo duba yaron nan." Dada ji ta faɗa tana kallon
Abeey. Sai da ya ɗaga kai ya kalle ta sannan ya ce bayan ya sauke numfashi kaɗan
"Ki bar ni da ita Dada ji, babu damuwa." Girgiza kai ta yi ta ce
"A'ah, kar ka yi mata komai. Na tambaya ne dai in ji ko ba ka sani ba, toh amma tun da ka sani
ɗin bar ta. Ta ci gaba da duk abin da ta ga shi ne daidai, babu damuwa." Dada ji ta ƙare
maganar tana irin murmushin nan na gefen baki.
"Ai Dada ji da kin bar Yaya ya yi mata ko ma mene ne, ban da iskanci kuna cikin gari ɗaya, gida
ɗaya a ce wai sau ɗaya ta zo ta duba Tareeq duk uban jikin da yake sha? Mu kan mu da ba ma
garin gaba ɗaya hankalinmu na nan, ba shi ne dalilin da ya sa muka dawo yau ba. Ai da ba yau
za mu dawo ba. Amma ita ki ga abin da take fa."
"Ummu Kulsum ki yi shiru ki bar mutum da halinsa, akwai ranar ƙin dillanci." Dada ta katse ta da
faɗin hakan. Jijjiga kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
... Tun da ta shigo Hidaya ke kallon ta. Ta tashi da sauri don ta taimaka mata saboda yadda ta
ga tana tafiya tana wani rangaji, sai Daneen ta yi amfani da hannunta wajen dakatar da ita kafin
a fili ta furta can ciki.
"Zan iya." Hidaya ba ta takura mata ba, ta koma ta nemi waje ta zauna, ya yin da ita kuma
Daneen ta ƙarasa kan gadon ta kifa kanta a kan gwuiwarta ta runtse idanunta. Sai a lokacin
sannan ta ji wannan abin da ya tokare mata ƙirji ya soma warwarewa, lokacin da wasu hawaye
suka taru a cikin idanunta, kafin ka ce mene wannan sun soma sintiri a kan kuncinta. Wasu
zafafan hawaye ne, da suke sakkowa da zafin su, wanda kuma ba na komai ba ne sai na
nadama, takaici, da kuma baƙin cikin ba da ƙodarta ga mugu, azzalumi, wanda ba ya tsoron
Allah!!
"Yah Tareeq!" Hidaya ta faɗa tana miƙewa bayan ta amsa sallamarsa.
"Wai da kanka?" Ta ambata tana kallonsa murmushi fall kan fuskarta. Shi ma murmushin ya ɗan
yi kafin ya jinjina kai kawai.
"Alhamdulillahi, sannu, ka ƙaraso Yaya." Babu musu ya ƙarasa shigewa cikin ɗakin a nutse cike
kuma da takatsantsan. Ya nemi waje ya zauna kan wata kujera, idanunsa a kan Daneen da ake
iya jiyo sautin shashsheƙarta. Sai da ya ɗaga kai ya kalli Hidaya kafin ya ce bayan ya ɗan
ƙanƙantar da kyawawan idanunsa.
"Subhanallahi! Har yanzu ba ta bar kukan ba?" Sai da Hidaya ta rausayar da kanta kafin ta ce
"Wallahi kuwa, na rasa yadda zan yi." Hannu ya saka ya ɗan murza goshinsa, har ga Allah ya ji
mutuwar yaron nan, ba kuma zai so a ce wadda ta zama silar ci gaba da rayuwarsa tana zaune
cikin wannan halin ba. Don haka cikin muryarsa mai daɗin saurara ya ce
"Sannu.."
"Daneen.. Yah Tareeq.." Hidaya ta faɗa tana murmushi.
