Showing 21001 words to 24000 words out of 81712 words
Chapter 8 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
ba. Ban san wannan tafiyar za ta taso ba, ina mai sake
ba ki haƙuri." Kalmar haƙurin da yake ta maimaitawa tabbas ta yi matuƙar tasiri a zuciyarta, sai
dai duk da haka, ba ta dena jin bugun zuciyar ba. Ta yi ƙarfin halin buɗe baki da ƙyar ta ce
"Babu komai, Allah Ya sa haka ne mafi alkhairi." Sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce
"Ameen, na gode."
Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintuna, zuwa can Alhaji Abubakar ya ce
"Bari na jira ki sai ki shirya koh? Kafin nan mun yi magana da Baffa." Da kai ta amsa masa
maganar, ba ta sake cewa komai ba ta faɗa cikin gidan tana tunanin ta inda za ta fara sanar wa
da 'ya'yanta tafiyar sati da za ta yi ta bar su cikin gidan. Kamar yadda ta umarci Ameer kuwa,
yanzu haka tare da Daneen ta same su suna shirya kayansu cikin jaka. Ya yin da ragowar da ba
za su ɗauka ba suna ninkewa suna mayar da su wajen kayansu. Ƙarasawa cikin ɗakin ta yi
jikinta a matuƙar sanyaye ta nemi waje ta zauna tana cigaba da kallan su.
"Inna mun gana haɗawa fa." Ameer ya faɗa yana murmushi. Ji yake tamkar ya yi ta tsalle
saboda farin ciki, don zai iya cewa kaff cikin su ya fi su farin ciki da barin ƙauyen nan da za su
yi. Murmushin yaƙe Inna-wuro ta yi kafin ta ce
"Ku zo ku zauna ku ji." Kusan a tare Ameer da Daneen suka ɗaga ido suka kalli Innar tasu jin
yadda maganarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan ɗin ba sabon abu ba ne a wajen su,
fahimtar halin da ɗaya daga cikin su ke ciki ko da ta magana ne kuwa, ba tare da ya sanar da
su ba. Ajiye Hijab ɗin da ke hannunta Daneen ta yi, ta ƙarasa gaban Innar tasu da sauri ta
zauna, ya yin da Ameer ma ya zauna a gefen ta, gaba ɗayan su jiki a sanyaye.
"Ku buɗe kunne da kyau ku saurare ni, ba don na so ba sai don haka Allah Ya tsara, zan bar ku
cikin gidan nan na tsawon sati guda. Kai tsaye nan za mu dawo mu ɗauke ku mu wuce da ku
inda za mu zauna. Kar ku damu, kar ku ɗaga hankalinku." Ta ƙare maganar a nutse, duk da ita
ma ba ta da nutsuwar zuciya, sai don kawai ta ba wa 'ya'yan nata ƙwarin gwuiwa.
"Inna.." Shi ne abin da Ameer ya yi ƙarfin halin faɗi yana cigaba da kallan Innar. Wata ƙwalla da
ta ji ta taho mata ita ce ta sanya ta saurin saukar da kanta ƙasa, wajen sakanni 30 kafin ta ɗago
tana kallan su su duka. Ta kamo hannayensu ta sanya cikin nata.
"Ba mu taɓa rabuwa ba tun da muke, sai ga shi yau ɗin za mu rabu na tsahon kwana bakwai.
Ina so na yi amfani da wannan damar wajen neman alfarmar yin haƙuri da zama da Dada cikin
gidan nan bayan ba na cikinsa. Akwai kuɗi a cikin jakata, duk abin da kuke buƙata ku yi amfani
da shi. Daneen ga Ameer nan, ki kula mini da shi har na dawo. Ameer ga Daneen nan ka kula
mini da ita har na dawo. Allah Ya yi muku albarka, Ya albarkaci rayuwarku, Ya raya mini ku." I
zuwa lokacin gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyin da suka kasa amsa addu'ar Innar. Kowanne da abin
da yake saƙa wa a cikin ransa.
