Showing 48001 words to 51000 words out of 81712 words
Chapter 17 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
faɗa." Girgiza
kai Tareeq ya yi kafin ya ce bayan ya riƙo hannun Maama.
"Maama ki bar ni na ga wadda za ta ba ni ƙodarta ba tare da wani dalili ba. Ina buƙatar ganin
wace ce ita tabbas." Tun kafin ya ƙarasa Maama ta katse shi da faɗin
"Rashin yardarka ya yi yawa Tareeq, har a kan lafiyarka ma?" Ta ƙare tana kallon sa. Iska ya
fesar daga bakinsa, ganin da ya yi kwata-kwata Maaman ta ƙi fahimtarsa, lokaci ɗaya kuma
yana mayar da jikinsa ya kwantar a kan gadon, har lokacin idanunsa a lumshe.
"Ya isa haka Fatima. Kin fi kowa sanin halin ɗanki, ina ga kuma hakan ba laifi ba ne. Amma dai
a halin da kake ciki ka fi buƙatar hutawa, so ka kwanta ka samu ka yi bacci zuwa an jima. Ni da
mahaifiyarka za mu yi magana da yarinyar." Jinjina kai kawai ya yi daga inda yake kwance ba
tare da ya ce komai ba. Maama ta bi shi da kallo cike da tausayawa. Hannunta ta kai a hankali
ta taɓa wuyansa, jin da ta yi zafin ba sosai ba ya sanya ta sauke ajiyar zuciya har cikin ranta
tana jin daɗi. Saboda yadda kwana biyu Tareeq ɗin ya din ga fama da matsanancin zazzaɓi mai
zafin gaske. Babu daɗewa aka turo ƙofar ɗakin, Sultanah ce da Hidaya cikin dogayen riguna
kusan iri ɗaya sai dai ba kala ɗaya ba ne. Da sauri suka ƙarasa inda Tareeq ɗin yake, kowacce
jikinta a matuƙar sanyaye.
"Sannu Yah Tareeq." Suka kusan haɗa baki wajen faɗin hakan. Ɗan lumshe idanunsa ya yi
kaɗan kafin ya ce
"Yawwah."
"Wai Yah Tareeq dama ka san da wannan ciwon?" Hidaya ta faɗa kamar za ta yi kuka. Girgiza
kai ya yi, yana ɗan ƙaƙalo murmushi a hankali ya ce
"Kaɗan kaɗan.. Ban san abin ya kai haka ba, duk da ina karɓar gwajin lafiyata a kai a kai, ban
san lamarin zai yi tsamari har haka ba." Ya ƙare a ɗan gajiye.
"Wallahi Yah Tareeq mun fi ka kula da lafiyarka. Kai dai kawai ciwon a jikinka yake, amma mun
fi ka damuwa da shi." In ji Sultanah tana kallon sa. Yanzu kam sai da ya ɗan yi dariya, daidai
lokacin da Abeey ya miƙe yana faɗin
"Ya kamata mu yi waje fa haka." Cikin girmamawa duk suka amsa da "Toh." Ba su ɗauki lokaci
mai tsayi ba gaba ɗaya suka fice suka bar shi shi ɗaya zuciyarsa cunkushe da tunane-tunane.
Cikin ikon Allah aka gwada ƙodar Daneen, kuma za ya iya cira a saka wa Tareeq. Don haka
Likitan ya tsayar da washe-gari a matsayin ranar da za a yi aikin.
Gaba ɗaya jikinta a matuƙar sanyaye yake, lokacin da take taka wa tana bin bayan wani da zai
raka ta ɗakin da Ameer yake ciki. Sai da ya tura ƙofar ɗakin sannan ya juya ya bar wajen.
