Showing 63001 words to 66000 words out of 81712 words

Chapter 22 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

kafin ta ce a sanyaye.

"Ga shi dai cikin farin ciki nake ji na Sisi, amma ban san me ya sa nake jin wata irin faɗuwar
gaba ba. Na kasa gane dalili." Murmushi Hidaya ta yi tana kamo hannun 'yar'uwar tata ta ce

"Cikin farin ciki kike jin ki fa Sulty, ina da tabbacin hakan na da nasaba da farin cikin. So ki
kwantar da hankalinki, burin ki ya kusa cika In Sha Allah. Yah Abdoul zai so ki fiye da yadda
kike son shi."

"Ina fatan hakan." Sultanah ta faɗa a sanyaye.

"Ya kamata mu je gidan Umma, kin san dai halinta da na Jawahir ɗin kanta. Biki yana ta
matsowa." Ajiyar zuciya Sultanah ta sauke kafin ta ce

"Wato Hidaya mu sake gode wa Allah da Ya ba mu ɗan'uwa irin Yah Tareeq wallahi, har abada
zan ci gaba da alfahari da shi, ki ga dai yadda silar sa nake ta farin ciki. Bikinsa kuma nan da
sati biyu, ai dole ne mu tashi tsaye. Daɗin abin kuma Jawahir ce matar. Allah dai Ya tabbatar da
alkhairinsa." Taɓe baki Hidaya ta yi kafin ta ce
"Ameen dai, duk da dai ni wallahi ban wani so haɗin nan ba." Duka Sultanah ta kai mata a kan
yatsun hannunta ta ce

"Ke Sisi."

"Yoh Allah kuwa." Motsin da Daneen ta yi ne ya sanya Hidaya kallon ta. Ta dubi Sultanah ta ce

"Kin ga kar mu tashi baiwar Allah, zo mu fita mu ba ta waje." Ta faɗa tana jan hannun Sultanah.
Babu musu Sultanah ta miƙe a nutse suka fice daga ɗakin. Wani irin gumi ke tsatstsafowa
Daneen tun da ta ji abin da suke faɗa. Ta kai wajen mintina goma tana sake tauna maganganun
nasu, kafin ta miƙe ta ɗauko wayar nan daga inda ta ɓoye ta. Hannunta har karkarwa yake yi,
lokacin da ta ke nemo number Yohana cikin karambani. Sai kuwa ga shi ta gano ta, ta danna
masa kira tana jin wani irin zafin zuciya. Idan har Tareeq ɗin ya yi aure ya bar ta cikin gidan me
kenan?

"Daneen." Ya ambata tun kafin ta ce komai. Ba tare da ta amsa kiran sunanta da ya yi ba, ta
soma faɗin

"Yanzun nan na ji ƙannensa na faɗin aurensa nan da sati biyu. Na rasa me ma zan ce ne ni
kam." Cikin wani irin tashin hankali Yohana ya miƙe tsaye, idanunsa har wani ƙanƙancewa suke
yi. Ya kai wajen mintina biyu bai ce komai ba, kafin daga baya ya buɗe bakinsa ya ce

"Ya zama dole mu tashi tsaye.. Kamar yadda yake, har yanzu babu abin da ya canja a
ƙudirinmu, sai dai a yanzu sati biyu ne da mu ni da ke. A cikin kuma sati biyun ne za mu yi duk
abin da ya kamata. Ki shiga cikin jerin abubuwan da suke kan wayar, za ki ga Whatsapp, ki
shiga ciki zan tura miki wasu hotuna, ki duba ki karanta da kyau. Zan yi miki bayanin komai ta
can. Abin da kawai nake so na tunasar da ke, dole sai kin dage, sai kin cije, kin saka wa kan ki
jarumta. Kin ji kowacce kasada ce za ki iya don samun damar cika burina, da kuma naki. Hakan
ma ya yi daidai, ko babu komai idan muka san muna da ƙayyadaddun kwanaki, za mu fi yin
aikin da sauri. Ki ajje wayar yanzun nan ki shiga abin da na faɗa miki." Daga haka ya yi mata
bayanin yadda za ta hau online ɗin yana jiran ta.