"Kar ku mini kuka." Inna ta faɗa tana girgiza kai lokaci ɗaya tana kallan su duk da ita ma nata
idanun cike suke da ƙwalla.
"Toh maza ki fito Hajjaju ta ɗaka, mijinki na jiran ki. Ko kuwa ƙaramar yarinya ce ke da sai an zo
an rarrashe ki kafin ki fito." Ta jiyo muryar Dada na faɗin hakan. Hannu ta kai ta goge fuskarta
da zuwa lokacin hawaye sun fara sauka, ta yi saurin ɗauke su don kar ta sake karyar wa da
'ya'yanta zuciya.
"Toh gani nan." Ta ɗaga murya wajen faɗar hakan, don Dadar ta ji. A hankali ta miƙe har lokacin
hannunta na cikin na 'ya'yanta da suka kasa furta komai.
"Ku yi haƙuri kar da ku karya mini zuciya. Ba na tafi kenan ba, nan da sati ɗaya zan dawo in
ɗauke ku da yardar Allah."
"Inna don Allah kar ki tafi." Daneen ta faɗa da muryarta da ke rawa, lokaci ɗaya tana rungume
Innar. Kukan da Inna ta ji ta fashe da shi shi ne ya sanya ta runtse idanunta, ta saka hannu ta ja
Ameer jikinta, ta haɗa su ta rungume waje ɗaya. Sun kai wajen minti biyu a haka kafin suka saki
juna. Inna-wuro ta saka hannu ta ɗauki jakar kayanta. Bin bayanta suka yi har zuwa tsakar
gidan. Kafin su kai ga fita daga cikin gidan wata da take kusa da Dada ta ce
"Wai dama ba a nan za ta zauna ba."
"A'ah nan cikin Kano ne fa za ta zauna." In ji Dada tana gyara zama lokacin da Inna-wuro ta
nemi waje ta zauna. Ba wata addu'a daga Dadar har Baffan suka yi mata ba, haka dai ta ja
ƙafafunta suka fice daga gidan. A sanyaye su Daneen suka gaishe da Alhaji Abubakar, ya amsa
cikin sakin fuska kafin ya karɓi jakar hannun Inna-wuro ya saka cikin mota.
"A kula, Allah Ya tsare mini ku, sai na dawo." Inna ta faɗa tana kallan su.
"Allah Ya tsare Inna." Suka haɗa baki wajen faɗar hakan. Ta lumshe idanunta tana juya wa a
hankali ta soma tafiya zuwa wajen motar. Dab da za ta ƙarasa, ta sake juya wa ta kalli 'ya'yan
nata. Sai ta juya da sauri ta shige cikin motar, saboda yadda ta ji a yanzun ba za ta iya jurewa
ba, zuciyarta ta gama karyewa. Ƙarasawa Alhaji Abubakar ya yi ya shiga motar, bayan wasu
sakanni ya tashi motar. Ƙasa da kanta Inna-wuro ta yi don tabbas idan ta cigaba da kallan
'ya'yanta za ta iya bijire wa umarnin mijinta ta ƙi binsa ta cigaba da zama da su. Don haka har
ya soma tafiya ba ta ɗaga kanta ba. Daneen da Ameer, suka cigaba da bin motar da kallo, har
zuwa lokacin da ta ɓace wa ganin su. Hannun Ameer Daneen ta kama ta riƙe sosai tana runtse
idanunta. Wani irin bugu zuciyarta take yi. A hankali kuma sai ta soma takawa zuwa cikin gidan,
ya yin da Ameer ya rufa mata baya.
Bin su da kallo Dada ta yi lokacin da ta ga shigowar su cikin gidan. Ta taɓe baki tana jinjina
kanta. Ita dama burinta bai wuce a bar mata 'ya'yan Inna-wuro a wajenta ba, ko babu komai ta
san za su dinga zuwa a kai a kai ana ajiye mata kuɗi da sauran su. Amma idan suka tafi da
'ya'yan suka manta da ita da wa ta ɓare kenan? Bar mata su da aka yi yana nufin samun wata
mafitar kafin su dawo, wadda za ta hana su tafiya da su duk da sun yi niyya.
