Showing 66001 words to 69000 words out of 81712 words

Chapter 23 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

saka
kanta cikin sashen nasa. Sai dai yaɓe-yaɓe! Don kuwa tana taɓa ƙofar ɗakin ta ji ta ɓame da
mukulli. Dakatawa ta yi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. 'Anya kuwa a kullen take?' Ta raya
hakan a ranta tana kallon ƙofar ɗakin. Sai kawai ta sake saka hannunta da ke ɗan rawa kaɗan
da niyyar turawa, nan ma dai shiru. 'Kenan ƙarya yake, da ya ce sashen nasa a buɗe yake?' Ta
tambayi kanta har lokacin idanunta a kan ƙofar. Shiru ta yi na tsawon sakanni, 'Toh ko dai yana
nufin sashen ne kawai a buɗe ban da ɗakunansa' Cikin lokaci ƙanƙani wannan tunanin ya faɗo
mata. Tunanin da ɗazun kwata-kwata bai kawo mata ba. Saboda yadda ta ƙagu da neman
hanyar shiga sashensa kafin cikar sati biyun nan. Cike da ɓacin rai ta fito daga sashe. Ko
dubawa ma ba ta yi ba ko da wanda ke kallon ta. Ta ci gaba da takawa gaba ɗaya fuskarta a
cakuɗe, jikinta a sanyaye ya yin da take taku cike da sassarfa kuma a hanzarce. A haka har ta
ƙarasa sashen Maama. Kamar wadda ba ta da laka, haka taka takawa cikin sashen, zuciyarta
gaba ɗaya a cunkushe. Ta ma rasa wanne tunanin za ta ba wa zuciyarta haɗin kai su yi? Ita dai
ta san burinta ɗaya ta samu damar shiga ɗakin Tareeq. Don haka dole ne ta miƙe tsaye, ta

samo ɗin ko a yi a wuce wajen.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Shi ne abin da kunnuwanta suka soma tsinto mata lokacin da
take dab da shiga ɗakin. Ta dakata tana jin yadda zuciyarta ta harba lokaci guda.

"Hatsari kuma? A ina? Tareeq? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Maama ta faɗa cikin wani
masifaffen tashin hankali. Cikin sakannin da ba su wuce goma ba, jikin Daneen ya ɗauki rawa
ba kaɗan ba. Ta runtse idanunta tana ci gaba da jin yadda kalaman Maaman ke mata
amsa-kuwwa a cikin kunne. Ta kai wajen minti 5 a hakan kafin ta buɗe idanunta.
"Yanzun nan zai fita? Yawwah ki yi amfani da wannan damar wajen shiga sashen nasa, kar ki yi
sanya. Na san ba yanzu zai dawo ba. Don haka ki yi abin da na sanar da ke. Sannan kuma
tsaya, ki sake tabbatar mini da yanzun zai fita." Maganganun da suka koma yi mata
amsa-kuwwa kenan a maimakon na Maama. Tuni ɓarin jikinta ya ƙaru, gumi ya shiga
tsatstsafowa daga ko'ina na jikinta. Ta runtse idanunta a karo na barkatai tana tunanin shin me
yake faruwa ne?


Afwan da ji na da kuka yi shiru kwana biyu. Na ɗan yi busy ne a kwana biyun, saboda ba na
gida. Amma In Sha Allah daga gobe shi kenan.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 26

Duk da yadda take jin ƙirjinta na bugawa ba a daidai ba. A hankali yake bugawa, sai dai da wani
irin ƙarfi, hakan bai hana ta yin kasada ba, kawai ta runtse idanunta sannan ta faɗa cikin ɗakin.
Daidai lokacin da Maama da idanunta suka yi jajir take faɗin

"Dada ji Tareeq ne wai ya samu hatsari." Yadda ƙafar Dada ji ta yi ƙass ne, tun farkon da ta ji
Maama ta ambaci sunan Tareeq ya sanya ta saurin koma wa ta zauna hannunta a kan ƙafar
tata. Sai dai cikin tashin hankali take faɗin; idanunta a kan Maama

"Hatsari? Ya Hayyu Ya Qayyum." Ta faɗa har lokacin hannunta na kan ƙafarta. Duk da yadda
take jin tana mata zafi, amma tashin hankalin da ta ji kanta a ciki na hatsarin Tareeq ɗin ya
danne komai. Ɗaukar mayafi kawai Maama ta yi tana shirin yin waje, Hidaya ta shigo cikin
ɗakin. Haka kawai ta ji zuciyarta ta buga tun kafin ta ji abin da ya faru. Kamar kar ta tambaya
saboda duk wasu alamu sun nuna ba lafiya ba. Amma kuma hakan ba za ta yiwu ba, don haka

ta ce bayan ta ɗan lumshe idanunta

"Maama me ya faru?"

