Showing 3001 words to 6000 words out of 81712 words
Chapter 2 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
kallan Inna-wuro. A
hankali ta ɗaga idanunta da suka yi laushi ta kalli Baffah, sai dai maimakon idanunta su faɗa
cikin na Baffah sai suka faɗa cikin na Dada. Tana shirin kautar da kanta ta jiyo muryar Dada na
faɗin
"Ai kam dai ya kamata.. Ka ganta nan ta yi kyau abinta, ai tun jiya na gama gyare maka ita tass,
kawai tafiya za ku yi babu wani ɓata lokaci. Malam ɗakko kayan Inna-wuro da na shirya mata
cikin jaka." Kallon Baffahn da ya tashi zungwui-zungwui Inna-wuro ta yi, tana mamakin jin wai
har an haɗa mata kaya amma duk ba ta sani ba. Toh yaushe? Kuma tana ina hakan ta faru?
"A'ah, dawo ka yi zaman ka. Ba sai an ɗauko komai ba, ni da ma Fatima na zo ɗauka ba wani
abu ba." Alhaji Baita ya katse Baffa daga yunƙurin shiga ɗaki da yake. Sai ya juyo yana faɗin
"Kai dai kullum ba ka gajiya da ɗawainiya. Toh madallah." Ya ƙarasa maganar yana murmushi,
lokaci guda kuma yana neman waje ya zauna. Miƙewa Alhaji Baita ya yi yana gyara zaman
babbar rigar jikinsa, ya saka hannu ya zaro kuɗi a aljihunsa ya dire a gaban Dada yana faɗin
"Ta same ni a mota." Daga haka ya juya don ficewa daga gidan. Cikin farin ciki Dada take faɗin
"Mun gode sosai, Allah Ya saka da alkhairi, Ya ƙara arziƙi." Be ce komai ba ya fice daga gidan.
Sai a lokacin Baffa ya kalli Inna-wuro ya ce
"Maza tashi ki wuce ku tafi, kar ki bar shi yana jira." Idanunta ta ɗaga ta kalli Baffa, kallo irin
wanda take fata ya ji tausayinta, ya kalle ta da idon mahaifi, ya kalle ta da soyayyar mahaifi, ya
kalle ta da wannan tausayin da yake kallan ta da shi tun haihuwarta, soyayyar nan tata da ta
ƙaru a wajensa tun da ta rasa mahaifiyarta. Sai dai kashh, wannan kallan ya daɗe da zama
tarihi. Wannan tausayin ya daɗe da zama shuɗaɗɗe. Baffan da take gani yanzu zaune a
gabanta ba halinsa ɗaya da Baffanta na da ba.
"Ki tashi ana miki magana, kin zauna kin kafe mutane da idanu kamar za ki cinye mu. Kin tashi
ne ko sai na tashi na kai ki da kaina." Dada ta faɗa a zafafe. Miƙewa ta yi a hankali tana jin
yadda jiri ke ɗibar ta. Ba ta damu da hakan ba sai shiga ɗaki da ta yi, ta saɓa Daneen da har
lokacin take bacci a baya. Ta ɗauki dogon hijabi ta saka. Abubuwan da ta san dole tana da
buƙatar su ta tsaya ta ɗauka a gurguje sannan ta fito. Gaba ɗaya jikinta ya yi wani mugun sanyi
haka ta fito, kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta lumshe idanunta ta ce
"Na tafi." Daga haka ba ta jira sun ce komai ba ta fice daga gidan. A cikin motar ta hango shi ya
yi ƙwam a driver seat. Ƙarasawa ta yi ta ƙarasa buɗe murfin gaban motar da ya soma buɗe
mata, ta shiga ta zauna. Kamar yadda be ce komai ba haka ita ma ba ta ce komai ba, ya tashi
motar suka bar wajen. Sun yi nisa da fara tafiya ya kalle ta, ya saki murmushi kafin ya maida
kansa kan titi kana ya ce
"Kin ƙara kyau abin ki 'yar fara tass tawa." A hankali ta ɗaga idanunta ta kalle shi, ta lumshe su
tana jinjina kai, ta buɗe baki a sanyaye ta ce
"Na gode." Bai sake cewa komai ba har zuwa lokacin da suka ƙarasa ficewa daga rugar gaba
ɗaya, suka miƙi hanya cikin gari. Ga mamakinta maimakon ta ga sun yi gida, sai ta ga ya yi
parking motarsa cikin wani private hospital, ta juya ta kalle shi cikin son jin ƙarin bayani. Be kula
ta ba sai fita daga motar da ya yi ya ce yana kallan ta.
