Showing 75001 words to 78000 words out of 81712 words
Chapter 26 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
faɗa, bai ce komai ba kawai ya jinjina kansa, suka wuce. Ita ma
Dada ji bin su ta yi da kallo cike da tausayin jikan nata.
... "Wai me kike jira ne? Ko dai kin haƙura kin fasa ɗaukar fansar ɗan'uwan naki? Ko dai ba kya
so a hukunta Tareeq ne?" Maganganun da Yohana ya faɗa mata ke nan, waɗanda suka saka ta
yin shiru kamar mai nazari. Kafin ta kai ga cewa komai ya sake faɗin
"Anya kuwa kina lissafin ragowar kwanakin da muke da su? Cikin sati biyu kwana nawa muke
da shi? Ki faɗa mini idan kin fasa ne in daina damun kaina." Sai a lokacin sannan ta sauke
ajiyar zuciya, ta buɗe baki da ƙyar ta soma faɗin
"Ina nan ina iya ƙoƙarina. Na matuƙar gode da kulawa, kuma in Allah Ya yarda za ka ji ni zuwa
gobe. Na gaji da zaman gidan nan kwata-kwata, ba na son ci gaba da kasancewa gida ɗaya da
mutumin nan. Ba na son ganinsa ko kaɗan, duk lokacin da na gan shi kewar ɗan'uwana dawo
mini take. Ina jin zuciyata na mini zafi, wani irin abu ke tokare mini a ƙirji ya din ga tokare mini
numfashi. Ba na son ganin sa ko kaɗan. Zan yi ƙoƙari in Allah Ya yarda a cikin kwana biyu in
san yadda zan yi in shiga ɗakinsa." Jinjina kai Yohana ya yi kafin ya ce
"Yawwah, ki ƙoƙarta. Kar ki manta har yanzu ruhin ɗan'uwanki na can cikin rashin salama.
Gwara a yi maza a hukunta shi ko ruhinsa ya samu salama." Jinjina kai kawai Daneen ta yi
kamar yana gabanta. Soma fahimtar halinta da ya yi ne ya sanya shi fahimtar ta ji abin da ya
faɗa. Don haka bai sake cewa komai ba, kawai ya katse wayar. Daidai lokacin da aka turo ƙofar
ɗakin aka shigo. Ita ma kuma daidai lokacin ta fito daga cikin toilet. Hidaya da Sultanah ne,
suka sakar mata murmushi kusan lokaci guda. Maida musu da martanin murmushin ta yi, kana
ta ƙaraso cikin ɗakin.
"Ohh, kwata-kwata ba na jin daɗin jikina yau ɗin nan wallahi." Sultanah ta faɗa tana ɗan dafe
kanta bayan ta zube a kan luntsumemen gadonsu.
"Ke dai malama kawai ki ce Yah Abdoul bai kira ki ba." Hidaya ta faɗa tana dariya. Harara
Sultanah ta jefa mata kana ta ce
"Lallai ma Sisi, wallahi ba ki da dama. Toh ko damuwar Yah Tareeq ai ta isa ta hana mu walwala
daga ni har ke ɗin." Cikin na'am da zancen Sultanah Hidaya ta kwantar da kanta kan pillow
kana ta ce
"Wallahi ke kam ki bari kawai. Duk jikina a sanyaye yake tun jiya wallahi."
"Daneen." Hidaya ta faɗa tana kallon Daneen da ta yi shiru tana kallon wani wajen kamar mai
tunani. Da sauri ta kalli Hidayan ba tare da ta ce komai ba. Cikin mamaki ta ce
"Lafiya kuwa?" Ɗan murmushin yaƙe ta aro ta yafa a kan fuskarta kafin ta ce
"Babu komai."
"Kin tabbatar 'yar'uwa?" Hidaya ta sake tambaya cikin kulawa. Jinjina kanta ta yi tana miƙewa.
Ta ce bayan ta kalli Hidaya
"Bari na ɗan fita." Jinjina kai Hidaya ta yi tana faɗin
"Tohm." Daga haka Daneen ta fice daga ɗakin, ya yin da Hidaya da Sultanah suka bi ta da kallo
har ta fice.