"Hidaya zo ki taimaka mini in miƙe mu tafi. Yayanku ne ya samu hatsari yanzun nan." Wani irin
harbawa da ta ji zuciyarta ta yi, shi ne abin da ya sanya ta saurin kai hannunta saitin zuciyarta
ta dafe. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka tara hawaye fall. Kwata-kwata ma sai ta kasa furta
komai. Ficewar da Maama ta yi ita ta dawo da ita daga hayyacinta. Kawai sai ta fashe da kuka,
daidai lokacin da ta ƙarasa inda Dada ji take. Ta sanya hannunta da ke karkarwa ta taimaka
mata ta miƙe.

"Ya isa, kukan ya isa haka Hidaya. In Sha Allah ba wani abu ne babba ba." Cikin muryar kuka ta
furta

"Ameen." Tana kai hannunta kan fuskarta ta share hawayen. A ranta kawai hasaso ɗan'uwanta
take. Fata take Allah Ya sa ba wani abu babba ne ya samu ɗan'uwan nata ba. A tsaye kawai
take kamar wadda aka dasa, ban da karkarwa babu abin da jikinta yake yi. Sai da suka fice
daga ɗakin gaba ɗaya sannan ta ƙarasa shigewa ciki. Kawai sai ta zube a kan kujerar tana
sauke numfashi. Ta kai wajen mintina biyar, kafin ta miƙe ta faɗa cikin ɗakinsu. Ba ta yi
wata-wata ba, wajen danna wa number Yohana kira ba. Ringing 1 ya ɗaga wayar, yana shirin
fara magana ta katse shi da faɗin

"Me ye alaƙarka da hatsarin da Tareeq ya yi?" Cikin wani irin amo Yohana ya furta

"Hatsari kuma? Yaushe? Ina Tareeq ɗin yake?" Cike da tsoron kar abin da take zargi ya tabbata
ta ce cikin dakiya.

"Kar ka nuna kamar ba ka sani ba mana." Ta faɗa da gaba ɗaya gaskiyarta, bayan ta yi ƙoƙari
wajen danne duk wani tsoro da fargabar da take ji.

"Amma ba ki kyauta mini ba Daneen, kuma a gaskiya zan faɗa miki ban ji daɗi ba. Me ya sa zan
saka hannu wajen yin wani mummunan abu a kan Tareeq? Bayan dukkanmu so muke a
hukunta shi a hukumance. Na ɗauka na tura miki abin da nake so ki samo mini a wajen Tareeq,
takardu ne fa kawai. Ban da su babu komai. Ke ce fa mai fansar da ta fi muhimmanci da kuma
girma, so kike a ɗaukar miki fansar ɗan'uwanki. Kuma shi ne dalilin da ya sa na dage, nake
kuma son ke ma ki dage. Amma idan kin ga ba za ki iya ba, ko kuma za ki saka zargi a cikin
ranki, toh ina ga babu amfanin ci gaba da zaman ki cikin gidan nan, kawai ki fito ki koma
ƙauyenku, ki sanar da su mutuwar Ameer kawai. Idan ya so sai ku nemi wata hanyar da kuke
ganin za a iya hukunta Tareeq ɗin." Ya ƙare maganar cikin wani irin yanayi, da ke nuni da yadda
ya ji babu daɗi da gaske. Shiru Daneen ta yi, tana jin yadda jikinta ke ƙara yin sanyi. Sai da ta
daure, ta yakice komai, sannan ta iya yago magana ta ce

"Toh amma me ya sa ka din ga tambaya ta da gaske yanzu zai fita?" Ta tambaya a sanyaye.

