Showing 15001 words to 18000 words out of 81712 words

Chapter 6 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

goshinta. Sai kuma can ta ɗago ta kalli Daneen ta ce

"Kar na sake ji Daneen.. Kar na sake ji kin ji koh? Ba ni tulun." Ta faɗa tana miƙa hannu, babu
musu ta saki tulun Inna ta riƙe. Ta juya ta kalli almajirinta da ke kwasar mata kaya idan za ta tafi
kasuwa ko kuma idan za ta koma gida.

"Ɗan yi maza ka je ka ɗebo mini ruwa." Babu musu ya amsa yana karɓar tulun. Bayan mintuna
kaɗan sai ga shi ya dawo. Cigaba da tafiya suka yi har zuwa ƙofar gidan. Sai a lokacin Daneen
ta karɓi tulun, Inna ta karɓi kayanta ta shiga da su cikin gida. Inda Daneen ta ci sa'a, zumuɗin
da Dada ke ciki ya sanya ta mantawa ma kwata-kwata da aiken da ta yi. Burinta kawai
Inna-wuro ta dawo ta sanar da ita sun yi mata miji.


... Su uku ne zaune cikin palourn, manyan mata guda biyu, ya yin da matashiyar budurwa ke
zaune ita ma a kan kujera. Sanye cikin wata doguwar rigar atamfa da ta matuƙar yi mata kyau.
Kyakykyawa ce ba can ba, hasken fatar da Allah Ya ba ta shi ya haska kyawun nata. Hannunta
ɗauke da waya tana dannawa, lokaci lokaci ta kan ɗaga ido ta kalli iyayen nata da ke magana.
Zuwa can ma sai danna wayar ya gagara, musamman da ta ji maganar da suka fara ɗin ta
shafe ta. Don haka gaba ɗaya ma sai ta ajje wayar ta maida gaba ɗaya hankalinta kan su.
Daidai lokacin da Momynta ke faɗin.

"Amma Maama ba kya ganin tun da bare ta watsa mana ƙasa a ido, me zai hana mu haɗa shi
da Jawahir, er uwarsa wadda dukka kowa ya san halinta" Murmushi matashiyar ta saki tana
sake kama kanta a kan kujerar da take. Ita a lallai dole kunya ta ji, saboda tana gaban sirikarta.
Buɗe ido Maama ta yi, kafin ta shiga jinjina kai

"Babbar magana.. Tareeq ɗin?" Ta ambata ba tare da wata damuwa ba. Jinjina kai ita ma Momy
ta yi tana faɗin

"Ehh shi fa Maama.. Ai hakan shi ne daidai. Don na san daga ke dai har Yaya ba za ku sake
bari ya nemo wata a waje ba, ballantana har a zo a samu matsala."

"Ba wannan ba ne Hajiya A'isha.. Na san halin Tareeq, ke kan ki kin san halinsa. So bayan duk
abin da ya faru ba na tunanin a nan kusa ze iya amincewa da wata kuma. Kin san dai yadda
abin da ya faru ya illata zuciyarsa. So gaskiya yana buƙatar lokaci kafin a je masa da irin
wannan maganar."
"Ba don kar ki ce na katse ki ba, da na sake tuna miki Jawahir fa er uwar Tareeq ce ta jini.
Wadda ya san halayenta, uwa uba kuma tana ƙaunar sa." Momy ta ƙarasa maganar tana dafa
kafaɗar Jawahir. Sake yin ƙasa da kai Jawahir ta yi tana wasa da yatsun hannunta da murmushi
kwance a kan fuskarta. Fatan ta ɗaya Maaman ta amince da wannan haɗi. Don ta san idan dai
har ta amince toh fa shi ma Tareeq ɗin abu mai sauƙi ne zai amince. Jin Maama ta yi shiru ya
sanya ta sake faɗin

"Ki yi tunani a kan wannan al'amari, sannan ki duba abin da idon basira. Za ki gane da gaske
Jawahir ce kawai ta dace da auren Tareeq.."