"Ba ta da walwala gaba ɗaya, kamar akwai wani abu da ke damun ta." Sultanah ta faɗa har
lokacin ba ta daina kallon inda Daneen ta ɓace wa ganinsu ba. Cike da amincewa da zancen
nata Hidaya ta jinjina kai kana ta ce
"Na gani fa.. Ga shi ba ta saurin sabo. Ta ƙi sakin jikinta kwata-kwata ballantana mu shiga
jikinta."
"Wallahi, abin na ba ni mamaki." In ji Sultanah.
A hankali take taka wa cikin palourn, sanye take cikin doguwar rigar atamfa, da kuma dogon
hijabin da ya wuce har ƙasan gwuiwarta.
"Ohk." Shi ne kawai abin da ta ji, wanda hakan ya matuƙar tsorata ta, don ba ta yi tsammanin
akwai wata halitta cikin ɗakin ba. Domin dai kuwa ita ba ta gani ba.
"Wayyo Allah na." Ta faɗa bayan ta dafe ƙirjinta, maganar tata ke nan da ta ɗauki hankalinsa.
Ya ɗaga kai ya kalle ta, daidai lokacin da ita ma ta sauke nata a kansa. Sam ba ta yi tsammanin
ganinsa a wannan lokacin ba. Kafin haɗuwar idanunsu waje ɗaya ta yi saurin janye nata tana
sakin ajiyar zuciya, lokaci guda rashin annurin fuskarta na sake bayyana. Wani irin ɓacin rai tuni
ya mamaye ta.
'Kar ki kwafsa' Ta ji wani ɓangare na zuciyarta ya gargaɗe ta. Ji take kamar ba za ta iya ba,
amma haka ta daure, ta cije, ta kuma yi iya bakin ƙoƙarinta wajen haɗa kalmomi ta ce
"Barka da wannan lokacin." Shiru ya yi yana nazarinta na tsawon sakanni. Kamar kuma ba shi
ba, sai ya janye idanunsa kafin ya ce
"Barka dai. Ina za ki je?" Ya ji tambayar da yake tsarawa cikin ransa ta yi masa katsalandan
wajen fitowa. Har ta ware idanunta da niyyar kallon sa, sai kuma ta fasa, don ba ta so kallon
fuskarsa ya tuna mata da waye shi. Dalili ke nan da ya sanya ta faɗin
"Na ga su Hidaya suna hutawa, shi ne na ce bari na tambaye ka ko za a gyara maka ɗaki ne."
Ta ƙare maganar ita a karan kanta tana jin wani banbarakwai. Shiru ya yi na tsawon sakanni ba
tare da ya ce komai ba. Har ta cire ran zai amsa, ta kuma ji haushin kanta sannan ta jiyo
muryarsa can ƙasa ya ce
"Yanzu dai ba na buƙata kam." Ya dakata a nan. Bai yi niyyar sake cewa wani abu ba, sai dai ko
babu komai ita ɗin mace ce mai muhimmanci a rayuwarsa, bayan haka kulawa ce ta nuna a
gare shi, yana da kyau ko ya ya ya nuna ya yaba. Don haka ya ce
"Amma idan ina buƙata zan yi miki magana. Kira mini Sultanah ko Hidaya." Ya yi maganar
lokaci guda. Cike da takaici da haushi ta juya ba tare da ta ce komai ba. Ya ɗan lumshe
idanunsa na tsawon lokaci yana saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa. Har bai san lokacin da Sultanah ta
ƙaraso cikin ɗakin ba. Sai da ya ji hannunta saman kujerar da yake kai sannan ya ankara.
"Yah Tareeq." Ta faɗa tana kallon yadda duk wasu alamomi suka nuna ya dawo daga tunani ne.
Ba tare da ya amsa kiran sunansa da ta yi ba ya ce
"Kai ni ɗakin Maama." Ya faɗa kai tsaye. Babu musu ta tura shi har zuwa bedroom ɗin Maaman.
Daga haka ta juya. Maama ta kalle shi tana faɗin
"A'ah, ƙarasowa ka yi kenan." Jinjina kai ya yi kana ya ce
"Ehh Maama, wata muhimmiyar magana nake so mu yi."
