Showing 6001 words to 9000 words out of 81712 words

Chapter 3 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

aura za ta haihu, 'ya'ya nawa zan tara kenan? Ni ba don ki haihu na auro ki ba.
Na auro ki ne don ina son zama da ke ke kaɗai, amma saboda ƙauyanci da gidadanci cikin
watannin da za a ƙirga su a hannu har kin yi ciki biyu? Ba zan iya ba. Ki je na sake ki saki uku,
na kuma yafe abin da kika haifa da kuma wanda za ki haifa nan gaba. Ki je ki riƙe kayanki ba na
so, ke kar ma ki taɓa tunanin suna da uba. Kar kuma ki taɓa nuna musu suna da uba. Ki manta
cewar ba ke kaɗai kika haife su ba, na yafe har gaban abada. Ke ke kaɗai kika haife su.
Saboda haka ke da kika haifa ke kaɗai suke da. Na bar miki su halak malak."

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 03

__ Idanunta a runtse suke tun daga lokacin da ya fara magana har ya kai ƙarshe. Duk yadda
ilahirin jikinta ke rawa hakan be sanya ta yi yunƙurin nema wa kanta waje ta zauna ba. Kalaman
Alhaji Baita ne kawai ke cigaba da yi mata amsa-kuwwa cikin kunnenta. A hankali wasu hawaye
masu ɗumi suka gangaro daga cikin Idanunta da har lokacin suke a rufe. Cikin ƙanƙanin lokaci
bugun zuciyarta ya ƙaru fiye da farkon lokacin da ya fara magana.

"Ki bar wajen nan." Ya faɗa a zafafe yana nuna mata hanya, ba tare da ya kalle ta ba. Don ba
ya so ya kalle ta ɗin ka da wani abu ya ɗarsu a ransa, har ya saka ya yi nadamar abin da ya
aikata. Ya riga ya tabbatar wa kansa daga yau Fatiman ba tasa ba ce, komai nata ya zama ba
nasa ba. Saboda haka kamar yadda ya yanke alaƙarsa da ita har abada ba ya so ya sake
kallon fuskarta, jikinta ko kuma ma duk wani abu da ya dangance ta. Maganar da ya yi ita ce ta
sake tuna mata da zafafan kalaman da suka yi nasarar jefa zuciyarta cikin wani irin yanayi mara
misaltuwa. A hankali ta ɗaga ƙafafunta da suka mata nauyi ta soma takawa don barin wajen,
daidai lokacin da ta buɗe idanunta da suka rine suka yi jajir, hawaye sun cika sun tumbatsa
cikin idanun, wanda hakan ya sanya take ganin dishi-dishi. Bugu da ƙari kuma maganganun
nasa da suka sanya jinta da ganinta ya ɗauke na wucin gadi. Babu abin da ke cigaba da zama
daram a ƙwaƙwalwarta, suka fi kuma kowaɗanne kalmomi maimaita kan su sai

"Ke da kika haife su ke kaɗai suke da. Na bar miki su halak malak."

Da ƙyar ta iya kai kanta ɗaki, sai a lokacin zuciyarta da ke cunkushe, ta ba ta damar fashewa da
wani irin kuka me cin rai. Kukan da ke fito wa tun daga ƙasan zuciyarta, me zafi wanda ke
taimakawa wajen rage raɗaɗin da zuciyarta ke ciki. Ta kwashe fiye da rabin awa tana kukan, ta
kasa hana kanta dena wa. Ba sakin da Alhaji Baita ya yi mata ne ya fi damunta ba, face yadda

