Showing 24001 words to 27000 words out of 81712 words

Chapter 9 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

soma nuna musu wani gida da ke ɗan nesa kaɗan da
inda suke kafin ya ce

"Kun ga wancan gidan, shi ne gidan Mai Unguwar nan Unguwar." Ba tare da damuwa da
bayanin da ya musu ba suka sake masa godiya cikin matuƙar farin ciki. Daga haka ya yi musu
sallama ya ƙara gaba, ya yin da suka nufi inda ya nuna musu.

Lokacin da suka isa, sun samu wani yaro tsaye a ƙofar gidan. Suka sanar da shi abin da ke tafe
da su na son ganin Mai gari.

"Ai kuwa dai Mai Unguwa ba ya nan, ya yi tafiya an yi masa mutuwa. Amma idan wani abun ne
ku faɗa sai na taimaka muku." Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, kafin suka maida duban
su kan yaron.

"Dama zuwa muka yi mu tambayi gidan wani Alhaji Abubakar, wanda ya yi aure kwanan nan, ya
auri wata Fatima." Tsayawa yaron ya yi yana kallan su irin kallan rainin hankalin nan. Sai dai
abin da ma ba su sani ba, cikin ransa tunani yake anya kansu ɗaya? Ya duk girman unguwar
nan amma su zo suna tambayar gidan Alhaji Abubakar wai wanda ya auri Fatima. Anya kuwa?
"Ba a nan garin kuke ba ne?" Girgiza kai suka yi. A wannan karon ma dai Ameer ne ya ce

"Daga ƙauyenmu muke. Muna neman su ne shi ya sa muka taho kai tsaye gidan Mai gari. Tun
da yadda muka sani duk wani gida da ke a ƙarƙashin ƙauyen Mai gari ya san masu gidan,lll shi
ya sa muka zo." Sai a lokacin yaron ya kaɗa kai, shi dama ya san a rina, ashe daga ƙauye
suke.

"Kun ga, nan fa ba ƙauye ba ne. Ba a ƙauyenku kuke ba. Kun ga ku rufa wa kanku asiri ku
koma inda kuka fito, tun da ba ku san inda waɗanda kuka fito nema suke ba. Wannan garin
yana da faɗi, ba kamar yadda ƙauyenku yake ba. Mu nan ba iya garin nan ba, duk wata unguwa
da ke cikin garin nan tana da Mai Unguwa, kuma Mai Unguwa ba shi da hurumin sanin mutanen
da ke cikin unguwarsa. Ka ga kenan ba za ku taɓa samun abin da kuke nema ba." Tun da ya
soma maganar suke kallan sa, har ya ƙare. Jiki a matuƙar sanyaye suka yi masa godiya. Bayan
ya yi musu sallama ya wuce cikin gida. Ba su taɓa tunanin haka abin yake ba. Sun ɗauka
tamkar yadda ƙauyensu yake nan ɗin ma haka yake. Shi ne dalilin da ya sa suka taho ba tare
da wani tunani ba.

***
"Sister ban san ta ina zan fara ba." Sultanah ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye. Gyara zama
Hidaya ta yi kafin ta ce

"Kin ga ki fara ko ta ina ne. Na ƙagu na ji me ke damun ki, tun da kuka dawo gida dama na
fahimci tabbas akwai abin da ke damun ki." Shiru Sultanah ta yi tana kallan Hidaya ba tare da ta
tanka ba. Hidaya ta kamo hannunta ta jinjina mata kai don ba ta ƙwarin gwuiwa.

"Ki sanar da ni." Ta faɗa har lokacin tana kallan ta. Ajiyar zuciya ta sauke, ta lumshe idanunta
kana ta buɗe bakinta ta ce a hankali

"Er'uwa ban san yadda za ki ɗauki zancen ba ke kanki, ballantana kuma har in yi wa Yah
Tareeq maganar. Amma tabbas na tsinci kaina dumu-dumu cikin ƙaunar Yah Abdoul." Ta ƙare
maganar tana jin yadda mikin da ke cikin zuciyarta ke famuwa. Hannunta Hidaya ta zare daga
cikin na Sultanah tana kallan ta sosai cike da matuƙar mamaki.
"Yah Abdoul kuma Sultanah?" Jinjina kai Sultanah ta yi a sanyaye, tana jin duk wani ƙwarin
gwuiwarta na zagwanyewa, ganin tilon er'uwarta da take saka rai a kanta tana neman watsa
mata ƙasa a ido.