"Toh! Ikon Allah! Me ya faru kai kam? Sanar da ni." Maama ta ƙare tana gyara zamanta. Ya yi
shiru yana nazarin ta inda zai fara maganar, duk da yadda duka jikinsa ya yi na'am da abin da
ya yanke. Bai san ya daɗe cikin ɗakin ba tare da ya ce komai ba, sai da Maama ta ce
"Tareeq!" Ta kira sunansa cike da mamakin yadda ta ga ya faɗa duniyar tunani. Duk da ta ga
tarin damuwa a kan fuskarsa, sai dai hakan ba abin mamaki ba ne, duba da abin da ya sake
faruwa tsananinsa da Jawahir. A hankali ya ɗan lumshe idanunsa a nutse kana ya buɗe su a
kan Maama. Cikin nutsuwa ya soma magana, kamar wanda ba ya so a ji abin da yake faɗa.
"Maama.."
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 30
"Ina ganin idan har kin amince da abin da zan faɗa, toh na samu mata." Ya ƙare maganar yana
kallon ta. Cike da mamaki wanda ya bayyana a kan fuskarta, Maama ke kallon sa. Jin abin take
kamar a mafarki. Ya samu mata fa yake faɗi? Ta yaya? A ina? Yaushe hakan ta faru? Anya
kuwa ma Tareeq ɗin ne? Duka waɗannan tambayoyin ita kaɗai take yi wa kanta cikin zuciyarta,
sai dai har lokacin idanunta na kansa. Bayan wajen shuɗewar sakanni talatin sannan ta ce
"Mata kuma Tareeq? A ina? Wace ce ita? Yaushe kuma kuka haɗu har ka ji ta kwanta maka a
rai, har za ka iya auren ta? Faɗa mini Tareeq." Ta yi maganar cike da zaƙuwa da jin amsar da
za ta fito daga bakinsa. Hannunsa ya kai a hankali ya ɗan murza goshinsa, kafin ya lumshe
idanunsa a nutse yana jin wani irin nauyi cikin ƙirjinsa. Ta ɗauka hakan da ya yi yana nuni ne da
ya haƙura da yin maganar saboda yadda ya ga tsananin mamaki a kan fuskarta. Sai dai ga
mamakinta sai ji ta yi ya ce
"Maama idan dai har kin amince, zan auri Daneen, idan ita ma ta amince." Wani irin kallo
Maama take bin Tareeq da shi, kallon da lokaci guda ya fassara shi da 'Anya kana da hankali?'
Bin sa da kallo Maama ta ci gaba da yi ba tare ta ce komai ba. Cikin zuciyarta addu'a take yi,
Allah Ya sa ba ƙwaƙwalwar yaronta ce ta taɓu ba. Daneen fa? Cike da fargabar da ta zo ta yi
mata dirar mikiya lokaci guda ta ce
"Tareeq." Ta faɗa bayan ta sake kafe shi da idanunta. Saukar da kansa ƙasa ya yi, jikinsa a
matuƙar sanyaye. Bai yi tunanin samun cikas tun a wajen Maama ba, shi ya sa ma ya fara yi
mata maganar.
"Ka san me kake cewa kuwa? Daneen ce matar da kake nufi ka samu? Da gaske kake yi?" Ta
faɗa cike da tashin hankali. A nutse ya ɗan sauke ajiyar zuciya, yana jin har cikin ransa daɗin
tambayar da Maaman ta yi masa. Ko babu komai zai fayyace mata komai, dalilansa na son
auren Daneen ɗin. Ya ɗan ja numfashi kaɗan yana ajiyewa, kafin ya buɗe baki a nutse ya soma
faɗin
"Maama na yi tunani, na yi tunani har na gaji. A zamanin nan ban san kuma wace mace ce za
ta so ni tsakani da Allah ba. Na gwada ta waje, ta ba ni kunya. Kun gwada 'yar'uwa, ita ma ta ba
mu kunya. Toh a duk tunanin da na yi, na ga babu wadda ta dace in aura da ta wuce Daneen."