ya nuna ba ya son abin da ta haifa, da wanda za ta haifa nan gaba, wanda ke cikinta a yanzun.
Shin ya rayuwar 'ya'yanta za ta kasance idan suka taso suka gane waye mahaifinsu? Wane hali
za su tsinci kansu duk lokacin da suka ji labarin mahaifinsu ba ya son su tun samun cikinsu har
haihuwarsu? Har ma an saki mahaifiyarsu ne saboda haihuwarsu? Haihuwar da wasu suke
ƙarar da dukiyarsu da duk abin da suka mallaka don su samu. Haihuwar da a kanta wasu suke
fitowa daga gidajensu. Lallai Allah mai mabambantan halittu, masu kuma mabambantan
halayyya. Wani numfashi ta ja tana runtse idanunta, kafin ta miƙe ta ƙarasa inda Daneen take,
ta ɗauke ta ta saɓa a baya. Hijab kawai ta ɗauka, ta ɗauki kuɗin da ta san ze kai ta gida, bayan
nan ba ta taɓa komai da ke cikin gidan ba. Don kuwa ba ta buƙatar komai da ya dangance shi
kuma. Kai tsaye ficewa ta yi daga ɗakin. Dab da za ta gifta inda suke zaune, Alhaji Baita ya
saka hannu cikin aljihunsa ya fito da kuɗi, ya jefa mata ƙasan ƙafarta daidai lokacin da ya ce

"Ki yi kuɗin mota."

Ba ta yi niyyar tankawa ba, sai dai yadda zuciyarta ke bugawa, tana ƙara zafafa da wannan cin
mutuncin da ya mata ya sa ta ji ba za ta iya ba. Shirun da za ta yi tamkar nuni ne da ta ji
haushin fitar ta daga gidan, wanda ta san tabbas hakan ze yi masa daɗi, ba ma shi kaɗai ba har
Hajiya Amina. Sai dai tana dakatawa da niyyar juyawa ta yi masa magana, zuciyarta ta
ƙeƙashe, tarin takaici ya cika zuciyarta. Ba ta jin tun da take a rayuwarta akwai fuskar da ba ta
ƙaunar sake gani kamar ta Alhaji Baita. Kamar yadda ya ce babu shi babu ita, babu kuma shi
babu 'ya'yansa, toh har abada sun rabu ɗin kenan. Daga haka ta gewaye kuɗin ta fice daga
ɗakin ba tare da ta sake ko da waiwayowa ba ne.

... A ƙofar gidansu ta tsaya tana kallan ƙofar gidan kamar wadda ta fara ganinsa yau. Ta yi shiru
tana cigaba da kalla zuciyarta na harbawa. Tunanin abin da ke cikin gidan take, tunanin da
wane ido za ta kalle su ta sanar da su Alhaji Baita ya sake ta take. Sai dai ko ma mene ne zai
biyo baya ta shirya karɓarsa. Tun da ba ta da inda ya wuce mata nan ɗin. Tuna hakan ya sanya
ta ɗaga ƙafafunta ta jefa cikin gidan nasu, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga gidan.

"A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim." Shi ne abin da Dada ta ambata ƙirjinta na bugawa tana
kallan Inna-wuro. Dakatawa Inna-wuro ta yi, jin da ta yi tun a lokacin gaba ɗaya ƙwarin gwuiwar
da ta ji kafin ta shigo gidan yana rugujewa yana yin nasa wajen. Tun kafin ta ƙara taku ɗaya
Dada ta matso tana faɗin
"Me ya dawo da ke gida kuma? Me kika zo yi mana a gida?" Buɗe baki ta yi jiki a matuƙar
sanyaye ta ce

"Dada.."

"Kar ki sake ki ƙara kiran sunana. Daga ganin idanunki akwai abin da kika shuka, faɗa mini me
ya faru. Me ya dawo da ke gida?" Girgiza kanta ta soma yi, daidai lokacin da wasu sabbin
hawayen suka sake cika idanunta taff, ta buɗe baki kamar me koyon magana ta ce

"Ya.. sake.. ni."

Salati da sallallamin da Dada ta soma yi shi ne ya fito da Baffa daga ɗaki, ya ƙaraso yana faɗin

"Lafiya kuwa Uwar gida?" Ya ƙarasa maganar daidai lokacin da idanunsa suka sauka a kan
Inna-wuro, da zuwa lokacin hawaye har sun jiƙa fuskarta.

"Inna-wuro?" Ya ambata yana kafe ta da idanunsa. Ɗaga jajayen idanunta ta yi ta kalli Baffan,
daidai lokacin da Dada ta fashe da kuka.

"Subhanallahi me ya faru?" Baffa ya tambaya yana kallan Dada.

