Showing 27001 words to 30000 words out of 81712 words
Chapter 10 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
sai ki haƙura ai mu sarara." Dawa ya faɗa yana kallan Daneen da ke kuka kamar ranta
zai fita. Tana kuma ƙoƙarin bin inda su Maada suka yi don fice wa daga wajen, amma Dawa ya
ƙi ba ta dama. Ganin da ya yi idan ya cigaba da biye mata za ta ɓata masa lokaci ya sanya shi
yin kanta gadan-gadan yana ƙarasa zame tazugen wandonsa gaba ɗaya. Wata ƙarar Daneen ta
saki cikin dashashshiyar muryarta. I zuwa lokacin ji take zuciyarta na dab da fito wa daga
ƙirjinta.
"Wallahi kika sake yi mini wannan ihun za ki ga yadda zan wulaƙantaki cikin daren nan." Dawa
ya faɗa a fusace, don tsoro yake ji kar garin ihun nan nata ta tona musu asiri tun kafin su shana.
Kwalar rigarsa da ya ji an kama babu zato babu tsammani, ita ce ta sanya shi dakatawa cike da
mamaki. Ya san babu yadda za a yi Maada ya yi masa haka, shi ya sa ya yi mamaki, sai ya
ɗaga kai ya kalli wanda ke riƙe da kwalar rigar tasa har lokacin. A cikin idanunsa ya sauke nasa
idanun. Cike da mamaki ya gyara tsayuwarsa
"Waye kai?" Ya faɗa cikin ƙarfin hali. Murmushin takaici Tareeq ya yi kafin bai ce komai ba ya ja
Dawa ta hanyar jan kwalar rigarsa zuwa waje.
"Malam me ye haka ne?" Ya faɗa cikin muryar nan tasa da ta jiƙu da shaye-shaye. Karo na
farko da ya buɗe baki, bayan ya kalli Abdoul da ke tsaye a wajen ya ce
"Ba shi ɗaya ba ne, ina iya jin sautin murya daga baya. Taimaka ka taso ƙeyar kowaye mu miƙa
su." Iya abin da ya faɗa kenan, har lokacin bai saki Dawa da ke cigaba da kallan sa ba. Amsa
wa Abdoul ya yi yana yin gaba. Daidai lokacin da Dawa ya soma faɗin
"Ka san wani abu Boss? Ka yi haƙuri ka rufa mana asiri kar ka miƙa mu wajen kwalawa. Wallahi
tallahi babu abin da na yi wa yarinyar mutane. Dama razanarwa ce kawai ehh ka gane ai. Ban
da haka babu wani abu. Ba na son haɗuwa ta da kwalawa ko kaɗan, muna da case da su
dama. Ka yi haƙuri ka mini afuwa ka bar ni na je, ba ma za ka sake gani na a arear nan ba." Ya
ƙarasa maganar daidai lokacin da Abdoul suka ƙaraso da su Maada da Ameer. A guje Ameer
ya ƙarasa ya rungume Daneen, a ruɗe yana faɗin
"Babu abin da ya same ki ko Adda? Babu abin da ya same ki?" Ya faɗa shi kansa jikinsa ko'ina
rawa yake. Rungume shi ta yi, ko ta ji sauƙin abin da take ji cikin zuciyarta. Ta shiga jinjina kai
har lokacin hawaye ba su dena sintiri a kan fuskarta ba.
"Taso mu tafi Adda, ba za mu sake kwana a wajen nan ba. Taso mu tafi." Ameer ya faɗa bayan
ya miƙe, yana riƙo hannunta. Ita ma miƙewar ta yi, tana saka hannunta ta goge gefen fuskarta.
"Ki dena kukan toh kin ji?" Ameer ya faɗa cike da kulawa. Jinjina kai ta yi tana jin zuciyarta na
sake karye wa. Sai dai ba ta bari hawayen sun zubo ba. Ta saka hannu ta ɗauki jakarta, shi ma
tasa ya ɗauka bayan ya tura kayansa ciki kafin suka fito. Suna tsaye su biyu, Tareeq na daga
baya, ya yin da Abdoul ke gaba. Da alama dama inda suke ya nufo. Ɗaga ido suka yi suka kalle
su kafin suka ɗauke.