"Kawai so nake na ji, saboda ki je sashensa. Shi ne kawai dalilin da ya sa na tambaye ki. Ban
da haka ina ruwana da inda zai je da kuma yake? Duk fa saboda ke ne. Ki yi tunani mana."
Shiru Daneen ta yi tana nazarin duk maganganun da ya faɗa. Wajen minti 2, sannan ta sauke
ajiyar zuciya, wadda shi kansa sai da ya jiyo sautinta. Ya gyara zamansa daga inda yake zaune
kafin ya ce

"Ban ji daɗin yadda zargi ya shiga tsakaninmu ba." Ya faɗa a hankali. Wata ajiyar zuciyar
Daneen ta sake saukewa kana ta ce

"Ka yi haƙuri, na kasa ƙaryata abin da zuciyata ke ta hasaso mini ne." Daga haka kawai sai ta
ajiye wayar ba tare da ta sake jin wani abu da ya ce ba. Ta zauna yaɓar a kan gadon ɗakin
zuciyarta na wani irin zafi. Wata irin kewar Innarta ta ji tana ratsa ta, gefe guda kuma tunanin
Ameer ɗin da kullum yana cikin mafarkinta. Ta ƙagu komai ya kammala ta gan ta a kusa da
Innarta. Ko ta samu ta ɗora kanta a kan kafaɗarta ko cinyarta su yi kukan rashin Ameer tare, su
yi wa Ameer addu'a tare, su kuma tuna shi tare. Miƙewa ta yi a hankali ta shiga zagaye ɗakin,
hannunta duka biyun cikin na juna. Gaba ɗaya kwanyarta ta cushe da tunanunnuka kala-kala.
Tsoron ta ɗaya kada a ce Tareeq ya rasu a asibiti yanzun. Ba ta so ya mutu ba tare da an
hukunta shi ba, ba ta so ya mutu ba tare da an masa hukunci daidai da muguntar da ya yi wa
ɗan'uwanta ba. Don haka za ta yi ta masa addu'ar ya rayu, ko don ya karɓi kashinsa a hannu.
Tana ci gaba da zagaye ɗakin Sultanah ta shigo da sauri.

"Sister shirya mu wuce asibitin da aka kai Yah Tareeq. Yah Tareeq ne ya yi hatsari." Sultanah ta
yi maganar, gaba ɗaya yanayinta na nuni da yadda take cikin tashin hankali. Bin ta da ido kawai
Daneen ta yi, ita ma duk nata hankalin a tashe yake. Sai dai ba na komai ba ne face kar ta je
Tareeq ya mutu ya bar ta da fansar da ba ta ɗauka ba. Dogon hijab ɗinta Sultanah ta ɗauka ta
saka a gaggauce, sai da ta yi hanyar fita sannan ta ce

"Ki fito mu tafi." Daga haka ba ta jira Daneen ɗin ta ce komai ba ta fice daga ɗakin. Babu musu
Daneen ta bi bayanta, gwara ta kasance tana kusa, ko babu komai za ta din ga sanin a halin da
Tareeq ɗin yake ciki.

... Lokacin da suka isa, an daɗe da shigar da Tareeq emergency, saboda mummunan raunin da
ya samu a ƙafarsa. Babu wanda ya samu damar ganinsa. Dukka sai suka yi cirko-cirko suna
jiran jin halin da yake ciki hankali a tashe. Sai dai kowannen su addu'a yake, Allah Ya sa ko ma
mene ne zai zo ya zo da sauƙi.
"Ubangiji Allah Ya ba ka lafiya yaron nan." Dada ji ta faɗa a sanyaye. Sultanah ce ta iya amsa
wa da "Ameen." Ita ma jiki a sanyaye. Ita dai Daneen sai raba ido take. A zahiri ita kanta ma
neman lafiyar tasa take, sai dai abin nasu ya fita daban. Don su suna so ne ya samu lafiya
kawai, ya yin da ita kuma nata son ya samu lafiyar saboda fansarta ne. A nan suka ci gaba da
zama har zuwa shuɗewar wasu lokuta masu tsayi. Zuwa lokacin har Abeey ma ya iso shi da
babban amininsa Alhaji Abubakar. Abdoul ma tuni ya iso, don har ya riga ma su Abeey zuwa

cikin asibitin.


