Showing 69001 words to 72000 words out of 81712 words
Chapter 24 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
Jawahir.
"Jawahir, waɗannan kayan fa?" Ta faɗa tana nuna su. Buɗe idanunta Jawahir ta yi ta kalli
kayan, sannan ta gyara zamanta a kan kujerar ta ce
"Umma kayan kitchen ne fa." Ta ƙare maganar tana turo baki.
"Iyeeee, yau na ga ikon Allah. Wai Jawahir me ye haka ne? Ba za ki iya haƙuri cikin satin nan
na je na siyo miki duk abin da kike buƙata ba?" Sake tura bakinta ta yi kafin ta ce
"Toh Umma ba ga shi na rage miki wasu abubuwan ba. Kuma ma na ga har yanzu kin ƙi zuwa,
bayan bikin saura 'yan kwanaki." Dariya Umma ta yi tana girgiza kai. 'Wato a kan Tareeq
Jawahir ba ta da kunya.' Ta raya hakan cikin zuciyarta. Ya yin da a fili kuma sai cewa ta yi
"Toh ya yi, sai ki tashi ki shigar da su ciki ki wuce mu je mu duba jikin Tareeq." A razane ta ce
"Jikinsa kuma? Me ya faru da Yah Tareeq ɗin?" Ajiyar zuciya Umma ta sauke kafin ta ce
"Ba ki ga missed call ɗina a wayarki ba? Wallahi ya samu hatsari ne."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Na shiga uku? Amma dai babu abin da ya same shi?" Ta
tambaya a ruɗe idanunta a kan Umman.
"Tashi mu je." Umma ta faɗa tana miƙewa. Ko sake bi ta kan kayan ba ta yi ba, ta ɗauki jakarta
ta zura a hammata, har tana riga Umman ma ficewa daga ɗakin.
A cikin satin aka yi wa Tareeq aiki a ƙafarsa, aikin da cikin ikon Allah aka dace matuƙa yadda ba
su yi tsammani ba. Don haka cikin farin ciki Likitan da ya jagoranci aikin yake miƙa wa Abeey
hannu fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin
"Congratulations Sir, an yi aiki cikin nasara In Sha Allah." Cikin wani irin farin ciki Abeey ya miƙa
masa hannu suka gaisa, fuskarsa na nuni da irin farin cikin da yake ciki.
"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah." Shi ne abin da Abeey ya din ga faɗa. Likitan bai
tari numfashinsa ba, sai da ya gama sannan ya ce
"Sai dai za a ɗan ɗauki lokaci gaskiya kafin ya iya taka wa da ƙafar tasa. Ina nufin za a samar
masa kujera ne ya din ga duk wasu abubuwa da zai yi a kai. Aikin ƙafa kam an yi nasara, amma
ba yanzu zai iya takawa ba, sai zuwa lokacin da Allah Ya nufa, amma fa a yadda muka ga ƙafar
tasa, muna kyautata zaton nan ba da daɗewa ba ne In Sha Allah." Jinjina kai Abeey ya yi, duk
da yadda ya ji jikinsa ya yi sanyi. Amma kuma idan ya tuna inda Allah Ya taimake su aka yi aikin
lafiya sai ya ji sanyi a ransa. Godiya sosai ya yi wa Likitan da ya yi ta sinnar da kai cike da
kunyar jin Alhaji Dikko guda na yi masa godiya haka tamkar wanda ya yi masa wani babban
abu na musamman.
Ta ɓangaren Daneen kuwa abubuwa sun cakuɗe mata, domin kuwa idan dai har tana lissafi
daidai, yanzu haka saura sati ɗaya bikin Tareeq. Don haka gaba ɗaya ta ruɗe, duk wata hanya
da za ta sada ta da ɗaki, wajen ajiyar kayan Tareeq kawai shi take nema. Sau da dama ta kan
faki idanun mutane ta je sashen nasa, sai dai kamar kodayaushe a kulle dai. Ga shi kusan
kullum suna asibiti. Babu damar ta ce ba za ta je ba, don tana tsoron kar a zargi wani abun.