Daneen ta bi shi da kallo kafin ta maida idanunta cikin ɗakin. Runtse idanunta ta yi, tana jin
yadda zuciyarta ta karye, saboda hango ɗan'uwanta da ta yi kwance, har kuma lokacin ba ya
iya numfashi shi ɗaya sai da taimakon na'ura. Kamar wadda ke tsoron taka ƙasa haka take
takawa zuwa cikin ɗakin idanunta a kansa. Ta zuba wa kyakykyawar fuskar Ameer idanunta
lokacin da yake bacci kai sai ka rantse cikin kwanciyar hankali yake, babu wani abu da ke
damunsa. A nutse ta kai hannunta ta riƙo hannunsa cikin nata, tana jin wata irin ƙwalla na tarar
mata. Idanunsa ya shiga buɗewa a hankali kamar ya san wadda ke tsaye a wajen. Sai dai shi
ma cike yake da fatan a ce ya buɗe idanunsa ya ga 'yar'uwarsa a gefensa. Aikuwa cikin ikon
Allah yana buɗe su ɗin kuwa ya sauke a kan Daneen. Runtse idanunsa ya yi kafin ya buɗe a
hankali daidai lokacin da wasu kyawawan ƙwalla suka zubo daga cikin idanunsa.
"Ameer." Ta faɗa, tana kai hannunta kan bakinta ta toshe don kar kukan da take ta riƙewa ya
fito.
"Adda." Ya yi ƙarfin halin faɗa. Rasa abin da za ta yi ne ya sanya ta zube wa a wajen kawai, ta
kifa kanta a kan gadon ta shiga raira kukanta a hankali. Hannunta da ke kusa da na shi ya riƙo
sosai, dalili kenan da ya sanya ta saka hannunta ta share fuskarta kafin ta miƙe tsaye tana
kallon sa.
"Kin ga abin da na ja mana koh?" Ya faɗa a raunace. Girgiza kai ta yi tana barin hawayen cikin
idanunta damar zubowa.
"Ka dena mini irin wannan maganar Ameer, ba ka ja mana komai ba. Duk abin da ka ga ya faru
dama rubutacce ne. Bawa kuma ba ya taɓa wuce wa ƙaddararsa." Murmushin yaƙe Ameer ya
yi, yana sake jin yadda gaba ɗaya duniyar ta fice masa a ransa. Ji yake tamkar zuciyarsa za ta
yi bindiga saboda tsananin ciwon da yake ji a cikinta. Cikin sanyi da ƙarfin hali ya soma faɗin
"Adda ba na tunanin zan rayu kowanne irin aiki aka yi mini. Ni kaɗai na san abin da nake ji.
Bayan zuciyata Adda cikina na yi mini wani irin ciwo da na kasa fahimtar wane iri ne shi. Idan
na mutu ki nemar mini yafiya gurin Innarmu, duk abin da ya faru ni na jawo. Sai da kika ce mini
kar mu baro ƙauyenmu amma na kafe, yanzu ga abin da ya faru." Ya kai ƙarshen maganar yana
sauke wani numfashi a mugun wahalce.
"Ameer ba na so, ka dena na faɗa maka. Ba za mu koma wa Inna a wani irin hali ba, In Sha
Allah za mu koma mata ne a yadda muka baro ƙauyenmu. Za ka warke da yardar Ubangiji. Na
kuma roƙe ka da ka cire wannan damuwar da kake ɗora wa kanka ko don samun lafiyarka,
Ameer ka san lafiyarka ita ce tawa don Allah." Daneen da muryarta ke fita da ƙyar cikin kuka ta
faɗi haka. Girgiza kai kawai ya yi ya ce
"Toh Adda na dena, na dena.." Ya faɗa yana wani lumshe idanunsa. Sai da ya yi bacci tana
cikin ɗakin sannan ta fice ƙwaƙwalwarta fall tunani kamar za ta tarwatse.
..Tana nan zaune inda Yohanah ya bar ta, bayan ya ba ta uzurin zai je ya dawo. Ta zauna ta yi
shiru cikin rashin sanin abin yi. Ita kanta tunani nema yake ya yi wa ƙwaƙwalwarta yawa, sai dai
babu yadda ta iya. Haka nan take zaune, a ido tana wajen amma a zahiri ita ce zaune a wajen
kawai, amma gaba ɗaya hankali da duk wani tunaninta yana wani wajen daban.
"Doctor na son ganin ki." Shi ne kawai abin da ta ji, wanda ya yi nasarar dawo da ita daga
dogon tunanin da ta tafi.