"Tambayi 'yarka, tambayi 'yarka kai kam. So take ta kashe ni wallahi" Shi ne abin da take
maimaitawa cikin tsananin ƙunar zuciya. Juyawa ya yi ya kalli Inna-wuro, ya buɗe baki da niyyar
tambayar ta, Dada ta ji ba za ta iya tsayawa har sai ta faɗa da bakinta ba. Don haka ta buɗe
bakinta ta ce
"Alhaji Baita ya sake ta, ya sake ta. Mu kuma shi kenan mun shiga uku."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Baffa ya ambata yana kallan Inna-wuro da ta kasa ko da
ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Idanunta na kallan ƙasa cikin rashin sanin abin yi. Kamar wadda aka
tsikara Dada ta miƙe ta dawo gaban Inna-wuro, ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce

"Saki nawa ya miki?" Ta tambaya cikin tsananin tashin hankalin da ba ta ji makamancinsa
lokacin da Inna-wuron ta ce an sake ta ba.

"Ɗaya ya miki koh?" Dadan ta sake ambata kafin Inna-wuron ta kai ga cewa komai. Cike da
tsoron jin abin da zai fito daga bakinta. Shiru Inna-wuro ta yi tana tunanin ta inda za ta fara, sai
dai kuma tana tsoro kar Dadan ta kawo mata duka, saboda wani irin kallo da take bin ta da shi.

"Saki uku." Ta faɗa jikinta na ƙarasa mutuwa gaba ɗaya. Ta riga ta saddaƙar yau ɗin Allah ne
kaɗai ze raba ta da Dadan. Sai dai Dada kasa cewa komai ta yi, ban da komawa da ta yi baya
ta yi zaman ɗabaro ta yi shiru, ban da bugawa babu abin da zuciyarta take, ta kuma kasa furta
komai.
"Inna-wuro ashe ba ki da hankali? Me kika yi wa mijinki ya sake ki?"

"Baffa babu abin da na masa.. Wallahi ban masa komai ba Baffa." Ta ƙare maganar tana kuka
jajayen idanunta a kan Baffa. Cike da fatan yau ɗaya ya ji tausayin ta, ko da kafaɗarsa ne ya ba
ta ta ɗora ta yi kuka ko da za ta ji sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta.

"Ƙarya kike munafuka, ƙarya kike yi. Yo ko yankar namanki yake ai kya zauna. Uban me bakinki
yake lokacin da kika ji yana ƙoƙarin ambatar sakin, mai ya hana ki saurin katse shi ba tare da ya

ƙarasa ba. Ashe mahaukaciya ce ke Inna-wuro ban sani ba? Ashe bayan kanki da kike yi wa
baƙin ciki har mu kike yi wa? Wallahi ko ki faɗa mini dalilin da ya sa ya sako ki ko in miki shegen
duka yanzun nan. Ki buɗe baki ki mini magana kafin na ci ubanki." Duk da zagin ta da ta yi
hakan be sanya Baffa ko da kallan ta ne ba, ballantana ya nuna ya ji zafin hakan. Shi kansa
kallan Inna-wuron kawai yake don jin amsar da za ta fito daga bakinta.

"Baffa ciki ne da ni, shi kuma ba ya so. Wallahi shi ne kawai dalilin, ya ce ya yanke duk wata
alaƙa ta da shi, har 'ya'yana ma."

Ɗauke wuta gaba ɗaya kansu ya yi, musamman Baffa. Ya rasa me ze ce? Ya ma rasa ta ina ze
fara. Sai kawai ya kama bakinsa ya yi shiru yana jira ya ji abin da Dada za ta faɗa. Wane
hukunci za ta yanke a kan Inna-wuron wanda duk hukuncin da ta yanke ya riga ya zauna
daram.
"Kin cuce mu wallahi, kin cuce mu." Dada ta yi maganar cikin ƙunar zuciya, tana fashewa da
wani sabon kukan baƙin ciki. Ji take kamar ta rufe Inna-wuron da duka ko ta ji daɗi, sai dai
yadda take jin zuciyarta idan ta fara dukan ta san za ta iya mata lahani. Tsabar takaici ma ta
kasa ko da yunƙurin dukan Inna-wuron ne.
"Toh yanzu da kika ɗauko ƙafa kika dawo gida, ba ma ke kaɗai ba har waccan yarinyar da ke
bayanki, da kuma abin da ke cikinki kina nufin mu za mu din ga ciyar da ku? Toh wallahi kin
yaudari kanki. Shigo idan zaman gidan kike so ga ki ga shi, amma fa tabbas ki sani za ki yaba
wa aya zaƙinta."
"Ki yi haƙuri Uwar gida." Baffa ya faɗa ƙasa-ƙasa ko hakan ze sa Dadan ta sakko daga fushin
da take. Sai dai cikin ɗaga murya ta ce