"Fito." Ya yi maganar cikin bayar da umarni. Sake kallan cikin asibitin ta yi, ita dai ba za ta ce ga
takamaimai abin da ya kawo su ba, tun da ya zo gidan kuma bai tambayi lafiyar ɗiyarsa ba,
ballantana ta ce ko ya kawo su ne domin a duba lafiyarta.
"Ki fito mana, a'ah.." Ya sake faɗa. Hannu ta saka ta buɗe motar ta fito, tana cigaba da kallan
cikin asibitin. Be ce da ita komai ba sai gaba da ya yi, babu ɓata lokaci ta bi bayansa. Kai tsaye
ɗakin likitan suka shiga, bayan doguwar gaisawar da suka yi da Alhaji Baita, wanda hakan ke
nuna sabon da ke tsakaninsu.
"Matata ce wannan, kamar yadda aka saba nake so a yi mata. Idan da akwai maganin da za a
ba ta kwata-kwata ta dena haihuwa a ba ta don Allah." Cikin wata irin ruɗewa Inna-wuro ta kalli
Alhaji Baita, zuciyarta na wani irin bugu da ya wuce na ƙa'ida. Girgiza kanta ta soma yi tana jin
yadda tarin ƙwalla ta cika idanunta. Ilahirin jikinta na rawa kamar mazari, cikin karyayyiyar
muryarta da ke rawa saboda tsabagen ruɗewa ta ce
"A'ah don Allah kar ka mini haka, kar ka cuci rayuwata, kar ka zama sanadin katsewar farin
cikina, ina son na haihu, ina son ganin 'ya'yana ko da guda nawa Allah zai ba ni ina son su. Don
girman Allah kar ka yi mini haka." Ta ƙare lokacin da wasu kyawawan hawaye suka sauka a kan
fuskarta.
"Ni kuma ba na so, ba na so kwata-kwata. Ke kan ki kuma kin san ba don ki haihu na aure ki
ba. Kar kuma ki yi tunanin don kin ce in ƙyale ki hakan na nufin zan ƙyale ki ko na datse alaƙar
da ke tsakaninmu. A'ah zama da ni yanzu kika fara, domin iyayenki sun riga sun ba ni ke halak
malak, don haka dole ki zaɓi mafita ɗaya. Ko dai ki zaɓi a cire mahaifar gaba ɗaya, ko kuma ki
yi planning na shekaru, wanda za ki din ga sake wa daga zarar lokacin lalacewarsa ya yi." Alhaji
Baita ya faɗa yana kallon cikin idanun Inna-wuro. Shiru doctor ya yi yana saurarar duk abin da
ke gudana. Lallai Alhaji Baita shege ne, kuɗi kuma kan su shegu ne, tun da ga shi mata
kala-kala na yarda su zauna ƙarƙashin Alhaji Baitan duk da yadda yake yadda ya ga dama da
su. Kanta ta ji yana wani irin juya mata, tana tsoro kar ta je ta amince da abin da ya faɗa a yi
mata abin da ya buƙata tun da farko. Idanunta da ke a rufe ta buɗe a kan fuskar Alhaji Baitan.
Ta riga ta san ba ta da wani 'yanci na neman saki a wajen Alhaji Baitan, tun da iyayenta suka
riga suka mallaka masa ita, duk da ba ta son sa, kuɗin da ya din ga musu ɓarinsa ne ya sa suka
ba shi ita. Ta buɗe bakinta da ya yi mata nauyi da ƙyar ta furta
"Na amince."
"Likita na shekara biyar nake so, kar a yi na ƙasa da haka. Shekarun na cika kuma za mu dawo"
Alhaji Baita ya faɗa yana kallan Likitan. Hannunsa da ya haɗe waje ɗaya ya raba su kafin ya ce
"Kar ka damu Yallaɓai. Ka bar komai a hannuna, ba za ka yi dana sani ba."