Daga haka ya ɗan dakata bayan ya sauke gajeren numfashi a hankali. Ba ya buƙatar jin wani
abu daga bakin Maama a kan maganar da ya yi, don haka ya ci gaba da faɗin
"Yarinyar nan ta ɗauki ƙodarta ta ba ni, ba tare da sanin waye ni ba. Ba tare da buƙatar komai
ba Maama. Ba kya tunanin ta cancanta na aure ta?"
"Idan kuma da wata manufar ta bayar fa?" Maama ta yi saurin katse shi da faɗin hakan, tun
kafin ya ida sauke maganar. Lumshe idanunsa ya yi a hankali, yana buɗewa lokaci guda.
"Ba haka ba ne Maama, hakan ne amma kuma har yanzu ba mu gane ta ba? Ko ma hakan ne
ƙoda fa ta ba ni Maama, idan dai har dukiyata take so, ba ma sai ta yi abin da Diyana ta yi ba,
wallahi zan iya mallaka mata. Wanda ba na tunanin ma hakan ce a ranta. Idan kuma za ta ƙi ni
ne saboda wani abu, ina ganin a yau ɗin nan zan fahimta. Don kuwa idan har kin ba ni dama,
toh zan je in same ta ne da maganar a yau ɗin nan. Ina so ranar da su Abeey suka shirya ɗaura
aurenmu da Jawahir, a ɗaura a ranar kar a fasa, idan dai kun amince." Ya ja wata ajiyar zuciya
yana lumshe idanunsa cike da gajiya da dogwayen maganar da yake ta yi, wanda za ka iya
fahimta ta cikin muryar tasa.
"Ko dai da ma tuntuni kana sonta ne?" Maama ta faɗa idanunta a kansa. Ɗan murmushin gefen
baki ya yi kafin ya ce
"Maama, a jiya na yanke shawarar auren ta, da ba a fasa aure na da Jawahir ba ba zan yi
wannan tunanin ba. Hakan na nufin akasin abin da kika faɗa kenan?" Ya ƙare maganar kamar
mai neman amsa, sai dai ba amsar yake so ba, don haka ya ɗora da faɗin
"Amma dai tabbas na amince zan aure ta, a matsayin mace mafi muhimmanci a rayuwata.
Wadda ta sadaukar da wani sashe na jikinta ta ba ni. Sannan kuma ta amince da aure na, duk
da yadda 'yar'uwata ta ƙi ni saboda ƙafata."
"Idan ta amince ke nan?" Maama ta yi masa wannan tambayar. Sai ya jinjina kai kawai a nutse.
Maama ta gyara zaman ta kana ta ce
"Ba mu san wace ce ita ba, ba mu san zuciyarta ba. Saboda haka sanar da ni, auren naku na
tsawon wane lokaci ne? Abin da kake nufi, za ka aure ta ne har zuwa lokacin da za ka warke ko
kuwa me kake nufi?" Cike da mamaki yake kallon Maaman, bai taɓa tunanin waɗannan
maganganun daga bakinta ba. Sai yake ganin kamar ba Maamansa ba. Anya kuwa ita ɗin ce?
Ya tambayi kansa. Sai dai abin da bai sani ba, tsantsar soyayyar ɗanta ce ke nema ta rufe mata
idanu.
"Ke nan hakan na nufin in aure ta saboda wata manufa Maama? Idan na yi hakan na yi wa
kaina adalci kuwa? Muna tare da Jawahir da Umma tun yarinta, amma ba mu taɓa sanin abin
da ke zuciyarsu ba sai yanzun. Kin ga ke nan rashin sanin wace ce Daneen ba komai ba ne.
Amma Maama ki faɗi duk abin da kike so na aikata, In Sha Allah ni mai biyayya ne a gare ki."
Shiru Maama ta yi na tsawon mintuna ba tare da ta ce komai ba. Bai ma yi tunanin za ta kuma
cewa komai ba, sai zuwa can ya ji ta soma faɗin
"Shi ke nan Tareeq, ina addu'a a kan duk abin da ya zama alkairi a gare ka ya dawwamar da
shi. Abin da ba shi da alkairi ya nesanta mini kai da shi. Duk da ban ji hakan ya kwanta mini ba,
amma kuma kai ya kwanta maka, na kuma san ba za ka zauna haka ba tare da neman zaɓin
Allah ba. Don haka na amince ɗari bisa ɗari, Allah Ya tabbatar da abin da ya fi alkairi." Lumshe
idanunsa ya yi yana jin nauyin da ke ƙirjinsa ya ɗan ragu, ya kai wajen minti ɗaya a hakan, kafin
ya buɗe idanunsa a kan Maama.