Kai tsaye ɗakinsu suka nufa suka yi shiru kowa da abin da yake saƙa wa. Ranar haka suka
wuni kamar masu zaman makoki, babu wanda ke cewa da ɗan'uwansa ko uffan ne.
Washegari jiki a sanyaye duk suka farka, sai suke jin su wasu daban, ba su taɓa farkawa ba su
ga Innarsu ba sai a yau ɗin. Ba su taɓa rabuwa da Innarsu ba sai a wannan karon. Suna ta farin
ciki abin farin ciki ya same su, ashe ba su sani ba kafin samuwar farin cikin sai sun soma
rayuwar kaɗaici. Da yake ranar babu makaranta ya sanya suna gida, tun safe bayan sun fito
daga ɗaki ba su koma ba. Shi Ameer yana can aiken da Dada ke ta masa, da kuma wasu
ayyukan. Ya yin da Daneen ke yi wa Dada girki da sauran ayyukan cikin gida.
.. "Me kake yi haka ne Ameer?" Daneen ta faɗa tana kallan Ameer da ke cusa kayan sakawarsa
cikin jakar islamiyya. Sai da ya ƙarasa cusa wadda ya ɗakko sannan ya ɗaga ido ya kalle ta ya
ce
"Inna zan bi." Da mamaki matuƙa Daneen ke kallansa idanunta a waje. Cike da mamakin dai ta
ce
"Inna kuma Ameer? Ka san inda ta je ne?" Jinjina kai ya yi kana ya ce
"Ehh, jiya na ji Dada tana faɗa wa ƙawarta wai sunan garin Kano. Ko ban san gidan ba, na san
muna zuwa muka tambayi Mai gari gidan Alhaji Abubakar ya sani. Tunda kin ga mu ma a garin
nan gidan waye Mai gari bai sani ba?"
"Ni yi mini shiru dallah.. Tashi ka tafi toh." Daneen ta faɗa tana shirin miƙe wa. Maida ta ya yi ta
zauna ta hanyar riƙo hannunta. Ya shiga girgiza kai yana faɗin
"Kar ki mini haka Addata. Idan har ke ba ki amince mini ba waye zai amince mini? Don Allah ki
duba abin da na faɗa ki bari mu tafi. Ni ba zan iya cigaba da zama da Dada ba wallahi. Ko ba ki
amince na bar garin nan ba, toh zan bar cikin gidan nan in tafi ko ma ina ne."
"Wai Ameer ba ka da hankali?" Daneen ta faɗa tana kallan sa a tsorace.
"Toh ki yarda da abin da na faɗa."
"Ba zan yarda ba." Ta faɗa tana jefa masa harara.
"Don Allah Addaneen tawa ni kaɗai. Don Allah.." Ya ƙare a marairaice. Sai a lokacin sannan ta
sake juyawa ta kalle shi sosai ta ce a hankali kamar me raɗa.
"Ameer wai da gaske kake?" Jinjina kai ya shiga yi lokaci ɗaya yana furta
"Wallahi da gaske Adda. Ji nake kamar ana azalzalata da in bar gidan nan, ki taimaka ki amince
mu bi Inna garin da ta je." Shiru Daneen ta yi na tsawon wasu mintuna. Rashin yawan tazarar
shekarun da ke tsakaninta da Ameer ya sanya wayonsu kusan ɗaya ne. Wani lokacin ma har ya
fita wayo. Don idan ya yi wani abun sai ka ɗauka shi ne babba, sai kuma wani lokacin ko ba a
faɗa maka ba za ka fahimci Daneen ce babba.
"Amma idan Inna ta yi faɗa fa? Tun da ka ga ta ce nan da sati ɗaya za ta zo ta ɗauke mu."
"Ba za ta yi ba Adda, ba za ta yi ba. Shi ma kuma sabon Abban ai yana da mutunci. Sai mu ce
zuwa muka yi mu gaishe su." Shiru Daneen ta yi na tsawon wasu mintuna kafin ta shiga jinjina
kai ta ce
"Toh." Ta ƙare tana ajje numfashi.