"Godiya nake Doctor." Alhaji Baita ya faɗa yana murmushi.
.. Har dare ya yi bai nemi ya ga ɗiyar da aka haifa masa ba. Tana zaune cikin ɗakin ta fito daga
wanka ya shigo ɗakin, ƙarasowa ya yi yana kallanta lokacin da take ɗaure da towel. Ya lumshe
idanunsa kafin ya ce
"Ki ɗauki yarinyar ki miƙa ta sashen 'yan aiki su kula da ita zuwa safiya. Sai ki taho sashena ina
jiran ki." Da matuƙar mamaki ta ɗaga kai ta kalle shi, bakinta har rawa yake lokacin da ta furta
"Watanta biyu ne fa..?"
"Ko yau kika haife ta.." Ya ba ta amsar cikin rashin kulawa. Kafin ta kai ga cewa komai ya ce
"Ina buƙatar ki, ki same ni a ɗakina. Ba na son ɓata lokaci." Daga haka ya juya yana shirin
ficewa, jin ba ta ce komai ba ya sanya shi dakatawa, ya juya ya kalle ta kafin ya ce
"Kin ji koh?" Jinjina kai ta yi kafin ta lumshe Idanunta daidai lokacin da ya fice daga ɗakin. Ta kai
wajen minti 10 a cikin ɗakin tana tunanin abin da ya kamata, kafin ta share hawayen fuskarta ta
ja Daneen a jikinta ta rungume, kusan mintuna 2 kafin ta sauke ta, ta shayar da ita na tsawon
mintuna masu yawa kana ta miƙe ta fice daga ɗakin. Kai tsaye sashen 'yan aikin ta nufa,
zuciyarta cunkushe da tunane-tunane kala-kala. Shin idan ta yi hakan ta yi wa yarinyarta adalci
kuwa? Da wannan tunanin haka ta ƙarasa, ta samu Atika da ta yarda da ita sosai ta miƙa mata
yarinyar.
"Ki kula mini da ita don Allah. Idan ta farka ki ba ta ruwa ta sha In Sha Allah za ta koma bacci.
Zuwa safiya zan zo na karɓe ta." Yadda take maganar a hankali kamar wadda ke shirin yin kuka
ya sanya Atika faɗin
"Rankiyadaɗe lafiya kuwa?" Ta tambaya tana karɓar fidar da Inna-wuron ta miƙa mata.
Murmushin yaƙe ta yi kafin tace
"Lafiya ƙalau. Ki kula mini da yarinya."
"In Sha Allah Hajjaju kar ki damu." Ba ta iya sake cewa komai ba ta fice daga sashen gaba
ɗaya. Kai tsaye sashen Alhaji Baita ta nufa, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe, jikinta kuma a
matuƙar sanyaye. Tana shigowa ya miƙe ya rungumo ta fuskarsa ɗauke da murmushin da
rabon da ta ta gan shi a kan fuskarsa tun bayan da ya fahimci tana da cikin Daneen. Ƙarasawa
ya yi da ita a jikinsa zuwa kan gadon. Kamar koyaushe cikin ƙanƙanin lokaci ya shiga fiddo da
zilamarsa a kanta a fili. Duk wata kewar jikinta da ya yi na tsayin kwanaki sai da ya fanshe a
daren.
"Shi ya sa kullum nake ƙara jin son ki a cikin zuciyata Fatima." Ya ƙare maganar yana shafa
doguwar baƙar sumar kanta da ke kwance kamar wadda ke saka wa relaxer. Wasu hawaye
masu ɗumi ne suka samu damar sakkowa zuwa kan fuskarta, waɗannan kalaman da ya faɗa
babu abin da suka haifar mata sai raunin zuciya da sake kashe mata jiki. Shin kowacce mace
haka take fuskanta a gidan aurenta? Shin da ma aure ana yin shi don wannan abun ne ko kuwa
dai ita nata kalar auren ne daban da na mutane? Ba ta taɓa samun farin ciki, ba ta ganin
murmushinsa idan ba a kan wani abu da ya shafi jikinta ba.