Abin da ya tsinta kenan lokacin da ya kawo kansa cikin ɗakin. Sai dai yadda fuskarsa take, kai
ba za ka taɓa cewa ya ji ko da makamanciyar maganar da suke yi ba. Yana sanye cikin wasu
sheggun ƙananan kaya da suka karɓi jikinsa. Ya yi wani shahararren kyau tamkar da ma don
shi aka yi kayan. Ya sakaya baƙar sumar kansa da wata haɗaɗɗiyar facing cap, hakan ne ya sa
ba a iya ganin sumar tasa. Sai dai ka hangi sumar da ke kwance luff a ƙeyarsa. Da sallama ya
shiga cikin ɗakin, ba tare da ya kalli kowa da ke cikin ɗakin ba. Duk kuwa da tun kafin ya shigo
ɗakin ya gama ganin su waye a ciki. Don haka gefen Maama ya je ya zauna. Cikin girmamawa
ya gaishe da Momy da ta katse zancen ta saboda ganin shigowar sa.

"Lafiya ƙalau Tareeq.. Ya kuma wannan abu da ya faru? Toh Ubangiji Ya sa haka ne mafi
alkhairi."

"Ameen." Kawai ya amsa da hakan yana maida duban sa kan Maama, don kwata-kwata ba ya
so zancen ya yi tsayi. Ya kuma san halin Momyn sarai na son gutststsira zance. Don haka dan
kada ma ta sake ce masa komai ya ce yana kallan Maama

"Barka da wannan lokacin Maama."

"Barka dai Tareeq, kana lafiya?" Shi ne kawai abin da ta faɗa. Duk da tana so su yi magana
sosai da ɗan nata, amma wanzuwar Momy a wajen ya sa ta kama bakinta kawai.

"Alhamdulillah.. Hidaya ba ta nan ne?" Ya tambaya saboda rashin ganin gilmawar ta, bayan
hakan ba ɗabi'arta ba ce, kusan kodayaushe ta fi zama gefen mahaifiyar tasu. Sai dai idan
sister ɗinta na nan, kuma ya san ba sa cikin gidan ma yanzu haka.

"Ohh, ta bi driver zuwa ɗakko su Sultanah." Maama ta faɗa. Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya
ce komai ba, yana shirin miƙewa Jawahir da ke ta sake gyara zama, tana tsara yadda za ta
masa magana ta ce

"Barka da wannan lokacin Yah Tareeq." Sai a lokacin sannan ya ɗaga idanunsa ya mata kallo
ɗaya, kafin ya ɗauke idanunsa. Ya ɗan ƙaƙalo murmushin da ya tsaya a kan laɓɓansa ya ce

"Barka Jawahir.." Daga haka ya maida duban sa kan Maama ya ce

"Bari na ɗan fita.."

"Toh Allah Ya tsare." Maama ta faɗa cikin kulawa. Amsawa ya yi da "Ameen" yana ficewa daga
ɗakin. Jawahir ta bi shi da kallo tana jin wani irin farin ciki na ziyartar ta. Wato duk lokacin da
aka ce wannan kyakykyawan, haɗaɗɗen guy ɗin ya zama mallakinta nata ita kaɗai, ba ta san
kuma a wane yanayi za ta tsinci kanta ciki ba.
"Allah sarki! Kin ga har yanayinsa ya ɗan chanja wallahi. Taimako ɗaya za mu masa mu nuna
masa ƙauna ta hanyar aura masa Jawahir a kurkusan nan ko don ya manta da raɗaɗin da mace
ta sanya shi a ciki." Momy ta sake faɗar hakan bayan fitar Tareeq babu daɗewa. Sauke
numfashi Maama ta yi, ita kam i zuwa yanzu ai ya ci a ce ta bar maganar gaba ɗaya ko don
fahimtar da ta yi ba ta da ra'ayi a kai. Don ita dai haka kawai ta ji haɗin bai kwanta mata ba.
Musamman kuma da ta san halin Tareeq ɗin. Ga kuma abin da ya faru.

"Amma me ya sa ba ki samu Yayanki ko Dadaji kin mata maganar ba?" Murmushi Momy ta yi
kafin ta ce

"Ke fa ke ce mahaifiyar Tareeq. Ke kika fi dacewa na fara tuntuɓa da wannan maganar. Idan har
ke kika fara masa maganar zai fi ɗaukar ta da muhimmanci. Kin fi kowa sanin halin ɗanki shi ne
dalili."

