Showing 18001 words to 21000 words out of 81712 words

Chapter 7 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

mata kenan tun kafin ta ida shigo
wa soron gidan. Gaba ɗaya sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ta girgiza kai kafin ta ce

"Na sanar da shi zan yi shawara, sannan kuma na nemi zaɓin Ubangiji." Inna-wuro ta faɗa a
sanyaye, cike da fatan Dadan ta amince da hakan, ko dan kasancewar yanzu ba kamar da ba
ne. Tun da yanzu da hankalinta ba kamar da ba.

"Toh ki koma ki sanar da shi kin amince.. don wallahi ba shawararki muke nema ba, umarni ne
muke ba ki. Ki koma ki sanar da shi kin amince, ko kuma yau ɗin nan wallahi ki ga abin da zan
muku cikin gidan nan, babu ruwa na da wasu 'ya'ya da kika tara wallahi ci miki mutunci zan yi."
Dada da ke dab da soro ta faɗa tana maka mata harara. Girgiza kai Inna-wuro ta yi ta ce a
sanyaye

"Dada.."

"Ka saka baki Malam.. Wallahi ba kirki ne da ni ba, ka da ki ɓarar mana da wannan damar."
Dada ta faɗa tana kallan Baffa da ke zaune a tsakar gidan. Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli
Inna-wuro ya ce

"Kin ga maza koma ki sanar da shi kin amince. Mun riga mun zaɓa miki shi, babu buƙatar wani
tunani kuma." Duk da yadda zuciyarta ke bugawa hakan be hana ta juya wa ba, ƙafarta har
wani rawa take lokacin da ta bi umarnin mahaifinta wajen koma wa wajen mutumin. Har ya
shiga cikin motar ya tayar da ita, ya hangi Inna-wuro da ta fito. Sai ya kashe motar cike da
mamakin abin da ya fito da ita bayan sun yi sallama. Kai tsaye inda take tsaye ya nufa yana
kallan ta.

"Ina so mu yi wata magana." Inna-wuro ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye. Ita kam ta rasa

wannan wace kalar rayuwa ce. Ta rasa mafita a rayuwarta. Tana so ta inganta rayuwar
'ya'yanta, sai dai da alama Dada tana so ta yi mata cikas. Maimakon a ce yanzu haka maganar
auren 'yarta ake, amma wai nata ake. Ba ta san dalilin Dada na saka mata ido ba. Ba ta san me
ye ƙudurin Dada a kanta na son sai ta yi aure ba.
"Ikon Allah! Ina sauraron ki." Alhaji Abubakar ya faɗa yana gyara tsayuwarsa. Sauke numfashi
Inna-wuro ta yi tana tunanin ta inda za ta fara. Sai dai kawai ta yi ƙundunbala wajen soma faɗin

"Ina da 'ya'ya guda biyu.. Ina neman alfarmar idan dai har za ka aure ni ka bar ni na taho da su.
Ni ba zan ɗora maka komai ba. Ni zan din ga musu komai da ake buƙata, ni dai buri na kawai
ka amince na zo da su gidanka." Cikin matuƙar farin ciki ya ce

"Kina nufin idan dai har na amince da hakan kin amince za ki aure ni?" Runtse idanunta
Inna-wuro ta yi, kafin ta shiga jinjina kanta a sanyaye. Murmushi ya yi, har cikin ransa yana jin
daɗi. Ya buɗe baki a nutse ya soma faɗin

"Ni da ba ki guje ni ba duk da ina da 'ya'ya, kika kuma amince za ki kula da su, mai zai hana ni
ma na kula da naki? Idan dai har kin amince da aure na, ni mai iya haɗa 'ya'yana da naki ne na
kula da su In Sha Allah." Wani irin sanyi ta ji yana ratsa zuciyarta. Farin cikin da ta daɗe ba ta
tsinci kanta a ciki ba yau ta ji shi. Har ba ta san lokacin da wani irin sassanyan murmushi ya
suɓuce a kan fuskarta ba. A kan laɓɓanta ta furta

"Alhamdulillah." Ta buɗe idanunta a nutse ta kalli Alhaji Abubakar ta ce muryarta na bayyanar
da farin cikin da take ciki