"Ina za ku je?" Abdoul ya tambaya yana kallan su sosai don fahimtar su. Shiru suka yi kamar
masu tunani. Kafin Daneen ta gama tsara abin da za ta faɗa Ameer ya ce
"Gida."
"Kuna da gida mai ya kawo ku nan?" A wannan karon Tareeq ne ya yi maganar yana kallan su
sosai, duk da ba ya iya ganin takamaimai ya fuskarsu take, saboda ƙarancin hasken da aka
samu a wajen yanzu ba kamar ɗazu ba.
"Wuce wa muka zo yi. Mun je unguwa shi ne muka yi dare." Ameer ya sake faɗa. Cigaba da
kallan sa Tareeq kawai ya yi, sai dai bai ce komai ba.
"Ko ma ina ne kuka je ku dena kai wa dare haka, kuna ganin gari ya yi shiru haka, babu kowa.
Ga ɓata gari sun yi yawa. Yanzu ga shi kuna gani ba don Allah Ya taƙaita ba, da sai dai Allah Ya
tsare. Ku din ga kula, kai wa dare a waje ba na 'ya mace ba ne." Abdoul ya faɗa. Jinjina kai
kawai suke yi kamar wasu ƙadangaru, ita dai Daneen ko ɗaga ido ta kasa yi ballantana ta kalle
su. Sai a lokacin Tareeq ya gyara tsayuwarsa, ya kalli Abdoul ya ce
"Ka ɗauke su ka kai su gida please, na kira Nuhu yana jira na." Ya ƙare yana kallan Abdoul,
kafin a karo na barkatai ya sake kallan Ameer. Sai dai har lokacin bai sake ce masa komai ba,
suka yi sallama da Abdoul ya wuce.
"Ku wuce in kai ku gida." Abdoul ya faɗa yana kallan su. Babu musu suka yi gaba, kamar da
gasken suna da gida. Har inda motarsa take suka ƙarasa, ya buɗe musu suka shiga, kafin ya
tayar da motar. Shiru kawai Daneen da Ameer suka yi jin yadda motar ke tafiya tamkar ba a kan
titi ba. Ameer ya kalli gefen su, don sake tabbatar da da gaske a kan titi suke tafiya ba wani
wajen ba.
"Mai ya sa ba ka bari mun ce masa ba mu da gida ba, ka sani ko ya samar mana aikin da za mu
yi mu samu kuɗin da za mu koma ƙauyenmu." Daneen ta faɗa ƙasa-ƙasa tana kallan Ameer.
"A'ah.."
"Wacce unguwar ce?" Abdoul ya katse wa Ameer maganar da ya fara. Sai kuma idanunsu ya yi
tsilli-tsilli, suka kalli juna cikin rashin sanin abin yi.
"A kan titin nan ne ai." Daneen ta yi ƙundunbalar faɗin hakan jikinta a matuƙar sanyaye. Cigaba
da driving ɗin ya yi har zuwa lokacin da Daneen ta sake yin ƙarfin halin faɗin
"Ya isa haka, nan ne." Ta faɗa ƙirjinta na wani irin bugawa. Sauka ya yi daga kan titin, kafin ya
ce
"Bari na ƙarasar da ku." Ya faɗa yana shiga cikin layin da ta nuna masa. Daga ita har Ameer sai
da cikinsu ya ɗuri ruwa. Amma haka suka yi shiru, suka cigaba da rarraba ido kamar shege a
rabon gado.
"Ya isa haka, mun gode." Daneen ta faɗa cikin sanyin muryar nan tata da ta sake yin sanyi
matuƙa. Jinjina kai ya yi yana tsaida motar, suka sauka bayan sun yi masa godiya sosai.
"Babu komai." Ya faɗa yana murmushi.
"Allah Ya saka da alkhairi." Daneen ta sake faɗa a karo na barkatai. A wannan karon murmushi
kawai ya yi, ba tare da ya ce komai ba. Ya bi su da kallo lokacin da suka shige wani waje da ke
nuni da gidan da suka nufa nan suke ƙoƙarin shiga. Sai a lokacin ya tayar da motarsa ya bar
wajen.