... Kansa a kwance yake a kan pillow, ya yin da hannunsa ɗaya ke kan fuskar tasa, idanunsa a
rufe. Turo ƙofar da aka yi ne ya sanya shi buɗe lumsassun idanunsa da kalarsu ta ɗan sauya.
Bai yi yunƙurin tashi ba, duk da ba ya iya ganin mai shigowar. Sai dai tun kafin ta ƙaraso ya
fahimci wace ce, don haka a hankali ya shiga miƙewa zaune. Da sauri Maama ta ƙarasa ta
gyara masa zaman. Ya zube idanunsa da suka faɗa a kan Maaman yana jin wani irin rauni na
kama shi. Ita ma shi take kallo ba tare da ta ce komai ba. Ta ma rasa me za ta ce, ko kuma ta
ina za ta fara.

"Maama ni kuma ƙaddarata a ciwwuwwuka take. Ina ta saka ku cikin fargaba koh? Ni kaina ba
na jin daɗin hakan. Amma ya zan yi Maama?" Ya ƙare maganar a sanyaye. Kafe shi da
idanunta Maama ta yi, tuni fuskarta ta ɗinke tsaff. Kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta
girgiza kai ta ce
"Ga ka dai a haka kamar ka girma ka yi hankali, har kana da ƙannen da za ka tsawatarwa, ashe
ba haka ba ne. Tareeq yanzu ni za ka kalla faɗa wa wannan maganar? Waye yake ɗora cuta?
Akwai wanda haka kawai yana sane zai ɗora wa kansa cuta? Allahn da Ya jarabce ka da ita shi
zai yaye maka In Sha Allah. Za ka samu lafiya cikin yardar Ubangiji." Lumshe kyawawan
idanunsa ya yi a hankali kamar mai jin bacci, ya buɗe su a kan Maama kafin ya ce

"Ki yi haƙuri Maama. Amma kuma kina tunanin wannan ƙafar za ta warke kuwa?" Ya ƙare
maganar idanunsa a kan ƙafarsa da ke ajje kawai a nannaɗe. Shi kaɗai ya san azabar da yake
ji daga cikinta, tamkar ana daddatsa ta da wuƙa irin kakkaifar nan. Ita ma kallon ƙafar tasa ta yi
da jajayen idanunta, ta kai wajen minti 1 tana kalla kamar mai nazarin wani abu, sannan ta buɗe
baki a nutse ta ce

"Ai Allah na ce." Jinjina kai kawai ya yi, yana koma wa baya, ya jinjina da pillow. A hankali ya
ɗan fesar da iska daga bakinsa, kamar wanda ke shirin sake cewa wani abun. Sai kuma ya
tsuke bakinsa ya yi shiru. Maama ta nemi waje ta zauna tana kallon ɗan nata cike da
tausayawa.

...."Alhamdulillahi, cikin ikon Allah abubuwa da dama da sauƙi. Sai dai kuma.." Likitan ya ɗan
dakata a nan yana girgiza bironsa a kan takardar gabansa. Jinjina kai Abeey ya yi alamar yana
tare da shi, hakan ne ya sanya shi ɗan ajiye numfashi kafin ya ci gaba da faɗin

"Ƙafarsa.. Gaskiya ƙafarsa ta samu mummunan rauni sakamakon yadda ta maƙale cikin motar
sosai, da ƙyar aka iya zaro ta. Kamar yadda aka sanar da ni kenan. Wannan ne dalilin da ya
sa.." Sai ya sake dakatawa a nan.

"Ya Hayyu Ya Qayyum." Abeey ya faɗa a fili idanunsa a lumshe. A ransa yana ji lallai lokaci ya

yi da Tareeq zai ajiye ko ma mene ne, ya tsayar da hankalinsa a kan kasuwanci kawai. A
hankali ya juya ya kalli likitan, yana jin yadda ilahirin jikinsa ya yi matuƙar sanyi, sannan ya ce

"Kaa ga kada ka ɓoye mini komai. Tareeq ɗana ne, saboda haka ka sanar da ni komai a kan
matsalar ƙafar tasa."