"Kar ki manta sati biyu ne kawai da mu." Ya sake maimaita mata kafin ta katse wayar. Tamkar

yana gabanta ta jinjina kai, tana jin ko ma wacce irin kasada ce za ta yi domin cikar burinsa,
daga nan kuma ya samu ya shigar mata da Tareeq ɗin ƙara, a ƙwatar wa Ameer haƙƙinsa.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 25

Kamar yadda ya kwatanta mata haka ta yi, kamar wadda ya koyawa ga ta ga shi, sai ga shi har
ta gane duk abin da ya koya matan. Maganarsa ce kaɗai cikin Whatsapp ɗin, don haka kawai
sai ta taɓa sunan nasa da ya yi saving da YOHANA B. Tarin messages ne, duka daga shi ɗaya.
Har bayan ta shiga ma wasu ba su daina shigowa ba. Tsayawa kawai ta yi tana kallon ikon
Allah. Duk da ya yi mata bayanin komai, amma a wannan karon kuma ba ta san mai za ta yi ba.
Amma dai sai ta shiga karanta saƙonnin da suke a rubuce ɗaya bayan ɗaya. Daidai lokacin da
wayar ta soma ƙara kenan. Yanzun ma dai shi ke kira, don haka ta ɗaga tana kara wa a
kunnenta.

"Kina ji na?" Shi ne abin da ya faɗa. Ta jinjina kai tamkar tana gabansa. Sai kuma tunawa da ta
yi ba ya ganin ta ya sanya ta buɗe bakinta ta ce

"Ehh.." Nan da nan ya shiga yi mata bayani tamkar ɗazun. Ta yi shiru tana saurara, da kiyaye
duk abin da yake faɗa mata. Wajen mintina 20, sannan suka yi sallama. Sai a lokacin ta koma
cikin Whatsapp ɗin suka ci gaba da magana ta nan. Ƙura wa wayar idanu ta yi tana kallon
takardun da ya turo mata. Ta iya karatu daidai gwargwado, saboda haka ta shiga karanta duk
abin da ta gani rubuce a jikin takardar. Wasu abubuwan ta fahimci me ake nufi, ya yin da wasu
suka yi mata tsaurin fahimta. Hakan ne ya sa maimakon ta fahimci abin da take karantawa, sai
ya zamana kawai karantawar take yi ba tare da tana fahimtar komai ba. Don inda ba ta fahimta
ba, ya fi inda ta fahimta sau fiye da biyar. Taɓe baki ta yi, tana mamakin dalilinsa na son nemo
masa irin takardun.

"Ashe ma shi duk a kan takarda yake wannan abin." Ta raya hakan cikin zuciyarta tana ɗan juya
manyan idanunta. Shiru kuma ta yi na tsawon mintuna, kafin murmushin gefen baki ya ɗan
bayyana a kan laɓɓanta, murmushin da yanzun ya maye gurbin murmushinta tun bayan
mutuwar Ameer. Ba ta taɓa tunanin bayan ganin gawar ɗan'uwanta za ta iya ci gaba da walwala
ko murmushi ko da kuwa na yaƙe ne ba. Ba ta taɓa tunanin idan Ameer ya rasu za ta iya ci
gaba da rayuwa ba. Sai ga shi ta iya rayuwar, har ma ga shi tana iya murmushi. Ta ɗan lumshe
idanunta da lokaci ɗaya kalarsu ta sauya daga fari zuwa ja.

"Toh ko dai ya yi haka ne duk saboda ni?" Ta sake raya hakan a ranta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ji

tabbas haka ne, idan ma ba haka ba ne, toh ko ma waɗanne irin takardu ne suna da
muhimmanci, duk da ita ba ta ga wani muhimmancinsu ba. Don haka ko ma mene ne za ta yi
yadda za ta yi ta ɗakko masa takardun. 'Don dai takarda?' ta furta hakan a kan laɓɓanta. Lokaci
guda tana lumshe idanunta. A ranta tana sake jinjina kirki irin na Yohanah. Gefe guda kuma
tana tuna yadda daga zarar ta ɗakko masa takardun, nan ba da daɗewa ba za ta ga Tareeq a
gaban kotu. Asirinsa ya tonu a idon duniya. Sannan kuma a yanke masa hukunci.