"Na gode sosai Maama, Allah Ya saka da alkairi." Ba ta iya amsawa ba, sai murmushi kawai da
ta yi a hankali.
... Da mamaki take kallon Hidayar da ta shigo ɗakin tana faɗin wai Maama na kiran ta. Ta tashi
zaune daga kwancen da take, idanunta sun sauya kala kamar wadda ta yi kuka.
"Maama na kiran ki." Hidaya ta sake maimaitawa ganin da ta yi kamar ba ta fahimci abin da
take faɗa ba. Jinjina kai ta yi tana faɗin
"Toh." Daga haka ta miƙe jiki a sanyaye ta bi bayan Hidayan.
"Ɗiyata, ki bi Hidaya, Yayanku na jiran ki za ku yi magana." Shi ne abin da Maama ta ce bayan
sun je inda take. Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Maama cike da mamaki. A kan laɓɓanta ta furta
'Yayanmu?' Har cikin zuciyarta tana jin wani banbarakwai, kuma da gaske wallahi ba ta gane
abin da take nufi ba. Ita ma Hidaya da ba ta san dalilin kiran Maaman ba, ya sanya cike da
mamaki ta ce
"Yah Tareeq?" Ta faɗa bayan ta buɗe manyan idanunta irin na Tareeq.
"Shi." Maama ta faɗa tana jinjina kai. Kiran sunansa da Hidaya ta yi, shi ne ya ƙara mata haske
a kan maganar Maaman. Nan take duk wani ragowar annurin fuskarta ya ɗauke ɗiff, take ta ji
wani irin bugun zuciya. Toh ke nan me ye dalilinsa na son ganin ta? Wace magana za su yi? Ita
kwata-kwata ba ta da buƙatar ganin sa, ballantana kuma har wata magana ta haɗa su.
"Maza Hidaya ki raka ta." Shi ne abin da Maama ta faɗa da ɗan murmushi a kan fuskarta.
Kamar wata saƙaguwa, haka ta soma tafiya, zuciyarta cunkushe da tunanunnuka kala-kala.
Gaba ɗaya kuma fuskarta a cunkushe. Dab suke da ƙarasowa inda yake, daga nesa tana iya
hangen sa daga kan kujerar da yake kai. Ba ka iya ganin komai na jikinsa sai baƙar
kwantacciyar sumar kansa, da ke ta sheƙi. 'Babu yadda za a yi ma ka ƙare rayuwarka da ƙafa,
mugu kawai. Allah ne Ya fara nuna maka iyakarka, sakayya ka fara gani tun kafin a je ko'ina. Ka
kuma jira hukuncin da alƙali zai yanke maka daga zarar na gama abin da ya kawo ni cikin gidan
nan' Abin da take raya wa a cikin zuciyarta ke nan, zuciyarta na mata wani irin zafi.
"Yah Tareeq ga ta in ji Maama, bari na koma." Hidaya ta faɗa tana murmushi. Ɗan gajeren
murmushi ya maida mata, kana ya jinjina mata hannu, alamar girmamawa. Ta yi dariya kafin ta
wuce daga wajen. Ci gaba da tsayawa ta yi a wajen kamar wata saƙaguwa. Ba tare da ta kalle
shi ba, don ba ta so ƙoƙarin wanzar da murmushi a kan fuskarta da take ta yi ya gagara. Bayan
wajen minti 2, don har ta gaji da tsayuwar, sannan ta jiyo muryarsa a nutse
"Ki zauna mana." Runtse idanunta ta yi tana ji kamar ta buɗe baki ta ce 'Ba zan zauna ba' Sai
kuma ta cije, ta daure ta ɗaga ƙafafunta da ƙyar ta nemi waje ta zauna. Ajiyar zuciya Tareeq ya
sauke yana tunanin ta inda zai fara. Idan