"Kar ki zama mutum ta farko da za ki fara ganin laifi na Hidaya don Allah." Sultanah ta faɗa tana
kamo hannun Hidaya. Murmushi Hidaya ta yi don saboda kar ta zubar wa da er'uwar tata ɗan
ƙwarin gwuiwar da take da shi ta ce

"Ba watsa miki ƙasa a ido zan yi ba Sultanah. Kawai dai abin ne na ji shi tamkar a mafarki, na
kuma yi matuƙar mamaki. Amma In Sha Allah zan taya ki da addu'a idan rabon ki ne shi ɗin
Ubangiji Ya juyo miki da hankalinsa tun kafin ki sanar da shi. Don ban san ta yadda za mu sanar
wa da Yah Tareeq kina ƙaunar Abokinsa ba." Ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce
"Ni ma abin da nake tunani kenan Hidaya. Ina tsoron Yah Tareeq ya ji zancen nan, amma ban
san yadda zan yi ba. Abin yana damu na matuƙa a cikin zuciyata."

"Ki yi haƙuri Sisi, In Sha Allah komai zai zo da sauƙi."

"Ke! Maganar wa na ji kuna yi?" Maami da ta fito daga cikin ɗaki yanzun ta faɗa tana kallan su,
tana sanye cikin doguwar rigar atamfa. Tsananin kamar da suke da Sultanah shi ne zai bayyana
maka mahaifiyarta ce. Gaba ɗaya ɗaga kai suka yi suka kalle ta a tsarge. Da sauri Sultanah ta
shiga girgiza kai
"Babu komai Maami."

"Anya kuwa?" Ta sake faɗa tana kafe Sultanah da ido, kamar mai son gano gaskiyar abin da
take faɗa a kan fuskarta.

"Ehh Maami." Hidaya ta faɗa. Jinjina kai kawai Maamin ta yi, tana wuce wa kitchen ɗin da dama
abin da ya fito da ita kenan. Wata gauruwar ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce

"Na gode wa Allah." Ta faɗa tana dafe ƙirjinta. Bin ta da kallo Hidaya ta yi, tana mamakin yadda
ruɗewar Sultanahn ta yi yawa. Sai dai sanin halin Maamin ya sanya ta girgiza kai kawai.


***
Ɗaga kansa ya yi ya kalli wanda ya shigo office ɗin, ya amsa sallamar yana maida dubansa kan
takardun, ba tare da ya kalli abin da ke rubuce a cikin su ba ya haɗa su waje guda. Ƙarasawa
Abdoul ya yi ya nemi waje ya zauna shi ma hannunsa ɗauke da wasu takardun.

"Ga waɗannan takardun, duk dai cikin na Diyana ne." Abdoul ya faɗa yana miƙa masa takardun.
Ba tare da ya ce komai ba, ya karɓa ya haɗa su waje ɗaya. Ba dan ba dan ba, yanzun nan zai
saka wani ya ƙoma masa takardun, sai dai ko ma mene ne, ba ya so komai da ya shafe shi ya
fita waje. Don haka bayan ya gama haɗa su waje ɗaya, sai ya nemi waje ya killace su. Sai a
lokacin ya mayar da duban sa kan Abdoul ya ce

"Ya ake ciki?"

"Na tura maka komai ta E-mail naka, ka bincika bayanin komai na ciki." Jinjina kai Tareeq ya yi
kafin ya ja laptop ɗin da ke gabansa ya shiga dannawa cike da ƙware wa. Kyawawan idanunsa
na bin duk wani rubutu da ke bayyana a kan fuskar laptop ɗin, kai ka ce haddace kowacce
kalma yake yi, saboda yadda yake bin su cike da takatsantsan da son tabbatar da duk abin da
ya gani gaskiya ne.