... "Ba kwa jan yarinyar nan a jiki, shi ya sa kullum take zaune ita ɗaya. Kada dai shiririta ta
mantar da ku alkairinta gare ku." Maama ta faɗa tana kallon Hidaya da Sultanah. Tareeq da ke
zaune ya kalle su a ɗan fuzge kafin ya ci gaba da danna wayarsa. Ita kanta Maama da take
zaune ba ta yi tunanin yana da abin da zai ce ba, sai lokacin da ta ji ya buɗe baki ya ce
"Kuma ina yawan ba su amanarta ba." Ya faɗa ba tare da ya kalle su ba.

"Yah Tareeq Allah kuwa muna kula da ita. Yanzu haka ma barin ta muka yi ta yi bacci." Hidaya
ta faɗa bayan ta karyar da kanta gefe.

"Ke Sultanah maza je kira mini yarinyar nan." Da "Toh." Sultanah ta amsa tana miƙewa. Kai
tsaye ta wuce ɗakinsu. Cigaba da zama suka yi cikin ɗakin, lokaci zuwa lokaci Maama kan jefo
wata maganar, shi ko Hidaya wani ya amsa ta. Har zuwa lokacin da Sultanah da Daneen suka
shigo ɗakin, Daneen na sanye cikin hijab ɗinta kamar koyaushe. Don ko a cikin gidan ma da
aka tashi yi mata siyayyar kaya, har hijabi suka kawo mata da yawa. Ba ta sani ba ko gani suka
yi tana son shi ko haka nan ne kawai, ita dai ba ta sani ba. A hankali take takawa cikin ɗakin,
kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Abin da ya ƙara wa tafiyar armashi kenan, sai ta zama
kamar tana tafiyar ƙasaita ne. Ƙasan kujerar da Maama ke kai ta nema ta zauna, a nutse ta ce

"Barka da rana."

"Barka ka dai, ya jikin naki?" In ji Maama.

"Alhamdulillah." Daneen ta faɗa har lokacin a sanyaye. Tun kafin ta iso cikin ɗakin ta tabbatar
da wanzuwarsa ciki. Sai kuma da ta yo kusa-kusa, sai ta ji duk ya cika ɗakin. Sai dai kuma gefe
guda, ita kaɗai ta san abin da take ji. Ta kuma saka ranta ba za ta gaishe shi ba. Akan me ye
ma za ta gaishe shi? Waye shi ɗin? Mutumin da ya yi sanadiyar mutuwar Ameer shi za ta
gaisar? Lallai kuwa da ta cika cikakkiyar mara lafiya.

"Toh Alhamdulillahi, Allah Ya ƙara afuwa. Sannu kin ji Daneen?" Maama ta faɗa tana murmushi.
Ita ma ɗan murmushin ta ƙaƙalo tana gyara zamanta. Kamar ya ce mata ya jiki, ko kuma dai
wani abun, sai kawai ta gintse, duk da ya san da wanzuwarta cikin ɗakin, amma bai nuna ba.
Don kuwa ci gaba ya yi da danna wayarsa kamar bai san ta shigo ba. Tun da har ba ta san ta
gaida babba ba, bari ya kama kansa, ko ita ma ta saita nata. Dakatawa kuma ya yi da danna
wayar, ya ɗan yi shiru sai dai har lokacin idanunsa na kan wayar ne. Amma kuma idan ya yi

hakan ya yi daidai? Yarinyar da ta ba shi ƙoda ba tare da wani dalili ba fa? Ya ɗan runtse
idanunsa hannunsa a kan goshinsa yana murzawa.