... Sam ta kasa zaune, ta kasa tsaye. Daga ta je can sai ta dawo nan. Ban da bugawa babu
abin da zuciyarta ke yi. Kanta gaba ɗaya ya kulle, tsoro da fargaba take ji matuƙa. Idan dai har
ba kuskure ta yi ba, tun da ta dawo daga gida haihuwar Daneen ba ta sake ganin baƙon
watanta ba. Duk kuma wasu alamomi da ta ji farkon cikin Daneen shi take ji a yanzu. 'Kar dai
abin da take tunani shi ne?' Ta tambayi kanta tana jin sabuwar faɗuwar gaba na ziyartar ta. A
hankali ta kai idanunta kan Daneen da ke kwance kan gado tana ta wasa, don yanzu ta sake
wayo sosai, ta yi ɓul-ɓul abin ta. Tausayinta ya kama ta, kawai sai ta ji ƙwalla ta taru a idanunta.
Daidai lokacin da Alhaji Baita ya shigo ɗakin. Ta yi saurin ɗauke ƙwallar tana juyawa da sauri ta
kalle shi.
"Me kike yi ne har yanzu ina jiran ki ba ki ƙaraso ba? Ko kin manta yau kwanan ki ne?" Ya
tambaya ba tare da ya damu da yanayin da ya gan ta ba. Girgiza kai ta yi kafin ta ce
"A'ah, Daneen ke kuka na tsaya rarrashin ta." Ta yi maganar idanunta a kan Daneen.
"Toh ki yi da jiki." Ya ƙare maganar yana fice wa daga cikin ɗakin. Ta bi shi da kallo kamar me
son gano wani abun. Sai da ya ida ficewa kafin ta dawo da duban ta kan Daneen. Tun dawowar
ta gidan har zuwa yau ɗin nan bai taɓa kula ko tambayar lafiyar Daneen ba, bai taɓa jin yaya ta
kwana ko yaya ta tashi ba. Bai taɓa damuwa da ya ɗauke ta ba, ko da hakan zai janyo ƙauna ta
shiga tsakanin su ba. Shi dai kawai abin da ya sani, tun da ba ya son cikin, ko da ta haihu ma
ba ya ƙaunar abin da ta haifa ɗin. Tun da da ma kamar yadda yake faɗa, be aure ta ba ne don
ta haihu. Sai da ta tabbatar ta ƙoshi sosai kafin ta ɗauke ta kamar yadda aka saba ta kai ta
wajen Atika kafin ta wuce ɗakin Alhaji Baita.
.. Su uku ne zaune a kan dinning suna break, Alhaji Baita, Hajiya Amina sai Inna-wuro da ke
zaune, ita ba cin abincin take ba, sai dai ta riƙe cokali ne kawai tana caccakawa cikin abincin.
Hira Alhaji Baita da Hajiya Amina (Abokiyar zaman ta) suke, sam hankalinta ba ya wajen. Ƙoƙari
kawai take ta iya tare kanta, ta riƙe kanta kar wannan ƙamshin abincin da ke tashi ya sanya ta
yin amai. Wani yamutsawa da 'ya'yan cikinta suka yi, shi ne ya sanya ta jefar da cokalin
hannunta. Ta guntse bakinta tana jan wata ajiyar zuciya, duk don kar ta yi abin da take ta gudu,
ko don gudun tonuwar abin da ta riga da ta tabbatar da lallai tabbas shi ne. Sai dai ina
kwata-kwata ta kasa, cikin sauri ta miƙe ta nufi toilet ɗin da ke cikin palourn ta shiga kwara amai
kamar za ta amayar da kayan cikinta. Cikin sauri Hajiya Amina ta ajje cokalin hannunta, ya yin
da Alhaji Baita har bai san lokacin da cokalin hannunsa ya suɓuce ba. Cikin tashin hankali suka
bi ta da kallo, sai dai babu wanda ya iya furta komai. Har bayan wajen minti 5 sannan Inna-wuro
ta fito daga banɗakin cikin mutuwar jiki, ba tare da ta kalli inda suke ba, ta fara ƙoƙarin komawa
ɗakinta cike da fatan kar ya yi mata magana. Sai dai tun kafin ta yi taku 5 ta jiyo muryarsa cikin
kaushi yana faɗin
"Ke!" Dakatawa ta yi jikinta na ɗaukar rawa, ta runtse idanunta daidai lokacin da ta sake jiyo
muryarsa yana faɗin
"Kar ki sake ki je ko'ina, ƙaraso wajen nan tun kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba za ki taɓa
mantawa ba." Cike da sassarfa ta juya akalarta zuwa inda suke. Tun kafin ta ƙaraso ta jiyo
muryarsa da ke ɗauke da zallar tuhuma ya ce
"Me ye ma'anar wannan aman da kika yi? Me kike nufi? Ciki ne da ke?" Ya yi tambayar duka a
jere. Kasa ɗaga ido ta yi ta kalle shi, ballantana ta ce wani abu. Ta rasa me za ta ce, ta rasa ya
za ta yi, gaba ɗaya kanta a kulle yake.