***
Sosai dare ya sake tsalawa har lokacin suna tafiya, wani lokacin idan sun gaji su nemi waje su
zauna. Wani lokacin kuma su cigaba tafiya. Sai dai har zuwa lokacin ba su san takamaimai inda
za su je ba. Kuɗin da ya rage a hannunsu dududu bai fi na abincin da za su ci ba, ballantana su

yi tunanin komawa ƙauyensu, tun da dai wannan gari Allah Ya masa faɗin da sanin inda Innarsu
take kamar ba mai yiwuwa ba ne. I zuwa lokacin ban da kukan tsuntsaye, da motsin ƙalilan ɗin
ababen hawa babu abin da kake iya ji. Tsoro da fargaba tuni sun cika zuciyoyin Daneen da
Ameer. Musamman ma dai Daneen da ke cigaba da raba ido kamar munafuka.
"Adda wai tafiya za mu yi ta yi, ba za mu nemi inda za mu kwana ba." Ameer ya faɗa yana
dakatawa.

"Toh Ameer a ina za mu kwana? Ni na rasa ma mai zance wallahi."

"Kawai mu nemi wani wajen wallahi, kin ga fa titin babu kowa yanzu. Idan ya so gobe sai mu
nemi mafita." Cikin na'am da zancen Ameer ɗin Daneen ta gyara zaman jakarta, suka cigaba da
tafiya suna kalle-kalle, ko za su samu inda za su yar da haƙarƙarinsu. Lumshe idanu kawai
Daneen ke yi, saboda baccin da ke ta kawo mata hari, dalili kenan da ya sanya manyan
idanunta suka ɗan taasa kamar waɗanda suke ciwo.

"Bacci kike ji ko Adda?" Ameer ya faɗa cike da kulawa. Jinjina kai ta yi tana kai hannunta saitin
bakinta lokacin da ta yi hamma. Ta ɗan runtse idanunta tana sake buɗe su, daidai lokacin da ta
jiyo muryar Ameer na faɗin

"Laa Adda kin ga wani waje can wallahi ki zo mu je. Za mu iya kwana abin mu." Ya faɗa yana jin
yadda farin ciki ke mamaye ilahirin jikinsa. Inda yake nuna wa ta bi da kallo. Trader ce irin ta
mai shayi. Wadda da alama mai ita ba ya zama, ko kuma wani dalili ya hana shi zama yau ɗin.
Saboda yadda masu shayi kan kai wa dare, bai ci a ce har ya tashi i yanzu ba. Juya wa Daneen
ta yi ta kalli titin da motoci ke cigaba da wuce wa. Kafin ta dawo da dubanta kan trader. Kawai
sai ta ji jikinta ya sake yin sanyi. Tabbas da ta san ba za su haɗu da Innarsu ba, ba za ta taɓa
yarda su fito daga gida ba ko me Dada za ta musu. Ba ta taɓa tunanin akwai gari mai girman da
za a ce kowacce unguwa akwai nasu mai unguwar ba sai yanzu. Ba ta taɓa tunanin ƙaddarar
rayuwa kan iya jefo su har suna shirin kwana a kan titi ba. Shin me ya sa ta biye wa Ameer
suka fito daga ƙauyensu zuwa wannan garin mai girman da da alama ya ninka ƙauyensu sau
babu adadi. Shin me ya sa suka yi wannan gangancin na biyo Innarsu ba tare da sun san
takamaimai inda take ba.

"Ki zo mu ƙarasa." Ameer ya faɗa yana jan hannun Daneen, ganin da ya yi da alama ta yi nisa a
tunanin da ta tafi. Babu musu ta bi bayansa. Shi ya fara yin gaba, ya yin da ta bi bayansa. Har
ciki suka shiga kasancewar babu ƙofa. Sai dai wajen irin keɓantaccen nan ne. Don haka ko da
suna ciki babu wanda zai iya ganin su. Karɓar jakar hannunta Ameer ya yi, ya ajje ta gefe, ya
sanya hannunsa ya ɗakko rigunansa guda biyu ya shimfiɗa, kana ya kalli Daneen ya ce

"Adda taho ki kwanta." Ya yi maganar lokacin da yake gyara zaman jakarta don ta ji daɗin yin
pillow da ita. Kallan Ameer ɗin Daneen ta yi, ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba.
Ƙaunar Ameer a gare ta yawa gare ta, haka zalika ƙaunar ta gare shi tana da yawa. Don ji take
tamkar ta fi ƙaunarsa ma a kan yadda take ƙaunar kanta.