"Na'am?" Ta ƙare maganar da alamar tambaya tana kallon wadda ta yi mata magana. A karo na
barkatai ta sake maimaita mata saƙon Likitan tana nazarinta. Miƙewa Daneen ta yi tana faɗin
"Tohm." Daga haka ta bi matar a baya zuwa office ɗin Likitan. A bakin wani ɗaki suka rabu, ya
yin ita matar ta kalli Daneen ta ce
"Ki shiga." Kallon ta Daneen ta yi tamkar mai neman ƙarin bayani, sai dai kuma ba ta ce komai
ba, illa jinjina kai da ta yi. Daga haka matar tayi gaba ya yin da ita kuma ta tura ƙofar ɗakin da
sallama ɗauke a kan laɓɓanta. Kusan a tare suka amsa sallamar, dukkan su idanunsu a kanta.
Kasancewar ba ta san za ta yi ido huɗu da wasu fuskokin ba, ya sanya ta yin turus tana ɗauke
kanta daga kallon su.
"Ƙaraso mana." Maama ta faɗa har lokacin idanunta a kan Daneen. Cike da sassarfa Daneen ta
ƙarasa cikin ɗakin tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa.
"Taho ki zauna a nan." Maama ta faɗa, ba tare da jin komai ba ta ja hannun Daneen ɗin ta yi
mata mazauni a gefe kaɗan da ita. Babu musu Daneen ta zauna hannunta ɗaya cikin ɗaya,
zuciyarta fall tunanin shin su waɗannan ɗin su waye su?
"Ina wuni?" Ta yi ƙarfin halin faɗa a hankali.
"Alhamdulillahi, ya jikin ƙanin naki?" Maama ta faɗa.
"Alhamdulillahi." Ita ma Daneen ta ba ta amsa a sanyaye. Hidaya da ke gefen Maama ta ce
"Wai ita ce za ta ba wa Yah Tareeq ɗin ƙoda?" Jinjina kai Maama ta yi tana murmushi. Cikin
matuƙar farin ciki Hidaya ta miƙe ta koma kusa da Daneen, tana jin wata irin ƙaunarta lokaci
guda. Tun shigowar ta take yaba irin kyawun da Allah Ya ba ta, sai dai da yake ba ta san wace
ce ba ya sanya ta kama kanta.
"Amma na ji daɗi, Allah Ya ba ki abin da kike nema duniya da lahiya, Allah Ya biya miki
buƙatunki na alkhairi."
"Ameen." Sultanah ta amsa addu'o'in Hidaya tana murmushi.
"Ya sunanki?" Hidaya ta faɗa tana kallon Daneen da murmushi a kan fuskarta. Sai da ta ɗaga
kyawawan idanunta da suka ƙanƙance sannan ta ce
"Daneen."
"Woww, suna mai daɗi. Sannu Daneen." In ji Hidaya tana murmushi. Godiya sosai suka ci gaba
da yi wa Daneen, suna kuma yi wa Ameer addu'a. Abin da ya matuƙar faranta ranta kenan.
"Sultanah ku je gida tare da ita ta samu ta yi wanka ta yi bacci ta huta kafin goben da za a yi
aikin." Maama ta faɗa bayan ta miƙe tsaye. Da sauri Daneen ta kalli Maama tana girgiza kai.
Tana kai wa ƙarshen maganarta ta soma faɗi cikin sanyayyiyar muryarta.
"A'ah, ba zan iya tafiya in bar ƙanina ba. Ki yi mini afuwa don Allah ba zan iya ba." Kallon ta su
duka suke yi, abin bai ba su mamaki ba, don duk tana hakan ne a kan ɗan'uwanta. Su ma kuma
sun san me ake nufi da ɗan'uwa.
"Shi kenan, ki je zuwa an jima sai ku dawo idan kin huta." Kamar za ta fasa kuka haka ta ji.
Tabbas matar ta yi mata kwarjini amma duk da haka ba ta ji ko nan da can za ta iya matsawa
daga asibitin, bayan Ameer na ciki a kwance. Don haka cikin girmamawa ta ce
"Don Allah ki yi haƙuri ki bar ni wajen ɗan'uwana." Ta faɗa lokacin da ƙwalla ta cika cikin
idanunta. Cike da tausayawa Maama ta ce
"Babu damuwa. Allah Ya ƙara lafiya, Ya kuma saka miki da alkhairi." Wata ƙatuwar ajiyar zuciya
Daneen ta sauke, tana jin wani sanyi na ratsa ta. Haƙiƙa ta ji daɗin kai ƙarshen maganar da
matar ta yi, don da ta ci gaba da cewa ta je ɗin ba ta tunanin za ta iya ci gaba da yi mata musu.