"Toh shi kenan, Ubangiji Ya zaɓa abin da ya fi zama alkhairi."

"Ameeeeen.." Momy ta faɗa tana jan Ameen ɗin cikin farin ciki.


... A nutse ta ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin jikinta a matuƙar sanyaye. Don haka kawai ta ƙi
jinin kiran Dada, domin da wuya idan na alkhairi ne. Ƙarasawa ta yi ta nemi waje ta zauna cikin
ladabi ta ce

"Dada ga ni." Ƙarasa abin da take Dada ta yi, kafin ta dawo ta nemi waje ta zauna gefen Baffa
ta ce

"Toh ke sai ki fara shiri, domin kuwa mun yi miki miji. Miji ya zo, Baffanki ya gan shi ya masa, ni
ma kuma na gan shi ya yi mini. Don haka gobe zai zo ki je ku gaisa. Ba wani da yawa za a saka
ba, cikin ƙanƙanin lokaci za a yi komai a gama." Dada ta faɗa maganar tamkar da ita mutumin
da ya zo suka yi magana. Tun lokacin da Dada ta ambaci miji ta ji zuciyarta ta buga. Ba ta tsaya
ba, sai cigaba da bugawa da ta yi. Ta runtse idanunta tana tuna lokacin da suka gabatar mata
da Alhaji Baita a matsayin mijin da za ta aura. Daga zuwa siyar nono. Ba tare da sanin waye shi
ba. Mene ne asalinsa, su waye iyayensa duk ba su sani ba. Haka kawai suka ɗauke ta suka ba
shi don kawai ya yi musu ɓarin kuɗi. Toh idan kuma shi ma wannan ɗin halinsa ɗaya da Alhaji
Baitan fa? Abin da ya fara zuwa kwanyarta kenan, tana jin wani sabon tashin hankalin na
ziyartar ta. Duk wani tunaninta, burinta, da duk wani fatanta ba ya wuce a kan inganta rayuwar
'ya'yanta. Toh idan dai har suka ce ta yi aure yaya rayuwar 'ya'yanta za ta kasance? Ko kuwa
wanda suka sake zaɓar mata a karo na biyu zai yarda ya riƙe 'ya'yanta? Tunanin nata ya katse
ne, lokacin da hayaniyar da ake a waje take sake kusanto gidansu.

"Ɓarawo, Ɓarawo.." Shi ne abin da kafatanin mutanen ke faɗa cikin ɗaga murya. Haka nan
kawai ta ji ƙirjinta ya sake bugawa a karo na barkatai. Daidai lokacin da aka soma buga ƙofar
gidan da ƙarfi, wanda ke bugawa ɗin yana faɗin

"Ina mutanen gidan suke ne? Ku fito tun kafin in ba wa mutane umarnin shigowa su muku
rashin mutunci wallahi. Ku fito na ce.." Ya ƙare maganar yana sake dukan ƙofar kamar wanda
ze jijjige ta. Kusan a tare dukansu suka miƙe. Daneen ma da ke cikin ɗaki ta yo tsakar gidan
babu shiri. Gaba ɗaya suka nufi ƙofar gidan don ganin abin da ke faruwa, ko kuma ma ya
farun..

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 07

__ Dandazon mutanen da ta gani a ƙofar gidan nasu, shi ne abin da ya sake tsinkar mata da
gaba. Ta runtse idanunta tana ambaton sunan Allah, lokaci ɗaya tana buɗe idanun, a daidai
lokacin da ta sauke idanunta a kan Habule da ke riƙe da kwalar rigar Ameer. Ya cukwuikuye ta
kamar wanda ke shirin zame ta daga jikinsa.
"Ɓarawo." Kunnenta ya sake tsinto mata wannan kalmar.

"Ya isa haka.." Mutumin da ke riƙe da kwalar rigar Ameer ya faɗa bayan ya yi amfani da
hannunsa wajen alamta musu abin da ya faɗa. Kamar dama shi ya saka su, sai kuwa suka yi
shiru.

"Ameer." Daneen ta faɗa idanunta da take suka sauya a kan Ameer, ban da lugude babu abin
da zuciyarta take.

"Na shiga 3 ni Hanne.. Me kuma ya faru?" Dada ta faɗa har da dafe ƙirji kamar gaske.