"Kai fa?" Ta tambaya tana kallan sa.

"Ki fara kwanciya, ni ma zan kwanta." Ƙarasawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike fall da
tunane-tunane. Sai dai abin da ya fi tsaya mata a rai, shi ne yadda za su samu kuɗin motar da
za ta maida su ƙauyensu. Sai a lokacin sannan Ameer ya nemi waje shi ma ya yi shimfiɗa ya
kwanta.
Sosai dare ya cigaba da tafiya, gari na sake yin shiru, ƙarar kukan tsuntsaye na daɗuwa. Sautin
ababen hawa na raguwa. Har zuwa lokacin da motsin su ya ɗauke kwata-kwata.

"Baba yau fa so nake na afa aji garau ɗin nan da yawa, don wallahi so nake na haura hazo na
yi ta shawagi ni ɗaya." Sautin da ke fita a daddaƙire, cikin irin muryar en shaye-shaye ta doki
dodon kunnen Daneen da baccin nata kwata-kwata bai yi nisa ba.

"Kar ka damu. Ni kaina yau ɗin nan so nake na yi mugun cajin da na daɗe ban yi ba." Wanda
suke tare ya faɗa. Lokacin da suke ƙara kusantar trader. Kai tsaye can suka nufa, suka nemi
waje suka zauna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka baje kayan harkarsu. A hankali Daneen ta tashi
zaune, tana jin yadda zuciyarta ke buga wa tamkar za ta faso ƙirjinta. Ta lalubi fuskar Ameer ta
taɓa, ta ji bacci yake. Sai ta ɗauke hannun nata tana koma wa ta zauna a kan shimfiɗarta,
bugun zuciyarta har wani sauti yake bayar wa 'dif, dif, dif' saboda tsananin tsoron da take ji.

"Kai.. Ni fa kamar motsi nake ji a cikin abar nan." Ɗaya daga cikin su ya faɗa yana ɗan
waigawa. Buɗe idanunta Daneen ta yi jin abin da ya faɗa, daidai lokacin da wasu hawaye suka
samu damar zubo wa a kan kuncinta lokaci guda.

"Kai ni ma fa kamar na ji. Waye a nan?" Ya faɗa a ɗan tsawace yana kallan cikin trader. Runtse
idanunta Daneen ta yi tana karanto duk wata addu'a da ta zo ranta, lokaci ɗaya tana haɗe
jikinta waje ɗaya, kanta ɗore a kan cinyarta, zuciyarta na wani irin harbawa, tsoron da tun da
uwarta ta haife ta ba ta taɓa jin sa ba na cigaba shigar ta.
"Ya kamata mu duba fa." Ɗayan ya faɗa yana miƙe wa. Shi ma miƙe wa ɗayan ya yi suka shiga
takawa zuwa inda su Daneen suke. I zuwa lokacin zuciyar Daneen bugawa ne kaɗai ya rage ba
ta yi ba. Kawai sai ta cigaba da addu'a tana miƙa wa Allah lamarinta kawai. Don ba ta san kuma
abin da ya kamata ta yi ba bayan wannan.
"Kai! Wallahi kamar mace nake hange a ciki fa. Kar dai a ce yau rabon farka wata yarinya ne ya
fito da mu." Wanda da alama ya fi ɗayan tantiranci ya faɗa yana dariya, lokaci ɗaya yana kallan
Daneen, hannunsa a kan haɓarsa yana shafawa.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 11