"Tambayarki nake ciki ne da ke?" Ya yi maganar yanzu a tsawace. Runtse idanunta ta yi tana jin
yadda ta ji muryar tasa har cikin kanta. Ta buɗe baki da niyyar yin magana, ya katse ta da faɗin
"Kar ki sake ki faɗa mini ba daidai ba, sanar da ni abin da ke faruwa da gaske. Ciki ne da ke?"
Jijjjiga kai ta shiga yi tamkar wata ƙadangaruwa, har lokacin kuma ba ta kalle shi ba.
"La ha ila ha illal lahu.." Hajiya ta soma faɗa tana tafa hannu. Shi kuwa Alhaji Baita shiru ya yi
don gaba ɗaya kansa ya kulle, ya ma rasa me ya kamata ya yi. Ciki? Ciki ne da Fatiman? Abin
da yake ta masa yawo a ƙwaƙwalwarsa kenan. Ya sauke wani zazzafan numfashi yana tunanin
ta ina zai fara? Tabbas yana ƙaunar Fatima, uwa uba kuma jikinta. Kaff matansa, da duk irin
aure-auren da yake har yanzu bai samu irin Fatima ba. Duk kuwa da ta haihu, amma kullum jin
ta yake kamar sabuwa. Sai dai duk da haka ba ya tunanin ze iya zama da ita. Don yana da
tabbacin idan dai har ya cigaba da zama da ita, toh kowacce shekara sai ta haihu. Be san
yawan adadin shekarun da za su ɗauka tare ba tare da ya gaji da ita ba, kenan 'ya'ya nawa za
ta haifa? Ya kuma san ko me ze yi ba za ta yarda a yanke mahaifarta ba, don kuwa ya kwana
da sanin ko kaɗan dukiyarsa ba ta gaban ta.
"Ciki kika sake yi?" Tambayar da ke ta masa yawo a ƙwaƙwalwa, ta samu damar fitowa kan
laɓɓansa yana kallan Inna-wuro. Da mamaki ta ɗaga jajayen idanunta tana kallansa, kafin ta kai
ga cewa komai Hajiya Amina ta ce
"Toh ai Alhaji ina ganin kamar laifinka ne, garin yaya ka bar ta ta shigo cikin gidan nan da
mahaifa? Ka san fa 'yan ƙauye da ma akwai zilama." Be bi ta kan abin da Hajiya Amina ta faɗa
ba, duk da ta wani ɓangaren maganar tata ta shige shi, amma kuma tun da mai afkuwa ta afku
zancen yaushe kuma?
"Wai ba kafin mu shigo gidan nan sai da na kai ki asibiti aka tabbatar mini an tsayar da
haihuwar ba? wace irin zulamammiya ce ke? Duk da planning ɗin da kika yi amma sai da kika
ɗauki ciki?" Alhaji Baita ya ƙarasa maganar yana jin yadda zuciyarsa ke tururi, tarin baƙin ciki da
ɓacin rai na sake tunzura fusatacciyar zuciyarsa.
"Ka yi haƙuri Alhaji." Hajiya Amina ta faɗa cikin salo na kwantar da murya.
"Kin ga maza je ki tattara kayanki ki bar mini gida, ki ɗauki abin da kika haifa, da wannan cikin
da ke jikinki ki fice a gidan nan. Wallahi ba zan iya cigaba da zama da ke ba. Idan na ce duk
macen da na