"Na amince. Allah Ya tabbatar da abin da yake alkhairi a gare mu." Ta ƙare maganar tana
lumshe idanunta, a ranta tana fata hakan ya zame mata alkhairi, kamar yadda take fata. Ko ma
wane irin hali ne da Alhaji Abubakar ɗin, idan dai har tana tare da 'ya'yanta za ta ji sauƙi. Ta
kuma san In Sha Allah Allah zai taimake ta, ya taimaka mata wajen kula da rayuwar 'ya'yanta.
*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 08

Kusan a tare suka sauko daga cikin motar. Dukkansu fuskarsu ɗauke da annurin da ke bayyana
farin cikin da suke ciki. Hidaya ce, sanye cikin doguwar rigar da ta matuƙar amsar jikinta, ta
kuma haska kyakkyawar farar fuskarta mai kama da Tareeq. Gefen ta wata budurwar ce, wadda
a kallan farko za ka iya kiran su da sa'anni. Ko ma kai tsaye ka kira Hidaya da babba saboda

yadda ta fi Sultanah cika ido. Sai dai a zahiri Sultanah ta ba wa Hidaya kusan shekaru biyu ne,
wanda a ido ba za ka taɓa faɗa ba idan dai har ba faɗa maka aka yi ba. Uwa uwa kuma yadda
suke abubuwan su tare, suke komai tare, kai tsaye idan ba ka kira su da tagwaye ba, za ka kira
su da sa'annin da suka fito daga gida ɗaya.
"Na yi matuƙar kewar gida." Sultanah ta faɗa tana murmushi. Ita ma Hidaya murmushin ta yi
kafin ta ce

"Ki bari kawai Sisi, shi kansa gidan ya yi kewar ki." Ta ƙare dimple ɗin da ke gefen kumatunta na
lotsawa. Daidai lokacin da wata babbar mace sanye cikin wata hamshaƙiyar atamfa ɗinkin bubu
ta fito daga cikin motar da su Hidaya suka fito daga cikin ta. Kunnen ta kare da waya tana amsa
wa. Idanunta saye cikin glass, hannunta kuma ɗauke da jakar da ke ɗore a tsintsiyar hannunta.
Ba tare da ta dubi inda 'yan matan ke tsaye ba, kai tsaye ta wuce sashenta tana cigaba da
amsa wayar.

"Sultanah bari na je, ki fara zuwa ki huta yanzun dai." Hidaya ta faɗa tana kallan Sultanah.
Girgiza kai ta yi kafin ta ce

"A'ah ni kam.. Sai na fara zuwa na gaishe da Dadaji, tun da dai yanzu haka Abeey ba ya cikin
gidan nan." Dariya Hidaya ta yi kana ta ce

"Toh shi kenan mu je." Daga haka suka maida akalarsu zuwa sashen kakar tasu. Daidai lokacin
da Tareeq da Abokinsa Abdoul suke dab da ƙaraso wa wajen. Ƙirjin Sultanah ya buga, ta runtse
idanunta tana ambaton sunan Allah. Daidai lokacin da suka ƙaraso.

"Yah Tareeq." Hidaya ta faɗa kyakkyawan murmushin nan da ke ƙara wa fuskarta kyau kamar
koyaushe yana kan fuskarta.

"Da alama shi kaɗai kika gani?" Abdoul ya faɗa yana kallan Hidaya, lokaci ɗaya yana ɗage
girarsa. Dariya kawai ta yi tana gaishe da Abdoul ɗin.

"Yah Tareeq barka da wannan lokacin." Sultanah ta faɗa tana jin kewar yayan nata.

"Barka sweetsis.. Kin dawo lafiya?" Jinjina kai ta yi kafin ta ce

"Eh, na yi kewar ka sosai." Ta faɗa kawai, dan ta so ba a gaban abokinsa ba ne, da hugging
nasa za ta yi. Sassanyan murmushi ne ya tashi a kan fuskarsa kana ya amsa da

"Missed you more Sulty." Sai a lokacin sannan ta maida duban ta kan Abdoul ta gaida shi. Tun
da ta masa kallo ɗaya ba ta sake bari ta kalle shi ba. Don kwata-kwata ba ta iya jure kallan
nasa. Daga haka ba su ƙara mintuna masu yawa ba, Sultanah da Hidaya suka yi sashen
Dadaji, ya yin da Tareeq da Abdoul suka wuce.