"Ohh.." ya faɗa yana ɗage girarsa ɗaya. Kamar daga sama ta ji sunan Tareeq da Hidaya ta
ambata, sunan da tun da Yohana ya sanar da ita shi ne ɗan gidan Alhaji Yohana ta ji ta tsani jin
sunan, ballantana kuma a kai ga ganin mamallakin sunan da ba ta taɓa ganinsa ba. Sai dai
tarin abin da ya bar mata danƙare a cikin zuciya na da yawa. Har ba ta san lokacin da ta ɗaga
jajayen idanunta ta sauke su a kan Tareeq ba. Karo na farko da ta fara ganin kyakykyawar
fuskar Tareeq, wadda a gare ta baƙa ƙirin ce, fuska mafi muni a rayuwarta, fuskar mutumin da
ya zamo silar wargajewar farin cikinta. Shi ma wannan ne karo na farko da ya soma ganinta.
Idanunta cikin nasa suka faɗa, saboda yadda ta ɗago ba tare da ta shirya ba. Duk da tsananin
tasirin da idanun Tareeq ke da shi, hakan bai sanya ta ko da ƙoƙarin janyewa ba ne, sai ma ci
gaba da jefa masa wani mummunan kallo da ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da zafi,
wata uwar wutar fansa na sake ruruwa a ƙirjinta. Cikin basarwa, duk da yadda ya tsargu da irin
kallon da take bin sa da shi, sai dai ƙaryar mutum ya fahimci hakan, ya ɗan gyara zamansa
kaɗan kana ya ce
"Ya ƙarin haƙuri? Ki yi haƙuri Allah Ya gafarta masa, Ya sa can ta fiye masa nan. Ke kuma Allah
Ya saka miki da alkhairi. Na gode sosai, na kuma yaba da ƙoƙarinki." Runtse idanunta Daneen
ta yi tana jin yadda kalamansa ke ratsa kunnuwanta, jin tasirin su take tamkar ana soka mata
mashi a ƙirji. Jin su take kamar yana watsa mata ruwan zafi tafasasshe.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 23
Har kusan bayan minti ɗaya da gama maganar ba ta ce komai ba. Shi ma kuma bai damu ba,
don ko shi wani lokacin ya kan tsinci kansa cikin rashin son yin magana. Musamman ita kuma
da take cikin wannan hali, dole ne ya yi mata uzuri. A nutse cike kuma da takatsantsan ya miƙe
tsaye ba tare da ya sake kallon inda Daneen take ba ya dubi Hidaya, kafin ya ce komai ta ce
"Yaya sai haƙuri, mutuwar ta taɓa ta sosai wallahi. Tun kuma da aka ce an fitar da gawarsa
daga cikin asibitin nan abin ya sake yin gaba. Ka ga duk ta takura kanta, tun ɗazu ba ta umm ba
ta umm umm. Kawai dai a takure take." Ta ƙare maganar a dame. Ɗan lumshe idanunsa ya yi,
yana buɗe su lokaci guda. A nutse ya ɗan juya ya kalli Daneen kafin ya juyo bayan ya ɗan
sauke numfashi. Sai da ya kai hannunsa saitin ƙirjinsa kafin ya ce
"Allah ne Ya sa zan rayu, amma ta sanadin yarinyar nan, saboda haka ki kula da ita tamkar
yadda za ki kula da kanki Hidaya. Ko da yaushe ki din ga tuna akwai muhimmiyar tsokarta a
jikina, wadda nake tsaye a nan saboda ita." Murmushi Hidaya ta yi, saboda yadda ta ji matuƙar
daɗin yadda ya nuna damuwa da kulawa a kan yarinyar da bai taɓa ganinta ba sai yanzun.
"In Sha Allah Yah Tareeq. Ko ba ka faɗa ba wannan ya zame mini dole." Jinjina kai ya yi yana
ƙoƙarin ficewa daga ɗakin, Hidaya ta yi saurin faɗin
"Bari na taka maka." Daga haka suka jera suka fice daga ɗakin.
Tun lokacin da ta ji wannan kalaman nasa ta ji wasu irin hawaye sun tarar mata cikin idanu, sai
dai ga mamakinta wannan raunanniyar zuciyar tata, sai ta neme ta ta rasa, kawai dai wani irin
zafi take ji da kuma raɗaɗi mara misaltuwa. Maganganun nasa sun matuƙar ɓata mata rai, wato
nuna wa yake shi ɗin mutumin kirki ne. Abin da ya fi komai tsaya mata a rai, shi ne maimaita
yana rayuwa ne ta dalilinta. Idan ta tuna ta sadaukar da ƙodarta ga mutumin da ya zama silar
mutuwar Ameer ɗinta, ji take gaba ɗaya ta tsani kanta, ji take da tana da hannun dawo da
agogo baya, da ta dawo da shi, ta ƙi ba shi ƙodarta.