"Ke don tantiranci ma kawo kanki kika yi? Lallai abin zai bayar da citta." Ya ƙare lokacin da ya
ida ƙarasa tura kansa cikin wajen da su Daneen suke. Har kuma lokacin shu'uman idanunsa na
kanta, yana bin ta da wani kallo kamar tsohon maye. Cikin saurin da ba ta san tana da shi ba, ta
miƙe daidai lokacin da ta ida buɗe kumburarrun idanunta a kansa.
"Me ye haka kuma? Ina kike ƙoƙarin zuwa? Maada ƙaraso da gulafarka ciki mana." Shi dai
wanda ya soma magana tun farko ya sake faɗa. Kamar cikin mafarki Ameer ya soma jiyo
maganganu ƙasa-ƙasa. Babu shiri ya buɗe idanunsa da ke ɗauke da bacci. A kan Daneen ya
sauke su lokacin da take zube a kan ƙafafunta, kyawawan idanunta sharkaf hawaye. Tun da
Inna-wuro ta haife ta, ba ta taɓa tsintar kanta cikin tashin hankali irin wannan ba.

"Don girman Allah kar ku yi mana komai, ku bar mu mu tafi don Allah. Wallahi ba za mu sake
zuwa wajen nan ba, don Allah." Ta ƙare hannayenta biyu a haɗe waje guda. Dariya Maada ya
sheƙe da ita, yana kallan Dawa kafin ya ce

"Kaa ji me take cewa fa." Ya faɗa yana nuna Daneen da yatsan hannunsa. A tare suka sheƙe
da wata sabuwar dariyar suna kallon Daneen da har lokacin take zaune a kan gwuiwoyinta.

"Bari ka gani." Dawa ya faɗa yana soma sassauta ɗaurin tazugen wandon da ke jikinsa.

"Adda." Ameer ya faɗa yana miƙe wa lokacin da ya gama fahimtar maza har biyu sun shigo
cikin trader yana bacci. Ga kuma abubuwan da ya ji suna faɗa. Abin da ya tayar masa da
hankali kenan, ya kamo hannun Daneen ya riƙe gam cikin nasa, kafin ya maida dubansa kan su
ya ce
"Don Allah ku yi haƙuri." Da mamaki Dawa ya ɗaga ido ya kalli Ameer, don kwata-kwata bai lura
da wanzuwarsa cikin wajen ba sai da ya yi magana.

"Maada yi mini waje da wannan wawan, kai ma ka ɗan ba mu waje, idan na gama sai ka shigo
ka ɗora." Tun kafin ya ida maganar, Maada ya ƙarasa ya cafki hannun Ameer da niyyar fidda shi
daga cikin trader. Ganin da Ameer ya yi da gaske so suke su fitar shi, ya bar su kenan tare da
Addarsa? Hakan ne ya sanya shi sake riƙe hannun Daneen gam-gam cikin nasa, ita ma hakan
ce ta faru. Duk da yadda ilahirin jikinta ke ɓari, sai ka ce wadda zazzaɓi ke shirin rufe wa, ko
kuma ya rufe ɗin ma. Gaba ɗaya ta rikirkice, ta ruɗe, ta rasa abin da ya kamata ta yi. Sai dai har
lokacin ba ta dena ambatar sunan Allah cikin ranta ba. Ganin da Maada ya yi Ameer zai ɓata
masa lokaci ne ya sanya shi saka hannunsa gaba ɗaya ya soma ƙoƙarin saɓa shi a kafaɗa.

"Ka sake ni, ka sake ni malam. Ka sake ni." Shi ne abin da Ameer ke ta faɗa yana ciccije wa,
yana kuma sake riƙe hannun Daneen da ke cigaba da riƙe na shi. Duk inda Maada ya ja shi sai
Daneen ta bi shi, don haka kawai ya saɓe shi gaba ɗaya. Daidai lokacin da hannun Ameer da
na Daneen ya rabu, ta buɗe duk wata murya da take da ita ta yi wata ƙara, da tunani tare da
fatan wani ya ji ya zo ya taimaka musu.

"Ka sake ni, kar ku cutar mini da Addatah. Kar cutar mini da Addatah, kar ku taɓa mini ita. Ka
sake ni." Ameer ya cigaba da faɗa lokacin da yake kafaɗar mutumin, yana dukansa da duk wani
ƙarfi da ya san yana da shi. Amma ko bi ta kansa bai yi ba, sai cigaba da tafiya da ya yi da shi.

"Toh ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login