A sanyaye ta amsa da
"Ameen." Daga haka suka yi sallama da Daneen suka fice daga ɗakin. Ita ma ba ta ƙara wasu
mintina ba ta fice zuwa inda take zaune ɗazun.
Washegari ita ce ranar da za a yi wa Daneen aikin cire ƙoda, ya yin da za a yi wa Tareeq na
dashen ƙodar. A kuma safiyar ranar ne Yohanah ya je ya biya duk kuɗaɗen da ake buƙata na
aikin da za a yi wa Ameer. Cike da mamaki Likitan ke kallon sa, ya ce har lokacin ya kasa dena
tantamar anya kuwa Yohanahn kafiri ne da gaske?
"Amma me zai hana ka nuna fuskarka wajen Alhaji Alhassan. Alkhairinka yawa gare shi wajen
iyalinsa." Murmushi Yohanah ya yi kafin ya ce
"Babu damuwa, ina yin komai ne saboda Allah, kuma ba na so ya sani. Akwai dalilin yin hakan,
ina so ne na rama abin da ya yi mini. Kamar yadda yake taimakawa mutane a bayan ido, shi ya
sa nake so na rama masa ba tare da ya sani ba." Jinjina kai Likitan ya yi, bayan ya sauke ajiyar
zuciya ya ce
"Duk da haka, ko da sau ɗaya ne ka bari ya ganka ya gode maka. Ka samo wadda za ta ba wa
ɗansa ƙoda. Duk da a matuƙar buƙatar kuɗi take, hakan bai sa ka bar ta da shi ba. Ka kuma ƙi
barin Alhaji Dikko ya biya kuɗin aikin a matsayin kuɗin ƙodar yarinya, shi ma ka ɗauke masa.
Kuma duk da haka ba ka so ya sani, bayan kai ɗin na daban ne, mai ɗumbin alkhairi a gare
shi." Kafin Yohanah ya ce komai wayarsa ta shiga ringing, ya kalli mai kiran nasa, kawai sai ya
tura ta cikin aljihunsa kafin ya ɗaga idanunsa ya maida su kan Likitan ya ce
"Please doctor a yi abin da na ce. Ita yarinyar babu damuwa za ta iya haɗuwa da shi, amma ni
babu buƙatar hakan kamar yadda na faɗa maka." Yohana ya ƙare maganar yana sakin wani
murmushi, lokaci ɗaya yana kai hannunsa guda ɗaya ya shafa haɓarsa har lokacin idanunsa a
kan Likitan.
#YOHANAH
#KIDNEY
#DANEEN
#TAREEQ
#AMEER
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 20
Jinjina kai Likitan ya yi kafin ya ce
"Shi kenan, Allah Ya saka maka da alkhairi. A madadin Alhaji Dikko, ina sake miƙa godiya gare
ka." Ba tare da Yohana ya amsa ba ya miƙa wa Likitan hannu har lokacin fuskarsa da murmushi
suka gaisa. Daga haka ya yi waje, Likitan ya bi shi da kallo yana ci gaba da mamakin
kyawawan halaye irin nasa.
Cikin nasara, ikon Allah da kuma tarin addu'o'i daga bakunan iyalan Dikko aka yi wa Daneen da
kuma Tareeq aiki.
.. "Sannu yaron nan." Dada ji ta faɗa tana kallan Tareeq cike da tausayawa. Jinjina kai ya yi
daga inda yake kwance, yana sake lumshe idanunsa. Shafa goshinsa Maama ta yi tana jin wani
irin tausayin ɗan nata, saboda sanin halinsa da ta yi, idan dai har ka ga ciwo ya kayar da shi,
toh da gasken ciwon nan ya shahara. Ba ta ce komai ba, sai neman waje da ta yi ta zauna,
daidai lokacin da aka turo ƙofar ɗakin. Sultanah, Abdoul da Hidaya, su ne suka shigo. Idanunsa
a kan Abdoul ya sauka, cike da mamakin yadda suka shigo tare da su Sultanah. 'Ko dai har
abin nasu ya ɗore haka?' Ya raya hakan a ransa, yana fatan a ce da gasken haka ne.