"Na bar muku sashena a buɗe, wata a cikin ku ta ɗan je ta gyara mini. Zan ɗan fita ne." Da
mamaki Maama ta kalle shi ta ce

"Unguwa kuma Tareeq? Ina za ka je?" Sai da ya ɗan gyara zamansa sannan ya sanar da ita
inda zai je. Ta yi masa addu'ar Allah Ya tsare, ƙannensa na amsawa da Ameen sannan ya fice
daga ɗakin. Ta lumshe idanunta tana jin wani irin daɗi na ratsa ta, 'Sashensa a buɗe?' Ta sake
tuna hakan cikin zuciyarta tana ji kamar ta tashi ta taka rawa. Ba ita ta bar palourn ba sai da
Maama za ta wuce ɗaki ta ɗan yi bacci. Ta yi sallama da Maaman, don dama ɗazun su Hidaya
sun fita. Daga haka Maama ta wuce daƙinta, ya yin da Daneen ta wuce nasu ɗakin. Babu ɓata
lokaci ta kira Yohana ta sanar da shi abin da ke faruwa. Ya yi shiru yana saurarar ta har ta
gama, sannan ya ce yana murmushin da har a cikin muryarsa kana iya ji.

"Da gaske?"

"Ehh.." Ta amsa masa a taƙaice, kamar yadda ya taƙaita tambayar tasa.

"Yanzun nan zai fita? Yawwa toh ki yi amfani da wannan damar wajen shiga sashen nasa, kar ki
yi sanya. Na san ba yanzu zai dawo ba. Don haka ki yi abin da na sanar da ke. Sannan kuma
tsaya, ki sake tabbatar mini da yanzun zai fita." Ba tare da kawo komai ba ta jinjina kai, kafin ta
buɗe baki ta ce
"Eh, yanzun nan ya fita."

"Toh shi kenan zan ajje waya. Ki yi duk abin da ya dace ina jiran kiran ki."


.... A fuzge ya kalli wayarsa da ta shiga ringing. Ya ɗauke kai yana maida hankalinsa kan driving
ɗin da yake, Abdoul da ke gefensa ya kalli mai kiran. 'Jawahir' Shi ne abin da ya bayyana a kai.

"Ba za ka ɗaga ba ne?" Abdoul ya faɗa yana kallonsa. Lumshe manyan idanunsa ya yi kafin ya
ci gaba da driving, kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya sanya hannunsa ya ɗauki wayar. Bai
kai ga ɗagawa ba ya ce

"Haka na faɗa maka?" Ya faɗa bayan ya juya ya jefa masa harara. Murmushi kawai Abdoul ya
yi, saboda ganin da ya yi ya kara wayar a kunnensa, alamar ya ɗaga. Ajiyar zuciya Jawahir ta
sauke kafin ta ce

"Har na cire ran ba za ka ɗauka ba wallahi."

"Saboda haka ne halina?" Ya faɗa cikin basarwa, lokaci ɗaya yana sauya hannun da ya riƙe

wayar da ɗayan hannun. Duk sai ta dabirce, ba wai don wani abu ba, sai don yadda ya yi
magana ya dake ta, har sai da ta ji wani yarr.

"A'ah.. fa.. ba haka.. nake nufi ba." Ɗa. Jinjina kai kawai ya yi a hankali kafin ya ce

"Toh yanzu dai ya aka yi? Ina driving ne." Ya yi maganar a haɗe.

"A'ah babu komai, kira na yi kawai na ji muryarka, sannan na sanar da kai yadda na yi kewar
ganin kyakykyawar fuskarka." Ta ƙare maganar tana ɗan sauke numfashi gami da murmushi.
Ɗan sauke wayar ya yi daga kunnensa, yana jin waɗannan kalmomin nata sun daɗe da
ginsarsa. Ko ba ma haka ba, ya daɗe da daina jin wasu abubuwa da suka shafi soyayya za su
birge shi. Sai dai kuma ita burinta kullum ta faɗi yadda take ƙaunar ganin kyakykyawar fuskarsa,
abin da ba ya so kenan, amma ta kasa ganewa.

"Toh ya yi, zan samu na shigo." Ya faɗa kamar a gajiye. Murmushi ta yi tana faɗin

"Yawwah sai ka zo Habiby." Daga haka ya sauke wayar ya ci gaba da driving ɗin da yake.