.... "Sannu Yah Tareeq." Hidaya ta faɗa a karo na barkatai. Murmushi Tareeq ya yi har fararen
jerarrun haƙoransa na bayyana kaɗan.
"Hidayaaaa.." Ya ɗan ja ƙarshen sunan, jin yadda motsi kaɗan sai ta ce masa sannu. Murmushi
ta yi kana ta ce
"Na'am Yah Tareeq."
"Na warke fa." Ya faɗa yana ɗan gyara zaman ƙafarsa.
"Allah Ya sa." Ta faɗa a sanyaye. A hankali ya ɗan kalli gefensa kafin ya maida duban sa kanta
ya ce
"Ina Daneen?" Da mamaki shimfiɗe a kan fuskarta ta ɗaga kai ta kalle shi. Tana matuƙar
mamakin yadda yake iya kula da rayuwar Daneen ɗin, sosai da sosai yake barin ta da mamaki
ya kusan kashe ta. Yadda ya haddace sunanta cikin ƙanƙanin lokaci, yana ɗaya daga cikin abin
da ke matuƙar ba ta mamaki. Sai dai abin da ba ta sani ba, kula da rayuwar Daneen ya zama
dole a wajensa. Ko babu komai yanzu haka rayuwa take a cikin gidansu. Ya zama dole ya saka
wa duk wani takunta ido. Duk yadda aka yi ma Hidaya manta halinsa ta yi. Gefe guda kuma
take-taken yarinyar bai yi masa ba. Dalili kenan da ya sa yake lura da duk wani motsinta.
"Yah Tareeq.." Ta ambata cike da mamaki ba tare da ta ba shi amsar tambayar da ya yi masa
ba. Sarai ya fahimci abin da take nufi, don haka ya saki wani miskilin murmushi da ya matuƙar
ƙawata fuskarsa kafin ya ce
"Ba ni amsa ta." Ya faɗa cikin basarwa. Kafin ta kai ga cewa komai, Daneen ta yi sallama cikin
ɗakin kanta a ƙasa kamar wata munafuka. Dukkan su suka bi ta da kallo, kafin Tareeq ya janye
nasa idanun. Ga maɗaukakin mamakinsa, abin da bai taɓa ji daga bakin yarinyar ba, sai ga shi
ta ce
"Barka da wannan lokacin." Kusan a tare shi da Hidaya suka sake kallon kyakykyawar fuskarta
da har zuwa lokacin ba ta ɗaga ta ta kalle su ba. A karo na biyu ya sake janye idanunsa yana
ɗan taɓe bakinsa, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce
"Barka dai. Ya jikinki?" Har ta ɗaga kai za ta kalle shi, sai kuma ta fasa, don so take duk wani
zargi da ta fara karanta a kan fuskarsa ya fice masa a rai. Don haka so take ya ɗauka kunya ce
da rashin sabo ke hana ta gaishe shi, ko kuma yi masa ya jiki, duk da yadda shi ba ya gajiya, a
kullum idan za su haɗu sai ya yi mata ya jiki, duk kuwa da ta warke, sai ɗan abin da ba a rasa
ba.
"Alhamdulillah. Ya jiki?" Ta yi ƙarfin halin faɗar hakan, a yanzu tana kallonsa. Ba tare da ya kalle
ta ba ya amsa da "Alhamdulillah." Daga haka gurin ya ɗauki shiru. Ita dai Hidaya kallon su
kawai take yi su duka kamar ta samu T.V. Sai zuwa can sannan ta ce
"Sister ki zo ki zauna mu yi hira." Murmushin nan na yaƙe, wanda ake cewa ya fi kuka ciwo
Daneen ta saki tana girgiza kanta. Da ƙyar ta iya furta
"A'ah, bari na ɗan je waje." Ta yi maganar tun kafin ma Hidaya ta ce komai ta fice daga ɗakin.
Hidaya ta bi ta da kallo tana murmushi kafin ta maida duban ta kan Tareeq.