"Na san zuwa yanzu kun fahimci abin da ya faru. Yaron nan ya yi mini satar zogale. Ni kuma
wallahi ba zan haƙura ba, don haka zuwa na yi a biya ni kuɗin abin da ya tsinkar mini." Habule
ya faɗa yana gyara tsayuwarsa. Tun da suka zo wajen kwata-kwata Ameer ya kasa ko da ɗaga
idanunsa ne ballantana ya kalli mutanen da ke tsaye a wajen. Shi kaɗai ya san yadda kalaman
da ake faɗa suke sukar zuciyarsa. Ya rasa abin da ze yi, ya rasa ya ze yi. Be san cewa mutane
da dama ƙiris suke jira a kansu ba sai yanzu, sai da abin nan ya faru.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ameer! Yanzu nan sai da ka nuna halinka a waje? Sata da farar
ranar nan? Oh jama'a.. Jinin Hadeeza sun shiga 3." Dada ta yi maganar tana tafa hannu. Babu
shiri Ameer ya ɗaga idanunsa ya kalli Dada, cike da mamakin maganganun da suke fito wa a
bakinta. Cikin sauri kuma sai ya mayar da idanunsa kan Inna-wuro da ta runtse idanunta cikin
rashin sanin abin yi. Girgiza kai ya shiga yi tamkar tana kallansa

"A'ah Inna, kar ki yarda da abin da suke faɗa, wallahi ban yi masa sata ba. Ɗansa ne ya ce mini
in je in tsinka tun da ban samu na siyarwa ba. Inna kar ki yarda, wallahi ban yi masa sata ba
Inna." Ya ƙare maganar gwanin ban tausayi. Shi gaba ɗaya abin da mutanen ke masa be
dugunzuma masa hankali ba kamar tsoron ka da Innarsa ta yarda da abin da suke faɗa.
"Dallah rufe mana baki ɓarawon banza ɓarawon wofi." Wani da ke gefen Habule ya faɗa yana
tunkuɗa masa ƙeya. Ya tafi kamar ze kifa kafin ya dawo a kan ƙafafunsa. I zuwa lokacin
zuciyarsa ta yi taurin da yake ganin ba ze iya jure wannan cin mutuncin ba. Wani irin zafi
zuciyarsa take masa, ji yake kamar ya fasa ihu ko ze ji sauƙin abin da yake ji. Don haka a
fusace ya juya ya cakumi wuyan wanda ya tura shi yanzun. Cikin ƙanƙanin lokaci maganar
mutane ta soma tashi a wajen, kowa da abin da yake faɗa. Tuni ya ƙwace jikinsa daga hannun
Habule. Kamar yadda ya cakumi wuyansa, haka shi ma wancan ɗin ya cakuma, suna shirin
soma faɗan ya ji an riƙo hannunsa. Cakk ya dakata, ya ɗaga idanunsa ya sauke a kan fuskar
Inna da ta riƙe hannunsa. Ta girgiza masa kai a sanyaye, muryarta ma a sanyaye ta furta

"Rabu da shi.. Allah zai saka maka." Ta ƙare maganar tana jan hannunsa. Babu musu ya sake
shi, har lokacin yana jin yadda zuciyarsa ke cigaba da wani irin zafi, gefe guda kuma wani rauni
ne a cikinta. Ganin da Habule ya yi Inna-wuro ta ja hannun ɗanta ya sanya shi saurin faɗin

"Ina za ku je ba tare da kun.."

"Daneen ɗakko kuɗi ki ba shi." Maganar Inna-wuron ta katse masa maganar da ya soma. Ya ja
ƙwafa yana faɗin

"Ah toh." Kusan a tare suka shige gidan su ukun, har lokacin Inna-wuro na riƙe da hannun
Ameer.

"Don Allah ka yi haƙuri, ka san halin 'ya'yan yanzu.. Ka yi haƙuri amma tabbas zan tsawatar
masa, ta yadda ba zai sake marmarin ɗaukar abin wani ba." Maganar Dada kenan, wadda ta
sauka a kunnen Daneen lokacin da ta fito daga cikin gida, hannunta ɗauke da kuɗi ta miƙa wa
Habule, ba ta jira ya ce komai ba ta koma cikin gidan tana cigaba da tariyar kalaman Dadan.
"Babu komai." Habule ya faɗa lokacin da yake ƙirga kuɗin hannunsa.