Tun kafin su ƙarasa shiga ta tafi a guje tana faɗin

"Dadaji tawa." Ta faɗa tana rungume tsohuwar da ke zaune a kan lallausan carpet ɗin da ke
malale a tsakiyar ɗakin.

"Oh ni ɗiyar babana, yau ga Sultanah na neman karya ni." Ta ƙare tana yamutsa fuska.

"Kai Dada tsananin kewar ki da na yi ne fa." Sultanah ta ƙare tana turo baki.

"Eh dole ai ki yi kewa ta mana.. Ke ni ba wannan ba, tun da dai yanzu Allah Ya dawo mini da ke
lafiya, maza tashi ki shiga kitchen."

"Kai Dadaji daga dawowa ta?" Ta ƙare tana waro ido. Taɓe baki Dadaji ta yi ba tare da ta ce
komai ba. Sultanah ta sake faɗin

"Ga Hidaya nan da babu gajiyar komai a tare da ita."

"Ni! Raba ni da wannan malalaciyar." Dadaji ta ƙare tana auna wa Hidaya harara. Dariya Hidaya
ta yi tana faɗin

"Toh shi kenan ki bari Sulty ta shiga tsakaninmu. Ni dai babu ruwa na." Ta ƙare tana gyara
zamanta. Dariya Sultanah har ma da Dadajin suka yi jin abin da Hidaya ta faɗa.


... A ɗaya ɓangaren kuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka tsaida ranar auren Inna-wuro da Alhaji
Abubakar. Babu daɗewa Inna-wuro ta sanar da su Daneen canjin da suke ƙoƙarin samu, na
barin ƙauyen gaba ɗaya zuwa can wani waje su rayu. Farin ciki kamar su taka rawa haka suka
ji. Ko babu komai za su rabu da Dada. Matar da zuwa yanzun suka sake fahimtar kwata-kwata
ba ta ƙaunar su, ba ta son duk wani abu da ya shafe su. Musamman ma dai Ameer da tun da
abin nan ya faru ya ɗauki gaba da Dadan. Sai da Inna-wuro ta fahimci abin da ke faruwa
sannan ta tsawatar masa. Shi ne ya sassauta saboda gudun ɓacin ran Innar tasu.


A ƙofar gidan ya yi parking na matarsa, kamar kodayaushe sanye cikin shadda ɗinkin babbar
riga. Bai kai minti 3 da tsayuwa ba, Baffa ya fito daga cikin gidan.

"Ƙaraso ciki mana, ai yanzu ka tashi daga ɓako ka zama ɗan gida. Kwana nawa ne ya rage?"
Baffa ya ƙare maganar yana murmushi. Shi ma murmushin Alhaji Abubakar ya yi kafin ya
gaishe da Baffan cikin girmamawa. Ya amsa yana yin gaba don ba wa Alhaji Abubakar damar
shiga gidan. Babu musu ya bi bayansa, cikin ransa yana saƙa lallai ko ma mene ne dalilin kiran
nan nasa yana da matuƙar muhimmanci, tun da har aka umarce shi da shiga cikin gidan. A soro
suka dakata, Baffa ya nuna masa wata tabarma ya ce

"Bismillah." Babu musu Alhaji Abubakar ya tuɓe takalmansa, ya nemi waje ya zauna bayan ya
tattare babbar rigarsa. Baffa da takaimaimai bai san dalilin kiransa ba ya shiga gidan don kiran
Dada. Tun kafin ya ƙaraso ta ce

"Mu je, ai na shirya ma." Ta faɗa tana gyara zaman gyalen da ta yafa a kanta, sai dai gaba ɗaya
ta kwashe shi zuwa kan kafaɗarta, har rigar jikinta ana gani. Babu musu ya juya, ya bi bayanta,
don har ta riga shi fita.