.... Shiru Maama da Dada ji suka yi, bayan da suka gama sauraron bayanin Abeey duka. Bayan
wajen shuɗewar mintina biyu sannan Maama ta ce
"Yanzu ya za a yi kenan?" Ta tambaya a sukwane. Ajiyar zuciya Abeey ya sauke kana ya ce
"Toh! Ni dai ban yanke komai ba. Amma abin da yake akwai kawai shi ne aurensa da Jawahir
za a yi cikin satin nan kar a fasa. Idan ya so kin ga faɗuwa ta zo daidai da zama, sai ta ci gaba
da kula da shi. Amma ya kika ce Dada ji?" Cikin na'am da zancen Abeey Dada ji ta ce
"Tabbas zancenka ya yi Alhassan, kuma In Sha Allah hakan shi ne mafita. Ko babu komai
Jawahir 'yar'uwar Tareeq ce, kuma tana son shi, kula da shi a yanayin da yake ciki In Allah Ya
yarda ba zai zama matsala ba. Abin da nake so da ku kawai, ku fara shirye-shiryen aure, domin
kuwa kamar yadda aka tsaida shi sati mai zuwa, ba za a daɗa ba, ba za a rage ba. Za a ɗaura
shi In Sha Allah. Allah Ya sa hakan ne mafi alkhairi, Allah Ya ba su zaman lafiya, Ya ba wa
yarinyar nan ikon kula da Tareeq har zuwa lokacin da zai warke."
"Ameen." Dukkansu suka amsa da hakan, cikin na'am da maganar Dada jin ɗari bisa ɗari.
.... A karo na barkatai ya sake kallon kyakykyawar matarsa da ke zaune a kan kujera. Sai dai ta
kwantar da kanta a kan hannun kujerar da take kai ne, hannunta ɗaya yana gefenta kan kujerar,
ya yin da ɗayan yake lilo kusa da kanta. Idanunta a lumshe suke, sai dai duk da haka, hakan
bai hana ƙwalla sauka a kan kyakykyawar fuskarta ba. Cike da tausayawa yake kallon ta. A
kullum a kodayaushe yana rasa ta ina zai soma rarrashinta? Ta ina zai ba ta baki a kan yanayin
da ta tsinci kanta? Yana ji a jikinsa tamkar shi ne sila, shi ne silar rugujewar farin cikinta. Sai dai
duk da haka, ya zai yi? Ta ya ya zai iya jure ci gaba da kallon ta cikin wannan yanayin? Tunani
ya yi wa ƙwaƙwalwarta yawa, a kodayaushe tunani take. Idan aiki take tunani take, idan ta
zauna ta yi shiru tunani take, idan bacci take ma duk mafarkin abu ɗaya take, haka zalika ko
magana suke, sai dai ya ji shiru, idan ya kalle ta kawai sai ya ga alamar ta faɗa wata duniyar
tunani. Wataran kuma sai dai kawai ta zauna ta yi ta kuka, musamman ma idan ba ya kusa da
ita, shi ya sa kwata-kwata ba ya son yin nesa da ita. Don ba ya so abin ya yi yawa, kar ya janyo
mata babbar matsalar da ta fi wadda take ciki a yanzun wato Depression.
"Fatoum.." Ya faɗa a sanyaye kamar yadda ya saba kiran ta da hakan. A karo na farko ba ta ji
ba, sai da ya sake maimaitawa sannan ta buɗe idanunta da sauri ta tashi zaune sosai tana
kallon sa da jajayen idanunta.
"Na'am." Ta faɗa tana yin amfani da hannunta wajen goge fuskarta.
"Ba za ki yi ƙoƙari wajen rage damuwar nan ba koh? Kin manta abin da Likita ya faɗa koh? Ki yi
haƙuri don Allah ko da ba za ki daina duka ba, don na san hakan abu ne mai matuƙar wahala,
amma a ƙalla ki rage don Allah. Ko da ni ma zan samu salamar zuci. A kullum idan na kalle ki
cikin irin wannan yanayin, ina ji tamkar ni ne sila, kai ba ma tamka ba, ni ɗin ne dai sila. Don
Allah ki yi haƙuri Fatoum ki fawwala wa Allah komai, za mu dace In Sha Allah." Duk tsayin
maganar nan da ya yi, murmushi kawai ta yi idanunta na kallon wani wajen ta ce
"Uhumm." Ta faɗa tana girgiza kai. Shiru ya yi yana kallon ta, ya sauke ajiyar zuciya kafin a
sanyaye ya sake kiran sunanta a tausashe. Sai a lokacin tamkar wadda ta dawo daga tunani
sannan ta kalle shi, a hankali ya ɗaga mata kai kafin ya ce
"Ki yi mini magana mana." Tamkar jira take, sai kuwa ta shiga girgiza kai, tana jin ɗacin kalaman
da take tattarawa za ta faɗa. Tun kafin fitar su ma tana jin ɗacinsu ballantana kuma ta faɗe su.