"Ka yi haƙuri." Baffa da tun ɗazun be ce komai ba ya faɗa yana kallan Habulen. Jinjina kai
Habule ya yi yana kallan mutanen da suka biyo shi ya ce

"Ku wuce mu je." Duk sai suka ɗunguna suka bi bayansa. Dada da Baffa suka bi bayansu da
kallo har sai da suka ɓace musu da gani. Ƙwafa Dada ta ja ba tare da ta ce komai ba ta shige
cikin gida, babu daɗe wa Baffa ma ya bi bayanta zuwa ciki.

A ɗaya ɓangaren kuwa, a sukwane Daneen ta nemi gefen Ameer ta zauna, yana zaune kansa
ɗore a kan gwuiwarsa. A hankali ta kai hannunta ta dafa kafaɗarsa, cikin sanyi ta ce

"Ɗan'uwa." Runtse idanunsa ya yi kafin ya buɗe, ya ɗago a hankali ya kalli Daneen. Girgiza
mata kai ya shiga yi yana jin yadda zuciyarsa ke karyewa.

"Adda wallahi ba sata na yi masa ba." Ya ƙare yana riƙo hannunta. Idanunta da suka cika taff da
hawaye ta lumshe tana buɗe wa a lokaci guda. Sai ta shiga jinjina kai tana riƙe hannunsa sosai.

"Na sani Ameer.. Inna ma ta sani, ka dena damun kanka."

"Amma kin ji abin da Dada ta faɗa koh? Tun da nake na taɓa sata a rayuwata ne? Me ya sa ne
muke rayuwa a cikin gidan nan Adda? Babu wanda ke sonmu fa sai mu kanmu. Ni ba ɓarawo
ba ne Adda. Wallahi ba ɓarawo ba ne ni." Ya ƙare yana fashe wa da kuka. Sai a lokacin kukan
da ita kanta Daneen ɗin ke riƙe wa ya fito fili, ta ja Ameer jikinta ta rungume ita ma tana fashe
wa da kukan.

"Ya isa haka Ameer.. Ya isa haka.." Ta yi ƙarfin halin faɗa. Cigaba da girgiza kai ya yi, don
tabbas abin da ya faru ya masa zafi, kukan da yake shi ne kaɗai zai sanyaya masa zuciya. Ita
ma Daneen ɗin ba ta hana shi ba, ta bar shi ya yi kukan, dan ta san hakan zai taimaka wajen
rage raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa.
"Ku dena kuka In Sha Allah, Allah zai kawo mana mafita nan ba da daɗewa ba." Inna ta faɗa

tana haɗa su su duka ta rungume. Ba ta so ta bar wata alama da zai sa su fahimci ita ma tana
cikin damuwar. Sai dai za ta iya cewa abin da take ji cikin zuciyarta ya fi wanda suke ji. Ita kaɗai
ta san abin da take ji a duk lokacin da kalmar 'ɓarawo' ta faɗo mata cikin rai. Mummunar kalmar
da aka jefi ɗanta da shi. Mummunar kalmar da mutane da dama suka kira ɗanta da shi. Kawai
sai ta runtse idanunta tana jin yadda Ameer yake sauke ajiyar zuciya cikin ƙunar rai. Lallai yau
ɗin tabbas abin ya taɓa zuciyar Ameer, tun da har yake kuka, duk kuwa da ƙarfin zuciya irin
nasa duk da ƙananun shekarunsa.

Ranar dai haka suka wuni babu walwala. Cikin sa'a kuma ita ma Dada sai ba ta kula su ba. Ta
cigaba da harkokinta daga tsakar gida zuwa cikin ɗaki.

Washegari da ta kasance babu makaranta bin Innar suka yi kasuwa. Ba su suka dawo gidan ba
sai da yamma. Har kuma zuwa lokacin Ameer be koma daidai ba. Daneen da Inna-wuro ke ta
ƙoƙari wajen ganin sun kwashe damuwar da ya ɗora wa kansa.


... "Kin sanar da shi kin amince?" Tambayar da Dada ta jefa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login