Tana nan zaune har zuwa lokacin da Hidaya da Sultanah suka shigo. Ko ɗaga kanta ba ta yi ta
kalle su ba, don gaba ɗaya ba ta ƙaunar ganin su. Duk da yadda zuciyarta ke raya mata ba su
san waye ɗan'uwansu ba, amma yau dole ta bi abin da wani sashe na zuciyarta ke raya mata.
Ci gaba da kaɗaicewa ita ɗaya shi ne mafita. Su ma ba su takura mata ba, suka ci gaba da
zama kawai.
Bayan kwana bakwai.
Abubuwa da dama sun faru a cikin kwana bakwai, ciki kuwa har da ci gaba da kula da lafiyar
Tareeq da kuma Daneen. Ta kowanne ɓangare Alhamdulillah ana samun ci gaba. Sai dai
Daneen da kullum tamkar ana ƙara mata kewar Ameer ne. Duk lokacin da kewar ta tashi, sai
dai ta zauna ta yi kukanta ta gode wa Allah. Don ma dai in da aka samu sauƙi, tana jin sassauci
idan ta tuna abin da ya ci gaba da zaunar da ita cikin asibitin. Duk da ba ta da tabbacin idan ta
koma ƙauyensu za ta tarar da Innarsu, amma dai tabbas daga zarar komai ya kammala can ɗin
za ta nufa.
Kullum sai Tareeq ya zo duba ta, ta ɓangaren ta ban da wutar fansa da ke ci gaba da ruruwa a
cikin zuciyarta babu abin da zuwansa ke haifar wa sai hakan. Dalili kenan da ya sa ta ga
alamun zai shigo za ta fake da bacci ko dai wani abun, wanda zai sa ba za ta haɗa ido da shi
ba, saboda yadda take jin wata irin tsanarsa a can ƙarƙashin zuciyarta. Ta ɓangaren sa kuwa,
samunta tana bacci ko wani abun bai taɓa damunsa ba. A wajensa ma ya fi son hakan, ko babu
komai za ta sake warwarewa sosai. Ya kuma san a cikin kwanakin dole ne ta ci gaba da kewar
ɗan'uwanta. A lokacin ne kuma aka sallame su su duka, da niyyar za su din ga dawowa ana
duba su lokaci zuwa lokaci.
... "Doctor Adam ya sanar da ni Yohana ɗan'uwanki ne wanda kike da shi shi kaɗai yanzu bayan
ɗan'uwanki da kika rasa. Sai dai yau kuma na ji wani batu daban, ya ya abin yake kenan?"
Abeey da ke zaune kan kujera ya faɗa yana kallan Daneen da ta yi shiru ita ma tana zaune,
kanta na kallon ƙasa. Sai da ta runtse idanunta sannan ta buɗe, ta tuna maganar da suka gama
da Yohana yanzu, inda yake jaddada mata kada ta manta, kada ta taɓa ambatar tana da iyaye,
idan har da gaske tana son ɗaukar fansar ɗan'uwanta. Don haka ta ɗan sauke numfashi kafin ta
soma faɗin
"A wajen kishiyar kakarmu muke, wadda ta haifi Innarmu, ita ce ba ta sonmu, kullum cikin
muzguna mana take. Ameer da kansa ya ce mu gudu mu bar mata gidan kafin ta ƙara yi mana
wani abun. Shi ne ma dalilin da ya sa muka baro ƙauyenmu. Muna so ne mu gina rayuwarmu
kafin mu koma mata." Jinjina kai Abeey ya shiga yi kana ya ce
"Iyayenku fa..?" Wani irin bugawa ƙirjin Daneen ya yi, sam-sam ƙarya ba halinta ba ne, ba ta
saba yi ba kwata-kwata, shi ya sa take ta kame-kame. Yanzu kuma ga shi ya yi mata tambayar
da ba ta tunanin za ta iya amsa ta. Ta ya ya za ta buɗi baki ta kashe iyayenta? Innarta fa?