"Yawwah Addata." Ameer ya faɗa yana murmushi. Cikin zuciyarsa yana jin wani shahararren
farin ciki na kama shi. Da gaske har cikin ransa ji yake tamkar ana azalzalarsa da barin gidan.
Kuma da gaske yadda ya faɗa ɗin tabbas da Addar tasa ba ta amince da bin Innarsu ba, yau ba
zai kwana cikin gida ɗaya da Dada ba. Shi da kansa ya tashi ya ɗauki jakar islamiyyar Daneen
ya shiga saka mata kayan sakawarta ciki. Ya samu dama da yawa kuwa sun shiga saboda
yadda yake cusa su don ma kar a gane meye a ciki. Sai da suka gama tsaff, kafin ya miƙe ya ce
"Adda riƙe jakarki mu tafi." Babu musu ta karɓa ta rataya ta cikin hijabin makarantar islamiyya
da ta saka. Shi ma ya rataya tasa jakar saman uniform ɗin islamiyyar. Ba tare da tunanin komai
ba suka fito daga cikin ɗakin. Dada na zaune tana jin Radio a kan tabarma, ya yin da Baffa ke
mata fifita yana daga gefen ta.
"Dada, Baffa mun tafi." Daneen ta faɗa, don tana da tabbacin idan ba ta faɗa ba Ameer ba zai
faɗa ba. Ɗaga idanunta Dada ta yi ta kalle su, Radion da take ji ya sa ba ta iya tantance iya
Daneen ce kaɗai ta mata magana ba. Tsaki ta ja kafin ta soma faɗin
"Ni fa makarantar ma na gaji da ganin ku kuna zuwan ta wallahi. Haba." Ta ƙare yanzu kuma
tana sakin ƙwafa.
"Kin ga ƙyale su su tafi, kar shirin nan ya wuce ki. Idan kin gama ji in ya so duk hukuncin da za
ki yanke sai ki yanke kafin su dawo." Baffa da ke cigaba da firfitarsa ya faɗa yana kallan ta.
Shiru ta yi na tsawon wasu sakanni kafin cikin na'am da zancen nasa ta ce
"Haka ne kuma.. Ku tashi ku tafi." Tun kafin ta ida faɗa har Ameer ya miƙe, kafin ka ce mene
wannan ya fice daga cikin gidan. Ta ja ƙwafa tana cije gefen leɓenta, a ranta tana saƙa yadda
za ta yi maganin yaron cikin ƙanƙanin lokaci.
"Kin gani ko Adda? Kin ga abin da nake faɗa miki koh? Kin ji fa wai makarantar ma hana mu
zuwa za ta yi, toh me ya sa?" Ya ƙare tambayar yana kallan Daneen da ta sauke ajiyar zuciya
saboda ganin da ta yi Dada ba ta gane kaya ne a cikin jakunkunansu ba. Jinjina kai ta yi ba tare
da ta ce komai ba. Cigaba da tafiya suka yi, sai da suka yi tafiya mai nisa kafin suka isa wani
titi. A nan suka samu motar da za ta fitar da su inda za su samu motar da za ta kai su Kano. Da
kuɗin da Inna ta ba su suka yi amfani wajen biyan mai motar kuɗinsa lokacin da ya sauke su.
Sai suka sake tarar wata motar wadda ita ma dai ba Kanon direct za ta wuce ba. Don haka
bayan ta sauke su a nan suka yi tambaya suka samu motar da za ta wuce Kano. Cikin matuƙar
farin ciki suka hau motar. Motar da ba ta kai ga cika ba, don haka aka tsaya ana jiran wasu
passengers ɗin kafin motar ta tashi.