"Ba zan ɓoye maka ba Ranka ya daɗe, fatanmu na warkewar ƙafarsa har ya miƙe ya ci gaba da
tafiya ba shi da yawa. Ƙafarsa ta samu mummunan rauni kamar yadda na faɗa maka, wanda
zai iya taɓa lafiyar tafiyarsa. Ba ma fata, ba kuma za mu cire rai ba, In Sha Allah za mu yi masa
aikin da idan Allah Ya yarda za a dace. Amma sai dai ka yi haƙuri Yallaɓai, don hakan ba lallai
ba ne." Likitan ya ƙare maganar a sanyaye, saboda yadda ya ga yanayin Abeey. Ya san yadda
yake matuƙar ƙaunar yaransa, musamman ma kuma Tareeq. Sai dai ga shi Allah Ya fi
jarabtarsa da ciwuka. Bai ga kuma amfanin ɓoye masa komai ba, tun da da kansa ya nemi ya
sanar da shi hakan. Gwara ma ya sanar da shi gaskiyar, ba su da tabbacin za a samu nasara a
aikin, saboda kar sai an yi ba a dace ba, a zo ana wallahi tallahi.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 27

Ɗan jimm Abeey ya yi na tsawon minti ɗaya ba tare da ya ce komai ba. Kafin zuwa can ya
sauke ajiyar zuciya, a hankali a kan laɓɓansa ya furta

"Ya Ilahy." Kafin ya maida dubansa kan Likitan ya ce, ilahirin jikinsa a sanyaye.

"Na gode." Shi ne abin da ya iya furtawa kawai, daga haka ya miƙe ya miƙa masa
hannu kana ya juya ya fice daga office ɗin. Bin sa da kallo Likitan ya yi, yana jin wani irin
tausayinsa da na ɗan nasa na kama shi. Kai tsaye Abeey ɗakin da Tareeq ke ciki ya nufa. A
hankali ya tura ƙofar ɗakin har lokacin jikinsa a matuƙar sanyaye. Har zuwa lokacin Maama
tana zaune gefen ɗan nata. Ya ƙarasa a sanyaye bakinsa ɗauke da Sallama, ya ja kujera ya
zauna daidai lokacin da Maama ke amsa sallamar tasa. Gaba ɗaya idanunsa na kan Tareeq da
sai a lokacin ya amsa sallamar Abeeyn, saboda yadda hankalinsa ya ɗan yi wani wajen.

"Tareeq." Abeey ya ambaci sunansa.

"Na'am Abeey." Ya amsa yana kallon sa. Sai da ya kalli ƙafarsa kafin ya ce bayan ya maida
duban sa kan Tareeq ɗin.

"Ya ƙafar taka? Ya kake jin duka jikinka?" Shiru Tareeq ya yi na ɗan wasu sakanni, yana nazarin
abin da ya kamata ya ce. Don kuwa idan har gaskiya zai faɗa, toh ba zai iya kwatanta abin da
yake ji a cikin ƙafarsa ba. Ya ɗan sosa goshinsa a nutse kafin ya ce

"Alhamdulillahi Abeey, da sauƙi." Murmushin yaƙe Abeey ya yi, a ransa yana ji ina ma a ce
hakan ne. Domin kuwa, daga yanayin yadda Tareeq ɗin ya yi magana za ka fahimci kawai ya
faɗa ne.

"Allah Ya ƙara lafiya Tareeq. In Sha Allah za ka samu lafiya, kamar ba ka taɓa yin ciwo ba."
Jinjina kai ya yi yana murmushi, lokaci ɗaya yana gyara zamansa saboda ciwon da ƙafarsa take
ya ɗan motsa. Maama ce ta amsa da "Ameen." Ya yin da shi kuma ya sake kwantar da kansa
gefe idanunsa a lumshe.

.... Kallon ta kawai Umma take, duk lokacin da ta shigo ba tare da ta ce da ita ko uffan ba. Ita
ma ba ta ce wa Umman komai ba, fita kawai take yi, ta ɗauko kayan ta shigo da su sai kuma ta
sake fita. Har zuwa lokacin da ta dawo cikin ɗakin ta zauna jagab a kan kujera tana faɗin

"Washh.." Ta yi maganar tana zame hular kanta idanunta a lumshe. Sai a lokacin sannan Umma
ta ce, bayan ta ɗauke duban ta daga kan kayan zuwa kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login