"Ayyah, ba dai sun mutu ba?" Ta jiyo muryar Abeeyn kamar ya san me take tunani. Jiki a saluɓe
ta ɗaga kai ba tare da ta kalle shi ba, don gani take kamar idan ta ɗaga kai ta kalle shi zai
karanto ƙaryar da ta masa.
"Ya Salaam.. Allah Ya gafarta musu, Ya sa sun huta." Ba ta iya amsawa ba, sai shi ya amsa
abarsa da kansa. Bai kuma damu da hakan ba, don ya san wataƙila ta tuna da iyayen nata ne.
Don haka ya gyara zamansa kafin ya ce
"Ki kwantar da hankalinki, In Sha Allah daga yau kin zama ɗiyata. Zan ɗauke ki na tafi da ke
gidana a matsayin 'yata albarkacin wannan alfarmar da kika yi wa shalelena. Za ki rayu a
gidana ba a matsayin wata daban ba, a'ah kamar yadda na faɗa miki daga yau ke ɗin 'yata ce.
Zuwa nan gaba kaɗan, In Sha Allah ni da kaina zan kai ki ki ziyarci ita kakar taki, ba kuma da
niyyar in mayar mata da ke ba. A'ah, zan kai ki ne kawai ku gaisa, don za ki zauna tare da ni ne
In Sha Allah har Allah Ya kawo miki mijin aure." Ɗaga raunanan idanunta Daneen ta yi ta kalli
Abeey cike da mamakin jin abin dake fito wa daga bakinsa. Lallai wannan mutumin akwai
karamci. Duk wasu alamomi kuma sun nuna bai san waye ɗansa ba, bai san abubuwan da
yake aikatawa a ɓoye ba. Sai da ta harhaɗa kalmomin da za ta faɗa sannan ta buɗe baki da
ƙyar ta furta
"Na gode sosai, Allah Ya saka da alkhairi." Cike da yabawa da hankalin 'yar ƙaramar yarinya
mai juriya ya ce
"Allah Ya yi miki albarka, Ameen." Daga haka ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa.
Kafin ya kai ga ci gaba da tafiya ya ce
"Ki shirya duk abin da kike buƙata, za a shigo a ɗauka, sai ki fito da su Hidaya mu wuce."
"Tom." Nan ma ta faɗa a sanyaye. Sai da ya fice daga ɗakin sannan ta miƙe tsaye, idanunta a
lumshe take hango yadda za ta kasance cikin gidan na Alhaji Dikko, da niyyar ɗaukar fansa.
Kamar daga sama ta jiyo jagwalgwalalliyar hausarsa lokacin da yake faɗin
"Na gode wa Allah." Dalili kenan da ya sanya ta buɗe idanunta da sauri ta sauke a kansa.
Hannunsa ya zura a aljihu ya fito da wata babbar waya ya miƙa mata. Bin wayar ta yi da kallo,
kafin ta ɗaga kai ta kalle shi. Ya jinjina kai yana nuna wayar da bakinsa.
"Karɓi ki ji mana." Ya faɗa a ɗan dame. Hannunta ta saka ta karɓi wayar, daidai lokacin da ya
soma faɗin.
"Ki riƙe wayar nan, zan din ga kiran ki a cikinta lokaci zuwa lokaci. Ki kasance ko da yaushe
kina kusa da ita, kar ki yi nisa da ita, saboda yadda zan din ga jin duk abubuwan da suke
faruwa. Kar ki yi wasa don Allah. Kusanci kawai nake so ki samu da 'yan gidan, daga nan zan
sanar da ke abin da za ki yi mini." Jinjina kai Daneen ta yi, kafin da muryarta da har lokacin ba
ta koma ainahin tata ba ta ce
"Ban iya amfani da ita ba."
"Riƙe, zan sanar da ke yadda za ki yi amfani da komai. Na saita miki komai, idan kuma na kira,
za ki ga wajen accept nan za ki danna." Jinjina kai dai Daneen ta kuma yi ba tare da ta ce
komai ba. Ya juya baya da sauri jin kamar motsi.