Ajiyar zuciya Ameer ya sauke kafin ya ce
"Addaneen."
"Na'am." Ta faɗa tana kallan sa.
"Allah Ya taimake mu, amma yanzu ya za mu yi?" Ya tambaya a dame. Kallan inda suke ta yi na
tsawon sakanni, kafin ta ce
"Kawai mu zauna a nan zuwa gobe mu nemi aikin da za mu samu kuɗin koma wa gida. Ni ba
na son garin nan, kwata-kwata bai yi mini ba. Ba na son shi." Daneen ta ƙarasa maganar tana
lumshe kyawawan idanunta. Kallan jar fuskarta da ko'ina na jikinta ya yi jajir Ameer ya yi kana
ya ce
"Ni ma haka, ba na so. Ina so mu koma ƙauyenmu kafin Inna ta dawo. Na yi kewar ta, ina so in
gan ta." Ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba. Ta nemi waje ta tsuguna, tana
tunanin ta inda za su fara.
Cikin ikon Allah tun da suka zauna a wajen, babu wanda ya fito daga cikin gidan da suke zaune
a ƙofarsa, ko kuma wani ya zo wuce wa. Musamman da yake gidan ba a waje yake sosai ba, an
yi wasu en dabaru wajen kare shi. Hakan ne ya sa suka zauna a nutse, sai dai fa bacci babu shi
babu alamar sa. Suna nan zaune har aka kira sallahr Asuba. Ameer ne ya samo musu famfo
suka je suka yi alwala, suka dawo suka yi sallah a wajen, kafin suka cigaba da zama. Lokacin
da gari ya ida buɗe wa, sosai Daneen ta shiga buɗe idanunta tana kallan irin gidajen da ke
zagaye da su. Gidaje ne waɗanda ba ta taɓa tunanin akwai su a gaske ba. Gidaje ne
maka-maka, haɗaɗɗu na gani na faɗa, waɗanda ba ta taɓa ganin irin su ba.
"Kin ga wancan Adda." Ameer ya faɗa yana nuna mata wani gidan da shi ma ya gaji da haɗu
wa.
"Kuma gidan ne fa da gaske koh?" Ta tambayi Ameer a sakarce. Sai da juya ya kalli bayansu
kafin ya ce
"Toh mu gwada buga wannan mana sai mu tabbatar." Riƙo hannunsa ta yi da sauri tana girgiza
kai
"A'ah babu ruwa na wallahi."
"Ba sai mu ce aiki muke nema ba, idan za su ba mu kin ga ai sai mu yi mu samu kuɗi." Ya ƙare
maganar yana murmushi. Shiru Daneen ta yi kamar me tunanin wani abu, kafin ta sake ɗaga
kai ta kalli gidan. A sanyaye ta kalli Ameer ta jinjina kanta ta ce
"Toh mu gwada koh?" Ta sake tambayarsa. Sai ya jinjina kai yana murmushi.
"Kin ga idan ba su ɗauke mu ba ma ai dai mun ga gidan nasu mun yi musu wayo." Ya ƙare yana
dariya. Ita ma er ƙaramar dariyar ta yi tana sake kallan gidan a karo na biyu.
Sai da gari ya sake yin nisa sannan Daneen ta amince Ameer ya je ya ƙwanƙwasa gidan nan.
Shi ko tsoro ma ba ya ji, ita ya bar ta da faɗuwar gaba. Shiru babu alamar za a buɗe. Ya juya ya
kalli Daneen, kafin ya ce komai ta ce a hankali
"Ko dai ba gida ba ne?"
"A'ah fa gida ne ke kam." Ya ba ta amsa cike da tabbatarwa kamar da gasken ya sani. Be jira ta
sake cewa komai ba ya juya ya cigaba da ƙwanƙwasawa. Babu daɗe wa suka ji ana ƙoƙarin
buɗe ƙofar. Kallan juna suka yi shi da ita, Ameer ya yi murmushi kawai, ba tare da sun ce komai
ba suka maida duban su kan wadda ta zo ta buɗe ƙofar. Tun daga sama har ƙasa take kallan
su, kamar wadda ta ga baƙin halittu. Tana sanye cikin wata doguwar rigar da ba ta kai ƙasa ba.