"Da Allah ni ƙyale ni, ka rabu da ni in ji da abin da ke damu na. Idan ba haka ba daga kai har
'yar taka zan haɗa in ci wa mutunci wallahil azeem. Don na ga kai ma ka fara canja hali, za
kuma mu haɗu da kai." Bin ta Baffa ya yi da sauri yana ba ta haƙuri, sai ka ce yaron da ya yi wa
uwarsa laifi yake so ta haƙura. Ita kuma ko kallan inda yake ba ta yi ba ta wuce ɗaki, ya bi
bayanta ba tare da ya sake bin inda Inna-wuro take da kallo ba. Runtse idanunta Inna-wuro ta
yi, tana jin yadda tausayin kanta, da na mahaifinta na kama ta. Ta ɗaga ƙafafunta da suka sage,
tana jin yadda Daneen ke mutsu-mutsu a gadon bayanta, wanda hakan ke alamta mata
farkawar da ta yi. Ƙarasawa ta yi cikin ɗakinta da ya canja. Ta ɗan gyara a gurguje ta sauko da
Daneen, kafin ta nemi waje ta zauna. Gaba ɗaya yinin ranar babu wanda ya sake kula ta, daga
Dadar har Baffan. Sai ita ma ta kama kanta ta yi shiru cikin ɗakin tana tunanin yadda rayuwarta
da ta 'ya'yanta za su kasance cikin gidan.


... Karɓe kwanon da ke hannun Baffa, Dada ta yi da sauri tana faɗin

"Wallahi ba za ta ci ba, ba ka isa ba. Ƙatuwa da ita da 'ya har da cikin wani a ce mu za mu din

ga ciyar da ita? Toh wallahi ba a gidan nan ba. Waye ya hana ta zaman aure? Idan da ita wata
ƙatuwar mai hankali ce komai yake mata ai zauna wa za ta yi. Amma da yake shashasha ce
duk irin arziƙin da ke gidan Alhaji Baita sai da ta yi abin da ya sa ya sako ta. Toh wallahi ko dai
ta fidda miji ta yi aure ko kuma takura da gallazawa yanzu ta fara ganin su cikin gidan nan."
Shiru Baffa ya yi jikinsa a sanyaye don be yi tunanin Dadar za ta gan shi lokacin da ya kawo wa
Inna-wuro abincinsa ba. Ya haɗiye shakkarta da yake ji ya ce a hankali

"Don Allah ko don shayarwar da take ki bar ta ta ci abincin nan don Allah."

"Na ce ba za ta ci ba." Ta faɗa tana shirin barin wajen, bayan ta makawa Inna-wuro wata uwar
harara.

"Toh ko yaya ne a din ga ba ta. Tun da dai kin ga yanzu ba ta damar yin aure har sai ta haihu,
daga nan duk abin da kike so sai a yi." Baffa ya faɗa yana kallanta cike da fatan ta amsa
roƙonsa. Wani kallo ta ƙarasa juyowa ta watsa masa, mamakinsa na kama ta. Lallai dole ne ta
tashi tsaye a kan mutumin nan.
"Malam..?" Ta ƙarasa ambatar sunan nasa da alamar tambaya.