Da mamaki shimfiɗe a kan fuskar Alhaji Abubakar yake kallan Dada, ƙwarai da gaske ya yi
mamakin ganin ita ke son magana da shi. Duk da tun bayan da ya ya soma zuwa wajen
Inna-wuro ya soma fahimtar halayenta. Amma duk da haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba wajen
gaishe ta cikin girmamawa.
"A'ah lafiya ƙalau Alhamdulillahi. Wallahi mun gode Allah." Ta faɗa tana gyara zama. Kafin ya ce
komai ta cigaba da faɗin

"Dama abin da ya sa na kira ka.. Ba wata doguwar magana ba ce. Magana ce a kan 'ya'yan
Inna-wuro da na ji ka ce za ka riƙe. Toh ka san yanzu yadda rayuwar nan ta sauya, 'yan gulma
sun yi yawa. Sai a dinga gulmar ko ma dai mata biyu ka aura ne ba ɗaya ba. Toh saboda gudun
hakan ya sa na ce bari na faɗa maka.. Idan har niyyar kula da su ka yi, ni ɗin nan kakarsu ce,
zan iya kula da su fiye da yadda kake tunani. Idan ya so duk wata sai ka dinga yo aiken abin da
za a kula da su. Ai hakan ba wani abu ba ne." Ta ƙare tana dariya gami da gyara zama. Shiru
Alhaji Abubakar ya yi na tsawon wasu sakanni yana nazarin maganganun Dadar. Kafin can ya
ce, bayan ya sauke ajiyar zuciya

"Babu komai Baba. Ni ma ina da 'yan matan har guda biyu, shi ya sa ma nake so na haɗa su
waje ɗaya. Hakan ba abin damuwa ba ne. Zan kula da su idan babu damuwa."

"Toh! Ikon Allah!" Dada ta faɗa a wani sheƙe tana kallan Alhaji Abubakar. Ji take kamar ta tashi
ta rufe shi ta tsinannan duka ko ta ji daɗi. Sai dai kafin ta ida tsara abin da ke cikin ranta ta jiyo
muryarsa yana faɗin

"Ga wannan.. Na gode sosai Allah Ya saka da alkhairi." Ya yi maganar bayan ya ajje kuɗi a
gaban Dadan. Don ba tun yanzu ba ya fuskance ta, ya kuma fahimci me ye damuwarta. Sai
kuwa ta fashe da murmushi tana riƙo kuɗin lokaci ɗaya tana furta

"Duka dai? Kai dai ba ka gajiya." Ta ƙare tana murmushi. Shi dai be sake cewa komai ba ya
miƙe ya saka takalmansa. Ya yi sallama da Baffa ya fice daga gidan, a ransa yana cigaba da
bitar kalaman Dada.

Babu jimawa lokacin da aka saka na biki ya zo. Ranar wata juma'a aka ɗaura auren Inna-wuro
da Alhaji Abubakar. Tuni dama Inna-wuro ta ajiye sana'ar nan tata. Musamman da ya kasance a
lokacin tana da kuɗin da za su yi amfani da shi wajen harkokin yau da kullum. Ga kuma Alhaji

Abubakar da shi ma ba ya barin ta haka, duk da yadda take nuna ba ta so. Amma sai ya nuna
mata tamkar yadda ya yi alƙawarin kula da 'ya'yanta to zai fara ne tun yanzu. Ita dai Inna-wuro
sai dai ta runtse idanunta tana gode wa Sarki Allah buwaya gagara misali, wanda ya ba ta Alhaji
Abubakar. Mutumin da tun kafin a yi nisa duk wasu kyawawan halayensa suka bayyana,
mutumin da ya nuna ƙaunar 'ya'yanta, ya nuna zai kula da su duk da kasancewar ba shi ya
haife su ba. Ita kuwa me za ta yi idan ba ta cigaba da gode wa Allah ba?.

Tana sanye cikin atamfa riga da zani, da mayafi sabbi gall. Ta yi kyau matuƙa, idan dai har ba
sani ka yi ba, ba za ka ce ita ce ta ajje Daneen da Ameer ba. Sabuwar wayarta da Alhaji
Abubakar ya ba ta ita ce ta shiga ƙara. Ameer da ya fi kusa da wayar ya ɗauka ya miƙa mata
yana faɗin
"Inna ana kiran ki." Miƙa hannu ta yi tana faɗin

"Miƙo mini." Babu musu Ameer ya miƙa mata, ta karɓa idanunta a kan fuskar wayar don ganin
mai kiran.