"Aboki Allah Ya sa sau kana son Jawahir." Abdoul ya faɗa yana kafe shida idanunsa, kamar
mau son gano gaskiyar abin da zai faɗa. Tareeq bai kalle shi ba, illa ci gaba da abin da yake yi
da ya yi. Bayan shuɗewar minti ɗaya, wanda sai ka ɗauka ba zai amsa ba ne sannan ya ce
bayan ya sauke gajeriyar ajiyar zuciya
"Idan dai har na aure ta zan koyi sonta. Abin da na sani kenan." Ya yi maganar kamar ya gama
kenan, sai dai kafin Abdoul ya ce komai ya cigaba da faɗin

"Amma idan dai har halayenta sun yi mini." Da mamaki Abdoul ya kalle shi cikin rashin fahimta
ya ce

"Ban gane ba? Idan kuma halayen nata ba su yi maka ba fa?"

"Za ma su yi mini, tun da har na amince da ita yanzun." Jinjina kai Abdoul ya yi yana murmushi
kafin ya ce

"Toh Allah Ya tabbatar da alkhairi. Ameen." Ya yi addu'a da amsar duka a tare, don ya san halin
mutumin nasa ba lallai ya amsa ba. Ko zai amsa ma sai dai ya amsa a zuciya, wanda shi ba zai
gane ya amsa ɗin ba.

"Sauke ni nan Tareeq." Abdoul ya faɗa yana kallon inda suke ƙoƙarin wucewa. Babu musu
Tareeq ya gangara gefen titi ya tsaya. Suka yi sallama da Abdoul sannan ya tashi motar ya bar
wajen.

Sanye cikin hijab ɗinta take ci gaba da tafiya, ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ba ta
waige-waige saboda kar a gano ta. Dab da za ta isa sashensa, ta yi kiciɓus da Sultanah da riƙe
da waya a hannunta. Dakatawa ta yi tana jin zuciyarta na harbawa, ita ma Sultanah dakatawa
ta yi tana kallon ta da murmushi a kan fuskarta ta ce
"A'ah, Daneen.. me ya fito da ke?" Wani daƙiƙin murmushi Daneen ta ƙaƙalo tamkar za ta fashe
da kuka.

"Ko kin gaji da zaman cikin ne?" Sultanah ta katse ta da faɗin hakan a daidai lokacin da take
tsaka da lalubo abin da za ta faɗa. Har wata ajiyar zuciya ce ta suɓuce mata, sai kawai ta shiga
jinjina kai tana murmushi.

"Allah Sarki mu je in taka miki." Lokaci guda gaba ɗaya murmushin ya ɗauke. Ta yi maganar
tana soma takawa. Kamar ta rusa ihu haka ta ji, sai dai babu yadda ta iya, haka ta bi bayanta
suka soma tafiya. Tun kafin su yi nisa, wayar Sultanah ta shiga ƙara. Daneen ba ta ji abin da
aka faɗa daga can ɓangaren ba, ta dai ji Sultanah ta ce a sanyaye
"Toh Maami." Daga haka ta sauke wayar daga kunnenta. Ta kalli Daneen a nutse ta ce

"Ki ƙarasa kawai 'yar'uwa, bari na je ciki, Maami na kira na."

"Tohm." Daneen ta faɗa tana jin wani irin farin ciki na mamaye ta. Sai dai ba ta nuna a kan
fuskarta ba, saboda yadda take ji a ranta ya zama dole ta saita kanta, ta sauya takunta, idan ba
haka ba a ramfo ta. Sai da ta daina gano Sultanah sannan ta ci gaba da tafiya, addu'a take a
ranta kada Allah Ya sa ta sake haɗuwa da kowa har ta je inda za ta je. Addu'ar tata kuwa ta
karɓu, don har ta ƙarasa inda yake da tabbacin nan ne sashen Tareeq ba ta haɗu da kowa ba.
A wannan lokacin ma sai da ta ɗan tsaya ta dudduba, ta ga babu kowa sannan ta wuce cike da
sassarfa, har tana ji kamar za ta kifa. Wata kasalalliyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe
idanunta da ke a lumshe a kan ƙofar sashen nasa. A hankali ta saka hannunta ta tura. Kamar
yadda ta tsammata kuwa, a buɗe take. Ta ji wani sanyi ya ratsa ta, ta saki murmushi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login