Hannunta ɗore a kan gate ɗin tana cigaba da kallan su.
"Lafiya?" Ta faɗa kai tsaye tana jefa musu wani kallo. Kallan juna Daneen da Ameer suka sake
yi kafin Daneen ta buɗe baki a nutse ta ce
"Aiki muka zo nema, ko kuna da buƙata." Har za ta buɗe baki ta ce ba sa buƙata, sai kuma ta yi
shiru. Ta sake kallan Daneen a karo na barkatai kafin ta ce
"Ku shigo." Ta yi maganar tana ba su hanya. Babu musu suka sanya ƙafafunsu zuwa cikin ,
gaba ɗaya idanunsu a kan cikin gidan, suna kallan irin zubin da aka yi masa, tamkar ba a
duniya mutum yake ba. Gaba matar ta yi, ya yin da suka cigaba da bin bayanta.
"Ka sanar wa da Auntyyy ta yi baƙi." Ta faɗa lokacin da suke dab da wuce wani da ke zaune a
kan kujera yana danna waya.
"Auntyyy, kin yi baƙi." Wani gabjejen mutum da muryarsa ta fi kama da ta er budurwa ya faɗa
yana kallan matar da ke zaune a kan kujera. Sanye cikin doguwar rigar wani material, a ƙalla a
shekaru ta ba wa 50 baya. Fuskar nan ta yi ɗau ta yi jajir da farin bature. Sai dai wani sashe na
fuskarta duk ya yi baƙi-baƙi, musamman ma daga gefen idanunta. Kanta ɗaure da ture kaga
tsiya, ta baza uban ƙananun kitson da suka zuba har gadon bayanta. Kujerun da ke gefen ta
kuwa wasu manyan alhazai ne su biyu, da ke sanye cikin shadda ɗinkin babbar riga. Kowanne
da ka gan shi ka san kuɗi ya zauna masa babu wai.
"A shigar mini da su ɗaki, ka dai san ina tattauna wa ne mai muhimmanci. Zan ƙaraso daga
zarar na gama." Ta ƙare maganar tana wani karairaya kamar wata yarinya er shekara 20.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 12
Kallan juna Daneen da Ameer suka yi, lokacin da suke ƙoƙarin zama a ƙasan kujerar ɗakin da
aka shigar da su. Babu wanda ya ce da su ko uffan, haka aka fice aka bar su ciki su kaɗai. A
karo na barkatai suka sake kallan junansu kafin Ameer ya ce
"Adda kar fa mu je en yankan kai ne." Ya faɗa yana sakin jakar hannunsa idanunsa sun yi
tsilli-tsilli. Wani yawu da ya tsaya wa Daneen a maƙogwaro ta haɗiye tana sake bin ɗakin da
kallo ta ce a sanyaye
"Toh mu jira dai mu gani." Ta faɗa tana gyara zaman ta. Cikin ranta tana fatan Allah Ya sa ba
gidan en yankan kai suka kawo kansu ba.
Bayan wajen minti 30 suna zaune cikin ɗakin amma shiru babu wanda ya leƙo. Zuwa lokacin
sun fara ruɗewa.
"Ni dai wallahi ki tashi mu tafi, hmm uhmm." Ameer ya faɗa yana girgiza kai. Ita ma a ɓangaren
ta hakan take saƙa wa a ranta, su tashi su fice daga gidan, don da alama ma waɗanda suka
kawo su sun manta da rayuwarsu. Tun da ga shi tun da suka tafi ba su sake bi ta kansu ba.
Kafin wani a cikin su ya sake cewa komai, sai ga motsi an shigo cikin ɗakin. A tare suka ɗaga
ido suka kalli matar da ta shigo. Wannan matar ce ta ɗazun da ke zaune da wasu maza. Cikin
shigar ɗazun dai take, da alama ta gama da waɗancan ɗin shi ne tayo nan. Tun da ta shigo
idanunta ke kansu, har ta ƙarasa ta nemi waje ta zauna tana cigaba da bin su da kallo.