"Adda yunwa nake ji." Ameer ya faɗa yana ɓata rai. Hannu ta saka ta karɓi jakar hannunsa, ta
ce tana kallan waje
"Ka ga wata mai siyar da awara can, je ka siya ka ci." Ta faɗa tana zaro kuɗi a jakar Inna ta
miƙa masa. Hannu ya saka ya karɓa yana sauka daga motar, kai tsaye wajen mai awarar ya
wuce. Ta bi shi da kallo tana lumshe idanunta, daidai lokacin da bugun da numfashinta ke yi ya
cigaba da fita a gurguje kamar wadda ta yi tsere. Bayan wasu mintuna sai ga shi ya dawo. Yana
dawowa kuma, motar na gama cika. Don haka bai daɗe da zama ba, motar ta tashi aka soma
tafiya.
.. "Maza maza mun zo tasha. Ina na Kano su sauko." Abin da kwandastan motar ke ta faɗa
kenan lokacin da yake a waje, hannunsa ɗore a kan motar yana ɗan bubbugawa. Kallan juna
Daneen da Ameer suka yi, kafin a sukwane suka sakko daga cikin motar. Dama tuni sun ba wa
kwandastan kuɗinsa, don haka sai suka soma taka wa suna rarraba idanunsu a inda suke.
Daneen ta haɗiye wani busshashshen yawu da ya haɗu cikin bakinta da ƙyar zuwa
maƙogwaronta. Ta kalli dogon titin da suke kai, wanda kwata-kwata bai yi mata kama da titin
ƙauyen su ba. Ita kwata-kwata ma ba ta ganin ƙarshensa, kai ba ma ƙarshensa ba, wajaje take
gani duk inda ta juya, maimakon ta gan su a haɗe kamar yadda nasu gidajen suke. Sai dai
kwata-kwata ma ita ba ta hangi wani gida ba, kenan ina ne gidan mai gari? Shi dai Ameer ban
da sake rungume jakarsa babu abin da yake yi, lokaci ɗaya kuma yana bin garin da duhu ke
sake mamaye shi da kallo. A karo na barkatai suka sake kallan juna, idanun kowannensu ya yi
tsilli-tsilli, ya raina fata, gaba ɗayansu kuma da abin da suke saƙa wa a cikin ransu. Sai dai abin
da ya fi yawo a zuciyar kowannen su shi ne 'Shin ina ne nan ɗin suka kawo kansu?'
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 10
Idanunta da suka yi rau-rau ta ɗaga ta kalli Ameer ta ce jikinta a matuƙar sanyaye
"Na shiga uku Ameer, ina ne nan?" Cikin rashin sanin abin yi Ameer ya girgiza kai kafin ya ce
"Ni ma ban sani ba Adda." Ya faɗa yana sake maida kansa inda suke. Duk da yadda take jin
tsoro na sake shigar ta, hakan bai hana ta kallan wani mutum da ke gefen su ba. Cikin sanyin
murya ta gaida shi, ya amsa yana kallan yanayin shigarta.
"Don Allah gidan Mai gari muke nema." Ta yi ƙundunbalar faɗin hakan, cike da fatan su samu
abin da suke so.
"Toh ikon Allah! Mai gari ko Mai Unguwa?" Ya tambaya yana kallan ta. Shiru Daneen ta yi tana
tunanin abin da ya kamata ta ce, sai dai kafin ta ida tunanin ta tsinto muryar Ameer ya ce
"Eh shi." Ya yi maganar yana jinjina kai kamar ƙadangare, lokaci ɗaya kuma yana sake
rungume jakarsa a hammata.
"Toh da yake dai babu nisa daga nan, ku biyo ni na nuna muku, idan ya so sai na wuce inda zan
je." Cikin matuƙar farin ciki suka shiga yi masa godiya, a ransu duka ji suke tamkar su taka
rawa. Bin bayan nasa kuwa suka yi kamar yadda ya faɗa, suka soma tafiya. Duk inda suka gifta
sai sun bi wajen da kallo.
"Ai dama na faɗa miki Adda, yanzu ba ga shi ba har mun samu gidan." Ameer ya faɗa farin cikin
da yake ji na bayyana a kan fuskarsa da kuma muryarsa. Ita ma murmushin ta yi kana ta ce
"Ai kuwa dai. Allah har na ƙagu na yi ido biyu da Innarmu." Ta yi maganar daidai lokacin da
mutumin ya juyo ya kalle su, sai da ya