"Ki yi haƙuri." Ya yi saurin faɗin hakan yana shirin juyawa jiki a sanyaye da irin kallan da ta
masa. Kafin ya kai ga wuce wa Dada ta ce

"Shi kenan. Na yarda da abin da ka faɗa, amma fa tabbas sau ɗaya zan din ga ba ta abinci,
zuwa lokacin da za ta haihu. Daga nan ko dai ta fidda miji, ko kuma ta koma ciyar da kanta, ko
kuma gaba ɗaya ma ta bar gidan." Ba ta jira wani daga cikin su ya ce komai ba ta bar wajen, ta
bar su da bin ta da idanu.
"Na gode sosai Baffa." Inna-wuro ta faɗa da sanyayyiyar muryarta, a ranta tana addu'ar Allah
Ya sake dawo mata da Baffanta daidai ko ta ji sauƙin rayuwarta cikin gidan.

Haka rayuwar Inna-wuro ta cigaba da tafiya ita da ɗiyarta. Baƙin cikin yau daban na gobe
daban. Ko da wani lokacin Baffa ya yi niyyar taimaka mata ko kallanta da idon rahama sai Dada
ta san yadda ta yi ta hana hakan faruwa. Shi kuma da ta yi magana shi kenan yake shiga
taitayinsa. Sai dai zuwa lokacin Dada tana yarda ta ba ta abinci sau ɗaya a rana, daga nan
kuma ko kallan inda take ba za ta sake yi ba. Wani lokacin sai dai a ɓoye Baffa ya kawo mata
nasa. I zuwa lokacin kuwa ta soma ramewa, musamman da ya kasance ga shayarwa da take,
ga kuma cikin jikinta. Sosai abubuwan suka haɗe mata, cikin lokaci ƙanƙani ta soma sauyawa
daga ainahin Inna-wuronta, ga babu isasshen abinci, ga babu laifi cikin na matuƙar ba ta
wahala, lokaci guda kuma ga Daneen da ke fama da rashin lafiya, duk ta bi ta rame saboda
haƙori da ya saka ta gaba. Wannan ya taka muhimmiyar rawa wajen sake taɓarɓarewar lamarin
Inna-wuron, ta zama abar tausayi. Idan ka yi mata kallo ɗaya ita da Daneen sai sun ba ka
tausayi, musamman ma dai ita da duk ta bi ta lalace tamkar ba a gidan mahaifinta take ba.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 04

__ Babu wani sauyi da ya samu har zuwa lokacin da ta haife abin da ke cikinta, a cikin gida
kamar yadda ta haifi Daneen cikin sauƙi da rangwamin Ubangiji. Sai dai wannan karon namiji
Allah Ya ba ta, kyakykyawa mai kama da 'yar'uwarsa. Lokacin da ta haihu shekarar Daneen
ɗaya, don haka ta yaye ta a wannan lokacin. Ko arba'in ba ta kai ga yi ba, ta ga zama cikin
gidan nan haka kawai ba zai yi mata ba. Idan ba haka ba, ba jaririnta ba, ba Daneen ba, ita
kanta yunwa za ta mata lahani. Dalili kenan da ya sa ta tattara duk wani abu da ta mallaka ta
siyar, ta siyar da saniyar da Allah Ya taimake ta Dada ba ta ƙwace ta yi rara-gefe da ita ba.
Kasancewar ba a gidan take kiwon ta ba. Da wannan kuɗaɗen ta haɗa ta soma siyar da abinci
da fura da nono a cikin kasuwar ƙauyen nasu. Yaro ta samu shi ne wanda yake taya ta ayyuka
saboda kula da 'ya'yanta. Wannan sana'ar, ba ƙaramin taimaka mata ta yi ba, domin kuwa za ta
samu ta ci abinci, Daneen ma ta ci, sannan kuma jaririnta da ya ci suna Ameer ma ya samu ya
ci.


.. "Ni fa na faɗa maka ba zai yiwu ba. Ta yaya za a yi a ce ƙatuwar mata har da 'ya'ya biyu a ce
a gida za ta din ga zama. Daga wannan layin sai wancan layin. Fisabillahi a haka za a rayu?
Haka za mu cigaba da zuba mata idanu ta yi ta zama babu aure?" Ta jiyo muryar Dada daga
tsakar gida, daidai lokacin da take shayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login