"Tare kuke ne?" Dada ji ta yi tambayar tana kallon Abdoul, tambayar da take ta masa yawo cikin
kai. Don haka sai ya maida duban sa kan Abdoul don jin amsar da zai bayar, cike da fatan Allah
Ya sa burin ƙanwarsa ya cika.
"A'ah, a cikin asibitin muka haɗu." Ya ba wa Dada ji amsar cikin girmamawa.
"Ayyah." Ta yi maganar a taƙaice. Daga haka ya gaishe ta, kafin ya gaisa da Maama. Sai kuma
ya ƙarasa inda abokinsa yake.
"Sannu! Ya ƙarfin jiki?" Ya tambaya cikin kulawa. Sai da Tareeq ya lumshe idanunsa kafin ya ce
"Alhamdulillahi."
"Allah Ya ƙara sauƙi, sannu." Yanzu kam jinjina kai kawai ya yi yana sake lumshe idanunsa don
so yake ya ɗan sake runtsawa, don jin sa yake tamkar an canja ji. Wani daban yake ji tun bayan
da aka yi aikin. Sai dai shi a karan kansa ya matuƙar jin daɗin jikinsa, wanda ya yi kwana da
kwanaki rabon da ya ji irin hakan. Su ma Hidaya da Sultanah gaishe da yayan nasu suka yi.
Zuwa can Abdoul ya ce
"Maama zan so na ga wadda ta sadaukar da ƙodarta a kan Tareeq ɗinmu, ko don in yi mata
godiya." Da sauri Dada ji ta kalle shi ta ce bayan ta soma tafa hannunta.
"Kaa ga aikin shiririta, daga zuwa ɗazu tana bacci babu wanda ya sake komawa. Ke maza ku
tashi mu je wajen baiwar Allah ɗin can." Ta ƙare maganar tana miƙewa tsaye. Babu musu
dukkansu suka miƙe. Maama ta kalli Tareeq, ganin da alama kamar bacci ya ɗauke shi ne ya
sanya ta bin bayan su Dada ji da suka yi waje.
"Allah kuwa Yah Tareeq yana jin jiki, wallahi duk jikina a sanyaye yake." Hidaya ta faɗa a
marairaice, tana hango fuskar yayanta da ta ɗan sauya, kamar ba shi ba.
"Wallahi ke kam.." Ita ma Sultanahn ta faɗa a sanyaye.
Hidaya ce a gaba, don haka ita ce ta yi amfani da hannunta wajen tura ƙofar ɗakin. Sultanah,
Maama da Dada ji suka bi bayanta. Sai Abdoul da ke a ƙarshe, wanda sai da Maama ta ce ya
shigo sannan ya bi bayan su. Gaba ɗayansu idanunsu na kan gadon. Tana kwance har zuwa
lokacin tana bacci, duk da yadda take bacci hakan bai hana bayyana yadda idanunta suka
ɓurma suka yi ciki ba.
"Allah Sarki baiwar Allah." Dada ji ta faɗa tana kallan innocent face ɗin Daneen, wadda
yarintarta ta gama bayyana ko daga kallan fuskarta. Tun kafin su kai ga zama, Daneen ta wani
irin zabura daga baccin da take, a firgice ta furta bayan ta tashi daga kwanciyar da take.
"Ameer!" Gaba ɗaya idanunsu sai suka sake koma wa kanta. Tarr ta buɗe idanunta cikin ɗakin,
sai ta shiga rarraba manyan idanun nata, tana kallon duk mutanen da ke ciki.
"Ameer." Ta sake faɗa a kan laɓɓanta har lokacin ba ta daina kallon su ba. Hidaya ce ta tashi ta
ƙarasa inda take, ta nemi waje ta zauna kafin ta kalli Daneen da ke takure waje ɗaya ta ce
"Sannu." Kamar sai da ta ce sannun sannan ta tuna abin da ya faru, saboda yadda ta kai
hannunta ƙirjinta ta dafe. A hankali ta buɗe baki ta ce
"Tohm."
"Ya jikin?" Sake dafe saitin ƙirjinta ta yi tana sauke wani numfashi kamar wadda ta yi tsere, ba
tare da ta ba wa tambayar Hidayan muhimmanci ba ta ce
"Ƙanina.."
"Hidaya taimaka mata ta gyara jikinta, sai ta je ta ga ƙanin nata." Maama ta faɗa. Da