"Inna in haɗa har da wannan?" Daneen da ke haɗa kayanta da na Ameer ta faɗa tana kallan
Innar. Ɗaga kai Innar ta yi ta kalli kayan kafin ta ce

"Eh ki haɗa da shi, haɗa da wancan ma." Ta ƙarasa maganar tana mai nuni da wasu kaya cikin
kayan da Daneen ɗin ke duba wa. Sai ta ɗauka kuwa ta haɗa cikin waɗanda take haɗa wa. Ya
yin da ita kuma Inna-wuro ta ɗaga kiran da ake mata.

"Amarya ba kya laifi." Daga can ɓangaren Alhaji Abubakar ya faɗa yana murmushi. Duk sai ta ji
kunya ta kama ta. Ta yi murmushi tana gaida shi. Amsa wa ya yi, kafin ya ɗora da

"Na san dai kina cikin gida yanzu haka. Toh idan babu damuwa ki leƙo akwai wata muhimmiyar
magana da za mu yi." Haka nan kawai ta ji faɗuwar gaba ta ziyarce ta, sai dai ta basar kafin ta
ce

"Toh ga ni nan." Daga haka ta katse wayar. Ta ɗan yi shiru na wasu sakanni kana ta maida
duban ta kan Ameer ta ce

"Ameer ka tashi ka taya Addarka shirya kayan nan, ka bar ta tun ɗazun tana yi ita ɗaya." Miƙe
wa ya yi yana faɗin

"Toh Inna."

"Kafin na dawo kun gama uhmm?"

"Toh Inna sai kin dawo." Daneen ta faɗa har lokacin idanunta na kan kayan da take shirya wa.

Kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa, yana ƙofar gidan, ganin ta da ya yi ya sanya shi faɗaɗa
murmushin kan fuskarsa. Ya ƙaraso yana sake zolayarta. Ita dai sai babbasarwa take yi dan har
ga Allah kunya yake ba ta.

"Amm.." ya faɗa bayan ya yi gyaran murya. Nan ma sai da ta ji gabanta ya tsinke ya faɗi. Ta yi
saurin runtse idanunta tana ambatar sunan Allah.

"Wato Fatima tafiya ce ta taso mini bagatatan, yau yau ɗin nan zuwa Abuja ya taso mini. Yanzu
ma haka ni ake jira mu wuce. Ban san da wane ido zan kalle ki in sanar da ke yau ɗin za mu
wuce Abuja ne tare da ke kawai ba. Idan ya so da mun tashi dawo wa, kai tsaye nan za mu
dawo mu ɗauki 'ya'yanmu mu wuce da su gida." Cikin lokaci ƙanƙani zuciyarta ta cigaba da
bugawa fiye da zato. Jin da ya yi ba ta ce komai ba ne ya sanya shi faɗin

"Kar ki damu, kwata-kwata ba za mu wuce sati ɗaya a can ɗin ba. Na kuma yi miki alƙawarin
daga can ɗin nan za mu wuto babu wani tsaye-tsaye." Ya ƙare a tausashe duk dan ta fahimce
shi. Duk da yadda ya yi maganar tabbas ta ji ta yadda da abin da yake faɗa, sai dai ba ta san
dalilin da ya sa zuciyarta ta ƙi na'am da hakan ba. Sam hankalinta ya ƙi kwanciya, ji take kamar
ba za ta iya barin 'ya'yanta na tsawon sati guda cikin gidan nan bayan ba ta cikinsa ba. Sam ta
kasa gane dalilin hakan. Ga kuma faɗuwar gaban da ta ƙi barin ta har zuwa yanzun.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 09

Jin da ya yi ta yi shiru na fiye da tsawon minti ɗaya, ya sanya shi gyara tsayuwarsa ya ce a
tausashe

"Ki yi haƙuri, kar ki ce ban yi miki adalci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login