"Ina wuni?" Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Sai da ta ɗan yi jimm kafin ta ce
"Lafiya, ku ne baƙin nawa?" Ta faɗa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sake ganin gaba
ɗaya yanayin Daneen, zubin halittarta da komai na jikinta. Jinjina kai suka yi kafin Daneen ta ce
cikin siririyar muryarta
"Eh."
"Kuka ce aiki kuke nema?" Ta ƙare tana jin wani murmushi na taho mata.
"Eh." Daneen ta sake amsa wa a wannan karon ma. Jinjina kai Auntyy ta shiga yi kana ta ce
"Toh, kun samu." Cikin wani irin farin ciki suka ɗaga kai suka kalle ta. Ta sake jinjina kai sannan
ta ce
"Ƙwarai kuwa. Abin da nake buƙata kawai sirri, da kuma haɗin kai. Ba na son taurin kai ko
kaɗan. Yin sa kan sa na kori mutum na har abada. Idan dai har kun amince shi kenan, maganar
kuɗi kuma za ku iya samun sa duk ranar da kuka yi aiki. Ke aikin ki ya fi yawa, saboda haka da
ke zan fara." Ba tare da kawo komai a kan zancen ta ba Daneen ta ce
"In Sha Allah ba za ki yi kuka da mu ba."
"Haka nake so." Aunty ta faɗa, kafin ta ɗan ɗaga murya ta ce
"Shanawa zo ka shigar mini da yarinyar nan ciki." Shiru ne ya wanzu a wajen, zuwa can
wannan mutumin na ɗazu ya shigo cikin ɗakin. Cikin muryarsa ta mata ya ce
"Aunty ga ni. Ina yarinyar?" Ya faɗa yana jefa idanunsa da yake ta wani fari da su cikin ɗakin.
"Tashi ki bi shi, zai kai ki inda za ki yi wanka ki shirya." Kallan Ameer da shi ma ita yake kalla
Daneen ta yi, kafin ta maida duban ta kan Aunty a sukwane ta ce
"Wannan ƙanina ne." Ta faɗa tana nuna shi.
"Kar ki damu, zai zauna a ɓangaren maza ne. Ki je ki yi wanka ki shirya ke dai, shi ma zai je ya
gyara jikinsa." Jin abin da ta faɗa ya sanya ta ji daɗi. Ta miƙe tana ɗaukar jakarta. Da sauri
Aunty ta ce
"A'ah ajiye ta, akwai komai na buƙata a ciki." Babu musu ta ajiye ta, ta kalli Ameer ta ce
"Bari na je, ka je ka shirya kai ma ka ji? Sai mu fara aikin da wuri ka ga gidan na da girma." Ta
faɗa ƙasa-ƙasa. Jinjina kai Ameer ya yi. Daneen ta bi bayan mutumin nan. Tafiya suka soma yi,
suna tafiya yana karairaye karairayensa, shi a lallai dole mace. Ita dai sai taɓe ɗan mitsitsin
bakinta take saboda haushi da ya ba ta. A haka har suka ƙarasa wani ɗaki. Tsaya wa ya yi a
wajen, ya dakata ya yi knocking na ƙofar, zuwa can aka zo aka buɗe. Wata dattijuwar mata ce
da a ƙalla za ta yi shekaru 40 ko da wani abun. Tana sanye cikin riga da zani da ɗan'kwali irin
na da ɗin nan.
"Toh ke ga baƙuwa nan kin samu. Na san Aunty ta gama miki bayani." Jinjina kai matar ta yi
kafin ta kalli Daneen ta ce
"Shigo." Haka nan kawai ta ji ƙirjinta ya buga, har sai da ta kira sunan Allah, kafin ta soma taka
wa. Ta saka ƙafarta cikin ɗakin. Daga haka shanawa ya juya, ya yin da matar ta rufe ƙofar
bayan Daneen ta shige cikin ɗakin. Kallan ta matar ta shiga