Showing 81001 words to 81712 words out of 81712 words

Chapter 28 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

daga baya."


... Tsaki ya ja a karon farko yana kallon mai kiran nasa. Kamar kar ya ɗaga, sai kuma ya tamke
fuskarsa, yana shirin ɗagawa kiran 4ps ya shigo wayar. Sai ya sauke ajiyar zuciya, duk da ya
san shi ma ɗin ba lallai ne su kwashe ta da daɗi ba. Kara wayar ya yi a kunnensa bayan ya
ɗaga, daga can ɓangaren Pops ya ce
"Yohana."

"Yes, Pops."

"Kana ina?" Pops ɗin ya faɗa, cikin muryarsa babu alamun wasa.

"Me ya faru?" Ya katse shi da tambayar hakan.

"Ka zo ka ɗauke ajiyar ka."

"Amma Pops.."

"Na dai faɗa maka, barin garin ma za mu yi gaba ɗaya. Idan kuma ba ka yi hakan ba za ka ga
ba daidai ba." Numfashi ya sauke yana jin ransa na ɓaci, be ce komai ba ya datse kiran yana
jan tsaki. Har wani huci yake fitarwa saboda tsabar ɓacin rai. Wato Babansa na son ya kwaɓa
masa aiki. Ya dafe goshinsa yana tunanin ta ina zai fara?

... Tun ɗazu yake ganin wayar tana kawo haske babu ƙaƙƙautawa. Alamar kira ne ke ta
shigowa. Don haka ya ɗan ja gajeren tsaki, kafin ya janyo wayar. Ganin sabuwar number ce ya

sanya shi jefar da wayar ya kwantar da kansa kan bangon gadon idanunsa a lumshe. Zuwa can
sai ya ji alamar shigowar saƙo, ya ɗan gyara zamansa kana ya janyo wayar ya buɗe saƙon,
cikin zuciyarsa yana mamakin yadda ya ji ya zaƙu da son karanta labarin tun da ya ji alamar
shigowar saƙo.
"Shege, wai har ni za ka nuna wa ba ka gane waye ni ba? Duk iya shegen nan fa mu ma mun
iya shi, ka fi kowa sanin hakan. Shi ya sa na yi yadda zan yi na nemo number ɗinka, na kikkira
kuma ka ƙi ɗagawa. Dalili kawai nake so na ji na abin da ka aikata. Amma dai kar ka manta duk
iya shegen nan ni ma na iya fa, musamman ma kuma yanzu da na ƙaro wani."
Ya karanta message ɗin ya kai sau biyar, kamar wanda ke shirin haddace duk wani rubutu, da
kuma wasalin da aka yi amfani da su wajen rubuto saƙon. Ya yi shiru yana jin yadda zuciyarsa
ke ɗan bugawa, wanda hakan ya tilasta masa lumshe idanunsa. A hankali ya sake kwantar da
kansa jikin bangon gadon, yana jin yadda saƙon ke ci gaba da yi masa amsa-kuwwa cikin
kunnuwansa, tamkar wanda ake sake karantowa. Ba ya fatan abin da yake tunani ya tabbata.
Ya fi awa ɗaya a hakan, yana ci gaba da saƙawa da warwarewa, zuciyarsa tamkar za ta yi
bindiga. 'Ko kuwa dai batun aurensa ne ya zagaya har inda ba su yi tunani ba, wanda hakan ka
iya janyo tabbatuwar tunaninsa?' Ya tambayi kansa, duk da ya san babu mai ba shi wannan
amsar.


... Washe-gari ta kasance ranar Juma'a, wato ranar da za a ɗaura aure. Bayan an yi Sallahr
Azahar, a babban masallacin Dikko da ke cikin unguwarsu, Abeey da ya zama waliyyin amarya,
ya karɓi sadakinta a hannun Alhaji Abubakar (Mahaifin Abdoul) wanda shi kuma ya zamo
waliyyin ango. Cikin ƙanƙanin lokaci dubban mutane suka shaida ɗaurin auren DANEEN da
kuma angonta TAREEQ ALHASSAN DIKKO. Ɗaurin auren da duk da ba a wani shirya masa
ba, amma manyan mutane da dama sun samu halartar ɗaurin auren. Kafin ka ce mene ne
wannan, tuni maroƙa sun fara shela, ta hanyar faɗin

"Allah Ya nufa. Tabbas Allah Ya nufa. Aure ne irin na girma, an ɗaura auren Shalele, ɗa ga
Alhaji Dikko, Tareeq, tare da amayarsa Daneen. Alƙawarin Allah Ya cika." Maganganun da suka
tilasta shi runtse idanunsa ke nan, wani babban al'amari da bai yi tsammani ba, shi ne bugun
zuciyar da ya ji ya ziyarce shi. A nutse ya buɗe bakinsa, a kan laɓɓansa ya shiga furta.
"Ya Hayyu Ya Qayyum."


Alhamdulillah! A nan na kawo ƙarshen littafin DANEEN Book 1. Mai son ci gaba da karanta
DANEEN Book 2 har zuwa Book 3, zai tura ₦500 ne ta..

8124818273
Zahra'u Yusuf Ishaq
Opay

Shaidar biya ta wannan number 08124818273

Ko kuma kai tsaye a tuntuɓe ni ta 08124818273.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login