Sai dai duk da haka, hakan bai hana ta soma faɗin
"Na rasa yadda zan yi, ban san me zan yi in ji daɗi ba. Tunanin nan da nake zaunawa na yi shi
kaɗai ne mafita ta. Duk da yadda nake ji tamkar ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Amma ba zan iya
hana kaina tunanin yarana ba. Ni idan da mutuwa ne ma suka yi, zan haƙura, na san zuciyata
za ta fi samun salamar suna can cikin kwanciyar hankali In Sha Allah. Amma yanzu fa? Ban san
inda suke ba, ban san suna cikin wane irin hali ba. Shin a wane waje suke rayuwa? Shi ma ban
sani ba. Yaushe ne Allah zai haɗa mu? Duk ban sani ba. Yallaɓai ina ji tamkar zuciyata za ta
faso ƙirjina ne ta fito ta tarwatse, ina ji kamar ƙwaƙwalwata za ta fashe idan ina tuna su. Ina iya
ƙoƙarina wajen ganin na bar wa Allah komai, amma na kasa daina tunaninsu. Kullum suna cikin
ko'ina na jikina a manne, komai nake su ɗin ne dai a raina. Shin ya zan yi ni kam da raina? Ina
zan ga yarana?" Ta yi maganar a raunace. Ajiyar zuciya ya sauke, yana jin daɗin yadda yau ɗin
ta amayar da abin da ke cikin zuciyarta. Ba kamar sauran ranaku da ta fi son ta yi shiru, ko
kuma ta yi guntuwar magana ba. Ya runtse idanunsa yana ji da gasken gaske shi ne sila! Shi ne
silar raba wannan uwar da 'ya'yanta. Shin me ya sa ma ya shiga rayuwar Fatima? Tabbas da ya
san haka ne zai faru, da bai yi yunƙurin neman auren Fatima ba. Ko kuma ma tun farko ya yi
fatan kar Allah Ya haɗa shi da Fatima.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 28
Ya shafe kusan mintuna biyu ba tare da ya ce komai ba. Kallon ta kawai yake yi cike da
tausayawa, zuciyarsa kuwa wani irin raɗaɗi yake ji, raɗaɗin kuma ba na komai ba, sai na
zamowarsa silar rugujewar farin cikin Fatimarsa.
"Ki yi haƙuri, in sha Allah yaran nan suna cikin ƙoshin lafiya, kuma za su dawo miki cikin ƙoshin
lafiyar. Abin da nake so da ke kawai ki ci gaba da addu'a, sannan ki rage wannan damuwar da
kike yi. Kada ki manta da shawarwarin likita da ya ba mu. In Allah Ya yarda nan ba daɗewa ba
za mu samu labarin inda suke, tun da har yanzu ban daina cigiya ko Allah zai saka a dace ba.
Ki yi haƙuri ki yi shiru." Ya ƙare maganar cikin rarrashi da taushin murya. Hannu Inna-wuro ta
saka ta goge fuskarta a nutse, idanunta a lumshe tana ci gaba da jin bugun zuciyar da take
fama da shi kusan kowanne lokaci. A hankali ta buɗe baki da ƙyar ta furta
"Allah Ya sa." Ta faɗa tana maida bayanta ta kwantar kan kujerar da take kai cikin rashin sanin
abin yi. Bin ta ya yi da kallo ba tare da ya ce komai ba. Ya rasa ta inda zai ɓillowa wannan
al'amari. Shiru kawai ya yi ya ci gaba da kallon ta yana tunanin hanyar da zai bi wajen tsananta
bincike ko Allah zai sa a dace su sami inda yaran nan suke.
... Turo ƙofar da aka yi shi ne ya sanya Maama ɗaga ido ta kalli mai shigowar. Umma da kuma
Jawahir suka ƙaraso cikin ɗakin. Da murmushi ta miƙe tana faɗin
"Lale marhaba." Maida mata da martanin murmushin suka yi kana Umma ta nemi waje ta
zauna. Ya yin da Jawahir ta tsaya a gefen kujerar Umman tana sunnar da kai ƙasa. Gaisawa
Umma da Maama suka yi, Umman na tambayar jikin Tareeq.
"Jiki Alhamdulillahi wallahi, zuwa gobe ma idan Allah Ya kai mu, muke saka ran sallama, kamar
yadda suka faɗa."
"Kai Alhamdulillah, Alhamdulillah. Ashe ƙafar ta yi sauƙi ke nan, ko ma in ce ta warke?" Umma
ta faɗa tana murmushi. Sai da Maama ta kalli ƙafar Tareeq ɗin da idanunsa ke a lumshe kamar
mai bacci kafin ta ce
"Alhamdulillah kam, ta warke za a ce. Sai dai... Ba ku yi magana da yayan naki ba ne?" Ta ƙare
maganar da sigar tambaya. Girgiza kai Umma ta yi tana faɗin
"A'ah, ba mu yi ba kam. Amma yau sun haɗu za su yi magana da Abban Jawahir."
"Barka da wannan lokacin Maama." Jawahir ta faɗa tana murmushi. Amsa mata gaisuwar
Maama ta yi cikin sakin fuska, har ranta tana ji in Allah Ya yarda ta yi sa'ar suruka. Sun kwashe
wajen minti 20, kafin Tareeq ya buɗe idanunsa.
"Sannu Tareeq." Umma ta faɗa tana kallon sa. Sai da ya ɗan saki murmushi kaɗan, wanda ya
ƙawata kyakykyawar fuskarsa sannan ya ce
"Yawwah, Barka da wannan lokacin." Ya yi maganar a haɗe.
"Barka dai, ya jikin?" Sai da ya jinjina kai sannan ya amsa da
"Alhamdulillahi." Nan ta sake yi masa fatan samun sauƙi, Maama ta amsa da "Ameen."
"Yah Tareeq ina wuni?" Jawahir ta faɗa tana satar kallon wannan kyawawan ƙwayar idanun
nasa. Ta kafe shi da idanunta, tun kafin ma ya ɗago nasa ta kasa kalla. A hankali ya ɗaga nasa
idanun ya kalle ta, ya ɗan lumshe su, lokaci guda yana buɗewa ya ce
"Alhamdulillah Jawahir, kina lafiya?" Ya yi ƙarfin halin faɗin hakan. Sai da ta gyara tsayuwa tana
jin wani irin farin ciki na mamaye ta sannan ta ce
"Lafiya ƙalau." Daga haka ta sake mazewa a gefe ba tare da ta zauna ba. Hannu Maama ta
saka ta yafito ta tana faɗin
"Kin ga ni ba na son wata kunya zo ki zauna. Baƙuwarki ce ni?" Ta ƙare maganar tana dariya.
Ita ma Umman dariya ta yi, ya yin da Jawahir ke ta murmushi kawai. Kamar yadda Maaman ta
faɗa, don haka ta nemi waje ta zauna kuwa.
Bayan shuɗewar wasu mintuna aka fara kiraye-kirayen Sallahr Maghrib, duk suka yi alwala
suka dawo cikin ɗakin. Maama ta kalli Tareeq ta ce
"Za ka yi alwalar ne?"
"Ehh.." Ya amsa mata da hakan. Ƙarasawa ta yi keɓantaccen wajen da aka ajje masa kujerar
da ba a daɗe da kawo ta ba, ta ɗakko ta, ta ƙaraso da ita inda yake. A hankali ta shiga taimaka
masa don ganin ya zauna a kan kujerar. Wani irin ƙwarewa Umma da ta zuba ruwa a tambulan
tana sha ta yi, ruwan da ta ji ya shige mata har tsakar ka. Ta saka hannunta ta shiga bubbuga
kanta har lokacin idanunta a kan Tareeq. Har ba ta san